Showing 273001 words to 276000 words out of 388021 words

Chapter 92 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8294

Nace mama shin wai har mi da dami zaki na fada maki don Allah kada kuyi wani dawai niya mai yawa,
Mama tace ina wagga zance ai dashi mahaifinki ka kwana da shi yaka tashi,
Har adashe naji yasa akan zancen amma sai dai basu jittu ba da masu adashen don sun kai shi nesa kwara,
Tambaya nayi nace halan har nawana kwasa Mama, ?
Tace wai dubu saba,in na sun kasa kwasa shina yashiga ga kuma zancen tafiyan su ya taso shina yace in abin ya tabbata shi yaron ga sai ta kama fita da mota tai zuwa jigila don a samu kudin kashi,dana zubi,
Duk wanan lokacin da mama tafara bayanin ta hannuna yana a cikin jakata, a lokacin,
Na zaro sabbin yan dubu guda da dari biyar biyae na ajesu a gaban ta ina cewa tau Mama ni dai ke ga abinda anhannuna don haka sai a fara amfani da suwa,
Zancen kuma ace wai yaya Ibrahim ya dinga amfani da motar Baba ni dai ban yarda ba mama abar mashi motar shi idan ya dawo sai yaci gaba da amfani da abin shi,
Tace min mi zamu ci idan ya tafi halan yar baba
Ina gyara mike kafana nake cewa akwai Allah mama kuma shi wanda ya kai su ai bazai bar ku hakana ba,
Sai lokacin taga gudin dana zube a gabanta take cewa,cikin mamaki,
Ina kin ka samo wanga kudi masu yawa haka yar baba, cikin mamaki tare min wani irin kallon
Mama kudin da Yaya yake yawan bamune sune naita tarawa a guri na don wanan laluran,
Tace tau Allah shi kyauta Allah yai maku albarka yabaku diya masu rama maku alherin ku,
Kullun ina jin dadin irin kalaman Mama a gare mu don kalamanta suna sanyaya min zuciya ta akoda yaushe,
Mamana mutum ce wace bata shiga harkan kowa agidan mu hakan yasa su Mama Ladi ke ce masu wai masu zurfin ciki,
Don bazaka taba jin halin da take ciki ba sai dai kagan ta acikin rufin asirin Allah,
A nan Mama na take kara ja min kunne akan zance auren da Yaya Abubakar yakara a lokacin,
Mama tace min kada ki yarda da hadin kan kishiya domin kishiya duk sunan ta kishiya,
Ki yi al,amarin ki gwargwado da kowan su tsakani da Allah,
Tace balle yanzu idan Allah ya saukeki lafiya kin samu abokin hira idan ma mace ce abokiyar shawara kika samu,
Nai murmushi nace Mama Allah dai yasa macen ce wallahi,
Tace idan mace ce shikenan haka tsayuwar ki da rayuwar ki za su tsaya,
Amma idan namiji ne kika fara samu zaki kara tsawo kadan bisa ga yadda kike,
Sannan kuma wani irin hankali da natsuwa zasu ziyarci rayuwan ki sosai, sai dai idan mutum ba mai rabo bane daga Allah to ba zai daina aikin shirmay ba,
Daga gurin da nake zaune nace tau fa ashe haka zancen yake ke nan ,
Aiko ban taba sani ba ni wallahi tace yar Baba har yaushe kike da zaki san abubuwan rayuwa, haka,

****** ********* ******
Kwanan mu biyu a Birnin Kebbi mukai shirin komawa washegari,
Malam tsoho da na shiga gayarwa a sashen shi yake cewa, maman biyu ina ce ko kinzo haihuwan ne ai, nai murmushi nace ba, yanzu ba malam,
Sai naji yace min kaiyya Aminatu naso ace kin haihu anan kusa da mu wallahi,
Shiru nayi ina sauraren shi don irin yadda yai magana nasan cewa da wata ma,ana acikin ta sosai,
Wani murmushi naji ya sake, yana cewa to bari dai na dan saki a hanya don ki gane,
Ya ce haihuwar ki a hannun mu yana da babban amfani sosai bisa ga irin yadda rayuwar yau da kullum ta koma wa mutane,
Da farko kin sannirin rikici da faman da mukai tayi da mahaifiyar kishiyar ki,
Sai a lokacin gabana ya fadi don sam na manta da zancen wata wai Hajja,
Malam yace kinga kuma yadda uwar mijin ki take har yanzu ba wai hankali gare ta ba zata iya cewa idan a can kika haihu zata biku can ayii buki da ita,
Nandai ya dinga kawo min musalai masu amfani sosai yadda har jikina yai sanyi don da duk ban kawo su a kai ba, ni,
Zance Hajja tafi tsaya min arai amma sai kuma na yi amfani da kalman malam na karshe da yake cewa ai duk sherita batai Allah ba don Allah da ya baki ya na tare da ke,
Lafiya kalau zaki haihu insha Allahu, babu abinda zai faru dake har dan cikin naki,
Nabar wajen malam tare da yi mashi sallama jikina duk ba kwari akai,
Na samu mahaifina a part din mu nan muka zauna tare da shi muka dan taba hira dashi yana ta yi min nasiha akan rayuwar duniya,
Kafin mu dawo naiwa Yaya Abubakar magana akan ya samu abinda yabar wa su Baba wanda zasu barwa iyalin su a gida yace ba matsala a hakan zai duba yasan yadda akayi,
Tafiya saura sati uku zuwa hudu su tashi yanzu don haka a cikin shiri suke gaba dayan su,
Baba yai min nasiha akan inyi kokari indawo gida kafin haihuwana yazo inda nake ce mai ba matsala da na koma insha Allahu zan shirya indawo,
Mun iso sokoto misalin shabiyun rana tun a mota na sheda mai cewa zan dawo BK badadewa ba,
Saboda yadda Baba ya umurce ni dayi kenan kada na tsaya sokoto in haihu a gidan uncle dina,
Yake ce min idan na shirya zai ce Aliyu yazo ya daukeni,
Da sauri na ce mai a,a gaskiya bazan bishi ba don kada ma ya fara, wanan zancen ne ya bata mai rai,
Fada ya keyi cewa, shi mai nake son mayarda Aliyu ne don ya ga ina kokarin bata masu alakar su da Aliyun,
Bayin magana ba sai dai hade rai danayi nai shiru yana zuba min maganganu wai tsakanin shi da Aliyu ya wuce yarda nake tsanmani don haka na shiga hankalina,
Shiru,nayi har ya gaji da zancen shi ni dai bance uffan ba a lokacin don bazan iya bashi amsa ba,
Nadai sa a raina cewa Aliyu dai ne ban bi kamar yadda yake so, kafin mu isa yadan sake ranshi yana cewa, idan ya samu time zai dawo kafin su wuce zuwa saudiya,
Mun isa mu kayi sallama dashi na shiga gidan mu sai dai har lokacin rayuwana babu dadi,
Mun dan yi hiran rayuwa da anty na kwanta don na huta saboda jikina duk ban jin dadin shi a lokacin,

****** ********** ******
Ya Abubakar ya isa gidan shi a gajiye inda ya samu iyalin shi lafiya suna zuwa daya bayan daya suna mai sannu da zuwa,
Nan ya haye sama part din shi don ya dan watsa ma jikin shi, ruwa yayi alwala don yai sallah,
Ya dauki lokaci kafin ya fito yana saye da wandon tree quarter a jikin shi,
Sau yar riga mara hannuwa da yasaka tare da feshe jikin shi da kamshi mai dadin shaka,
A hankali ya kai zaune tare da, dan daukan remote ya kunna tv, don ya saurari, network, news,
Fatima ce tafara shigowa falon tana saye da dogon rigar atamfa a jikin ta wanda yai fitar mata da surar jikin ta da da kyau, ta samu guri ta zauna daga gefen shi
Bata kai minti biyu ba ko uku da shigowa sai ga Salawatu ta shigo ita kuma buje da rigar lace ke saye a jikin ta, ya matse ta tsab ta ko ina,
Nan suka zauna kowa tana gwada wa maigida nata irin bajin tar daga zaune a cikin tako,
Can sai ga Sadiya tafito ita ma jikin ta saye da dogon rigar jallabiya brown colour,
Ta zaune tare da yi mai ya gajitan hanya da ja,aman gida ya karba acikin dan lumshe idon shi,
Salawatu ce take cemai saboda son jin kwan, ka koga Meenatu,
Yana kokarin rage volume din tv yake ce mata na ganta mana ai muna tare don tare muka tafi BK da ita,
Gaba,dayan su yana cewa hakan sai da rayukan su ya dan sosu saboda, kishin da ya ziyarci zukatan su,
Anty Sadiya ce tai karfin halin cewa ayya yanzun kan ai ta yi nauyi da yawa,
Bai bata amsa ba kamar yadda tasan cewa ba lalai ne ta samu ansa daga gare shi ba,
Yana ta dan,ne dan,nen tashoshin a tv bai tankawa ko wacer su ba su ma ko,wace da irin abinda take sakawa a zuciyar ta,,
Fatima ba karamin dadi taji, ba da Abubakar ya kyale, Sadiya, akan zancen Meenatu da ta tambaya,
Sai da ya dauki kamar minti, biyar zuwa sama sanan ya dan juya gurin Sadiya,
Yace cikin furzar da dan iska mai zafi daga sama yace ai ina ga bata,da nisa,da haihuwa, kila,
Salawatu tace cikin dan tabe fuska da baki shi cikin har ya girma ne ake zancen haihuwar shi,,
Daga gurin da Fatima take zaune tana kallon fuskan Salawatu yadda ta tabe shi sai cewa tayi, a ranta ita wanan ke nan kowa kishin shin ta takeyi,
Sarai ya fahinci irin yanatin ko wacen su amma sai ya nuna tankar bai fahinci, may suke nufi ba a hakan da su keyi, din,
Bayan ko wace ta gama nata irin takon zuwa wani dan lokaci da guda, guda suka watse kowa ta kama gaban ta,
Yayin da maigidan ya mike a hankali zuwa nashi part din don ya huta,

****** ********** ******
Sati guda bayan dawowan mu muka shirya Anty Amarya da wata yar uwar ta su ka rakani gida acikin motan Uncle dina,
Malam tsoho wanda ya kasa boye, farin ciki sosai a lokacin da ya gane mu,
Sun,zo da abubuwan da duk Anty Amarya tasan cewa zan bukata, a zamana tun daga dangin kayan amfanin jiki da na ci da sha, duk anzo min da su,
A bakin Mama Ladi Yaya Abubakar ya samu labarin dawowa na gida haihuwa,
Inda ta bugo waya tana mai korafin cewa ya kashe min kudi haka masu yawa saboda kawai zan zo gida haihuwa zai kashe kudi irin haka. ?
Kuma ace idan na haihu sai ya kara sayen wani abin yakara kawo muna ai wan,nan ya zama kasuwanci ke nan,
Da mamaki Yaya Abubakar ke tambayan Mama Ladi cewa Meenatu ta dawo gidane, ?
Mama tace kana nufin cewa kai baka da labarin cewa, andawo da ita dazun da rana, da matan kawun ta,
Mamaki sosai ya Abubakar yayi a lokacin da yaji abinda Mama tace mai
Abinda ya fara zo mashi a rai shine, cewan da nayi ban yarda da Aliyu yazo ya dauke ni ba,
Watau abinda nake nufi kada in fada mashi ya turo min Aliyu shiyasa naki fada mai ke nan ko,
Cikin taushin murya yace Mama gaskiya ban da labarin zancen dawowan ta gida,
Wani irin nauyi da kunya ne ya kama Mama don ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????tayi fadan karya bata sani ba,
Mamaki takara yi don jin cewa bai, masan da zancen ba gashi kuma taga irin yawan abubuwan da nazo dashi gida,
Nan take fada ma Yaya cewa kada ya ko ce zai wahal da rayuwan shi gurin yi min wani da wainiya tunda dan uwan mahaifiyana yai min,
Yaya Abubakar yace haba Mama ai baza ai haka ba tunda tana da hakki a kaina,
Nan dai ya samu ya lalashi mama Ladi don dai, kawai ta kwantar da hankalinta kada ta sa wa kanta damuwa,
Saidai kuma a zuciyar shi fam yake da fushi akan may zan koma gida batare da ya sani ba,
Don haka sai kawai ya share ni batare da ya ce min uffan ba akan zancen,
Waya ma sai bai bugo min ba kamar yadda ya,saba yi min duk dare na mu kwana lafiya,
Da farko na dan sa damuwa don rashin jin kiran shi da baiyi min ba ga ranan,,
Amma daga baya sai na fitar da damuwan tun da nasan cewa a gida nake zaune yanzu
Sosai nake samun kulawa daga gurin mahaifiyata, da mahaifina wanda sai haba, haba su keyi dani,
A kasarin zaman nawa a part din malam tsoho na ke yin shi don in samu natsuwa saboda babu yara a part din da yawa,
wanan abin da nayi yasa matan malam tsoho sun ji dadin yin hakan a ransu sosai,
Mahaifina ya bawa mahaifiyata shawaran cewa na koma daya daga cikin dakin matan malam tsoho da zama gaba daya,
Hakan yasa ni komawa dakin mahaifigar Baba Wadda wace ita ce take yawan sake min fuska tun farko,,
A cikin dare Mama Sare taba kan,nena kayan amfanina suka kawo min part din yan tsofaffin
Kafin kayan su zo tana cewa na tashi na koma part din mu kada dare yayi sosai sai murmushi nayi kawai nace ai a tare zamu kwanta a saman gadon nan naki na karfe,
Dariya tayi tana cewa haba yar nan ina zaki iya kwana saman wanan karfen ai sai mu,
Sallaman yaran ne ya katse ta suna cewa ina zamu kai maki kayan Anty Meena,
Nace ku shiga dashi dakin Dije mamaki sosai ya kamata tana cewa yanzu dama da gaske a nan din zaki kwana,
Kai amma dai naji dadin hakan sosai wallahi ashe nice mai wanan masaukin bakin,
Allah ubangiji ya jissheki lafiya yasa yan kuda suna kwana a lokacin,
Kamar yadda na nace haka na haye dan gadon karfen dake cikin dakin Mama Dije, na kwanta barci,
Kafin barci ya dauke ni inajin Mama Dije da uwargidan ta tana sheda wa malam tsoho cewa ai ina nan part din su, anan zan zauna
Sai da ya kurkure bakin shi da ya cika da ruwa kafin ya ce au,to ku ce min ina da bakuwa a shiyan nawa ke nan,
Mama Dije wacce itace mahaifiyar Baba Wadda tace ai ina ga tayi barci
Don da alaman bata da nisa sosai don yau, tun da rana ina hankalce da ita
Saboda duk wani alama na haihuwa ba nisa ya baiyyana a gare ta,
Daga gurin da nake nai murmushi na, ce kai Mama Dije hoo,
Bayan asibiti sun auna ni sun ce da sauran lokaci zaki ce min hakan wai kin ga an kusa haihuwa,
Nidai tun ina jin su har barci ya zo ya kwasheni ban sake jin zancen su, ba kuma,

****** ********** ******
Tun da mutanen gidan mu su,ka fahinci cewa a part din malam tsoho na ke zaune ba part din iyayyen mu ba sai wani sabon gulma ya fara fitowa a cikin gidan, cewa
Mahaifana sunyi hakane don sun,ga cewa zan haihu basu aje komai da zasu min na fita kunya ba,
Zance iri iri suka dinga sakewa akaina badon komai ba sai don duk diyan gidan mu dake dawowa haihuwa babu wace aka taba kaiwa gurin matan malam din don zaman shan ruwan zafi,
Niko iyaygena suna da hadi da fulani sun san kunya sosai, don
A gare su tunda suna da magabata a gida bai, dace su zauna dani a cikin part din mu ba,

Mama Ladi tafi kowa daukan zafin zancen don da tasha zuga sai kawai ta hau yada magana tana cewa,
Ita fa bazata yarda a mayar mata da Dan, ta shanun tatsaba a dinga fakewa ana ci mai dukiya,
Malam tsoho shine ya jawa mahaina kunne akan cewa kada ya yarda ya kulla da zancen Mama tun da bata da tunane ita,
Kauna ta (Sister) dina, itace ta shigo part din malam da safe muka gyara komai nawa yadda ya kamata muyi,
Abin gwanin ban sha,awa idan ka gani da kaina na fito na,fara gyaran tsakar gidan malam din duk da su Mama Dije sun hana ni yi komai amma saida na gyara ko ina tsab,
Abincin da sukayi sai suke ganin cewa wai bazan iya ci ba sai gani su kayi kawai na ci tuwon masra da miyan busassan kubewa yaji kifi da man shanu,
Hakan ya kara sa,susakin zucitar dani suka kara sakani a jikin su,
Su ko mutanen sassan gidan muna sai shige da fice su keyi wai don kawai su kara tunzura Mama Ladi,
Ni ba mai yawan son hiraba bace ko hayaniya tun farko, don haka koda zasu shigo don ganin abin da na keyi sai su samay ni a cikin daki abina,,
Sai ku ma a koma ana gulman cewa ban aikin komai sai kwanciya kawai na ke,yi ban motsa jiki irin na masu ciki wai,
Matan malam tsoho sune masu mai da martani a cikin magana a dunkule,
Ni nawa dariya ne kawai don nasan cewa rashin na yine ya kawo hakan wa mutane,

Yau kwanana uku da zuwa Birnin Kebbi Yaya Abubakar bai bugo min waya ba kamar yadda ya saba,
Don haka, na kau da girman kai irin na muna matan hausawa a zuciyana nace bari ni na kira shi,
Sai dai wayan wai switch off, hakan yasa ni gane cewa yana, cikin meeting ko kuma busy a office a lokacin,
Don haka sai na kira Anty Amarya mu kadan gaisa da ita sama sama don wani irin abu da naji a can kasan marata tankar ansa min allura an tsikare ni,
Nai mata


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login