Showing 369001 words to 372000 words out of 388021 words

Chapter 124 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8262

10:29 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
1? 0? 6?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH AN NUR


Kamar kullum idan ya shigo haka muka samu kulawa daga maigidan kamar yadda ya saba idan yana a gari,
Har yai muna kwanakin da ya Saba yi muna idan yazo garin,
Da zai tafi yai muna irin sallaman da ya saba muna idan zai koma gurin aikin shi,
Ya koma muna cike da kewan shi damu da yara dama duk wani wanda ke gidan a lokacin,
Munci gaba da harkokin mu, kamar yadda muka,sabayi yau da kullun,
Abinda na fara lura dashi shine irin yadda aka kwana banji kira daga Yayana ba,
Har a,na batun kara kwana banji ya kirani ba kamar yadda ya,saba kiran mu da safe da rana idan ya fito sallah azahar da kuma dare kafin mu kwanta,
Nice na kawar da halin mu na matan hausawa naga ya kamata na kira shi don muji lafiyan shi,
Amma sai na samu layin shi a busy yake don haka,sai nafan dakance shi har ya kare wanacan called din,
Don nasan idan yaga nice zai yi calling back don muyi magana,
Amma sai naji sabanin hakan don har nafara jin barci na dan daure na kira layin nashi,
Irin yanayin da ya karba min ya sa jikina yin sanyi inda niko kamar yadda na saba nake cewa Yayyana acikin wani irin murya da nasan yana bukatan nakira shi,
Ina cewa a cikin shagwaba bakaga kirana bane da kagama waya,
Ya amsa a wani irin murya yana cewa nagani mana yaya akayine, ?
A rin yanayin da yai magana sai naji banji dadi ba amma sai na daure nace Yaya,love munyi missing dinka ne tun jiya aiki ya rike muna kai,
Tsuki naji yayi a cikin fada yake cewa idan babu wani dalili kwakwara bana son kira hakana please,
Don banda enough time din yin shirmay yanzu please take note,
A sanyaye a cikin kunya na amsa mai da cewa tau Yayyana insha Allahu,,,,
Wani irin dummm ne ya ziyarci zuciyana don ban taba jin yanayinshi a haka ba koda fada yake min kuwa,
Amna sai na anyana a zuciya wata kila akwai abinda ya bata mai rai ne a lokacin shine na hadu da fushin,

****** ********** ******
Na shiga cikin tashin hankali don yau kusan sati babu kiran Yaya Abubakar gashi kuma yai warning dina na daina kiran shi any how idan har ba reason,
Ina gani kamar ni kadai ce a cikin matsala sai daga baya na fahinci har da Sadiya da Fatima,
A gurin Salawatu ne kawai muke dan jin labarin shi koshi ba wai ta fada muna ba sai dai muji tana waya ko zance tace ai yai tafiya ko kuna tace ai anyi kaza a can garin da yake aiki,,,,,
Wanan abin yai matukar tayar muna da hankali a gidan amma ni saboda ina tare da Ramatu da kuma mai rainon yarana sai damuwan ya dan rage min, ba kamar Sadiya da Fatima ba,
Yau dai nace barin sauke girman kai na kira layin nashi,
Ai har kiran ya katse bai daga ba nasake kiran shi again gab da wayan zai tsinke ne yadaga yana cewa,
For Allah sake Aminatu baki barina wai na hutane da wanan bakin kiran da kike min ne wai, ?
Idan ba so kike ki tarwatsa min zuciya ba don Allah ki barni na huta please,
A take naji zuciyana tankar zai fashe don tsoro da fargaban abinda kunnuwana suka jiyo min daga bakin Yaya Abubakar yau,
A cikin kuka nace Innalillahi wa,ina alaihin raji,un,
Nace a cikin kidimay wa Yaya Abubakar may ne maka ne wai don darajan Allah ka fada min, ?
Yace shout,up my friend na fada maki ban son yawan damuwa wallahi,
A hankali na maimai ta ina cewa acikin wata yar siriyan murya,
Yaya nice kuma mai sakar ma da damuwa yau, ?
Don Allah idan wani abin nai maka kayafe min don ban san may nayi ma har yai zafi haka ba,
Idan baki da na fadi zan kashe wayana don aiki nake, daga hakan ya ko k?she wayan dip,
A tsaye ya barni cike da mamaki zuciyana a lokacin jinta nake kamar zata fashe, kirjina tafito don tsabar bugawan da takeyi,
Dafani naji anyi daga bayana ashe Baba Ramatuce tace cikin dan fuska mai nuna yanayi samu guri ki zauna sai muyi magana,
Daya daga cikin kujerun falona na zauna a kai, yayin da ta miko min Amira wace ke bukatan shan nono,
Na karbi yarinyar duk a lokacin ban a cikin yanati duk a rikice nake hankalina a tashe,
Saida taga na gyara na fara bawa yarinya nono duk tana tsaye a kaina take cewa,
Uwar dakina duk mace mai aure idan tana da keep shiya takan fuskanci itin wanan yanayin ,
Yau dadi gobe hakkuri don haka idan ma har shiga tsakani ne akayi to ki daure ki nuna a fili komai ba komai bane,
Saboda na fahinci ba ke kadai ke cikin irin wanan halin dashi ba harda Fatima da uwargidan ku,
Saboda naji ita Fatima tana waya a gidan su tana fadan cewa tana cikin wani hali don gaba daya mai gidan ya fita zancen ta
Asmau na ce ta shigo ganin irin halin da nake a ciki ya sata tambaya a cikin rudewa
May yafaru ANTYNA ?
May yasamay ta Baba Ramatu, ?
Ko yarinyar ce bata da lafiya duk a rude take jefo wanan tambayan a lokaci guda,
Ganin yar uwata ta rude kuma nasan halin irin na Asmau kamar fetur take wuri ci na dan kirkiro yar murmushi a fuskana,
Amma duk da haka bata yarda ba sai ma kara matsowa gab dani da tayi don ta ji ko may ke faruwa,
Nace a cikin yanayin bacin rai, Asmau ba komai bane kawai dai al,amarin Yaya Abubakar ne wallahi,
Nan na kwashe yadda mukayi nake fada masu inda kafin na karasa mai reno, Anty reno tashigo, dakin,
A tare suke cewa wanan shiga tsakani ne wallahi mutumin da yazo aka rabu lafiya dashi,
Tace naji uwargidan ku tana cewa har yanzu ace bai zoba bayan har lokacin zuwan shi garin ya wuce tun sati biyu da ya,shige,
Amma sai dayan kishiyan naku ke cewa wai ai baya kasan yai tafiya ya tafi kasan China aiki,
Da sauri nadago kai ina mata kallon mamaki nace a cikin mamaki baya ma kasan ke nan tace eh amma, wai a jiya da naji suna magana zai shigo Nigeria din,
Innalillahi na fara maimaitawa don samu sauku a zuciyata saboda wani irin zafi duk jikina ya dauka,
Anty Wallahi kada ki sa zancen shi a ranki ya halakaki ga banza don ke ga ko kin mutu shi baida hasara tunda ba ke kadai bace gare shi,
Iyayyen ki da dinyanki damu yan uwanki mukai hasara,
Gaba dayan su sukace wa Asamau wanan gaskiya ne to amma akwai damuwa a irin haka,
Don babu dadi ba fada kayi da mutum ba amma ya canza maka yanayi a lokaci guda, haba dai hakan baiyi ba wallahi,
Ramatu tace cikin gyara zaman ta a kusa dani ni abinda nake so Uwar dakina shine ki kwantar da hankalin ki kada sauran su fahinci cewa kina cikin rudani don Allah,
Ki dake ki daure kibar wa Allah al,amari sai kiyi takai kukanki ga Allah ai Allah ba azzalumin kowa bane,
Insha Allahu in har shiga tsakani ne abin ba zaiyi wani tasiri ba in har kina kai kukanki ga Allah,
Abinda duk mai kishiya dole sai taga hakan sai dai ta wata tafi ta watane,
Kawai dai kema yanzu dolene ki tashi tsaye a gurin neman tsari da kuma bawa yaran ki su ma don har da yaran ana iya fitar mai dasu a rai,
Asamau tace wallahi da yaji kunya kuwa yaranshi yayi banza da su?
Antyn raino tace kai Asmau ina ruwan asiri da yaran shi ko uwar shi ba sai arabata da shi ba,
Asamau tace don Allah Anty share shi kawai, ki kama harkokin ki indon wanan tsohuwar matar tashice ai jin su za,ayi,
A wanan ranan nasan advantage din zama da mutane kirki a duniya dakuma zama a kusa da mutane da mu,amula acikin mutane,
Ashe yana ragewa mutum tension sosai don daga zancen da kowan su keyi nake ta picking din solution akaina,
Ashe shiyasa ma,aikata maya kamar malaman asibiti da malaman makaranta masu cudanya a cikin mutane basu yawan shiga matsala saboda suna sharing din a ideas a tsakanin su ,
Don haka sai nayi kamar yadda sukace min na gyagije tankar babu wani abin dake damun rayuwata a lokacin,

****** ********** ******
Kwana biyu a tsakani ina nan a cikin damuwa amma a boye, babu irin tunanen da banyi ba a lokacin ba
Amma sai na ke kai kukana agurin Allah don samun mafita akai,
Baba Wadda ya shigo rai a bace ina zaune da Fattu muna duban wasu turaren wuta da Mama biu tazo dashi daga Maiduguri, ta sayo muna tace mu bata dan kudi kalilan akai,
Na gaida shi cikin girmamawa kamar kullun a matsayin shina kanin mahaifina
Yana daga tsaye batan Fattu ta gaida shi yake cewa Meenatu shin may ke faruwane gidan nan wai, ?
Naga yanzu ko keys din mota sai mai sunan malam yace wai muba wanan doguwar mai kama da waya ko wani abu muke so yanzu gurin ta muke zuwa,
Murmushi na dan kakaro a fuskana nace hai Baba ai kasan tun can itace mai yawan kula da kayan yace cikin sauri ba gaskiya bane,
Don ai shi da kan shi yake cewa muyi hakali da ita don kada ta sayar mai da kaya ko ta bata,
Nai murmushi nace Baba da ne can baya yanzu ya fahince ta ai komai ya wuce,
Sai naga ya kai zaune a cikin takaici yace wai ko kin san cewa gobe zata tafi can inda yake aikin,
Kafin in magana Fattu tace cikin wani irin waigowa tana fuskantar Baba Wadda tace Pothercourt din zata tafi ko may wai, ?
Sai da ya hade yawu bakin ciki yake cewa can din mana wai shi bai ko jin kunya ace matar shi ce Salawa,
Nace wani irin kunya kuma Baba mutum da matar shi ta dace taje ne shi yasa ya tafi da ita,
Sai dai abinda basu sani ba a lokacin wani irin naji numfashina ya kusa daukewa wani azababben kishi ke, taso min ina jin kamar numfashina zai tsaya,
Da kyat na iya matse hawayen dake, shirin kwaranyo min a zuciya ta, a lokacin,,
Ga gabana dake bada wani sauti dam a lokaci lokaci na shiga cewa cewa a raina lalai tabas Salawtuce umul,aba,isin jefa rayuwan mu a haka ,
Sai kuma nai saurin yin istigifar don zato zunubi ne koda ya zama gaskiya,
Wata kilama ba ita bace, wani dan akasine aka samu can daban,
Haka na daure har dare wanan daren haka nagan shi idona tangaran babu irin tunanen da banyi ba akai,
Da naga abin zai iya yi min illa sai na mike na fada bathroom na dauro alwala nafara salloli ina kai kukana ga ubangiji hawaye yana shatata daga idanuwana ,
Ina zaune a haka ina tsabhi har akafara kiran sallah Allah ya taimakeni babu yaron daya farka daga barci a ranan,
Daga nan namike nagara dauro alwala nazo na tayar da sallah ina ma kara mika kukana ga Allah ubangiji subbahanahu wata ala,
Ranan don kada naga takaice kwanciyana nayi daki ban fito ba don kar naga tafiyan ta,
Yadda tafiyan nata ya gudana shine,
Bayan an fita mata da kayan tafiyan ta ne tafito tana saye acikin wani dogon riga marun colour ta saka wani dan karamin gyale a wuyan ta acikin sauri tafito don gudun makara,
Ganin Fatima a falo take cewa to ni zan tafi ina sauran mutanen gidan, ne ?
Ina zaki tafi Fatima take tambayan ta acikin son sanin ida zata tafi,
Tace gurin Oga a takaice ,
Bata tsaya jin may zatace ba ta nufi gurin Sadiya daga can ta fito zuwa dakina,
Ina zaune ina waya da Anty Amarya tashana wani rawan kai,
Ina ganin ta naji raina ya wani dan baci amma a fili sai nake murmushi na gaisa da ita acikin fara,a
Ta dan kureni da ido tana cewa zata tafi nace ina fa sai take cewa gurin yayanki yau zan tafi,,,
Tana mai kureni da Idanuwan ta don taga irin reaction din da zan nuna don jin inda zata tafi,
Cikin fara da yar dariya nace kice yau Yayana yana da babban bakuwa ashe ?
Muna gaisheshi da aiki aiki ya rike muna shi kwana biyu Allah dai ya tsare Allah yakai lafiya adawo lafiya,
Nace cikin fara,a har ina cewa bari muzo rakiya mu ga tashin ku,
Tace cikin wani yanayi aida kun bari kawai don airport zamu tafi da jirgi zan tafi,
Nace ai yafi sauki don tafiyan mota akwai nisa sosai wallahi,
Ta amsa a dan getsire azuciyan ta tana zagina wanan shegiyar yarinyar ita bata damu ba da tafiyana take nufi komay wai ?
Muna tsatsaye muna daga mata hannu Lawal mijin Fattu yaja mota da ita suka wuce zuwa airport,
Suna bacewa na sauke wani irin ajiywn zuciya duk da dai nasan cewa ni a lokacin ai ba girki na karba ba,
To amma ai ya kamata na samu kulawa daga maigidan na mu, bawai sai ina duty ba kamar kowa,
Muna shiga daga ciki, na samu Fatima a haukace tana ta fitina, duk da nima ina jin zafin kishi a lokacin amma sai da tabani tausayi abinda naji tana fada tana cewa,
Wanan wani irin rashin adalci ne ace mutum mai mata hudu ya mayar da hankalin shi a gurin guda gaba daya duk ya canza a gidan nan,
Wallahi ita bazata yarda ba tunda mace ba finta kama tayi ba ba,a fita da komai ba har za a dinga mata wulakanci, akan mace yar uwar ta,
Murmushi nayi ina cewa Maman Aina maynene duniya wai,?
Idan ki kayi hakkuri watarana kema dake za,a tafi, insha Allahu,
Sai a lokacin ta dan sasauta murya tana cewa, haba Meenatu wanan abin da mutumin nan ke yi gaskiyane,
Kwanaki fa can idan kin tuna tare suka tafi kasan waje da ita yanzu kuma ace wai itace zata samay shi a garin da yake,
Mu ana nufin ba mata bane ko may ko itace tafimu waye ne wai,?
Nai yar dariya nace ba hakana bane kawai dai kila akwai dalilin da yasa yace tazo din,
Sadiya da take daga bayana tsaye tace, wanan ba gaskiya bane kawai dai akwai wani abune wallahi,
Don wanan munafukan matar da kike gani muguwace har ta karshe wallahi ni ina zargin da akwai wani mugun abin da take kullawa agidan nan ,
Wanda ba kowane, yasan tanayi ba amma ni kinga ina zargin koma may ye wallahi da Lami ake kulla shi,
Mukace Lami kuma ?
Tace eh Lami fa don itace ta kai mu gurin wani mai magani wai na samun haihuwa shine ita muguwar naga ta mayar da gurin wurin zuwan ta akoda yaushe,
Nace Allah ya fita duk wani Sherri da zata kulla akan ta zai koma in har bamu da alhakinta a kan mu, ,
Nan hira ya kaure a tsakanin mu kowa tana fadin irin mugun abinda ya sani akan salawatu,
Sam ban yarda na fadi komai ba akai don nasan cewa sunfi kusa kada nace tak nawa ya fita nasu ya boye,
Don haka nace Uhmmm, kawai ku kyale ta idan badon Allah bane tafiyan ai Allah na ganin ta,
Daga haka na juya nabar falon zuwa part dina kamar babu abinda ya damay ni a zuciyana,
Zuciyata jinta nake kamar zata fashe min don dunkule min da naji tana cushe min, guri guda,
Rana gidan namu zakace ba kowa acikin sa sabda tsit din da gidan yayi,
Kowacen mu tana dakin ta zuciya babu dadi ko kadan sai kishi dake cin mu, daga karshe nabarwa Allah komai na ci gaba da harkoki na kamar kullun ina hira da yan dararakuna kamar yaddana saba bisa umurnin Anty Amarya,
Hakan yasa aka zaci cewa ban damu da tafiyan Salawatu gurin maigida ba,
****** ********** ******
Isan Salawatu gurin shi komai ya canza, don rayuwan shi gaba daya duk ya canza
Ya manta da wasu matan shi can a gida sai yake ji kamar salawatu ce kawai matar shi a duniya,
Baya ganin kowa a idon shi sai Salawatu wanda hakan ne ma yasaka shi matsa mata da cewa sai ta biyo shi nan garin Porthercort, da yake,
Duk da zuwan ta ya dan saukan mai da nauyin da yake ji a kan ta, hakan yasa a fannin Salawatu,
Take shan jiki a gurin shi domin Abubakar ba karamin jarumi bane,
Amma duk da haka Salawatu, ta daure tana daukan dawainiyar shi, tana yawan jure bukatan shi, koda ace bata da bukatan shi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login