Showing 69001 words to 72000 words out of 388021 words

Chapter 24 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8246

masu kuka wi ,wi, wi,


ZEEE MAKAWA YALWA
[7/20, 9:53 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
2? 9?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH-AL-FATTAAH


Har muka kai Sokoto, idona da yana zubar da hawaye,
Don sai nake ganin tankar dai, na,rabu da mahaifana ke nan,
Amma da sannu anty tana ta yi min nasiha da kuna fada inda ya dace sai naji zuciya na yadan rage, radadi, ban san lokacin da na sake jiki na ba,nafara harkoki na, kamar yadda na saba,
Yau Monday, ce ko Bature yana tsoron ta, tun safe da na fita ban da wo ba sai biyar saura,
Don haka agajiye na shigo gidan, mummy ce a falo tana gyara, sai kuma kamshin girkin da naji tana yi,
Na gaida mummy yayin da nai mata sannu da gida,
Itama dai din sannu da dawowa tai min tare da cewa amma yau kun dan jima ko?
Ina kokarin kwabe hijab dina na ne nake ce mata mummy kin san yau Monday ne shiyasa, muna da full lectures,
Kokarin karban kyalen da take goge goge nakeyi amma sai Mummy take cewa,
Je ki ci abinci mana yanzun nan fa kika shigo gidan shine har zaki hau aiki,
Karban kyalen nayi daga hannun, ta, ina cewa yau Monday Mummy ina azumi ne ai
Hakane fa akwai ki dai da kokarin wanan azumi, murmushi nayi don jin abin da tace,
Tana kokarin gyara kyallayen kujeru ne take cewa kardai ki je gidan mijin ki, ki ce zaki dinga daukan azumi kamar yadda kikeyi a nan gida,
Inda taci gaba da cewa Meena kina da hakkuri sai dai kuma kikara wani a saman wanda kike dashi,
Don zaman aure dan hakkuri ne balle irin auren ki na hadi, sai kin kai zuciyar ki ni,sa sosai, gaskiya,
Don zaki fuskanci kalubali da yawa da farko amma idan kin daure, sai komai ya wuce,
Tun da Mummy ta fara magana na dan rage aikin da na keyi don in saurare ta,
Nasiha sosai Mummy tai mun a lokacin don har sai da nai mamakin ta, kwarai don ban taba zaton haka daga gare ta ba,
A hankali na dan dago ido na da suka kawo ruwa ko jira suke su tsiyaye,
Naso tun tuni dama in samu time in maki wanan nasihan
Ki zama mai dauriya akan duk yanayin da kika tsunci kan ki a ciki,
Muryan yara da suka fita da Anty anguwa ne suke ihun dawo wa,
Kayane acikin ledoji da gani daga gurin shopping take,
Mummy wace ke min nasiha sai naga ta kama gaban ta bata kara ce min komai ba,
Azuciya na nace o,o zaman mummy da anty sai Allah,
Zamane irin da kowa yasan matan hausa nayin shi na kiyi nan inyi nan,
Zamane na sakewa juna, hausa ta yadda dan uwa zai shiga damuwa
Koda bako dan uwa yayi ba lalaine wanda ke gida alokacin ya tari bakon ba,
Zamane na yan uwan junan su suma ahaka suke koda an hadu da wanda duk ke hurda da kai ba dole bane ku gaisa,
Sai dai ni tun farko ban yarda da wanan a,kidar na su ba, don duk da akidar ba bakuwa bace agurin saboda nima ai al,adar mutanen mu ne na kyabi,
Kayan da yaran ke ja saboda sun rinjaye su dauka nakama masu da sauri zuwa sashen mu,
Anty daga bayan mu take cewa ai da kibari su karasa dashi cikki raggaye kawai,
Saman dogon kujerar dake dakin ta fada tana cewa, waini Allah Walleh duk nagaji yau,
Ruwa na dauko mata da cup a fridge din ta na daki,
Ce mun take, badai yanzu ke ma kika dawo ba ko ?
Anty kin san yau Monday ai mukan dade a can
Sai kuma ta tabe baki tana ce min, ita wanan ko gyaran falon bata gama ba har yanzu,
Murmushi nayi nake cewa ai, nice na karba don na karasa mata,
Kai don Allah bari ragguwa ce kawai bata son motsa jiki ta dama,
Murmushi nayi azuciya na nace badai kishi ba Anty,
Bayan mu idar da sallolin dare ne take ce min ,
Meenatu jawo ledojin nan da na shigo dasu dazun mu gani,
Daya bayan daya take fitar da kayan daga cikin leda,
Wasu dinkakku ne wasu kuma English wear ne masu masifar kyau da daukan ido,
Gaba na ta turo min kayan gaba daya tana cewa kudin da Malam tsoho ya bani sune Uncle din ki yace ai maki wanan sayayyan kamar yadda tsohon ya ce ayi,
Sai ki gwada din,kunan mugani wanda bai yi daidai, ba sai amayar ko,
Wani iri na ji na dago, kai ina son ince wani abu amma bazan iya fada ba,
Anty Amarya tace kada ki yarda ki zauna a kazance ko yaushe,
Kin ga su wayan nan dinkunan sai da rana zaki dinga amfani dasu, agida,
Amma su English wear sai dare yayi idan maigidan ku yana gida zaki dinga sakawa,
Ai basai na fada maki ba don a gaban ki akai fadan don Uncle din ki ya yaba kwalliya na,
Dariya maganan ta ya bani don nasan yadda take zama ta bata lokaci gurin gyaran jiki kafin uncle ya dawo gida da marance, (yamma)
Kamar yadda ta umurce ni da in gwada kayan haka na fara gwada su daya bayan daya sai faman koda ni anty keyi tana kara gyara min da kuma koya min yadda ya kamata in sa kayan , koda yaushe,
Kai kawai nake gyada mata bawai don na gam su ba
Sai naji ta nacewa ai ko ita wanan cingun din da ta leke mashi ire,iren su nasan take amfani dasu har ya kasa rabuwa da ita,
Azato na Anty Sadiya Anty Amarya ke magana sai kuma naji tace ai,kin san matan Abuja an iska ne idan sun lakewa namiji baida hanyar escaping,
Ga yadda naji yaya tana fadi ai duk ta girmay ku daga ku har mijin naku,
Wani irin kara naji cikina yayi don tsoro kulukulu, sai naji daga tsayen da nake ina sauraron ta ina son in dafa wani abu kar in fadi,
Mirror din Anty dake kusa dani na dan dafa ita ko sai maganar ta takeyi batare da ta kula da halin da nake ciki ba tana cewa,
Karki yarda daya daga cikin su tafi ki da komai Meenatu a gurin miji,
Kema sai kin koma mashi karuwan gida kamar yadda sukeyi a waje,
Hakan zai sa ki samu karbuwa sosai a zuciyar mijin ku,
Duk kayayyakin dana hada maki Meena ki tabbatar da don Allah kina amfani dasu,
Bawai ance amfani dasu baida kyau bane tunda har ki kaji malamai sun san da cewa ana gyara da shi ai kenan, amfani da,shi ba illa ba,ne,
Kuma ko wani irin kabila na duniya sun san mace tana bukatar gyara, akoda yaushe,
Sai dai kawai ki kula da abinda ki ke yi din, karki yarda ki,bada karfi ga cushe,cushe don Allah saboda shi yana da illa babba ga mata,,
X Ki dai yi amfani da na sha din nan kawai wallahi masu kyau ne don har wani kauye hajiya tasa asamo mata abin hadin su,
Kai na kada don ansa mata maganan ta, tace wallahi, Menna sai kin yi hakkuri don zama da kishiya iyawa ne,
Acikin wardrobe din ta na taya zuba kayan done ? mugyara gurin tana cewa sai uncle di na ya,dawo daga gurin aiki a nuna mashi, tare da bayanin komai,

Ina shiga dakin mu na fada sama gado ina mai fadar Innalillahi, wa,inna,alaihim rajji,un,
Abinda kawai bakina ke iya fada ke nan saman dakin mu nake kallo amma sai gani najeyi tankar silin din na juya min a idons,
Wani kuma sabon masifa ne wanan ke shirin faruwa da ni,
O Allah yanzu ni kuma irin rayuwar da zan tsinci kaina ke nan,
A cikin kishiyoyi, kuma kishiyoyin duk sun mugun girmay min,
Allah ka tausaya mani kai min jagora ga al,amura na,
Daga haka barci ya dauke ni ban san ina nake ba sai dai ire,iren mafarkin da na ke yawan yi kwanakin nan mara dadi,
Kiraye kirayen Sallah da a,keyi na Asuba ya farkar dani daga juye juyen da nake yi a cikin barci na,
Ban kara komawa barci ba namike nadauro alwala,nafara nafila kafin a,tada sallah asuba,
Sai da muka gama duk wani abinda zamu yi kafin in, tafi school,
A mota Uncle dina ke ce min Antyn,ki ta nuna min kayan da ta sayo maki jiya kayan su yau kyau sosai,
Don dai bawai iyakar kudin da na bata bane ta saya da su,
Don Allah Amina, ki je kiyi ta hakuri kodon mahaifan ki ,
Ki daure ma duk wani abinda zaki gani a sabon rayuwar da zaki shiga
Mijin ki matashi ne mai ji da lokaci ga Ilimi ga Naira, ga Kyau, ga Asali,
Don haka ki daurewa, ki hadiye kinji Amina Allah yana tare da ke ,
To Uncle kawai na iya cewa don nasan idan na kara kuka zan mai a mota,,

****** ********* ******
Kuka take yi mai, wi,wi, acikin mota harda shesheka,
Yabi duk ya susucd ya rude ya rasa abinda ke mashi dadi a rai,
Gashi bazai iya bude baki ya yi rarashin ta, ba don yana ganin haka kamar zubar da mutunci sa ne, gare ta,
Dakarfi ya nashi sitiyarin motar shi da yake ja,
Cikin tsawa da wani irin murya ya ce,
Will you stop that my friend ?
What, the he'll is this ?
Tsoro taji ganin yadda yakoma mata tankar zaki a lokaci guda,
Iam trying to find a solution,
Kuma zaki isheni da kuka a mota,
So ki ke in bar maganar mahaifana,?
Ya girgiza kan shi yana fadin ,
"Nerve,
Komai zanyi sai da yaddan iyayye na don sune silan zamana haka,
Kallon shi Salawatu ke yi acikin mamaki
Shi Abubakar wai wani irin mutum ne wanda mace sam bata agaban shi ne,
Yau duk irin shirin da tayi ya tashi a banza ke nan ko ?
Yanzu idan tace zata biye mashi su bata shikenan fa zasu rabu,
Aiko da taji kun ya yadda mutane suka sa ido su gani in zai aure ta a haka?
Don suna ganin kamar wai tai mashi tsufa ita dai tasan cewa ya girmay ta, sosai fadin mutane ne kawai,, ke ganin hakan,
Cikin marairaice murya tace, dear dole ne inyi kuka saboda inaganin kamar parents naka bazasu bari muyi auren nan ba,
A, dan hasale alamar ya fara saukowa yace mata waya , fada maki haka,?
Kawai dai na basu time ne har tsoho ya sauko sai mu sasan ta,
Tissue ya miko mata daga gefen shi alamar ta share fuskan ta da shi,
Kalamin dayayi yasa ta dan jin sanyi a rayuwan ta sai daga haka daga shi har ita ba wanda ya kara magana har ya kai ta yai dropping din ta,
Gudu yake shararawa saman titin da zuwa yanzu yafara yin duhu don dare,
Wayan shi ce yake jin tana kara alokacin don haka ya mika hannu a hankali,
Ya dauko sunan Malam tsoho ne barobaro mamakine sosai ya kama shi don jin kiran tsoho a wanan lokacin da bai tsanmani hakan ba,
Salamu Alaikum ya ce a yayin da yake kokarin kara wayan a kunen shi,
Lumshe ido yayi a yayin da yaji muryan tsohon yana karba mai sallaman shi,
Gaiawa sukayi sai dai yau duk kan su ba wanda ya sake jikin shi da dan uwa kamar irin yadda sukan saba yi
Dan shiru jimmm,
Malam tsoho ya katse shirun da cewa,
Dama nakirakane in fada maka cewa
Ranan jumma,a idan Allah ya kaimu za,a kawo ma matar ka,
Kamar yadda nai alkawari,
Wani irin mamaki ne ya kama shi,
Wai malam wani irin mutum ne da zai yi mulki da diyan shi yayi da jikoki kuma, ?
Shirun da malam din yadan ji yayi ne batare da ya ce komai ba sa shi cewa kana jina kuwa, Abubakar ?
Eh malam ina jinka yace acikin sanyin murya,
Amma dama ai naso ne sai na shirya tukun sanan akawo ta ko ?
Abubakar ka fita ga ido na kaji ko wani irin shiri, zakayi wanda tunda ka dawo bakayi shi ba,
Mamakin wanan kakan nashi mai karfin zuciya irin mazan jiyane ya kamashi,
Sai kuma maganar da tsohon yayi daga karshe cewa zan turo ta
Idan sun kawo ta sai ka hado su da takardan ta su dawo mn da ita,
Daga haka ya kashe wayan batare da ya tsaya jin may Abubakar zaice ba,
Shiko Abubakar bin wayar shi yayi dakallon mamaki tankar malam din ne yake kallon,
Allah ya taimaka ya kawo site din su da kila ba,zai iya karasowa da kan shi ba,
Wanan tsohon ya hada shi da sabuwan fitina ya kwaso wata bakauyar yakara jibga masa again,
Yaya zai yi yanzu shi ahaka zai buge da zama da kauyawan mata, agida ,,,

****** ******** ******
A ranan da na gama exam da wuri nadawo gida, sai dai na samu anty amarya da wata mata mai zubin yan Sudan a babban falon gidan mu tana wa anty kumshi a hannu,
Ba bata lokaci anty tasa in maza in canza kaya inzo ai mun naso nace tabarshi kawai amma yadda tai min magana fuskan ta babu alamar wasa yasani saurin shigewa ciki don in canza,
Abin da yabani mamaki irin kumshi da kitson da matan tai min da kuma su gyaran jiki,
Batai wani dadewa ba don iyawan da tayi, gwanace sosai matar,
Saboda gajiyan da nayi yasa ni yin saurin kwantawa barci a ranan,
Sai dai kuma barcin baiyi wani nisa ba sosai na dinga jin hayaniya sama sama,
Naso komawa barcin amma kuma nagaji idona nakara lumshewa,
Sai dai muryoyin da nake ji daga cikin barcin sune suka sani saurin bude idona don gaskan ta abin da nake ji din,
Ai ban san lokacin da na zabura ba don ganin wa yan dake zaune ata kawo masu abin sha da na ci,
Sunan su na kira da cewa, gwago Habbi, da mama Sa,a sai Anty Rukaiyya diyar baba Shaibu babba da yar diyar ta,?
Murmushi sukayi don ganin na tashi, daga barcin a lokaci guda,
Gwago Habbi ce ke cewa yar tawace ta koma haka shin?
Ai inbadon sani ba bazan gane ki ba gaskiya, kinyi wani iri kyau kamar ba Amina ba,
Anty Rukaiyya tace gaskiya ko ni ban gane taba da farko wallahi,
Anty Amarys ce tashigo dakin dauke da cups da drinks tana cewa kuyi hakkuri bamu san cewa yau din zaku taso ba ai,,
Barcin da ban samu komawa ba ke nan ranan don mikewa nayi nima muka shiga hira da yan uwana,
Sai wani lokaci muka dan samu muka runtsa baimuyi wani dadewa ba gari yawaye,
Nai mamaki kwarai ganin wai ashe Anty amarya har ta gama hadawa bakin mi abin kari tun kafin shidda,
A dakin ta ce in yi wanka aranan, sai bayan nafito ina shafa mai ne tashigo dakin gurin danake ta zaune tare da aje min wasu sabbin kaya
Shaddane gezzinah masu ruwan makuba zaren da akai masu dinki dashi, fari mai ruwan silver,
Meena naji anty ta kira sunana abinda yasani dan dago kaina na
Yau zamu tafi Abuja mu kai ki gidan mijin ki insha Allah,
Don Allah ki natsu sosai ban son ki bar abin fadi don kin ga ga yan gidan ku atare damu,,


ZEEE MAKAWA YELWA
[7/21, 4:05 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
3? 0?

ZAINAB IDRIS MAKAWA


ALLAH-AL-A'LEEM


A Motar Uncle Nafi,u mu kai tafiyan inda shi Uncle da kan shi ya jamu zuwa Abujan,
Tafiyan ya kasance mu shidda da farko wai motan bazata kwashe mu ba, don haka
Sai dai Anty Amarya ta zauna yan uwa na da,suka zo daga gida mutafi da su,
Kuka na,sawa Uncle mai tsuma rai, don haka dole muka matse gaba dayan mu hudu a baya,
Tafiyan bai wani dauki tsawon lokaci ba irin zuwan muna farko da yan uwana, daga Birnin Kebbi,
Saboda yau mun iso kafin a,shiga massalaci,salkah jumma, a wani gari gab da zamu shiga Abuja Uncle ya tsaya yai sallah Jumma,a
Motar tai tsit baka jin komai sai sanyin A,C din motar dake ta aiki, muko sai faman raraba ido mukeyi muna kallon abubuwan mamaki ta ko ina,
Gwago Habbi Da Mama Sa,a sukace su,yan garin, don jindadi har da TV suke sawa a saman titi, kowa ya kalla,
Anty ce tace masu ba TV bane talkah akeyi a na abubuwa, amfani,
Mama Sa,a tace a hakan ?
Kwarai kuwa inji Anty Amarya,
Uncle ya daga wayar shi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login