Showing 153001 words to 156000 words out of 388021 words

Chapter 52 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8253

ko?
Murmushi, nayi gami da cewa yar kanuri ce tai min dai,
Ya ce uhumm ni kan nasani don su kadai ke wanan irin kitson haka ?

Sallawatu wani irin mamakine ya kamata har ta kasa daurrewa, tace,
Ina kuma namij yasan kan kitso har da kiran sunayen yan country,
Yace tunda anfada maki cewa ban san komai nagamay da mata ba,
Ba Sallawatu ba har Anty Sadiya saida zuciyar ta yadan sosu amma sai nai tankar ban fahinci su ba,
Na wuce ina wani juyawa cikin karairayan kugu, rigan dama yafitar min da hip's dina dakyau,
Sallawtu tace a cikin hausan Oga gobe ina so man ka kaini uguwa ?
Bai tanka mataba sai cigaba da bude system din shi yayi don duba sakkon ne,,,,,
Takara maimaita zancen ta yace kin taba ganin nakai mace anguwa a gidan nan,
Ban wanan sakarci ni bance bankai mace anguwa ba amma sai mai dalili
Don haka gobe sai ki fadawa Hamza ya kaiki idan kina so,
Tace Nop kadai bari inyi driving da kai yafi min fita tare da wani wanda ban masan asalin sa ba,



ZEEE MAKAW@ YELWA
[8/16, 9:59 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
5? 6?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH- AL- MUJEEB,,,,

Haba mutane, baku min uzuri please, nida nai hakkurin zaunawa na rubuta na turo,
Banyi fushi ba sai ku ne zakuyi fushin jiran network harda turo min zagi da bakaken magana,
Ba komai na gode Allah ya,bani ikon gama wanan novel din lafiya don na yi alkawari, tun da na fara dole in yi hakkurin karasa shi,,,


Zaune yake office din shi yana dan juyawa saman kujeran shi a hankali,
Jikin shi ya saye da,farar tie shirt, mai dogon hannu da,aninaiyya jere har kasa,
Wuyan shi nada necktie, daure mai dan tsawo har saman kirjin shi,
Wandon jikin shi baki sai kafan shi dake saye a,cikin bakaken takalma,
Hannuwan shi na saman goshin shi ya dafe dafe shi da shi,
Kallo guda zakai mashi ka gane cewa,ya na dan cikin yanayin damuwa irin yadda yake zaune dafe da goshin shi,
Idon shi ya kara lumshewa yana tuna irin bakaken maganganun da Sallawatu ta fada mashi a daren shekaran jiya,
Idan akwai abinda baya so tun yana karami shine fitina da kuma mai yawan yin fitinan,
Gaskiya sam bazai lamunci, ta wargaza masa gida ba suna zaune kalau da matan sa,

****** ********** ******
Matar yaya Awal dan wurin baba musa ta haihu,
Sai barka mata ke zuwa yi a gidan tako ina yan uwa da abokan arziki,
Haihuwan yazo wa Baba, Musa a bazata don haka ba wani shirin da akayi a kai,
Yaya Awalu yana ganin dashi da mahaifin shi duk sun dan shiga damuwa,
Saboda sanin irin yadda buki fari yake, a garin Birni Kebbi,,
Mahaifiya na Saratu ita ce ta bugo min waya tana fada min cewa matar Yayan ki Awal ta haihu,
Don haka ki bugo waya kiwa dan uwanki barka tare da mai jego nace cikin murna insha Allahu mama zan bugo mashi,
Nace mama tace Yaya Ibrahim ya turo min da nomban nashi,
An turomin ba,a wani dade ba na kira Yaya Awalu cikin jin dadi,
A lokacin yana zaune a sashen mahaifan shi suna, dan tataunawa,
Ganin bakuwar noba ce yasa shi cewa bari kawai ya share nomban,
Har kiran ya katse bai dauka ba amma sai nace bari dai in kara kiran shi in gani,
Nakara dialing din nomban Baba Musa yace dauka mana kaji ko waye, ke kiran ka,
Mahaifiyar shi ta ce ai shima yasan musu barkana ka kira nai,
Ya dauki wayan tare da cewa Assalamu Alaikum, naji dadi sosai da naji muryan dan uwan nawa a lokacin,
Duk da nasan halin miskilancin shi iri gudane da na Yaya Abubakar don ko zubin halittan su iri guda ne,
Amma hakan bai hanani yi masa dan ba,a bayan na karba sallaman nace cikin dan zolaya
A Yaya Awal angon karni ashe mun samu karuwa na ?
Allah yaraya muna yasa albarka Allah sa dadin musulma ta,
Ya karba da fadin Ameen a dakile kamar yadda nai tunane,
Nace Yaya ina gaida, Jamila ina mata barka Allah shi raya muna,
Ya kara cewa Ameen,
Nace ina gaida su Baba ya amsa da zasu ji,
Mamaki yakeyi ko wacece take mai wanan waya haka,
Tambaya yayi da cewa shin wai wace,ta, ka magana don ban gane ba,
Yaya Meenatu ta fa,
Cikin dan sake murya naji yana cewa a,a Meenatu ke ta,
Wallahi, tallahi ban gane keta ba ?
Murmushi nayi nace ai na gane Yaya nima mamata, ta bugomin taka fada min cewa ai mun samu karuwa,
Yace walle gaskiya na ta yaya wajen maigidan naki ?
Lafiya yake Yaya,
Nace shin kako fada mashi,?
Ya ce walle Meenatu ban fada mashi ba,
Nace haba dai Yaya halan me ?
Yaya don Allah buga mashi, don kaga kaina ya kamata ka fada mai,
Yace to Meenatu zan kira shi insha Allah amma ina gudun kar mama Ladi ke dai san halin ta ai,
Nace ,a,a Yaya kai dai fada babu komai insha Allahu,
Nace zan kiraka yaya insha Allahu zuwa gobe da yamma,
Yace Meenatu na gode keji,,,
Allah yabar zumunci na ansa da fadin Ameen yaya sai anjima,
Bayan mun,gama magana dashine ya dan juya gurin da mahaifan shi, suke,
Ya ce, Meenatun Baba, Samaila ta wai Mama Sara ce ta buga mata waya tana sheda mata zancen haihuwan,
Nan dai ya kwashe duk yadda mu,kayi ya fada ma,su,
Baba Musa ya ce, tsoron Ladi mi?
Ladi ta zata hana ka zumunci da dan uwan ka kira shi dai kafada mai halan wani abunai kake so?
Yaya Awal shi malamin secondary ne gashi kuma ba,ai masu albashi ba don ana tsakiyan wata,
A take a gurin ya kira Yaya Abubakar, wanda ke zaune a office cikin damuwa,
Bayan sun gaisa yake ce mashi, ya bugone ya fada mashi matar shi ta haihu,
Barka Yaya Abubakar yai mashi baidai nuna mai wani, murna ba a fili,
Yadai mashi barka a dan dadare tare da Allah ya raya suka kashe wayan,

****** ********** ******
Ina ta murna har cikin rayuwa na da wanan haihuwa har cikin raina,
Bayan dawowan Yaya Abubakar, gida ya shige dakin shi,
Ban fito ba don nasan cewa, banice da girki ba a ranan,
Ina daki abina ina kallon wasan yara tashan cartoon,
Sallaman Yaya Abubakar ce ya naji a dakin nawa cikin wanan lokacin,
Na daga kai, da mamaki ina kallon shi, don nasan baya shigowa dakin mutum a wanan lokacin,
Kokarin mikewa nakeyi daga zaune,,
Yace No koma ki zauna abinki, dama nazo in fada maki cewa ne, dan Allah kafin indawo ki dan dafa min ruwan Lipton mai kayan yaji please?
Dan jim nayi sanin cewa yau ba ranan girki na bane,,,
Har ya kai kofa yace, ina da right din da zan sa kowace mace aiki a gidan nan,
Shiru nayi ba tare da nace komai ba har ya fita daga dakin nawa,,
Nisawa na yi tare da kokarin mikewa don zuwa, yin abinda aka umurceni da yi,
Kitchen din nafara shiga na har,hada kayan yaji na zuba a wani roba na fara wanke wa san nan na zuba a cikin pot tare da dauko Lipton guda biyu na kada acikin ruwan,
Sosai na barshi yai ta dafuwa a saman wuta, don yayi masa dandano yadda yake so,,
Bayan na gama hada komai a flask na dauka zuwa falo dashi,
Sai dai babu kowa a falon abin yabani mamaki don da wuya irin wanan lokacin a samu Sallawatu bata falon,
Amma sai gashi yau bata falon hakan ya bani mamaki matuka,
Juyawa nayi da flask din na mayar kitchen na samu guri na boye ,
Dakina na koma na gabatar da Sallah sai kuma na dan kara gyara guri,
Yan mintoci da dama aka dauka kowa bai fito ba nan na gane a kwai matsala a gidan,
Anty Sadiya ce ta fara fitowa tana saye da rigan barcin ta fari na cotton, har kasa yake rigan,
Bata jima ba Sallawatu tafito itama cikin wasu kaya kaman na yan ghana, ita aga?in ta wayewa ne,
Sai da na tabbatar da cewa nagama komai adakina nafito, wajen,
Kitchen nafara zuwa nadauko mashi dan wani flask karami baki da yake amfani da shi,
Tafe nake amma zaka ce ai rangwada na keyi a lokacin, don irin tafiyan nawa,
Cikin dogayen rigunan da Anty Amarya ta sayo min na saka guda,
Rigar irin in kana tafiya sai ya kama shocking yana wani dan fidda walkiya a jikin yadin,
Da yake darene sai ya kara ma rigan kyau da daukan ido,
Tun da na tunkaro hannu na yana dauke da flask din da cup duk hankalin su na a kaina,,
Nakarasa takowa a hankali gaban shi na durkusa tare da aje flask din ruwan a gaban shi,
Sai a lokacin ya dago kai yana cewa Ok har ya dafu ko ?
Na ansa da fadar eh yaya,
Kanshi yana duke ga system din shi yake cewa ki dauko min zuma a saman drawer a dakina please,
Ban dauka cewa dani yake ba don haka sai na samu gurin ina kokarin zama, a gefe,
Ya dan dago kanshi daga abinda yake yi yace bakiji bane wai ?
Sai na dan daburce nadan kalli Sallawatu wace ke da girki a ranan,
Yadda naga ta daure fuskanta tamau, ta wani hade rai, yasani mikewa,
Sai naji muryan shi yana cewa ki hado min da spoon please, na ce toh na juya zuwa inda ya aike ni,
Sallawatu wace ke kallon mu rai a bace tadan cije leben ta, tare da yin kwaffa,
Ban karasa hawa sama ba najiyo muryan ta tana cewa
Aiko baka nuna a fili ba kowa ya,san cewa, akan Meenatu zaka iya komai agidan nan ,
Yace au har kin manta da kince saboda tana yar uwana nake nuna mata hakan,
To ina son in gwada maki cewa,
Yar uwatace din ta kwarai don guri biyu take gare ni zuwa uku,
Kinga na farko yar uwar haihuwana ce,
Na biyu mata,ta,ce ta sunna,
Na uku yaruwata ce ga musulunci don haka babu ta inda ban hada da ita ba,
Don haka kalamin nan naki da kikafada shinake son gwada maki cewa, Meenatun zan iya sata zan iya hanata aduk sanda naso,
Tai wani har da ido tace ai sai ta haifa maka yara, mu gani ka cika gida dasu kuna cewa yan uwa kuke,
Sadiya wace tun fara zancen take sauraren su cikin bacin rai tace amma wanan abin naku bai kawo kallo ba, gaskiya
Tana kokarin mikewa tsaye take fadan haka gare su,
Ya nuna Sallawatu da yatsa adaidai lokacin da karaso????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ?  dauke da kwalban zuma a hannuna yake cewa,
Wanan macuciyar mata ce so take ta cuce inzalumci rayuwana in kone,
Bazaki bani dokaba agidana don nina ajeki bakece kika ajeni ba,
Kuma kin san ai ina da mata ki ka aure ni hakana da su,
So sai ko kiyi hakkuri ki zauna kamar yadda kowa cen ku ke hakuri da dan uwa,
Nikan ina aje kwallba na juya na nufi part dina cikin bacin rai ,
Muryan Sallawatu naji tana cewa, ashe dama kai haka kake ban sani ba,
Ya Abubakar yace o da kinga yaro kin zo ki min wayyo ko,
Look Sallawa the door is open,
Yo can go and live us pls,
Bazan taba bari ki cutamin aka rayuwana ba in kwashi dukiyar mutane in dinga narka maki any how,

Dakina fada ina mai kiran innalillahi,wa,inna alai,him,raj,um,
May ke faruwa haka tsakanin yaya da matar shi gaskiya abin baiyi kyau ba,
Har zan rufe kofa sai na tuna da ban dauko goran ruwa sha ba,
Don haka nafito don in dauka naji yaya yana cewa , I can't stay, with you, being my wife like dis,
Abuse me like a ashawo woman in front of my family,
Jikina yana rawa da gurin da nake na hango idon shi sun kada sunyi jajir a lokacin,
Narasa may yai zafi har ya kawo wanan fadan tsakanin wa yan nan ma,auratan, haka ?
Da sauri na karasa ina cewa Yaya kayiwa Allah kadaina wanan halin ba alheri bane please na karasa kamar zanyi kuka,
Juyawa yayi ya dan kalle ni da rinanun Idanun shi da suka kada sukayi masa ja,,,,
Ko may ya tuna sai naga ya dauki system din da flask din ruwan da na kawo mashi ya haye sama,
Gurin Sallawatu na juya wace ke cike da masifa saidai kuma fuskan ta ya manne da nadama, sosai don irin yadda tabi bayan shi da kallo da yake hawa sama,
Na juya gurin tare da mata wani irin kallo nace haba haba please hakan bai yi kyau ba gaskiya,
Bai kamata ace kuna haka ba wanan ba alheri bane gaskiya hakan ba zai kawo alheri ba gaskiya,
A cikin mamaki kamar ba sallawatu ba naji tana cewa Meenatu,
Babu abinda zaki fada min tunda harda ke gurin son kuga bayana agidan nan,
Murmushi mai daci na hade ina cewa badamu tunda kinsan da haka amma yanzu sai kiyi hakkuri saboda dare muryan ki zai iya kaiwa ko ina,
Amma shawaran da zanbaki shine ke mace ce kiyi kokari ko sasanta da miji ki ina ga zaifi daga haka najuya abina wuce,

****** ********** ******
Washe gari tunda safe Sallawatu ce ta buga min kofa,
Ina bude kofa nagan ta tsaye cikin wani dan yalalon hijjab dagage tun a kofa tace min ina kwana Meenatu,
Hanya na kauce mata don na fahinci tana son shigowa dakin nawa,
Tana raraaba ido ko ina adakin tana kallon yadda dakin nawa yake da tsari da tsabta,
Bakin gado ta zauna yanayin idon ta y nuna cewa tayi kuka sosai da dare,
Itace ta katse shirun da cewa Meenatu nazo ne in maki godiya akan abinda ya faru daren jiya,
Nagode kwarai don kin bani shawaran da babu wanda yabani shi,
Sai kuma don Allah ina mai baki hakkuri ga yadda nasa ki a cikin rikinci mu bakiji ba baki gani ba,
Sai gashi kuma duk da ina maki kallon yarinya kinbani shawaran da yai min dadi,
Don Allah kuma ina rokon ki da kikara ba yayan ki hakkuri akan abinda ya faru please,
Nace a,a gaskiya tunda har kun sasanta a tsakanin ku komai ya wuce don Allah sai kuyi ta hakkuri please,
Tace sherin shedan ne kawai don ba wani babban magana bane haka dai Allah ya kawo
Na tare ta da cewa Allah ya kyauta ya tsare muna gaba don Allah muyi ta hakkuri da junan mu,
Tamike tana cewa nagode nagode Meenatu,

Tana fita nabi bayanta da kallo ina tuna maganan Anty Amarya da take cewa irin su Sallawatu baka gane kan su,
Sai ka natsu sosai don yan duniya ne na karhe,
Lalai Anty Amarya ta fadi gaskiya don dubi yadda wai yau Sallawatu ce kamar da gaske tazo min daki,,
Daren jiyane fa take ta zumduma min zagi harda gorin haihuwa,
Amma yau wai itace tazo take min dadin baki, kamar wata ta kawarai Allah ya sauka
Na kara da cewa Allah yai min katangar tsari ga duk wani sheri na ta,
Na nade sallaya na dama tasamay ni zaune ne ina karanta Hasbunallahu wani,iman wakeel kafa dari hudu da hamsi
Gyaran safe nai ma dakina na koma na kwanta batare da nafito waje gyara ba,
Barci nakara komawa batare da nasani ba har zuwa lokacin da Yaya Abubakar ya shigo dakin nawa,
Yau shigan kanan kaya yayi wanda ya kara fito maahi da kurciyan shi a fili,
Suman kanshi daya dan taru ya kwanta mai a kai bakikirin, yai lub
Hannu shi ya na saye da wani agogon White, silver, sai kafan shi da ya sa wasu takalmi buth na maza masu tsada,
Barci kikeyi ne Meenat ?
Ya tambaya alokacin da yake kokarin juyawa daniyar fita daga dakin nawa ?
A hankali na bude ido,na na kuma sauke su ga fadadar bayan ya Abubakar dake niyar juyawa,
Murya na ya tsinkayo ina cewa Yaya ina kwana,?
Juyowa yayi yana cewa kin tashi ne ? kwanta abinki ni zan fita ne,
Nace Allah, ya tsare hanya,,
Har zai fita na mike zaune daga kwance da nake,
Yaya ya zance ya Awal ne ?
Cikin mamaki yake kallo na yana cewa Awalu ?
Nace eh Yaya bai fada maka cewa matar shi ta haihu bane,
Cikin daure fuska yace ya fada min mana nai mashi barka,
Na kara gyarawa nace amma Yaya ai ya kamata ka bada gudun mawan ka,
Hannu ya daga min yana cewa look Meenat may kuma kike son in mashi, bayan barkan ?
Cikin dan tsuke fuska nace amma dai Yaya kasan fa haihuwa wani abune


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login