Showing 288001 words to 291000 words out of 388021 words

Chapter 97 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8248

sai kawai ya,
Yara tafiya don ya bar gurin saboda kada ta san yana gurin,
Juyawan yai niyan yi sai yaji tana cewa na fada maki dama ai Yaya Aliyu ya,fada min cewa yana son Meenatu sosai cikin matan shi,,
Amma sai na mussanta mai nace ance bai damu da ita ba don auren hadine auren gida,
Yana kaiwa nan yai yar murmushi tare da murda sitiyarin motar shi, zuwa gidan hajiya Jummai don ya gane wa idon shi irin kayan da ta shigo mai da su,
Don Fatima yana ganin tafi duk sauran matan zafi don irin yanayinta yanzu ba wanda ya santa da shi bane da can baya,
Yana tafiya yana cewa a ranshi ashe shiyasa itama Meenatu bata ra,ayin zancen da ya shafi Fatima duk gautan ja ce kawai, indai mace ce,
Ya isa gidan Kayan sunyi mashi kyau sosai don yasan cewa za,a yaba da su don haka yasa a parker su a mayar a cikin akwatinan su kawai,
Ya fada mata cewa Baba Hamza da Baba Wadda zasu shigo su dauka idan zasu tafi kawai dai ta rufe mai su ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????da kyau,

Da dare kowa yana falon zaune yai shiru yana sauraren abinda mai gidan zaice akan zancen da suka kulla na cewa su karbi wani abu a gurin shi,
Idan yaso sai su sai dan abu kalilan su bayar suce mashi ya isa hakana, su dai kawai su samu na su rabon daga ciki,
Sadiya ce bata yarda da wanan hadin kan kishayan ba da za,ayi wanda ba na Allah bane,
Don ko fuska Fatima yar iyayi bata gani ba a gurin Sadiya balle ta, tun kare ta da zance,
Da farko ita ma Salawatu taso ta bijire mata amma da taji zancen yagar kudi ne sai kawai ta kawo nata gudun mawan ta yadda za su samu galaba, akan shi,
Sai da ya gama abinda ya keyi a cikin computer dake gaban shi sannan ya dago kai tare da sauke numfashi yana cewa,
Ok dama akan zancen zuwa gurin sunane yasa na kira ku nan yana magana yana kallon Sadiya,
Ya,ce don inji ko da wace ce zamu tafi don dole mu bar wata a gida bazamu kwasa mu tafi ba gaba dayan mu ,, ,
Akwai motan Bus ta ma,aikatan mu da na dauka saboda matan Lawals da sauran mutane masu son zuwa,,
Su har can zasu tafi basu jin nisan wanan tafiyan da akeyi ?
Salawatu ce tai wanan maganan batare da tai la,akarin komai ba,
Hakan yasa shi gane cewa bata da niyan zuwa gurin sunan ke nan don haka yace a ran shi zanyi maganin ki,
Ya ce da farko zanbawa kowacen ku dubu ashirin don babu kudi kunga ga tafiya agaban mu da zamuyi,
Don haka kowa yasai abinda yake son saya dashi, don laluran haihuwan,
Ya, dauki waya ya kira Baba Wadda yace ya cewa Hamza ya duba a mota ya shigo da ledojin dake cikin motan, shi,,,
Yaci gaba da cewa ke sadiya da Salawatu sai ku shirya mu tafi tare mu,bar ita Fatima a gida sai idan Allah ya dawo damu lafiya idan zan tafi gaida, su sai mu tafi tare,da ita ta gane su,
Gurin gaba daya yai tsit ba wani mai motsi don plan din kowan, su ya rushe ke nan a hakan,,
Hamza ya kawo ledojin ida ya mikawa kowan su nata a tamface da lace yace su samu na shiga buki saboda ba kudi,
Fatima wace sai faman jujuya kayan take yi da hannun ta duk da kayan suna da kyau sosai ga kuma daukan ido ga lace din,
Amma duk wanan kyau din kayan basu gaban ta don akwa abinda take son yi idan ta tafi BK din don tana son zuwa kangiwa,,
Dole ba yadda ta iya ta hakkura da zancen zuwa dole itace zata tsaya a gida,

****** ********** ******
Mutanen gidan mu kowa sai aiyu kan shi ya keyi na yau da kullun idan gari ya waye
Hakan yasa akabar ni a daki dagani sai dan jaririn dake barci, shi a gefena hankali kwace,
Don haka ni tunda yan hira basu, zoba kowa tana can tana rage aiyukan gaban ta ,yasani nima kokarin kwantawa don na huta,wa raina,
A hankali nakai kwance tare da sauke ajiyan zuciya yayin da na dan lumshe idanuwa na da niyar yin barci,
Waya tace tai kara alaman kira ya shigo min duk da na fara lumshe idona alamar barci bai hanani bude idona ba a lokacin,
Yaya Abubakar ne a layin yake kira na duk da nasan cewa shi ba mutum bane mai,kiran waya da safe saboda yana office a lokacin,,,
Kafin wayan ta tsike nadaga kira dauke da sallama irin ta musulinci a bakina,
A hankali naji yakira sunana cikin wata irin murya mai cike da kasala da birkita lissafin mutum wanda ma,auratane kawai suka san irin wanan yanayi,,
A,take wani irin kasala ya sauka min tare da kewan mijina wanda na manta tsawon lokacin dana dauka banji irin hakan ba a tare dani
Wani irin ajiyan zuciya na saki wanda shi kan shi Yaya Abubakar sai da yaji shi har cikin ran shi, daga bangaren shi,
Hmm naji yace tare da cewa maijego kin sha zafi, ya kuke Meenat ya Baby na, ?
Murmushi na sake a hankali tare da cewa cikin wani irin murya,
Muna lafiya kalau insha Allah, ya amsa tare da cewa masha, Allah
Yace insha Allah gobe zamu taso gaba dayan mu don saboda nisa
Domin idan mun ta so mu samu mu huta kafin mu koma,
Saboda haka idan akwai abinda za,a zo maki da shi sai ki fadi kafin mu taso din,
Sai yanzu na dan sauke ajiyan zuciya tun lokacin da ya fara min bayani,
Nace Yaya na babu abinda nake bukata daga can sai dai idan da guri kuzo muna da Irish da manja kawai,
Yace cikin nuna alaman murmusawa, su kawai za, a zo dasu nace eh su ma din wa mutanen gida don amfani, su,
Yaya Abubakar yace cikin kasalaliyar murya ina fatan uwar 'ya'yana ta daina fushin da takeyi da uban 'ya'yan ta,
Sai da na lumshe idona saboda jin dadin jin sunan da ya kirani da shi na uwar yayan shi
Cikin lumshe ido na
na?e haba dai Yayana akan may zanyi fushi da dan uwana rabin raina,
Yace amma badon zamu saudiya ba ai da nazo kawai sai na tayar wa malam da su Baba hankali cewa nida iyalina zan koma Abuja,
A hankali na sake wani dan murmushi mai sauti nace aiko da kakawo fitina don malam gaba zai saka mu, ni da kai, yace mun kawo mai sabon fitina,
Dariya naji Yaya yayi sosai tare da cewa zai koyi fitina yabar mu,
Yace ba komai duk fitinan da za suyi indai zan dawo da ku ai bazan damu ba ni,
Na ce haba yaya sai kace wanda baida mata agida da zakace mu dawo tun yanzun, da jegon mu,
Murmushi mai nuna ma,ana naji ya sake tare da canza akalar hiran na mu,
Ida yake sheda min cewa su Fattu da Anty Saloon za su zo su ma, tare da sauran jama,a
Murna nayi sosai tare da nuna farin cikina a fili don jin cewa mutanen arzikina za su zo gari wagari tun daga Abuja har KB,
Mundan jima muna hira da Yaya Abubakar wanda mun jima ba muyi hiran arziki irin hakaba dashi, tun kafin auren Fatima, da shi

****** ********** ******
Gida kowa gyaran jikine daga dangin kitso kunshi siffa, da sauran su,
Sai kuma dan kus,kus din da ke yawo cewa,
Mahaifana ba su aje komai ba don babu komai a part din mu wanda zai nuna alaman cewa akwai, wani hidiman, suna agaban su ba,
Don haka tun mutane ba su dauka har suka, f?ra yarda da zancen ta
Akai,ta suka na da mahaifana suna cewa wai ina zaune da mai hali amma naki tara komai muyi lalura,
Suke fadi kuma haka za,a kwaso jiki a zo a fada min ni da iyayyena duk abin da suka ce a can din ,
Idan na fada ma anty Amarya zancen da mama keyi sai tace dallah rabu da wanan Mata da batasan ciwon kanta ba, sam
Haka abubuwa su kai ta gudana kamar kowani gidan haihuwa yadda ake badakala, da jama,a,,,,
A fanin iyayyena su ma sai shirin suna sukeyi a bin su a hankali,
Amma mutane sai suke ganin tun da har, izuwa yanzu ba suga wani motsin kwarai ba daga sashen mu hakan ya nuna cewa maganan Mama Ladi akan mu gaskiya ne,
Mama Ladi yaran ta a sashen su sai shawara sukeyi suna kullawa yadda za suyi al,amurorin shagalin sunan su,
Anty Safiya da Anty Samira suka kaqo shawaran yadda za ai bawa mutanen gida abubuwan su,
Amma sai mamata kekashe kasa tace bazata bawa kowani part ba iyaka dai wanda ya shigo a dan bashi a leda kawai,
Basu son wanan shawaran na Mama amma kuma dole su bi shawaran mahaifiyar ta su,
Sai ana gobe suna mahaifiyar Fatima ta shigo barka ita da wasu mata mutum uku, sai wani kallon kurulla take min tankar itace kishiyar tawa,
Inda ta kawo, min turmin zani da sabulan wanka acikin wani farin leda,
Sai da dare mutanen Abuja suka iso gaba dayan su inda gida ya kaure da murnan ganin bakin mu,,
Sabon part din da Yaya Abubakar, ya gina don saukan mu idan munzo anan a ka sauke bakin mu da sukazo,
Daga cikin su harda Baba Ramatu, matar malam Abdullahi masinja,
Antyn Saloon Fattu da Maman Biu, sai matan wani abokin aikin su Yaya Abubakar su biyu,
Haba murna da farin ciki ba,a maganan on muka baje a dakin dije da bakin nawa duk da an ma su masauki a can part din,
Mukai wani lokaci zaune tare da su muna ta yaushe bayan robo ,
Inda gaba dayan su ,sun yaba da kyawondan jaririn dake kwance yana barci,
Sun tafi masaukin su don su dan kimtsa a lokacin ne yaya Abubakar ya shigo sashen da malam tsoho,
Daga cikin daki gurin da nake zaune ina iya hango shi cikin annuri,
Fuskan shi sai sheki yakeyi yana annuri baiwan cikar zatin shi ya baiyyana a fioli,
Ina jin muryan shi mai rikita may saurarenta tare da shiga yanayi ,


ZEEE MAKAWA YELWA
[10/21, 9:51 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
8? 6?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH AL AWWAL,,,,

Sai da ya gama barkwanci da matan malam tsoho a lokacin ina daga ciki zaune sai dan murmusawan jin dadi nake yi zuciya ta tayi fes saboda farin ciki,
Da Sallama ya dago labulen dakin da nake a ciki zaune, gefe guda a kasa saman tabarman kaba, ta saka mai launi kala, kala a jikin ta,
Jug ne a gefe guda na tab da kunun kanwa a cikin shi, sai wani roba dake shake da kayan yaji yaji daddawa da maggi da su tafarnuwa, acikin sa, sai sugar daga dayan gefen
Dakin sai kamshin jego ya keyi duk da kamshin turaren wuta yaso, ya rinjaye shi,
Idon shi kem a kan, dan jaririn da ke kwance cikin wasu zannuwa da aka dunkule a guri daya,
Sai kuma ya juyo gurin da nake zaune, ina wani dan noke noken kai kamar mai jin kunyan shi,
A hankali ya karaso bakin gadon inda yadan rankwafo jikin shi ya rage tsawon shi,
Bude jikin yaron dake nade a cikin showel yayi har zuwa kafafuwan shi kamar mai son ganin wani abu a jikin yaron,
Ajiyan zuciya naji ya sake a hankali tare da dan, juyowa gurin da nake yana cewa,
Sannu Meenatu gaskiya kinyi kokari wanan yaron babba haka kamar ba kece kika haifo shi ba,
Murmushi nayi kawai tare da dan kifta ido kamar mai marmada su nace cikin irin murya na,
Sannu da zuwa Yaya ya hanya ya aiki ya sauke ajiyan zuciya tare da kokarin kaiwa zaune yana cewa Meenatu barka da arziki, haka,
Ya kuke ya ruwan zafi da kuma kokari ?
Sai na rasa may zance kawai sai nake cewa ance da su Anty Sadiya kuka shigo garin ko,
Cikin mamaki yace basu shigo bane tun dazun da muka iso nace kila suna dan hutawa ne,
Yace kawai basu da hankali don banga amfanin zuwa dasu ba ,
Ace sun zo basu zo sun dubi wanan yaron ba to may suke a can uban wa suka zo yi a garin ?
Nasan yau ran maza ya baci tunda har da zagi naji daga bakin shi, akan bacin rai,
Waya yadaga yana tambayan su suna ina ne wai, gashi a part din da nake baigan su ba,
Muna nan gurin su mama inji Salawatu ta bashi amsa kai tsaye,
Ok kawai yace batare da ya furta wani abuba a gain don canzawan idon shi kawai ya isar min da sakon zuciyar shi,
Tafiya har da su Ramatu ashe da matan malam Abdullahi sai lokacin naji ya dan sake rai tare da ajiyan zuciyan tunanen da yake yi,
Yace Ramatu a ko da yaushe tana yawan tambaya na da cewa yau she ne uwar dakina zata dawo,
Hakan yasa nace ta shirya azo da ita ta gan ku ko hankalinta zai kwanta ita da maman Biu,
Murmushi nayi don jin dadi nace ai nagode kwarai wallahi,
Kafin nai magana sai naga jaririn yana dan wani wutsil,niya da kafan shi alaman zau farka daga barcin da yakeyi ke nan,
Ido na kura mai daga gurin da nake zaune ba tare da nayi kokarin mikewa na duba shi ba,
A hankali Yaya Abubakar wanda ke hankalta da abinda nakeyi ya mike tare da kai hannun shi da niyar ya dan jijiga shi,
Aiko kaman ance ya tsala ihu sai ko ya barke da kuka wiwi,
Daga waje Mama Dije ke cewa Meenatu, bakyajin kukan da dan bawan Allah ke yi ne,
Cak Yaya ya dauko shi tare da dangware min shi a saman jikina yana cewa wanan ai daukan alhakaki ne ko yaro na kuka gaki zaune kina kallon shi,
Cikin dan marairaicewa nace, yaya ai ina batun tashine dama shine ka miko min shi ,
A hankali nake kokarin bude nono na don nabawa yaron yayin da Yaya Abubakar ya tsure ni da idon nan nashi mai rikitarwa,
Kunya duk ya rufe duk nashiga rudu na rasa yadda zanyi naba yaro nono a gaban shi,
Muryan shi naji ya kira suna na a hankali yayin da na dago kaina na dan dube shi, cikin kunya ina kuma kokarin gyarawa,
Yace an darajan Allah da Annabin sa, ki taimaka min ki tallafi yaron nan amana,kamar yadda muma iyayyen mu suka tallafe mu,
A hankali nace yaya ai ina bashi nono kawai yau don dai, ka na gurin ne,
Ya girgiza kanshi cikin lumshe idanuwan shi tare da dan jingina jikin shi saman filo, yana mai kara lumshe idanuwan shi saboda sha,awan mu da ya kama shi,
Na turawa yaron nonon a baki yayin da ya cafke da sauri ya fara zuka,
Shiru dakin yayi tankar babu kowa a cikin dakin a lokacin sai dan jaririn ne ke yar ajiyan zuciyan kukan da yayi,
Zuba muna ido yayi yana kallon mu, cikin mamakin yadda nake dan rutse idona saboda zafin da nake ji yasa shi jin tausayina,
A gogon dake daure a hannuwan shi ya dan kalla tare da gyara zaman shi yana ma muna kallon tsab, ni,da baby, muryan shi na ji,
Yace to yaya zancen komawa tare da mu ina fatan yana nan dai ko ?
Ajiyan zuciya na sauke, tare da dan dago kai daga duken da nake, Murmushi nayi mai sauti tare da cewa ai da malam ya saka mu gaba don ko yanzu ba,a fita da yaron nan ko kofan dakin nan,
Nima wanka a cikin wanan dayan dakin da ba,a karasa ba yace a dinga yi min, har a yi sati guda,
Iska ya furzo daga bakin shi irin mai fitar da takaici di nan yace badon komai ba ne sai don wasu yan dalili da suka faru
Amma ai hakan yayi don badon Allah ya sa mun fargaba da wuri ba da an muna sakiya, da baruwa,
Wanan yaro Meenatu Allah ya kara tsare muna shi dashi da duk wani wanda ke a cikin matsala iri na mu,
A sanyaye na amsa da cewa Ameen
Jikina nane yai sanyi sosai, don jin may yaya Abubakar ya fada hakan ya sani gane cewa akwai magana babba a kasa,
Wayan shi ce da tai kara yasa shi dan dagowa daga dukawan da yayi gab da dan jaririn yana cewa, Ok ka iso ke nan ko ?
Sai na gane cewa da Aliyu yake waya a lokacin, saboda, muryan shi dana dan tsinkayo a wayan,
Da wuya na shigo nan again may be sai zuwa safe idan Allah ya kai mu don zamu tafi Kalgo ne yanzun nan,
Nace Allah ya tsare hanya a dawo lafiya tare da dan r ausaya kaina wanda yasha kitso sai sheki yakeyi, ga kumshi dana, sha,a hannu


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login