Showing 252001 words to 255000 words out of 388021 words

Chapter 85 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8203

sadiya take a gefen shi tana kallon yadda suke waya da Fatima wace kusan duk minti talati sai ta kirashi,
Tambaya Sadiya ta jefo mashi cewa, harda kai cikin rufe min zancen cikin Meenatu Abubakar ?
A bazata tambayan tazo mashi tankar bada shi takeyin magana ba don tankar bai jita ba ma
Sai da ya dauki yan min tuna sannan yake cewa, yadda kika tsunci zancen a nan haka nima na tsunce shi anan din,
Tace kana nufin cewa kaima baka san cewa tana dauke da ciki har ya girma haka ba,
Ya zanyi in sani tunda ni ba likita bane kuma ni ba mace bace balle na gane hakan,
Ya dan lumshe idon shi tare da lashe labben sa ya furza iska sannan yace,
Malam tsoho naji yana zancen haihuwanta abinda yasani sani ke nan da saidai kawai naji haihuwan ta kwasam,
A wani jahilcin ta,wai tana jin kunya fada min cewa tana da ciki,
Wai ita azaton ta zangani a idona , yayazan yi in san ciki wanda ko bari ba,a taba yi a gidan sa ba yagani,
Wani irin abu ne ya kara sukan zuciyar Sadiya don tasan cewa da ita yake ke nan,
Juyawa tayi tana mai kallon window motar tace a cikin bacin rai yanzu aga haihuwa nan za,a ma a gida sai kasan yadda yake ko tunda ba,a taba ma bari ba a gida,
Murmushi ya kara yi tare da dan shafa fuskan shi a cikin takaici yace,
Niba jahili bane nasan cewa Allah ne ke bayarwa ga wanda yaso kuma ahike hanawa a inda yaso don haka kada ki canza min zance please,,
Daga haka babu wanda ya kara cewa uffan acikin su, sai karan gudun mota kawai kakeji yana tashi
Wanan karon wayan shi tayi wani sabon sauti again suna a cikin gari ne kiran Salawatu ya shigo wace, tana son jin ko yana ina ne a lokacin don ta dawo daga gurin da ta tafi ansan kayan gyaran jikin mata,
Wanan halinta ne sosai haka takeyi idan tasan baya gida ko gari sai ta kirashi tankar kiran soyayya tana wani kashe murya tana cewa hello, sweet Oga ,,
Kana hanya ne yanzu shi kuma da yake na miji ne, bai san cewa tako bane ta hada mai sai ya bata amsa da cewa ya na guri kaza ai,
A hakan sai ta samu daman fita duk inda take so ko kuma ta karasa ayin abinda ta fita yi waje, alokacin,
Yauma hakane yana fama fadawa Salawatu cewa yanzu suke shigowa Abuja ,
Yakashe kiran ke nan zai aje wayan kiran Fatima ya shigo itama yake mata cewa ai sun shigo gari yanzun nan sai dai basu kai gida ba,,
Daga gefen da take ta sake wani irin tsuki mai karfi tare da dan gyara zaman ta saboda takaicin da take gani da ji a gaban, ta,
Yau Abubakar din tane mata ke ta tawanda da shi kaman wani kwallo, a gaban ta,
Duk da tasan cewa yanzu akwai canji sosai a tare da shi ba kamar da can baya ba da yake nata ita kadai,
Amma ai so da kaunan da take mai yana nan bai gushe ba, kuma tana kishin abinta,
Tunda shima duk da samun wasu matan da yayi ai fita batun taba yana dan lalabata a hankali,
Da farko bata jin zafin abinda take ganin ya na yi da wasu matan shi,
Saidai kuma yanzu zancen Fatima yasa tana jin zafi da kishin mijin ta don sanin da tayi na kowaye Fatiman tun farko,
Har suka karaso gida hankalin ta baya a jikin ta sam jin sun iso yasata daukan hand bag din ta zuwa cikin gidan, batare da ta tsaya jiran wani abu ba,
Da murna Baba Ramatu tazo ta tare ta tana raraba ido taga shigowa na daga baya,
Sai daga baya ne ta fahinci cewa badani aka dawo ba a falo suka yada zangon su inda salawatu tafito tariyan maigida cikin rangwada da kararairaya ,
Ruwan da Baba Ramatu takawo wa Anty sadiya shi take sha a hankali tare da sauke ajiyan zuciya,
Idon ta yana akan Salawatu wace kamar zata shige mai ajiki don mannewa da take mai,
Azuciyar Sadiya tace zaki ji jiki ai fon badan goyo bane wanan, din da kike gani,
Batakai karashen tunanen taba taji wayan Fatima ya shigo wsi tana mashi a huta gajiyan hanya,,
Yadda Salawatu ta hankalta da yadda yake kashe ido yana lumshe su tare da kwantar da kai yasa ta gane cewa akwai sabon kulli, don jin da tayi yana cewa agaida, Baby,
Daga ida Sadiya take zaune take kallon reaction din Salawatu dariya yaso kamata, amma sai ta cije tace kema kiji yadda kowa yaji, azuciyan ta,
Daga haka ta mike zuwa dakinta gyalen ta hannu rabi yana jan kasa dayan hannunta dauke da hand bag din ta,
Sai a lokacin bayan ya gama wayan da Fatima ya fahinci Salawatu ta dan tsargu ga yanayin ta yadda ya nuna ,,
Don haka sai ya sake mata wani killing smile tare da dan jawo
ta zuwa jikin shi,,
Don ta tabbatar da zargin ta sai ta daure tana cewa ina Meenatu may yasa bata dawo ba,
Murmushi yayi tare dan kokarin dagawa daga man,newar da sukayi da Salawatu yana cewa zata koma school ne shiyasa ta tsaya,
Tace taufa, kamar tace dawa kake waya sai kuma taga rashin da cewan hakan sai take cewa ayya ashe zamu sha kewan ta,
Yana kokarin hawa sama,ne yake cewa kila ma sai ta haihu zata dawo garin nan,
Amma zan so tazo kafin ta haihu wai,don mu ga likita da take gani,,
Pardon Sir kana nufin cewa ciki ne ga Meenatu ko waye kake zancen haihuwan ta, ne wai,
Saida ya hau stairs din yadan juyo inda ya barta tsaye yana cewa,
Zancen Meenatu muke yi da ke ko yanzu ko baki ji bane, ,
A hankali ta koma saman kujeran da ta tashi tana maimaita maganar shi ciki fa ?
As how har wanan karamar yarinyar ta dauki ciki ita tana jiran may ?

****** ********** ******
Tun bayan wucewan su ba muyi waya dashi ba bawai na manta ba ,a,a kawai dai ban kira bane,
Don nima ina son in dan gwada jan aji irin na mata saboda nima in san ko ina da star a zuciyar shi,
Har dare karfe tara ina shirin kwantawa mama na daga gefena a zaune tana gyaran Wani sarkan ta,
A lokacin ne wayana yai kara alaman kira na shigo min ke nan,
Banyi saurin daga wayan ba abinda ya sa mamana dago kai ta dan dubeni a hankali
Ganin hakan ya sani mika hannu na dauki wayan na danna received a hankali tare da manna wayan a kunne na ina cewa,
Assalamu Alaikum naji muryan Yaya Abubakar shima yana karba min,
Gaishe shi nafara yi naji ya karba min a dadare, nace a hankali ya hanya,
Ya ce ai baki damu da sanin ya hanyar ta mu ta kasance ba tunda baki kirakiji ba,
Watau ke kin samu mutanen gida kin manta da kowa ke nan tun da kina ganin ki a gida,
Nadan lumshe idona tare da dan gyara kwanciyana nace, sau biyu ina kira ana cewa not reachable,
Sai naji yadan ce hmm din da ya saba fada, yace ya kuke, ya kuma kowa agida ?
Nace lafiya ina su anty Sadiya da Salawatu da Baba Ramatu,,
Murmushi naji yayi tare da sauke ajiyan zuciya yace suna nan suna fushi dake dani,
Da sauri nace dani kuma Yaya may nai madu suke fushi dani,
Mamata ce naga ta dan kalloni a gurin da take zaune don haka sai na dan rage sautin muryana,
Yaya Abubakar yace zancen cikin dake a jikin ki da kika boyewa kowan su,
Da sauri nace to suyi hakkuri ba laifina bane nima ban san hakan ba,
Amma harda Salawatu ta sanine na tambaya a gagauce,
Yabani ansa da cewa ta sani mana nina fada mata dazun da na dawo,
Ban san lokacin da na lumshe idona ba ina cewa a zuciyata da tun farko na fada mai da haka zai fada maxu zancen,
Suko su sani da abincikin vikina agaba da suraitai barkatai,
Muryan shine naji ya katseni yanacewa cikin wani yanayi
Anya Meenatu zan ya iya barinki ki koma school kuwa saboda ina bukantan ku a kusa dani don ki dinga ziyartan asibiti a nan
Don haka sai ki shirya nan da kwana biyu zan dawo na dauke ki kidawo,
Ban san lokacin dana ce cikin dan marairaice murya haba sadauki yaushe har naje school nagama abinda nakeyi na fara lectures ?
Ok bazaki dawo ba ke nan ko ?
Zance mai ba haka nake nufi ba naji ya kashe wayan dip,,,,
Daga gurin da mamana take zaune ta kalleni cikin natsuwa tace so yake ki dawo ko ?
Na daga mata kai a hankali tare da cewa Ummm don raina ya riga da ya baci ko a lokacin,
Mama tace dama ai babanki ya fadi cewa baiso yatafi yabarki ba a yadda ya nuna mai ,
Shiru mu kayi gaba dayan mu dakin kowa da abinda yake sakawa azuciyar shi,
Ida mama na taci gaba da abinda takeyi batare da ce min kala ba kuma,
Azuciya ta nace gaskiya ni bazan koma ba sai dai na hada shi da malam tsoho ko Baba Buhari,
Muryan mahaifiya na ce yadawo dani daga abinda nake sakawa tana cewa
Tunda ya kashe a cikin fushi ki kirashi ki fada mai cewa yabari kije sokoton ki gani idan ba wani matsala zaki bugo mashi ,,
Kinga hakan zai saya san cewa bawai da son ranki kika tsaya ba kema,
Naji dadin shawaran mahaifiyata don shine ake son zama da manya a kusa,
Tace kin daiga kunzo a tare dadi dadi kowa yana sha,awan hakan, don haka kada ki rusa hanyar goben ki,
Nace to mama a hankali tare da kara lalabo wayana na kira shi,
Wayan tana ta ringing azatona ba zai daga ba tunda ya kashe,,
Gab da wayan zai tsinke naji ya daga yana cewa ya akayi kuma tunda kince bazaki dawo ba,
Nace cikin marairaice murya ba hakana bane Sadauki,
Idon shi ya lumshe tare da hade wasu yawu don jin sunan da na kirashi dashi,
Nace ainima bada son raina na tsaya ba zancen zuwa screening din nan ne kawai ya tsaidani don ina son dawowa tare daku ko don lafiya ta
Yace abinda nake maki duba ke nan nima don kada ki samu sauyin magani,
Nace to kayi hakkuri idan ranka ya baci dani please ?
Murmushi naji yayi ta wayan sai naji ya kira suna a hankali ya ce Meenatu na amsa na,am,
Yace mama tana kusa dake kenan ko, kai tsaye na bashi amsa da cewa eh,,
Sai naji yace nikan nasani don indon take ce bazaki kara kirana ba hakan,
Shiru nayi don banda ta cewa a lokacin banda sauraren shi,
Muryan shi naji yana cewa Meenatu gidan naji yaimin wani irin girma da baki,a gidan,
Don haka ina bukatanku a kusa dani ke da baby na don na ji dumin ku a tare dani,
Baiyyananen Murmushi zancen shi yasani nace insha Allah da zaran natafi zanbugoma kaji abinda ake ciki,
Yabani amsa da cewa kin kyauta sai na jiki ki gayar min da mama da sauran mutanen gida,
Na amsa dacewa zasuji insha Allah nagode a,huta gajiya daga haka muka kashe wayan,,,

ZEEE MAKAWA YELWA
[9/27, 9:18 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
7? 8?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH AL WA,AHID



Alhamdullahi anyi sunan Anty Samira lafiya taron jama,a sun halarci sunan,
Anyi shi bisa ga al,ada kamar yadda mutanen kasan Kebbi ke bukin haihuwan fari a al,adance,
Komai sam barka anyishi a acikin wadata inda Mama ladi sai washe baki take yi kamar auduga,
Duk da dai duk yawancin anin fita kunyan buki anty samira da anty Safiya ce su ka,yi a bin su bisa ga taimakon dan uwan su Abubakar da yazo,
Sai habai,ci, Mama Ladi take sakewa tana cewa ai ita Alhamdullahi don duk cikin diyan ta babu wace ta saka, ta kunya don Allah ya rufa masu asiri sun samu abin rufawa kan su asiri,
Ita don dole ne kamar yadda ta kai ita ma akawo mata babu zancen cewa harka yar gida ce ayi ragowa,
Mutane sun gane nufita da ni da mahaifana take wa, arashi,
Abu ga masu yi Anty Amarya tazo taron sunan daga Sokoto, saboda suna hurda sosai da Samira,
Daga gurin da take zaune a dakin da Samira take jego tana jin wanan zance,
Ta jefo amsa kamar haka shege akewa bai rama ba, ko shegen ma na da can ba na yanzu ba,
Iya kudin ku iya shagalin ku, yadda duk akai muna haka zamu yi, rayuwa dai yakai kowa ya sheda,
Don nunge nunge da takurawa diya sai sun kawo walau, sata walau maita mu duk ba ajin mu bane,
Allah dai ya nuna muna ranan da uwar diya ko da zatai kunya, a fillin Allah,
Ai inda ba kasa nan ake gardaman ko kuwa kowa yayi fito nafito a ga wanda ya dogara ga wani,
A take man Hausa akasa guda a na cewa yarinya Allah shi nuna muna lokaci mu kan mu bararake musha shagalin mu ko ba,aso ko dole mu wallah tun da abin walli yazo,
Shin mi akarasa Da,abbabu ko zanin goyo nai,
Suka kara sa ihu, da shewa sai guri ya kaule da guda da shewa kamar ba gidan malam.tsoho ba,
Daga haka Anty Amarya ta saba gyalen ta akai tare da daukan hand bag din ta tamikawa Samira dubu goma tace ta tafi,,,
Sai gurin ya hau rada da cece kuce mata mafi yawan taron suka ji dadin da ansar da Anty Amarya taba Mama Ladi wace take ta masu wani gani gani,,,
A part din mu ta samay ni tana ta huce ina ganin ta nagane cewa akwai magana,
Nace Anty har kin fito ne gashi ina sauri in samay ki can mu zauna zizan buki,,
Cikin fushi tace kada ki tafi part din nan don matar nan ba dattijuwar arziki bace,
Da sauri ni da mamana muke tambayan ta ko may ya faru,
Nan take mayar muna da yadda suka kwashe da Mama a cikin mutane,
Muryan Babana mukaji wanda sam bamu sancewa yana gurin bayan mu tsaye ba sai da mukaji yana cewa,
Ai inda Ladi ce tafi da nan ke dai Sumaiyya, sam ba matar arziki bace wallahi,
Mu fatan mu Allah ya sauke Meenatu Lafiya yaba bata rayayye mai albarka ,
Kowa dake gurin hardani da na karba cikin zuciya muka ce ameen,
Anty Amarya tace aiko zata sha kunya don sai na gigita wanan matan don sai an,dafa kifi da ruwan shi,,
Mamana wace bata kaunar hayaniya tace hai Sumaiyya ku kyale wanan matar ita haka take kullun kamar dujal,
Bakijin zancen alheri ga bakinta sai abinda za, ace ashha kawai zakaji yana fita daga gurin ta,
Kwakwalwanta kamar na kifi yake, ba wayau ko kadan a tare da ita,
Don haka banga abinta da jijiyoyin wuya ba anan, abin da ke gare mu shi zamuyi bamu karyan arziki mu,
Kafin wani yai magana mukaji Sallaman wani yaro yana dauke da leda da kaza a hannun shi,
Yace wai ance ina Meenatu zan ansa sai naji Babana ya na cewa may nene ?
Yaron yace cikin dan rudewa dama Hajja ce tace wai in kawo mata wanan kazan da shikafa wai ta dafa tayi hakkuri da shi, da tazo bata samu kawo mata komai ba,
Ina jin haka da sauri na furta A,zubillahi minal,shetanin rajin,,
A hankali na fara sulalewa zuwa cikin dakin don ban kaunar hada ido da wanan mugun sakon,
Babana yace yaro kodai ka bace hanya ne yace a,a itace dai tai min kwatance da hakan ,
Da yaron da kayan Baba ya tasa su gaba zuwa gurin malam tsoho,

****** ********** ******
Ikon Allah inji malam tsoho ya mike tsam zaune daga gurin da yake a kwance,
Yace wa yaro wuce muje, a take almajiran malam manya da wasu daga cikjn diyan shi suka mara mai baya,
Buuuu jama,a sai kofan gidan Hajja wace ke a bakin famfo tana diban ruwa don kaiwa dodon ta yasha da wanka,
Daya daga cikin mutanen malam ne ya kwada wani irin sallama a kofan gidan ,
Daga ciki take tambayan wane ke sallama yace ta fito tagani,
Ta dan dira zani a???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? kanta zuwa ganin mai sallama don sam rayuwanta bai bata cewa daga gidan malam tsoho bane,
Don sai zuwa dare take tsan manin wani abu yafaru agidan fitinanen tsohon,
Wanan ma dabaran bokantane yace su juya abin zuwa suffan kaza don kada mutane su gane, nufin ta,
Ai tana ganin malam tsoho tare da dattijan anguwa sai jikin ta ya fara rawa tana cewa halan mi, nayyi ?
Mi ankace kuma lafiya kun ka taho


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login