Showing 93001 words to 96000 words out of 388021 words

Chapter 32 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8299

away din dake gabana tayi sai kuma naga ta kalli kitchen din,
Ina kwana anty Sadiya duk da batai min sallama ba,
Murya cikin alamar mai tasowa daga barci tace, wai yau ba,a dafa komai bane gidan,
Banyi magana ba sai naji tayi yar tsaki tana cewa nifa bazan iya wanan harkan girki, girkin nan ba,
Kawai idan zamu hada girki mu hada don gaskiya da matsala idan ance sai nayi,
Bance mata komai ba sai ci gaba da taunar naman kazan da nakeyi a hankali, don cin dole manakeyi saboda cin abu mai nauyi haka tunda safe,
Take away din bai saura bane ki bani in ci naji tace cikin yin hamma,
Gaba daya na gabana na tura mata gaban ta tare da kokarin mikewa tsaye,
Kin gamane ke nace mata a hankali na ko shi, sainaga ta jawo tafara ci,
Mamaki ne ya kamani sosai ,
Wai ita wace irin mata ce shim?
Bata iya sallama ba balle maganar girma da arziki,
Sai zuwa goma da rabi na sa hijab dina wanda ya sauka har kasa,
Najawo kofan dakina na kulle da key, tare da kashe duk wani na,uran wuta,
Dakin Anty Sadiya na nufa don in mata sallama,
Wanka tafito tana daure da zani atamfa jikin ta duk ruwane,
Da sallamana nashiga dakin gani na yasa ta wani daure fuskan ta,
Anty zan dan shiga nan makwabtar mu inyi kitso yanzu,
Ok kawai tace min,
Nima ban tsan mani komai ba daga gurin ta na juya na,fita,

****** ********** ******
Ina fita kofan get din gidan nai,wa anguwar kallon tsab, ko ina gidaje ne na gani na fada, masu matukar kyau sai dai wani yafi wan kyawo,
Wani gida na hango a gefen gidan mu ginan shi baikai na kowa kyau ba a layin,
Gidan nada iccen umbrella, a kofan shiga get din gidan, ba a,yi plaster bangon gidan ba,
Gidan na tun,kara,, a hankali, na tura kofan shiga cikin gidan wanda wani tsohon, gambun karfe ne ja,
Da sallama dauke a bakina na shiga gidan, wanda babu kowa a tsakar gidan sai, kayayya kin aiki, a waje, tsakar gida,
A hankali na kara yin sallama a karo na biyu cikin gidan,,
Ina tsaye daga kofa shigowa gidan,
Mutum biyu ne su ka karba min a,lokaci guda kusan tare su ka laiko kowa daga dakin shi,
Wata dattijuwa ce Baka ta na rufe da gyale ja,a kanta har kasa,
Wanda zai nuna maka cewa da ga gabashin Nigeria take, watau shiyoyin kasan maiduguri,,,
Sai kuma wani dan matashi yafi yaya Ibrahim di na shekaru,
Ban sheda shi ba amma shi ya shedani sai cewa yayi ah, Amarya ?
Naji ya nacewa amaryan da aka kawo gidan mutanen nan ne da ba ruwan su da kowa,
Mamaki matar keyi don irin kallon da take min yai matukan bani tsoro,
Hausan ta ba pure hausa ba ne sai cewa tayi,
Yarinya lafiya dai ?
Sai a lokacin nace, ina kwana ?
Daga gurin da nake na,ke tsaye saboda sabon, da nayi da yin gaisuwa ,
In dai mutum ya girmay ni sai mun gaishe ka, wanan dokar malam tsoho ne,
A sama sama ta karba min da cewa, lafia,
Nace don Allah ina tambayan gidan da ake kitso a wanan area ?
Magana tayi kaman a cikin yaren su sai naji ana kiran wata, Fattu,
Fattu fattu kira daya biyu mai sunan Fattun ta fito daga daki tana kokarin daura zanin ta da goyon ta a hannu,
Ganin bakuwa a tsaye tsakar gidan su mai dan filin da baifi tako uku ba yasa ta tsayawa muna kallon kallo,
Gaishe ta nayi tankar na san ta dama, wanan saurayin ne ya dauko min wani farin kujeran roba, yana cewa ki zauna nan,
Inda nake fattu ta iso tana cewa cikin sakin fuska,
Daga ina yar uwa,?
Daga nan makwabtar ku na ke nazo don Allah tambaya ko ina zan samu kitso, ?
Ki,tso yar uwa ?
Nace eh a hankali,
Gaskiya ni a cikin gari nake zuwa amma in ba mai yawa kike so ba zan dan gwada yi maki ki gani,
Awaje muka zauna batare da bata lokaci ba tafara min kitso,
Kitso mai suna suna SHADE tai mun yan kakana a kaina,
Rana guda ake sabo don haka sakin fuska daga bangare na da nasu yasa muka dan saki jiki da junan, mu,
Dan zaman da nayi a gidan na fahinci cewa zama ne na uwar miji da sarakkuwar ta,
Fattu ce ke auren dan ita wanan dattijiwan watau Maman Bi,u kamar yadda na ji suna kiran ta,
Sai kuma kanin mijin ita Fattun mai suna Hamza wanan saurayin masu zama kofan gidan mu,
Na kuma fahinci cewa zama sukeyi na fahitar junan su sosai,
Don girkin ranan Maman ,Bi,u ce tai girkin idan ta girka masu Birabisco,
Ta karbi girkin ne don kawai, a samu ai min kitso,
Dan yaron da Fattu ke goyo Maman Bi,u ta dauki yaron ta goya abayan ta don yabar uwar shi, tai, min kitso,
Na kuma fahinci cewa Maman Bi,u bata jin hausa sosai don haka da tafara sai ta sa yare a ciki,
Bayan mun kamala kitson ne ina kokarin kakabe jikina,
A lokacin ne ita wanan Dattijuwar Maman Bi,u ta kawo min wani abu a cikin bakin leda,
Karban ledan nayi da hannu bibiyu ina mata godiya,
Da harshen yaren su take cewa Fattu wai in dinga amfani dashi turare ne dan maiduguri dana daki da na jiki,
Fattu ce ke fassara min da cewa, wai tace kada in dinga zama babu kamshi a jiki na,
Koda yaushe namiji zai iya shakan kamshin matar shi,
Nai dan murmushi nakara cewa na gode kwarai da gaske,
Dubu daya naba Fattu a matsayin kudin kitso
Amma sai tace ita bazata karba ba,
Daga can bayan mu, mukaji muryan Maman Bi,u tana cewa, A,a,a kada Fattu ta karbi kudina,
Wai ina laifi gida nawa ke a cikin uguwar amma na shigo nasu kai tsaye
Murmushi kawai nayi na kara gode masu sosai sai dai da zan wuce,
Yaron Fattu da Maman Bi,u kebawa abinci na saka mai kudin a cikin rigan shi nace asai mashi Pampers,

A gidan mu nasamu kofan gidan a sake kamar yadda na jawo shi da zan fita,
Hakan ne ya sani gane cewa tun fitana Anty Sadiya bata fito ba ke nan balle ta rufe gida,
Dakin ta na nufa don in sheda mata cewa na dawo daga gurin kitson da na tafi,
Na samay ta a kwance tana ta sharar barcin ta hankali kwance,
Najawo baya cikin mamakin ta na juya zuwa sashe na,
A falo na hadu da Hamza dan gidan da na fito kitso dauke da kula a hannun shi,
Sallama ya kara yi na ansa mai cikin mamaki daga gurin da yake tsaye ta kofa yake cewa ,
Mama tace wai in kawo maki Biski ne wai idan tai maki tayi acan ba,aki ci ba,
Banda yadda zan yi dole na karba na,dauko wani kula daga kitchen na juye aciki,
Daki na shiga na debo sabulu da omo nasa aleda nace ya kaiwa Fattu, yace na gode
Shi kuma na bashi dari biyu saboda dauko abincin da yai min,,
Saman dinning table na aje abincin na wuce zuwa daki,
Har na zauna sai na tuna da maganar Anty Amarya da tace duk lokacin da nake da girki in tabbatar da cewa na gyarawa maigida dakin shi tsab,
Don haka namike da sauri don zuwa na fara gyarawa kafin lokacin sallah ya karaso,
Kofan shigowa gidan mu na jawo,na rufe da key don kada wani ya shigo muna,
A hankali nake hawa saman benen da nake zaton dakin maigidan ne a can,
Kasan,cewar yace rana na farko da zan fara shiga dakin nashi,
Nayi zaton cewa zan samu dakin a rufe amma kuma sai na samu abude yake,
Abin yabani mamaki don azatona rufewa ya ke yi ,
Gashi matar gidan na ta sharan barci abin ta batare da ta damu ko wani zai iya shigo masu ba,
Kayane birjit ko ina acikin dakin babu gyara ko kadan
Zanin gadon yai wani motsu, mutsu saboda rashin gyara,
Dole na cire hijab dina na shiga aiki ba shiri, na kai wani lokaci acikin dakin,
Don har sallah aciki na gabatar na tara kayan wankin da suke gefen tarshe a kasa guri guda, na daure cikin zanin gadon da na kwashe,
Kafin wani lokaci dakin ya koma kamar ba shi ba don nan take yafara kamshi,
Sai karfe uku na sauko saboda unders din dana tsaya wankewa,,
A hankali nake tafiya zuwa kasa, don duk jikina yana ciwo saboda gajiyan aikin da na sha,
Don ina zaton tun tarewan su gidan ba,a taba gyaran dakin ba,
Tun saura steps biyu in sauko na hango Anty Sadiya a zaune saman kujeran dining tana cin Biskin da Maman Bi,u ta aiko min da shi,
Tafiya na da taji yasa ta dago kai don taga kowaye,
Wani kallo mai kama da harara tai min tare da dauke kai, taci gaba da cin abincin ta,,
Acikin sakin fuska nace har kin tashi,?
Acikin wani irin murya dasasshe tace eh,
Kanta a duke tace,
A,she har kin dawo har kin girka muna abinci, yanzu da na farka na,fitone nagani,
Amsa na bata da cewa ba,nice na girka ba ,
Gidan da na tafi kitso ne suka aiko min dashi, dazun,
Nazaci cewa bazata ci gaba da cin abincin ba amma sai naga kawai tana ci gaba da ci,abin ta,
Ban zauna ba sai da na gama hada muna abincin dare,
Nai sallah sanan nazo na zauna don inci abinci, tare, dan hutawa,
Ba laifi don girkin tsohuwar yai dadi sosai, ashe abin da ya sa Anty Sadiya ta ci fiye da rabin kulan, abincin ke nan,

****** ********* ******
Malam tsoho zaune tare da yaran shi da suke shawaran don zuwa Abuja su taya dan su murnan samun karin girma,
Sai da tsohon ya gama sauraren shawaran da baba Samaila suka kawo mashi shi da sauran yan uwan shi,
Sanan ya dan nisa a cikin jin dadi ya ce gaskiya yaji dadin wanan shawaran badon komai ba,sai don a nuwa jikan nashi irin kaunar da suke mai,
Amma kuma ga shawara guda ya kamata a fadawa mahaifiyar shi ko akwai daga cikin yan uwan ta da zasu,
Haka kuma can 2urin ita matar tashi don kada sai mun tafi su zo suce basu da labari,
Kowa yaji dadin wanan shawaran da malam tsoho ya kara kawo wa,

Baba Buhari yagama zaiyanawa Mama Ladi sakon malam amma sai cewa tayi ita gaskiya babu wani dan uwanta dazata fadawa cewa ya zo a tafi,
Baba Buhari yace har yayan ki bazaki fadawa ba ko zai samu zuwa,
Amma sai mama Ladi tace ita fa kada aiwa yara gaiyya zuwa gida yana fama da kan shi,
Baba Buhari yace wai ke Ladi, shin yaron ga ke kadai kika haife shi ne da kike nuna min haka,
To bari kiji yadda kike ganin cewa zaki yi iko da shi haka nan nake iya iko dashi ina dai kyaleki ne kawai don ba hankali gare ki ba,
Ai baka sanin banda hankali sai na sa yaturo maku da yar ku gida tukun,
Yanzu haka ma ina tsan manin ya a ko ta dai can gidan da take zaune ne a sokoto,
Nunata Baba Buhari yayi da hannu yana fadin ji mahaukaciya,
Ai in,kinga aure???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?n yaran nan ya mutu to babu gudan su ne,
Daga haka Baba ya wuce abinshi dama malam tsoho ne ya matsa akan wai yazo dai ya shawarce ta don a fitar mata da hakkin ta,

****** ********* ******
Wanka nayi inda na tsala kwalliya kamar yadda Anty ta fada mun in dinga yi,, da zaran mun raba girki,
Tun daga haraban gidan falon, gidan har zuwa kitchen da kuma,sauran sassan gidan yau fes,suke, sun sha gyara,
Uwa uba kuma dakin maigidan da bai taba ganin an mai hakaba,
Kafin shigowan shi gidan su Hamza ne suka kamo mai TV daga cikin kwalin shi sabo fil,
Anty Sadiya wace ke zaune a falon tana kallo season film kamar kullun a wanan lokacin,
Ta dan dago kan ta, tana gani tai saurin kau da kai gefe don takaici,
Da Sallama yaya Abubakar ya shigo gidan yana sagale da corth din shi ga kafadar shi,
Gaba daya yau sai ya ga gidan duk ya canza ma a lokaci guda,
Kitchen na fito dauke da jug, din ruwan sanyi hade da cup,a hannu na,
Daidai lokavin da ya ke zama saman kujera a falon,
Idon shi kyam a kaina baya ko kyaftawa, Anty Sadiya wace ke kallon shi ta wutsiyan ido taja dogon tsuki,
Murmushi yaya ya sake saboda ya fahinci abinda takewa tsakin,
Sai alokacin yadan kau da kan shi gareni cikin zuciyar shi fadi yakeyi ita dai wanan yarinyar komai nata daban ,
Har tafiyan ta da kuma iya ladabin ta nadaban ne,
Sai da nakai kasa na nafara tsiyaya mashi ruwa a,cikin cup nace mai sannu da dawowa yaya,
Shiru ba ansa yasani saurin daga kai yana rike sa goshin shi tankar yana masa ciwo,
Hakan ya tabbatar min da cewa yana dan cikin damuwa ne kila alokacin,
Ga ruwan nace masa abinda ya sa shin firgigi ya dan dago kai, tare da yin dan takai,taccen murmushi a lokaci guda,
Sosai naga yasha ruwan tare da sauke ajiyan ziciya yayin da uake aje cup din saman table,
Dago kai yayi ya dubeni sosai sai yace a kasalance,
Kedawa kukai wanan aikin haka ?
Kaina na dan dukar a kasa ina wasa da hannun jug din dake gaba na nace ni kadai, tare da kara sunkuyar da kai na akasa,
A hankali yace ki daina wanan wahalan idan ina gida zanyi da kaina.
Don Bake kadai bace ke batawa don haka kinfa wahalan zai maki yawa,
Daga haka ya mike zuwa sama inda dakin shi yake,
Gaba daya sai yaga dakin ya canza mashi, don bai taba zaton abinda ke ciki suna da haske haka ba,
Da mamaki a fuskan shi ya tsaya yana karewa dakin kallon cikin sha,awa,

Wanka yayi yafito cikin kananin kaya ajikkn shi sai kamshi ke tashi,
Tv da ya shigo dashine yakira mai hakawa don a haka a daki na,,,,,



ZEEE MAKAWA YELWA
[7/29, 10:05 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
3? 8?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH-AS-SAMI,

Tv plasma, yar madaidai ciya ta bango yaya Abubakar yasa a ka hada min a daki na,
Naji dadin wanan abin da, yaya yai min Ko banza zan samu abokin hira a daki na,
A yan kwanakin da na yi a gidan yayan mu na fahinci cewa yanzu komai ya canza agidan nashi bakamar wancan zuwan da mukayi da yan uwa na ba,
Ba sai an fadawa mutun cewa yanzu yaya Abubakar yana cikin walwala ba da falala da nasarorin rayuwa,
Hakan kan sa in,zauna ina tunanen shi yaya Abubakar wani irin mutum ne wai ?
Ace duk wanan tatin dukiyan da Allah ya bashi tun yana cikin kurciyan shi amma bai damu da iyayyen mu na gida ba, sam,
Irin halin rayuwan da nasan su na fama da shi kamar may ?
Amma shi kuma gashi cikin jin, dadin rayuwa, ya tara wasu irin motoci har guda uku a farfajiyan gidan shi,
Sai kyali da daukan ido sukeyi da ka tunkari gidan,
Yanzu falon gidan da ke samun gyara ko da yaushe, shima abin sha,awa ne,
Amma kuma fa, iyayyen na can a cikin wahala sai sun samo abinda za,aci agida,ko wace rana,
Girgiza kaina nayi saboda takaici, da bakin ciki,
Wasu siraran hawaye suka zubo daga idona saboda bacin rai,
Gefen bayan hannu na sa, na,shafe dan guntun hawaye,
Aiki nake a kitchen amma ina tunanen yadda zan fadakar da yaya mun cewa mutanen gidan mu suna bukatan taimakon shi,
Babu fuska agurin yaya Abubakar dan iya fada mashi wanan maganan,
Haka naci gaba da aikina batare da na samu wani mafita ba daga zancen,

Yanzu duk wani girkin gidan da gyaran gida ni ke yin don Anty Sadiya tace wa maigidan bazata iya ba ita,
Don duk tayi sai ace ba a iya ci,
Ya yace ai ba, ance bane don har da ke baki iya ci idan kinyi,
Tun da naga sun fara wanan gardaman na mike tsam nabar gurin don bazan tsaya agabana yana wa mace kamar Anty Sadiya fadan girki ba,
Wani lokaci kuma yaya zai ce kada na girka komai zai bada take away akawo muna,

Yau ma kamar kullun kasan cewa ranan jumma ,a ce, tun safe na tashi na gyara ko ina na gidan nai muna breakfast lafiyayye,
Kafin


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login