Showing 42001 words to 45000 words out of 388021 words

Chapter 15 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8198

mara dadi, agare ta,
Wanan girkin yaiwa Abubakar dadi sosai don rabo da yaci irin wanan girkin tun yana yawan zuwa gida hutu daga makaranta
Wayar shi ce tai kuka, wanda hakan ce ta da katar dashi daga cin abincin da yake yi,,
Yadaga don ganin mai kiran nashi a wanan lokacin da yake kwasan girki mai dadi,
Salawatu ce ke kiran shi a lokacin don haka ya dauki wayan a cikin murmusawa,
Mikewa yayi tare da kallon gurin da mama take zaune tana mai kallon kurulla,
Tun a gaban ta ya dauki, wayan sai dai a cikin harshen turanci yake magana,,
Don haka mama wace bataji may yake cewa ba sai bin bayan shi tayi da kallo kawai,
Amna dai gabanta ya fadi don hasashen da zuciyar ta yai mata akancewa Abubakar da wata mace yake zance, fa,
Idan ko hakane gaskiya za a dauko wani sabon zance ke nan agidan,
Don tasan cewa da yawa daga cikin yan uwanshi dama uban,nen su zasuyi farin ciki da wanan abin,,,,

****** ****** ******
Zaune take da tarin littatafai a gaban ta tana dubawa,
Kanta yana dan saye da farin gyale wanda ta dan yane fuskanta da shi,
Bitan littafan ta takeyi saboda , jarrabawan su da ke kara gabatowa,
Don haka tai matukar mai da hankalinta akan karatun ta yanzu,
Shigowan shi kenan gidan ya hango Meena zaune gurin da take bitan karatun ta,
Ya fi tsayin yan mintuna tsaye agurin yana kallon wanan yarinyar,
Ko kifta, idanuwansa ba ya yi farat daya yaji son ta da kaunar ta sun shige mai zuciya,
Kai tsaye yaji zuciyan shi na bashi shawaran ya tunkare ta don ya ji ita ko wacece,
Kamar kuma ya juya zuwa inda zashi bangaren yayan nashi sai ya ji sam bazai iya ba,
Sabosa haka gadan gadan ya cike da karfin zuciya ya nufi inda take,
Meen wace take duke ,
Zuciyan ta ya bata cewa tankar akwai wani mutum tsaye a kanta a lokacin,
Daidai wanan lokacin ne ta tsinkayi muryan shi yana mata sallama,
A dan firgice ta kara dagowa da sauri tana kallon shi
Daga gurin da yake a tsaye ya zura hannayen shi duk biyu acikin aljihun wandon shi,
Idon shi a cikin nata yake cewa kiyi hakkuri pls don naga kamar nadakatar dake daga karatun ki,,
Cikin maganar da yake yi ne ya tako izuwa gare ta,
Gap da inda take zaune ya karaso, inda har Meena zata iya dan jin hucin shi,
Mamakine kwarai ya kama Meenat din don haka ta kasa ko da wani kwakwaran motsi don fargaba,
Don dai ita asanin ta ga bakin dake zuwa gidan uncle din ta ba,
Ganin kamar ba zai iya dakatawa a inda yake ba yasa Meena tai saurin mikewa don barin gurin,
Muryan shi taji cikin wani irin yanayi yana cewa
Kiwa Allah da son manzon tsira ki dan bani minti biyu pls,
Cikin rintse ido da jin abinda bakon yace ta tsaya agurin da take,
Muryan shi takara ji a karo na biyu yana cewa don Allah a nan gidan kike da zama ne ?
Da sauri Meena ta dago kai ta dube shi ta ce, a hankali,
"Eh,
Ya kara gyara tsayin shi yace to amma ban sankiba beauty ?
Beauty kuma inji Meena ?
Cikin wani irin daga gira irin na mazauna kasan turai ya ce yes beauty, mana,
Kin ko gan ki kuwa, takar ke ce kika halitta kan ki,
A fusace Meena dake zaune tun shigowar shi ta mike tsaye,
Fuskan ta a daure tankar bata taba dariya ba a rayuwanta,
Rayuwan ta yai mata bakikirin a take idanuwan Meena suka kada, zuwa ja,
do yazuba mata still yana kallon irin yanayin da ta sauya atake,
Cikin dakewan murya Meena tace wani ne ya aiko ka ka tambaye ni, ko ?
Cikin murmushi yace mata kinga nayi kama da wanda za,a aiko ?
Kanta kawar gefe guda daniyar ta dan gezashi ta wuce abinta,
Gyalen kan tane ya dan silalo daga saman kanta zuwa kafadar ta,
A take gashin kan ta dake daure da wani ribbon ya baiyyana a fili
Wani iri ya na yi ya shiga cikin dan lokaci kadan,
Sai tsayawa ya yi yana mai kara kallon wanan yar matashiy?r budurwa da idon shi ya ga nan mai,
Ganin zata wuce ne ya iya bude bakin shi yace ,,,,,,
Iam ALI-ABBAS, MAHMUD, KA,OJE,
Cikin wani irin kallo Meena ke kallon shi don jin Mahmud din daya ambata,
Tasan cewa daga family din nasu yafito saboda su fulanin Ka,oje ne, ma,zauna sokoto,
Daga haka Meena ta dan gwauta shi ta wuce abin,ta
Kamshin turaren jikin ta da ta shafa, black s,s ya shaka,
A hankali ya dan lumshe, idon shi, don kamshin yai mai dadi so sai, har cikin ran shi,
Part din da take na Anty amarya can tanufa inda ta,samu babu kowa a,dakin nasu na yara,,
Sunan Ali,Abbas take nanatawa a zuciyan ta tankar mai mamakin sunan,
Hayaniya taji a falo hakan ne ya bata tabbacin cewa masu gidan sun dawo ke nan daga unguwar da suka fita,
Sai kuma ihun da taji duk ya gauraye falon da gidan alokaci guda,

Fitowa Meena tayi don tai masu sannu da zuwa da kuma ganin may sukewa ihu haka ?
Daidai gurin da ta tashi a nan wanan bakon yake zaune ga dan hankicin ta da tabari da sauran takardun ta a hannun shi,
Ido suka hada daga fitowan ta wanda hakan yai daidai da kai hankicin ta a hancin shi yana dan shaka tankar mai mura,
Wani irin shu,umin murmushi ya sauke mata a lokaci guda,
Wanda tai tankar bata fahince shi ba sai cewa tayi a kasalance mummy sannun ku da dawowa,
Mummy wace ke ta murnan ganin dan kanin nata a lokacin sun kaure da harshen fulanci,
Tankar ba shi ne dan gayen da zaka ce banda turanci bai iya komai ba abakin sa,
Mummy tace yawa, Meena sannu ko don Allah ki taimaka ki hadowa bakona drinks da abinci pls,
Hannu ya daga cikin muryan nan nashi maikama da sallo ya ce,
No ki barshi kawai ki bani cool water in dan sha pls, ?
A hankali Meena ta juya zuwa dauko mai ruwan sanyin da yace,
Don keta ruwa masu mugun sanyi har sun fara alamar kankara Meena ta dauko mai a cikin freezer su,
Tai hakane don taga iyakar turai da karyan sanyi,
Abin mamaki cikin rashin damu taga ya balle murfin goran ruwan,
Kai ya kafa ya fara kwankwada har saida ya kai karshen goran yan kankaru kawai suka rage a cikin goran,
Sannan ya aje goran a saman table din dake gaban shi, kusa da littafin Meenat din,,,,,
?nty amarya ce ta fara mikewa don barin falon inda Meenatu ta mike don tabi bayan ta,
Wata yar sassanyar ajiyan zuciya taji Ali,Abbas ya sauke, sanan yace ina kuka samu wanan Beauty, Queen din a gidan ku,
Gurin da Meenatu take mummy ta dan kalla inda tace a cikin fulanci kar dai ka fara kace kana son ta don kasan diyan gwago Buriji, nan na jiran ka,
A take yanayin fuskan shi ya sake inda yake cewa, na fada maku, bana son wanan zancen sam,
Mummy tana dariya take ce mashi ai sai, dai yayi hakkuri kawai don duk family din su ba wanda bai san da zancen ba,
A dakin Anty amarya Meena ta samay ta tana cire dankunne a kunen ta,
A lokacin ta dan waigo tana kallon Meena tace kinga bakon turai ko ?
Brother din Asma,u ne a England ya ke zaune yana karatu bayan ya gama ya fara aiki a can,
Yanzu ya dawo nan Nigeria ne don gwaunati tana bukatan yai mata aiki,
Allah sarki inji Meena batare da tacewa uwar dakin nata komai ba,
Ta juya abin ta da nufin komawa dakin su da suke kwana,
Yar wayan ta Nokia wacce uncle din ta ya saya mata, don kiran mutanen gida,
Abdulhameed ne ya kirata a lokacin don haka sai bata karasa fita daga dakin ba ,
Nan ta tsaya a kofan dakin tana ansa wayan ce mata yayi ta fito gashi a waje don zai yi tafiya zuwa Lagos gurin saro kaya,
Komawa Meenan tayi dakin Anty a gaban mirror ta dan gyara fuskan ta sama sama,
A falo ta kara samun wa yan nan yan uwan junan watau mummy da brother din ta,
A cikin yanayin takun ta mai kama da na yanga, ta dan fito daga cikin gida don ta ratsa su, gurin da suke zaune a falon,
Sannu, kawai tai masu inda ta sa kai zuwa hanyar fita waje,,
Bayan ta, Ali, Abba's yabi da kallo inda ya kara ganin halittan ta da kyau, abin sai da yai touching din zuciyar shi,
Saboda irin yarinyar da yadade yana cigiyar samun irinta ke nan a kasar hausa,
Abdulhameed ta hango a yar farfajiyar gidan uncle din nata
Yana zaune a bayan motar , jikin shi saye da wasu kananan kaya, sai jacket da ya dora daga sama, wanda hakan ya nuna mata a cikin shirin tafiya yake
Hannun shi rike da keys din motar shi yana kadawa, a hankali,
A cikin irin takun nata ta karaso gurin da yake a kunyace
Tai masa sallama,
Wani irin kallon na can kasan ido yai mata yana mai sake murmushi a fuskan shi,
Sannu da zuwa, Dan uwa,
Hmm yar uwa sai kika gan ni yau a wanan lokacin kuma ko?
Murmushi Meenatu tadan sauke a daidai lokacin da ta dan kwanta kadan a bayan motan,
Kasan hakan ai daurowa ce da ban ganka a yanzu din ba, don nasan baku da lokaci a cikin irin time din nan,
Murmushi ya yi don jin abin da ta ce a lokacin don yasan cewa gaskiya ta fadi basu da time sam da rana sai dai da dare kawai,
Yace wlh kaya aka shigo muna dasu daga waje kuma wanan ne farkon shigowa dasu kasan,
Don hakane muke son zuwa mu kwaso su don mu samu su shiga da wuri,
A hankali tace Allah ya taimaka Allah ya bada sa,a da rabo na alheri,
Ameen ya Allah yar uwa,ta nagode kwarai da wanan addu,an da ki kai min ,
Amma insha Allah idan nadawo za mu shiga gurin hajiya ta don su gan ki,
Murmushi Meenat tayi gami da dafe bakin ta da sauri tadan dago kai ta kalle shi ida sukayi ido cikin ido,
Meenat tai saurin cewa rufa min asiri don Allah ai bazan iya zuwa gidan ku yanzu ba dan uwa na,
A, haba dai saboda may, ?
Meena, ta dan Allah mu ma bar wanan zancen kawai, don dai gaskiya ba zan iya zuwa ba,
Abdulhameed ya ji dadi har a cikin ran shi saboda irin wanan halin ya ke kara alfahari da Meena din ,
Sosai suka nutsa a cikin hiran da sukeyi don Abdulhamed yana ta kokarin kara, kafa,wa kan shi tubali, a zuciyar Meenatu,
Ali, Abba's ne ya fito daga cikin gidan uncle yana kokarin gyara kwalar rigar sa,
Caraf idon shi ya sauka akan Meenat da Abdull din wa yan da suka yi nisa a cikin soyayya,
Gaba daya hankalin sa ya koma akan su kallon Abdul yake yi a zuciyar shi ya, ce wanan guy din shine ashe Yarinyar nan ke, kin sauraron kowa,
Wani irin kishi ne wanda bai taba jin kwatankwacin irin sa ba arayuwar shi,
Wani gumi mai zafi ne yaji ya keto mai a goshi alokaci guda,
Don haka da sauri ya kau da kansa gefe guda inda yataka da karfi zuwa gurin da ya aje motar shi,
Zuciyar shi sai faman tukuki yake yi bai san may yasa ba yau ,yau da ganin yarinya har ya fara jin feeling a kan ta,
Duk wana abin da yakeyi Abdullahameed wanda ke zaune saman motar shi yana dan kada kafar shi a hankali,
Meena waye kuma wanan bakon da nagani agidan ku,
Gurin da Ali, Abba's yake yana kokarin ta da mota Meena ta dan kalla
Juyawa tayi gurin Abdull tace mai nima ban san shi ba yanzu nagan shi da zan fito,
Amma ina ga dangin matan uncle ne tunda har ya shiga cikin gida,,,,,



ZEEE MAKAWA YELWA
[7/12, 10:34 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
1? 9?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH- AL-A'ZEEZ,,,


Tun zuwan Abubakar sai washegari musalin karfe goma na safe suka dan samu kebewa da kakan nashi malam tsoho,
Malam tsoho yana saman shifidar shi na gadon kara da ke kofan gidan shi,
Inda Abubakar din ke saman tabarman roba a kusa dashi zaune,
Daganin su kasan cewa ganawa sukeyi na musan man,
Don irin yadda suke zaune mutum zai iya gane hakan tun daga nesa,
Yan maganganu suka fara yi akan irin al,amuran da ke gudana acikin gidan su,
Sai kuma zancen gurin aiki, shi da suka saba yi da malam din a,duk lokacin da yazo garin,
Daga karshe ne shi Abubakar din ya jefo zancen son ya kara aure saboda wasu dalilai da bai fadi ba,
Malam tsoho wanda ke daga kishingide ya dan murmusa don dama yasan da cewa komai dadin dadewa irin wanan ranan zai zo,
Shiru yayi bayan ya gabatar da bukatan shi ga malam din don jin mai zai ce a lokacin,
Malam tsoho yadan gyara murya a hankali cikin natsuwa ya kai duban shi gare shi yace madalla maisuna nayi murna kwarai da jin wanan zancen daga bakin ka,
Ina mai adduan kulun kafin in kwanta dama in ga zurian ka a duniya,
Murmushi Abubakar yayi don dai shi a gaskiya irin wanan zancen ba wai ya damay shi ba ne a rayuwan shi,
Abubakar ya cigaba da cewa don haka akwai wata wace muka shirya da ita acan Abuja,
Dama ita ce nake son ko za a shirya sai su Baba su samu lokaci su tafi ayi duk wani abinda ya dace ayi ?
Jin malam tsoho yai shiru yasa shi dago kai ya dan dube shi don jin abinda zai ce,
Ganin yanayin fuskan tsohon kawai yasa shi gane cewa baiyi na,am da zancen ba,
A hankali Malam ya kira sunan Abubakar din sai yai shiru na dan wani lokaci,
Can yace mai zai hana ka duba nan gida ko a,cikin dangi kasamu wacce tai ma ku shirya,
Ina ga hakan zaifi ma don kaga mu a nan din ai muna da kyawawan yan mata irin yadda zaka so,,
Abubakar ya dubi kakan shi cikin yar natsuwa da kuma mamakin maganar shi ya ce,
Malam nifa bazan iya aure daga nan gida ba don ban son fitina da kuma raini,
Katse shi malam din yayi da cewa ai ba dole a nan gida zaka zaba ba ka zagaya acikin dangi ka duba ko, don akwai kyawawa nasani,
Malam inji Abubakar banda ra,ayin auren mace don kyaun ta ko wani abu,
Ni kwanciyar hankali kawai nake bukata, arayuwa na ,
Malam ya girgiza kai kawai don jin may Abubakar din yace a lokacin cikin takaici,
Shike nan Jeka mai suna zan zauna uban nen naka muga yaya za,ayi su samu lokacin zuwa kan zancen,
Godiya sosai Abubakar din yai mashi saboda yasan cewa tunda ya samu kan malam tsoho ya gama da kowa agidan ke nan ,,,,,
Daga haka ya bar gurin malam din zuwa gidan sarakuwar shi hajja,

****** ******* ******
Baba Buharine zaune tare da mahaifin shi suna magana akan zancen da Abubakar din ya zo dashi na son karin aure a can birni,,
Sai da Baba buhari yagama sauraren zancen da mahaifin shi ke koro mai a kan dan shi Abubakar,
A jiyan zuciya yayi inda ya dago kai a fusace yace wa mahaifin shi,
Amma malam wana shawaran na a,yar darwa yaron nan sam bai yi ba saboda babu alheri ko kadan ga auren bariki,
Murmushin jin dadi Malam Manya ya sauke saboda fahintar shi da danshi Buhari ya yi ,,
Amma a fili cewa yayi wa Baba Buhari abi shi a sannu don kaga ai auren shi na fari yai muna biyayya ko,
Baba Buhari ya ce amma malam sai naga bai fi yaran gidan da wani kama ba ko,
Malam ya ce ai shi ya ce ba ra,ayin shi bane auren mace kyakyawa don haka kaga yana da nashi irin zabin ke nan,
Don haka sai kuje ku fara shirin zuwa nema mashi aure kamar yadda ya bukata,
Baba Buhari ya dago kai kamar wanda zai yi magana, a lokacin sai kuma ya maida kan shi kasa yai shiru don biyayya saboda yaga ba wasa ga zancen tsohon,
Kusan duk iyayyen su Abubakar sun yi rashin


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login