Showing 177001 words to 180000 words out of 388021 words

Chapter 60 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8290

6? 2?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH- ASH -SHAHEED


Daga kwance nake rigingine fuskana yana kallon Ac din dakin da ke sako min ni ima wanda ke sani cikin wani yanayi mai dadi, ga kamshi dake tashi na turaren humra, daki,
Duk da Motsin da naji na shigowa dakina a lokacin, bai,sani juyawa don ganin kowaye ba,
Ya iso gab da gurin da na ke, zaune a bakin gado,,, yana min wani kallo acikin mamaki,
Muryan shi naji yana cewa lafiya kike kuwa yau, ?
Batare da na kalle shi ba nake cewa, lafiy kalau nake,
Hmmm naji yace,
Kamar zai juya amma sai naji muryan shi yana cewa,
Breakfast din Baba Wadda fa,?
Banyi ba na bashi ansa a takaice,
Saboda may ? ya tambaya cikin mamaki
Nace don banice da alhakin badawa ba nagani , yau din,
May kike nufi da hakan ne,?
Ai bani kadai bace da alhakin wanan laluran ko
Wani irin tsawa ya daka min tare da cewa
Ke ni zaki gaya wa magana haka kai tsaye kina rainawa hankali ina fadi ki na fadi ke ma,
Ban yi magana ba sai hawayen da idona ke fitar wa shar a lokaci guda,
Ki tashi ki fita ki girka mai abinda zai karya idan ya dawo,
Daga haka yasakai ya fita dakin a fusace cikin bacin rai,
Ban ce komai ba sai kokarin mikewa da na keyi don zuwa kitchen din,
Na jawo dan karamin gyale na na rufawa kaina tare da gyara daura zani na,
Abinci lafiyayye na hada mashi tare da ni da su Anty sadiya,
Nasa saura a kula don nasan cewa zuwa anjima kadan yunwa zai iya zo min,
Nakai abina daki na gyara gurin da nai aikin a lokacin na juya daki na shiga wanka,
Bayan na fito ina zaune a bakin mirror ina shafa mai don yanzu ba zama yin kwaliya na keyi ba,
Ina kokarin zura wani dogon rigan pepper lace da akaiwa combination,da shi,
Yaya Abubakar ne ya shigo dakin yana min wani kallo amma fuskan shi acikin daurewa yake,
Tambaya na abincin sa saboda yana son fita, ban kai ga bashi ansa ba idon shi ya kai, ga abincin da na zuba a plate saman mirror don yasha min isaka kafin in zauna ci,,
A tsatsaye yafara kai spoon abakin sa,yakai kusan sau biyar da yaci a tsatsaye don da alama sauri yakeyi a lokacin,
Bayan ya aje spoon din,Ya dan juyo gurin da nake tsaye ina gyara dankwalina yana cewa,
Shi zai fita amma da Baba Wadda zasu fita don akwai inda zasu tare,
Murya ciki, ciki nace Yaya lokacin komawa na sokoto fa yayi,
Wani kallo naga yai min na yarinyarga fa kin rainani naci gaba da cewa,
Don da mun koma zamu tafi final teaching practices din mu, inha Allah,
Tankar baiji may nace ba don bai ma nuna yaji din ba sai sa kai yayi yabar dakin,, abin shi
Ganin uana fita baice min komai ba nabi bayan shi da kallo,
Yana fita daga dakin gaba daya nasa wani irin kuka mai tsuma zuciyan mai sauraro ta,
Ina cikin kukan da babu mai rarashi na sai Allah naji anshigo dakin,
Yaya Abubakar ne ya dawo dakin yana cewa inzo mu gaisa da Baba wadda kafin su fita,
Ganin da yai min na kifa ciki ina kuka cikin filo ya sashi tsayawa yana kallo na acikin mamaki yana cewa,
May ke faruwa ne wai Meenatu ?
Banyi magana ba ya kara jefo min tambaya da cewa,
An maki wani abune wai don tun jiya nake ganin damuwa a fuskan ki,
Nadan tsakaita kukana ina cewa ni gida kawai nake son komawa yanzu,
Murmushin takaici yayi tare da cewa bazaki ba idan kuma kika matsa min karatun ma gaba daya sai ince a fasa yin sa,
Don dama banga amfanin shi ba don ba dai aiki zakiyi ba balle, jin haka yasa na,
Kara gumzan kukana nayi yadda zai tayar mai da hankali,
Da sauri ya juya ya bar dakin hankalin shi a tashe bai iya cewa Baba Wadda komai ba sai kawai ya nufi hanyar fita waje,
Shima Baba Wadda yana ganin haka ya tashi ya mara mai baya suka fita tare,,,

****** ********** ******
Labarin ciwon Anty Sadiya ya iso Birnin Kebbi ko
A, take zance ya fara yawo cikin gari kala,kala, don kowa da abinda yake fadi,
Wasu suce ai kishiyoyine sukai mata su suce ai sherin uwar ta ce,
Ranan da mama Ladi ta samu labari hankalin ta ya tashi sosai, don kada iyayyen Sadiya suji suce ba,a dauki mataki akan ta ba,
Don haka bata tsaya bata lokaci ko ina ba sai gidan Aminiyar ta Hajja,
Don kada taji labarin ga mutane tace ai ba,a fada mata ba,
Amma bayan zuwan ta sai tai mamaki da taji Hajja na cewa ai mai sunan malam ya bugo mata waya
Amma ta fada, ma shi cewa, ai basai ta tura,kowa daga nan ba,
Don a can ai,basu rasa mutane ko amma haka dai zai sa in tura mashi mutun daga nan,
Wama yasan ko may ke damun ta balle adawo nan ana yadda zance kan karya,
Abinda mutum baiji ba bai gani ba ya taho yace shi ya gano acan,
Don haka ni banga abinda za,a ce sai an tura wata ko wani daga nan ba,
Hakane inji Mama Ladi tace amma dai duk da haka da daga cikin yan uwan ta a samu wata a turata, mata can ina ga haka zai fi,
Don fa ranan wuya sai naka ,
Hajja ta tabe baki tana cewa, haka ne amma gaskiya ni babu wanda zan tura daga nan don
Ai fanin, ku, da kuma mijin ta baku rage ta da komai don haka abar zancen tura wani, saboda tana samun kula daga mijin ta ai,
Tun da Mama Ladi ta gane cewa Hajja bata kaunar zancen kwata kwata yasa ta kyale wa,,
Sai suka fara hiran wani abu can daba don sam bata kaunar wanan zancen,
Don zancen yana tayar mata da hankali saboda bata san may zatayi ba i yanzu akai,,
Haka mama ladi tai sallama da ita batare da ta gane komai ba gare ta,
Ga warin hamman Dodo da ya isheta tun zaman ta,


Amma anan cikin gidan mu gidan malam tsoho sai zance ya canza da cewa,
Ai sherin Hajja ce duk yadda akayi ke bibiyan don tunda har malam ya saka bakin shi ciki, zance,
Zance yazowa Mama Ladi cewa ai nayi barin ciki, a kwanakin nan,,
Anan Mama ta fara fitina tana zage,zage tana masifa,
Ita Allah ya tsare ta, da ta hada zuri,a da zuri,an irin Baba samaila,
Da kuma mahaifiyana ita dole Maisunan malam ya sako Meenatu, tun bata kara yin wani ciki ba,
Yanzu shi mai suban malam har may yagani ajikin Meenatu da ya,rude shi har ya afka mata wai harda samun ciki,
Aiko amanan ta ya ishi cikin ya zube don dai Allah yagani ita bazata hada da irin mu ba,
Kuma wanan sherin na malan tsohone shi da yai uwa yai makarbiya harda hada aure tsakanin jikokin shi,
Yakuma rasa wanda zai hada wai sai yar Samaila da na ta,
Dan dama, dama dama ace a cikin diyan wa yanda suka fito ciki guda da Baba Buhari ne zata dan yarda,
Dole sai Yaya Abubakar ya turoni gida kwanan nan inba haka ba zai hadu da fushin ta,

****** ********** ******
Tafiya ya keyi zuwa gida malam saboda karbo wa Sadiya magani shi da Baba Wadda,
Wayan ce tai kara yaga ashe Mama Ladi ce ke kiran layin nashi,
Sai da ya bari kiran ya tsaya kamar yadda yake mata kulun sai ya kara kiran ta,
Mama bata bari sun gaisa ba tafara cewa Kai mai sunan malam shin batun ga da najiya da gaskiya na ?
Yace cikin tambaya mama wane batu ke nan kika jiya ?
Tace wai Aminati tasamu tagon kaya ?
Kwanan nan shin ?
Yace cikin dakewa hakane Mama gaskiya na yayi barin kwanan nan,
Salati ya Abubakar yaji Mama ta sake a lokaci guda,
Tana ewa da ka tona min asiri maisunan malam ace duk cikin zuka zukan matan ka ka rasa wace zakaiwa ciki sai waga yar ficikan yarinya,
Me kagani gare ta shin ?
Me zaka ganewa gurin wagga dagin bararo,
Nace maza ka dawo da yarinyar nan gida kafin wani sati ya zagayo,
Kajiya ko ?
Shiru yayi Mama takara cewa shin kaji abinda na fada maka ko ?
Najiya Mama ya bata ansa da fadar hakana, a takaice,
To kadai jita nan zuwa wani sati ka turo masu ita gida su san wadda zasuyi da ita,
Ya kara ansawa da fadin to Mama zanturo ta kafin lokacin,
Su na kashe waya ya furzar da iska daga bakin shi yana mai dafe gefen kan shi da hannun shi guda da bai tuki dashi,,
Ya ce kai, Mama ho, ba dai fitina ba Mama, don kawai ata da sabon fitina a gida, ta dawo da wanan zancen,,
Baba Wadda wanda ke zaune daga gefe yace to wai ita, Maman Mariya dake cewa haka shin, may ye hujjan ta,
Babu inji yaya Abubakar ya bashi ansa da cewa, kawai dai akidace ta su irin na mata,
Wayan shi dake a gefe ya laluba ya na neman nomba Uncle, dina,
Ya ce hello Uncle su ka gaisa a cikin mutunci da girmamawa,,
Yace Uncle dama ina son don Allah a taimaka min a school din su Meenat don a bata excuse saboda tace zasu fara exam gashi kuma tana nan on medication,
Uncle ya ke ce mai zai tafi school din na mu ya bin cika ya gani, inda yadda za,ayi,,
Sukayi sallama acikin mutunci tare da yiwa juna fatan alheri,
Baba Wadda wanda ke daga gefe ya dan murmusa ya ce kai o,o yanzu, ita maijiran dawowan Meenatu fa can gida, murmshi kawai yayi,
Sun karbo maganin kamar yadda kullun ake zuwa karba ,
Ya tafi Baba Wadda ne don yaga wuri saboda ya dinga zuwa karba don shi baida enough time,
Baba Wadda ne ke tunasar dashi zancen sadakan da malam tsoho ya cd su yi,
Baba Wadda yace ina fa yin sa a wanan kauyen zaifi don ka ga acan cikin gari babu yaran da zaka bawa,
Yays Abubakar yace gaskiyane Baba barin wa malam magana sai a sayo min,
Shawaran Baba Wadda yai amfani sosai gurin, don yara har sunfito fiye da tsanmani saboda sun saba karban sadaka a gurin malam sun san da yana sada shiyasa da anfara cewa Ana Sadaka,,, zasu fito dayawa karba,

****** ********** ******
Sallaman Fattu naji a daidai lokacin da nike daga baya ina shanya kayan dana wanke muna,
Dan saukin da na samu ita Sadiya bata amfani da kaya sosai,
Sai godiya take min a lokacin da nashiga kwasan kayan wankin nata a dakin ta,
Nawa na fara wankewa na shanya sai na fara nata na shaya a daidai wanan lokacin ne Fattu suka shigo gidan ita da Antyn Saloon,
Da murna na tare su muka shiga ta falo don zuwa part dina,
Salawatu tana zaune a falo tana kallon wani tashan wakoki ata faman raye raye a cikin sa,
Da mamaki take kallon Anty mai Saloon don batai tsan manin cewa nasan irin ta ba,
Natura kofan dakina da na sakaya lokacin da zan fita zuwa backyard gurin wanki,
Sai kamshin dadi ke tashi tare da sanyin Ac daya gauraye dakin ,gwanin ban sha,awa,
Ga dakin ta ko ina yasha gyara da daukan idi sai kyali yake yi,
Bayan sun zauna na nufi kitchen don in hado masu drinks din sha,
Cikin wani tiren silver mai ruwan golden na zuba hade da ruwa da cup,,,
Ina direwa naji Antyn Saloon tana cewa yanzu ita wanan ce kishiyar kaunata,
Fattu na fadin wallahi itace Anty wanan ai zata ma iya haihuwan ki
Sai suka sa dariya irin na wayayyon mata nidai na aje masu ina murmushi,
Na samu gefe guda na zauna ina masu sannu da zuwa a cikin murmushi,
?ntyn Saloon ta dubeni tana cewa, kaunata duk kin ramay wallahi,
Nidai ina daga zaune sai murmushi nake sake masu,
Kawar Anty ce tace to ke ko ai dole ta ramay bakin ji abinda ya faru da ita ba,
Anty tace wallahi fa a kasuwa muka hadu da Fattu shine nake tambayan ki sai take sheda min ,
Sorry ko Allah ya kawo sabon rabo nace Ameen Anty, ya kuke ?
Ya kuke ya shago da yara tai murmushi tace komai Alhamdullahi kaunata,
Sannu ko
Nai murmushi kawai tare da cewa Anty kusha ruwan don Allah dai
Munkai wani lokaci tare da su muna fira sai nake cewa Fattu ai na kusa komawa sokoto insha Allah,
Fattu tace wallahi Meenat ni ban kan so tafiyan nan naki don idan kin tafi sai gidan nan naku ya koma tankar babu kowa a cikin sa,
Nai murmushi nace hai Fattu wanan ai sheri ne gida da mata biyu zaki ce ya koma tankar ba kowa acikin sa,
Kedai kawai don dani kika saba shiyasa kike cewa hakan,
Fattu tace Allah yasa kada Yaya ya barki ki tafi muga tsiya,
Da sauri nace ba amin ba Fattu aima dole ne ya barni tunda, karatu nakeyi,
Tambayana kawar Anty tayi da cewa ina dayan kishiyar tawa take,
Nake ce masu aitana daki bata da lafiya, suka tausaya mata sosai sai sukace idan zasu tafi sai su gaida ita,
Daga cikin sabulan da yaya yake sigo muna ban komai da su na zuba masu a leda da drinks din su da basu sha ba,
Dakin Anty Sadiya muka shiga tana daga zaune tana son ta tashi tundazun ta kewaya
Fattu ce ta taimaka mata shiga bayin tare da tsayawa har ta karasa,
Sai na fara gyara gadon da ta tashi sudai bakin suna kallon mu daga gefe zaune,
Godiya Sadiya ke muna tana kokarin zama da kyat don irin yadda take jin jiki,
Dayar matar da Antyn Saloon tashigo da ita ce ke cewa may ke damun Sadiya ne,
Fattu ce ta fara basu labarin abinda ya faru da ita sai inda naga zata zure in gyara mata,
Sun matukar tausaya mata har suke zancen mai kishiya bata mutuwar Allah,
Suna cewa ai kila sherin kishiya ce yanzun haka kila aike akayo muna ni cikina ya zube ita kuma ai mata wani sherin,
Nace a,a ni cikina fada mu kayi da Salawa, lokaci guda suka hada baki suna cewa fada har ciki ya zube,
Fattu aka shiga labarta masu zancen da yadda na sha wahala sosai a daren har nai zuban jini,
Nace to aike Fattu jiya mun tashi yin wani nabasu labarin abinda ya faru a tsakanina da Salawa,
Gaba dayan su har Sadiya suke ce min daga yau in daina bin mutun har daki don yin hakan ba daidai bane,
Hakan zai iya sa komai gaskiyan mutum ya dishe saboda kamar ai takaka na kai mata, a lokacin,
Ni mutun ce mai daukan shawaran naga da ni in dai har shawaran mai amfani ne,
Don haka nai masu godiya nan suke bani shawaran cewa, idan na girka har ina bukatan abina to in kwashe in boye kada inbarshi a fili,
Sai matar guda ke cewa amma gaskiya kamata yayi a samu wace ke kula dake sai a dinga biyan ta ina ga zaifi,
Fattu yar rigima kecewa maigidan kuwa zai yarda sai matar ke cewa ai ita wallahi da zata ganshi zata bashi shawara,
Tace saboda kinga wahala takeyi fa sosai a haka dubi fa tundazun take son kewayawa amma babu wanda zai taimaka mata dole tana zaune,
Anty Saloon tace dagama dai sun samu Meenatu yariyan ce mai kirki da tarbiya in ba hakaba aida tuni an bare wallahi,
Sukai mata sallama mukafito daga dakin Anty Sadiya don in masu rakiya,
Motar Yaya Abubakar ce ta Parker sun shigo shida Baba Wadda,
Fattu ke cewa su Yaya sannun ku da zuwa Yaya kamar yadda nake ce mai ita ma haka take fada mai,
Su Anty Sallon suka gaidashi a cikin girmamawa, tare da mutuntawa,
Daya matar da ke tare da Antyn Saloon wace ban san sunan ta ba,
Take cewa maigida ashe kuma madam ba lafiya haka cikin daure fuska Yaya ya amsa mata da cewa Eh,
Sai take cewa a cikin rashin damuwa, gaskiya yakamata a samo mata supporter wace zata dan dinga taimaka mata,
Saboda inda ka kula abin nason wanda zai zauna a kusa da ita akoda yaushe,
Ok idan har ka yarda ni zan iya samo maku mace mutumiyar kirki don ta taimaka maku,
Yana tafiya batare da ya tsaya ba ya ke cewa sai najiki, yashige abinshi yabar a tsaye muna bin bayan shi da kallo,,
Murmushi nayi daga gefena nake cewa hmm anty kin dai


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login