Showing 309001 words to 312000 words out of 388021 words

Chapter 104 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8276

daga sautin shi yana cewa, kuna dai lafiya ko,
Nace Alhamdullahi yayana ya al,amuran yaudan kullun ya iyali kuma dai ?
Yace suna nan kalau sai faman fitina gaba na ne ya fadi dam Lokaci guda sai naji yace,
For god sake yanzu yadace ace wai Fatima ta kwaso yaranta zuwa gidan nan su zo duk su takurawa mutane an hankali,
Ban san lokacin da nace Subbahanallahi ashe Yaya har yaran sun girmane suna
iya haddasa fitina haka, ganin yadda na san su kanani da su,
Ya amsa min da cewa basu girma ba sosai don babban zata kai kaman seven years,
Nace Subbahanalahi haba dai yaya akan kananan yara har zaka tsaya rayuwanka yana baci haka a banza,
Katuna cewa fa yaran marayu ne san nan kuma fa diyan matan kane
Idan har ka rike su Allah ma,aiki Allah kadai yasan irin alherin da zasu zama maka a nan gaba,
Ai, yaro na kowane Yaya mutuwa ce fa taiwa mahaifin su gagawa badon ya so barin su ba,
Mamaki naji danaji yai shiru kamar mai sayraren maganan da nakeyi tankar zancen ya shiga zuciyar shi,
Sai naci ga ba da cewa musali wanan dan guda da Allah ya bamu wayan gobe a kasan shi,
Da sauri naji yana cewa Ke, is enough hakana zancen ya wuce tunda zai maida su gidane,
Nace haba Yayana dan Allah dai kada kaiwa matan haka raba Da da mahaifi akwai zafi sosai wallahi, baida dadi,
Tambaya na naji yanayi cewa, ina Big Man nace cikin dan lumshe ido saboda jin dadi kamar yadda duk wata uwa da ake nunawa dan ta kulawa takeyi,
Nace yana a bayan Dije yana barci tun dazun da tai mai wankan marance,
Tambayana yayi da cewa yana fatan muna dai lafiya dagani har yaron na amsa da cewa lafiya kalau,
Bayan mun gama wayan ne zancen da nai mashi akan yaran ya kara kashe mashi jiki sosai,
Sai cewa yake azuciyar shi ita wanan yarinyar wai wani irin zuciya ne da ita haka wai,
Ban taba ji ko ganin Fatima ta tambayi lafiyan wanan dan jaririn da Meenatu ta haifa ba,
Daga haka yakai kwance ta baya yana mai wani irin lumshe rikidaddun idanusan shi, yace,
Zan kokarta naga cewa ya tafiyar da komai na gidan nan kamar yadda ake so,
Daga haka ya sha alwashin sa shi, akan zai jajir ce ga duk wani matsalam yaran matar tashi,
Munyi arbain don haka bayan kwana biyu muka je yawo gaida yan uwa da abokan arziki tare da sister dina wanda hakan ya saka yan uwana jin dadin ziyaran da nakai ma su,
Kafin duk yaya yazo tun bayan dawowan su mama Ladi daga gabas sai kuma ciwo mai karfi ya kama ta,
Wanda hakan ya,saka yaya cewa a dawo da ita don taga likitan ta da take ganin tun farko ,
A gagauce aka kwashe ta sai Abuja gurin danta da surikin ta inda suka bar mu a gida hankali mu atashe, don ganin irin yadda take jin jikin ta,


ZEEE MAKAWA YELWA
[11/8, 9:32 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
9? 1?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH AL MUTA,,A,ALI



Ina mai kara baku hakkuri a rashin jina da bakuyi kamar da can baya due to some problems da fatan zakuyi min afuwa please,,,,


Zuwan Mama Ladi da Anty Mariya shi ya kauwar da komai a gidan don tana asibiti kwance saboda ciwon ta ya tashi a sanadin aiyukan da su kayi a saudiya can baya,
Sosai take samun kulawa daga yaron ta don a koda yaushe yana asibiti tare da su,
Sai dai idan lokacin aikine bazaka samay shi a tare da su ba,
Baba Wadda da Babana Hamza sune ke zaune dasu asibitin,
Sai Lawal mijin Fattu wanda ke ta kai da koma wajen sayen magani da yin test,
Abinci kuma yanzu a na kawowa, daga gidan Yata Abubakar din saboda duk wace keda girki, sai ta kawo abincin ta,
Gidan su Fattu ma ana kawo wa duk da dai ance su daina amma kuma sai suna riga gidan yaya Abubakar kawo wa don haka dole, aka barsu suna kawowa acikin lokaci,
Daban daban suka zo gaida Mama asibitin wanda hakan zai iya sa mutum ya fahinci cewa a kwai matsala a gidan,
Bayan zuwan da su kayi babu wace takara cewa zata zo duba jikin dattijuwan, duk da irin sintirin da suka ga Dan ta yana yi zuwa da dawo wa,
Hakan ba karamin batawa Yaya Abubakar rai yayi ba sosai, don duk kan su babu wace take zancen mahaifiyar shi ko nuna damuwar ta akan rashin lafiyan nata,
A cikin ikon Allah zan kira na tambaye shi lafiyan Mama yakai sau uku ko sau hudu a yini,
Hakan kuma nake yawan kiran Anty Mariya ko,Baba Wadda akai, akai, don jin ya jikin Mama Ladi yake,
Yau ma, gaba dayan su suna cikin dakin da take a asibiti kwance, yayin d? na kira layin Anty Mariya don inji ko yaya suke,
Tana sauri ta dauki wayan kada ta katse don bata san ko wacece ba ke kiran layin,
Tadauki wayan bayan tagane murya na tana cewa ayya Meenatu ta,
Na amsa da bata amsan cewa nice sai take tambayana lafiyan mu dana yaron ta, bayan na bata amsa naje cewa Anty yaya jikin Mama Allah yasa yanzu dai tana cin abinci sosai, ?
Tabani amsa da cewa yanzu kan Alhamdullahi don sauki ya samu sosai, gaskiya,
Mundan kai minti uku muna magana da ita na kashe wayan sai na kira Baba Wadda, sai Yayanane kiran karshe,
Baba Wadda ne daga gefen da yake zaune, yake cewa Allah, sarki Meenatu duk ta damu ko yaushe a cikin kiran wayya take,,
Mariya tace akwaita kan da kokarin kira gaskiya don dai ba,a awa biyu cif bata kiramu ba,
Yaya Abubakar kan shi na kasa yana dan buga kafan shi a saman ties din dakin a hankali,
Yaba saurarwn abinda suke cewa batare da ya dago kan shi ba da idon shi da suke a lumshe,
Yana jin wani irin yanayin da bazai iya cewa ga irin shiba yana fisgan shi ,
Bai san may yasa ba duk yai waya da Meenatu yakan tsinci kan,shi a cikin irin wanan yanayi, na shauki,
Muryan Mama Ladi ce ya katse mai abinda yake ji inda take cewa,
Ai dole ne taka kiran ku taji ko mutuwa zanyi don su ji dadin cin karen su babu babbaka,
Baba Wadda ya yace kai amma dai ke kan shi ko kina nan miza,a fasawa sallah ko hissabi,
Ke dai ba ai maki abin Allah a rayuwan ki, wallahi yanzu da ita da ka kiranki da wa yanda ke nan cikin gari, basu kira suji lafiyan jikin ki ba wayafi,
Bude bakin Mama sai cewa tayi, ai su don kan su duk abinda sunkayi,
Baba Wadda yace ita fa shin walle Ladi kiji tsoron Allah,
A,a tsoron ka nakaji dama bana Allah ba kudai kun ka sani dan ku akaji yanzu,
Don dai ni nagane cewa matsuwa ankayi aji ko wani hali nake a ji dadin baradawa,,,
Zubur Yaya Abubakar ya mike tsaye yana cewa Lawal mutafi ko, kada go,slow yai yawa a hanya,
Mama Ladi, tawani tabe baki tabi bayan shi da kallo tana mai kawar da kai,
Anty Mariya ce take cewa yau da wuri zaku wuce kenan ko ?
Daga gurin da mama take kwance take cewa aidole yace zai taf tunda an,dauko maganan yan gidan su,
Murmushin shi mai kara mai kyau da annuri yayi yayin da hannayen suke saye cikin aljihun wandon shi ,
Batade da yace komai ba yake masu saida safe don bazai samu shigowa ba yau da dare,
Mama Ladi tace kesan yau kila diyan zabarmawa ta ka sanwa (girki) shinassa zai wuce da wuri haka,
Dariya sosai mutanen dake dakin ke yi, sai Baba Wadda,ne ke bata amsa kawai,,
Sun bar asibitin tare, da Lawal cikin yan mintina zuwa gida gurin iyalin su, inda su kai ma su Mama saida safe,
A hankali yake tukin mota amma zuciyar, shi yana tunanen irin kiyayyan da, ke tsakanin Mama da Meenatu, haka,
A zuwa yanzu ya fahinci cewa shekaru ko girma ba shi ke sa wayyo ba ko fahintan halin kwarai,
Don dai Meenatu karamace sosai a cikin matayen shi amma sai ya fahinci duk ta fisu hankali da sanin ya kamata,
Yarinya ce mai tarbiya da hangen nesa fa sanin darajan babba a gare ta,
Yasan cewa don Allah ne take ya wai ta tambayan lafiyan jikin Mama Ladin ba yadda Maman take nufi bane,
Kawai dai tsabageren kiyayyane ya rufe mata ido akan yarinyar har ta kasa fahintar, halin su Sadiya, da sauran matan,
Lawal ne ya katse mashi tunanen shi da cewa, kai amma dai a tsakanin Mama da Maman big man akwai dan matsala nake gani,
A hankali ya murda sitiyarin motar shi tare da dan lumshe idanuwan shi cikin kiftawa,
Wasu miyau ya dan hade, masu daci da kauri, a makoshin shi yana mai dan lasan leben shi a hankali,
Bai tankawa Lawal sai da ya sha kwanan da zai kai su titin zuwa uguwar su ne yake, cewa,
Wanan ai ba sabon abu bane a gare mu domin abin ya samo asaline daga can gida a tsakan iyayen mu,
Lawal bai yi shiru ba sai cewa da yayi, gaskiya hakan ba dadi domin yanzu, kaga anfara samun zuria a tsakani,
Idan , Allah ya raya yaran suka girma suka samu hakan abin ba zaiyi dadi ba,
Duk zancen da Lawal keyi bai sa Abubakar tanka mashi ba sai tukin motan shi yake a cikin gwanin ta,
Lawal dai baiyi shiru ba sai cewa yake ai Mama ce bata fahinta ba amma sai naga ai Maman big man tafi sauran saukin al,amari,
Bawai da wani manufane take bugo wayan ba kamar yadda Mama take tsanmani

****** ********** ******
Na dawo Sokoto don zana jerabawata na karshe, wanda daga gare shi insha Allah nagama karatuna ke nan,
Mun zo da Aisha yar gurin Anty, Safiya kaunan Yaya Abubakar wace tun haihuwan Amir, take min lake,
Da taji cewa zamu wuce sai ta saka kukan cewa dole sai na tafi da ita,
Badon naso bani da iyayyena dole mukazo da yarinyar a bisa umurnin su Malam da Baba, Buhari,
Saboda sanin cewa Mama Ladi idzn Allah ya dawo da ita za tai jidali akan tafiya da yarinyar,
Banda wani matsala a gidan Uncle di na saboda muna samu kyakyawan kulawa da ga duk kan matan uncle din, nawa,
Mummy yanzu na fahinci cewa ta sauko sosai daga nuna min ko in kulan da tajeyi a can baya,
Don tana yawan dan jana a jikin ta sai dai nice ban yarda na sake jiki da ita ba sosai,
Yau ma kamar kullun muna zaune da Anty bayan Sallah ,isha,i muna hira a kan exam din mu,
Ina rungumay da Amir yana zukan nono tankar ba gobe , kuma barci yake a hakan,,
Amma sai jan nono yake kamar zai shanye dukka a lokaci guda,
Anty Amarya ta jefo min tambaya da cewa nasan da zaran kin gama exam Abuja zaki koma ke nan,
Da sauri na dago kaina ina mai kallon ta cikin mamaki, ,,Sai kuma na dukar da kaina kasa tare da dan gyarawa yaron rikon da nai mashi,
Nace cikin bata fuska gaskiya Anty ni nafi son a barni na zauna BK yafi man kwanciyan hankali wallahi,
Da sauri naga ta juyo gurin da nake zaune tana cewa cikin bacin rai, amma baki da hankali Meenatu,
Abarki BK ki gane may a can,?
Ko tsoron kishiyoyin ki kike jine da zaki wani ce bazaki koma can ba,
Na dan sunkuyar da kaina a kasa don yadda take magana na fahinci cewa ba wasa a cikin sa,
Anty Amarya tace, yanzu, ke har da bakin ki karama da ke zakice wai namiji ya tafi ya barki,
Baki san cewa tazara tsakanin mace da na miji yana kawo wani matsala mai muhin manci ba sosai,
Hakan ma,ga yayyan da zasu haifa yana kawo matsala don yaran mace sai su tashi babu wani shakuwa sosai a tsakanin su da mahaifin su,
Ina sauraren ta take cewa ai hakan ma zaibawa kishiyoyin ki dama kara shigewa mijin ku, don ita wanan mai yan agolan diyan sai diyan nata su samu shiga sosai ga mijin ku irin yadda naki basu samu ba,
Maganar da ta sani dariya ke nan don nai mamakin yadsa hakan zai iya faruwa,
Tace aiko sai kiyi mamakina don wallahi in fada maki gaskiya matan yanzu abin tsorone, sosai ,
Nace amma aini Anty sai nake ga kamar duk irin haka bai damun shi yaya din,
Mutumin da ko kai matar shi bawai ya damu da damuwar ka bane balle na wasu diya can,
Kanta ta kawar gefe guda, cike da jin haushina da takaici, don zance sai take jin shi kamar na mara wayyo,
Cikin wani irin murya mai kaushi naji ta kira sunana har sau kusan biyu tana cewa,
Barin fada maki gaskiya wallahi sai kinyi dan mara sosai yanzu,,
Domin yanzu zaman kwari yake a gidan ku don kinga wanan Amaryan taku da kowa ke ta zancen ta sai kin bullo mata ta baya,
Nan ta shiga fada min wasu abubuwan da na manta da cewa zan riskesu idan mun koma da zama guri guda, take ce min gani da karamin yaro dole sai na maida hankali sosai a gurin tsabta kada a barni a baya,
A marairaice kamar mai shirin kuka nace wallahi anty abinda nake yawan tunawa ke nan a raina yadda zan zauna a tsakiyan su da kuma goyo a tare dani,
Baki naga ta tabe tana cewa aiko hakan ko zaki zauna ba bubu kuma yadda zasuyi dake,
Nace gashi tun banyi arba,in ba Yaya ke fadin cewa wai na koma Abuja da zama kafin su dawo,
Harara ta watso min tana cewa aidama nasani don wanan mijin naku mai irin akidojin hausawan da sam bama zai lamunce da zamanki nisa da su ba,
A hankali na nisa ina cewa to Allah ya kyauta take ansa min da cewa ameen ya Allah ,

****** ********** ******
Mama Ladi izuwa yanzu ta samu sauki har an sallamota daga asibiti, tana gida tana daukan treatment, a hankali,
Sai dai kuma zama a cikin iyalin gidan yana da dan mishikila don babu wace ke wani nuna mata kulawa na ,
Don ina kwana ma har sai kusan karfe daya ko biyun rana take samu don kowa tana can cikin part din ta a rufe,
Mama Ladi da Anty Mariya sai kuma Baba Wadda wanda akai akai yana tare da su suna debe masu kewa,
Hakan yana wa Mama Ladi dadi a rai don su kan dan rage masu dare,
Duk wani tsana wanda da farko Mama Ladi taiwa, Baba Wadda izuwa, yanzu duk ta daina shi,
A sanadin Wanan zaman da sukayi a gidan dan ta namiji a cikin matan shi,
Sai dai da yake shi ba mazauni gida bane sai bai san wainar da ake toyawa a tsakanin matan shi da mahaifiyar shi ba,
Yau ma kamar kullun sun zaune zaman kunci babu mai kula da su ,sai ga daya daga cikin yaranFatima ta fito zuwa gurin da su mama suke a zaune,
Ba,afi minti kamar biyar ba sai ga uwar tafito daga daki acikin sauri tana neman yarinyar nata,
Duk da ta ganta zaune a can daya daga cikin kusuwar falon gurin da Mama take a zaune ita da Anty Mariya,
Da karfi ta fisgi yar nata daga zaunen da take tana mai dangwarar mata kai, cikin fushi,
Anty Mariya ce kecewa haba dai rabuda ita mana yarinyace ita cikin fushi ta juyo tanacewa saida na fada mata cewa kada fito falon nan amma saida wanan yariyar ta fito,
Sai kawai ta kara kaiwa yarinyar duka akai abinda ya tunzura Mama Ladi ke nan,
Ta so tayi magana amna kuma sai taja bakinta tai shiru don ta fahinci cewa, Fatima ta hani yaranta da zuwa inda suke, ne,
Sai bayan ta shige da yarinyar a cikin part dinta Mama suka sauke numfashi ida taci gaba da cewa Alhamdullahi don kowa yasan cewa ni ba manya bace,
Ida ina maita aida baki zo kin auri Dana ba har ki zauna dashi da sunan aure,,
Anty Mariya ce tace wa Mama haba ba haka take nufi ba kawai dai iskanci ne irin na yan zamani ta keyiwa mutane,
Wanan abin shine ya bakantawa Mama rai sosai har take cewa ita gida zata tafi ko bata ji sauki ba,
Dakyat Anty mariya ta bata hakkuri ta yarda su dakata har zuwa lokacin da likita zai sallamay su,
Bayan haka da kwana biyu kuma sai ga sabon sallon Salawatu wace ta girka faten doya tace wai shi mama zataci a matsayin abincin dare,
Ranan hankali Mama yai matukar tashi saida Baba Wadda ya shigo gidan ne ya kwantar masu da hankali,
Inda yafita yadawo mata da gasassan kaza mai mai da yaji,tare da abinsha,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login