Showing 195001 words to 198000 words out of 388021 words

Chapter 66 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8269

shi har Lagos,
Saboda hakane kuka jini shiru
Wacce duk ta turo kudi ga account din akai ta yawo dashi, nawa
Ina mai neman gafaranta da ta yafe min dani da wace tai wanan posting din,
Don ban san ku ba bankuma san sunaye ku ba balle ince a mayar maku, da kudin ku
Saidai ina mai kara baku hakkuri da kuma gode maku akan kulawan da kuka nuna min,
Wanan ma kawai ya nuna min cewa na kara godewa Allah na,
Wallahi idan har ina son abu ne ta mutanen arziki ba sai ne shelar kaina haka ba don ina tare da mutanen arziki wallahi fiye da tsanmanin ku,
Wa yanda sai dai naga sun turo min kudi bada sani na ba,
Ko kuma inji sun ce naturo da account dina kuma kada na rubuta sunan su har duniya taji sunyi don Allah ne kawai ,
Wanda ke da irin su shine zai je yawon bara kuma a median haba haba yan uwa mudinga yiwa kan mu adalci pls,
Ba dan abu kadan kaman anajiranka adinga kokarin bata ka ga sauran al,umma haka

Kidaure ki kara karantawa wanan page 66 din don wanda a ka turo wanda na fara ne kafin wayan ya fara harking,,, wanan na gyara editing din shi,,, na gode kwarai da kulawan ku gareni =?O?=?O?=?O?=?O?=?O?
Nagode Nagode Nagode kwarai da nuna kaunar ku a gareni, dafatan zamu fahinci may sakon ke nufi

Washe gari muka waya da Anty Amarya na ke sheda mata abinda ke damuna, duk wanan kwanakin,
Shiru tayi zuwa dan wani lokacin kafin tanisa tace ita shawaran da zata ba ni shi ne kan mu tafi da Fattu wani asibitin don a tabbatar da zargin, da mu ke yi,
Yau Yaya Abubakar bai fita office da wuri ba ya na kwance a dakin sa yana barci, abin sa,
Sai after eight na safe ya tashi inda ya kimtsa don fita,
Yashigo dakina acikin shirin fita yau tufafin hausa yasa ajikin, sa farare Sol
Wanda hakan ya kara mai kwarji da annuri ya fito wani babban mutum dashi,
Acikin shirina nake, alokacin ina zaune a bakin gadona sai dai cikin dan yanayi damuwa,
Wanda fuskana ne kawai zai sheda ma hakan don sign
Tun a kofa ya fahinci hakan don haka yake tambaya na cewa may ke faruwa ne wai, ?
Dole na kakaro annurin da dan murmushin karya a fuska na nace ba komai yaya zandai dan hutane kawai,
Yace OK ni zan fita amma daga can zamu tafi gurin mai magani ni da Sadiya,
Don anjima zan turo a daukar min ita mu tafi don haka, kada kikaga ban dawo da wuri ba please,
Nace Allah ya tsare hanya yaya Allah ya bada sa,a,
Ya amsa min da fadar amin
Sai kuma na dan marairaice murya, na nace, Yaya dama ina son in rokeka dan Allah zamu je gaida wata yar uwar Fattu dake asibiti,
Shiru yayi tare da kura min ido kamar mai tunane sai kuma naji yai gajeriyar numfashi yace OK,
But wa zai kai ku ne ?
Nai shiru zuwa dan wani lokaci da bai kai second ba nace ina ga kamar Napep zamu shiga,
No, no naji ya ce da sauri ka da kiyarda inji cewa kin shiga motar hanya Meenatu, please
Zanbawa Hamza da Baba Wadda key su kaiku, duk inda zaku,
Nace cikin jin dadi na gode
Yaya, ya sa hannuwan shi a cikin aljihun wandonsa ya cire kudi zasu kai kaman dubu goma yace Abawa mara lafiya idan mun tafi na kara mai godiya so,sai,
Yace ba komai sai kun dawo ke nan don Allah kada ku dade,,,
Nace cikin jin dadi tare da sakin fuska insha, Allahu baza mu dade ba,,

****** ********** ******
Malam tsoho daga gurin da ya ke lazumin dare bayan ya idar da sallah asuba, yake gurin a zaune har zuwa wani lokaci,
A haka barci ya dan fisgeshi sai ya fara mafarki mara dadi wanda zuwa yanzun nan shine mafi mafarkin da ya ke yawan yi,,
Firgigit ya tashi bakin shi dauke da addu,an neman tsari daga shedan da sherin sa,
Wanan mafarki ya matukar tsaya ma malam a rai don a,kullun yanzu sai ya yi shi a jere da juna hakan ne yasa hankalin shi tashi sosai,
Sai dai kuma yana tunanen cewa a tsakanin Baba Buhari da Baba Samaila wa zai fadawa wanan zance,
Don a iya binciken da yayi, gaskiya abin akwai daure kai a cikin sa da tashin hankali,
Don haka yake shakkun fadawa iyayyen mu don baza su iya daurewa ba in har sun ji may ke nan.
Don yasan sai sun dauki mataki akai, saboda babu wanda zai iya jin cewa dan shi na cutuwa ya sa ido ga harkan,
Don haka yai shawaran daukan mataki a asirce ta yadda babu wanda zai iya ganewa, hakan
Bai wani dauki dongon lokaci ba ya fara kokarin ganin cewa, yafara aiwatar da shirin shi,
Shi bukatan shi ya samu inda hali ya warare matsalan batare da rayuka sun baci ba akai,
Wani aminttacen yaron shi shine ya ba wani abinda zai tafi ya watsa mai a bayan gidajen su da dare,,
Inda ya ja kunnen mutumin cewa kada ya yarda wani ya gan shi a lokaci,
Mutumin ya ce, insha Allahu zai kiyayye kamar yadda malam din ya bukaci a yi,
Ba bata lokaci, ya mashi godiya tare da barin malam din kafin jama,a su taru gurin malam din,,,

****** ********** ******
Tsaye nake a gaban mirror ina kara gyara zaman gyale na, dana yafa wa jikina,
Sai da na tabbatar da cewa babu sauran guri ko kadan, da zai baiyyana a jikina,wa
Kamshin nake kamar wata diyar shuwa, saboda irin asir tatcen kamshin dake fita min ajiki,
Ga shi sai wani dan haske danaga na kara a fuskana tare da jikina sai dai na dan ramay kadan,
Sai da na tabbatar da cewa na kashe kayan wutan dake daki na sai na jawo kofa na nasa mai key ,
Dakin Anty, Sadiya na fara shiga, inda na samay ta tanawa Ramatu sababi wai ta zubar da ruwan da ta shafa mata magani a kasan daki,
Gurin da ake cewa wai ruwan ya zube na fara kai idona sai naga baifi ko spoon biyu ba ma yawan shi,
Sai kawai naji banji dadin irin yadda na samu ta na zazaga mata masifa a kai ba,
A hankali na ce Anty don Allah kiyi hakkuri kila acikin rashin sanine ta zuba mata ruwan,
Sai cewa Anty Sadiya tayi a hassale ita makauniyace da bata, gani,
Shiru nayi saboda abin bai min dadi ba wallahi don dai a gaskiya Ramatu mutunce mai dadin zama,
Gata bata da keta, tana aikin ta yadda ya kamata don ma harda wanda ma ba,a sa ta ba tanayi,
Sanan ita anty yanzu idan Ramatu tai fushi ta wuce wa zai dinga mata irin wanan da wainiyar, datake yi da ita,
Na juya gurin Anty Sadiya nace zan fita tare da Fattu zuwa gaida wata yar uwar ta da ke asibiti,
Allah ya sauwaka kawai tace min batare da takara tankawa ba, ta ma kauda da kan ta gefe cikin bacin rai,
Ita ma Ramatu nai mata sai na dawo sai take, ce min ai ita,ma gida zata tafi ta dan zagayo, su yau,
Sai zuwa dare zata dawo saboda yau Anty tace, mata zata tafi anguwa,,,
Nace to Allah ya dawo da ita lafiya ni kan nasa kai na fita abina,,
Mun dan kai dan lokaci a gidan Fattu tana kimtsa gidan ta,
Nai mamaki kwarai ganin motar da Yaya Abubakar ya bayar akai mu anguwa dashi,
Baban motar shi ce da ya ke fita da ita idan zai fita zuwa wani muhin min guri, ita ce nagani Hamza ya jawo ya Parker a kofan gidan su,
Daidai fitowan mu ne zamu bar gidan su Fattu sai,ga Ramatu, ita ma tafito, daga gidan mu tana tafiya zuwa inda zata samu Napep,
Na cewa su Baba Wadda mu dan dakata mu dauke ta idan sun aje mu sai su kai ta gida,
Ramatu tana ta zabga muna godiya tare da cewa Fattu tana gaida mai jiki,
Wani asibiti da ganin sa na kudine muka nufa har ciki su Baba Wadda suka kai mu
A kusan tare mu ka shiga da motar likitan asibitin
Inda yabi motar mu da kallo har zuwa inda muka tsaya muna fita ,
Na ciro dubu biyu a post dina na ba Ramatu nace ta sai wa yara tsaraba,
Ta fara jero min addu,oi yadda har kai na ya dau zafi, don yadda, take cewa Allah ya kara rufa maki asiri hajiya Allah ya baki zuria mai albarka,
Allah ya haushe ki sherin makiya gida da waje
Na amsa da fadin amin ya Allah Ramatu, na gode sai kin dawo ke nan,
Na bude kofan mota na fita don Fattu ta riga da har tafita ko a lokacin,
Ina fita sukai ribas suka bar gurin zuwa kai Ramatu kamar yadda na umurce su da yi,
Baba Hamza ne ya fara magana bayan sun dan fita daga get din asibitin,
Gaskiya Hajiya Meenat tayi a rayuwan ta wallahi, babu ruwan ta ita
Don inda ace wata ce ita da wallahi bazata ko baki lift ba balle har ta ce a kai ki gida cikin wanan zungureri yan motar tasu,
Motar may gidan ne fa da yake yawan shigan ta idan zai fita,
Ramatu tace ai al,amarin Hajiya Meena a kwai sha,awa don sam bata da matsala, ita,
Baba Wadda ya ce ai duk uwar ta ce ta kwaso, don haka mahaifiyar ta take a gidan mu babu ruwan ta da babba da yaro a gidan duk nata ne,
Har zuwa lokacin da suka aje Ramatu a dan gidan su a cikin Garki village,,,

****** ********** ******
Kamar yadda muka ce haka muka fara yi muka shiga gaida wata yar yaren su Fattu, dake asibitin, yar yaren su ce matar,
Sai muka fito mu ka yanki kati, Allah ya tai make mu babu mutane da yawa a gurin sosai a lokacin,
Ba muyi wani dadewa ba sai kawai ga layi yazo a kan mu,
Fattu tace in shiga ni kadai don ba,a shiga mutum biyu, aciki,
Naiwa likitan bayani wanda na ga kamar yana min kallon sani, sai yace ai min photo, gwaji a gani,,
Ciki ne dan wata kusan uku, da kwanaki a kwance cikin mahaifana,
Sai aka rubuto min result na dawo wa likita da shi don ya duba,
Nan likita ya ke min murna ya na kara nanata min,cewa , ciki ne na wata uku, don haka sai na bishi a sannu saboda ina bukatan bed rest zuwa wani dan lokaci,
Wani irin dadi ne naji ya ratsa min zuciya abinda ya sa har na dan rutse idona a hankali don jin dadi,,
Na fadawa doctor zancen miscarriage din da akace nayi a kwanan baya,
Ya ce duk wanda yace miscarriage ne karya ne cikin dai ya dan so ya tabu a lokacin amma ai bai fita ba ,,
Sai kuma in har dama twins ne aciki dama ace dayan ya fita ya bar dayan,
Wani irin rutse idona na yi don wani yanayi daji cewa wai twins a cikina,
Doctor ya rubuta min magani yace in kula da zancen bed rest din don kada a samu matsala,
Fitowa na yai daidai da dawo wan su Baba Wadda daga gurin kai Ramatu da su ka tafi,,
Kafin su iso gurin da mu ke ne, nake wa Fattu bayani abinda, likita ya ce da kuma abinda zan kiyayye,
Fattu tace cafdi, ashe kuwa za a samu matsala da maigidan ki don dai idan har kince, bazai sani ba da farko,
Na nisa tare da dan langabe kaina tare da wani irin ajiyan zuciya,,
Yanzu yaya ke nan za a yi Fattu don ban san may zance ba ma, nake tambayan Fattu,
Kawai ki fada mai zaifi Meenatu, don ni wallahi, banga abin rufewa ba acikin abin farin ciki,
Na dan nisa nace Fattu ai ba wai, ina boyewa ko rufewa bane. A,a kawai dai irin yadda naga rashin imani a fili a gurin Salawatu shi yake bani tsoro,
May zata iya yi maki wanda Allah bai tashi yi maki ba Meena, ?
Kawai ki fadawa Yaya mu kan mu ga irin farin cikin da zai yi yau, na girgiza kai na
Nace sai dai na kira Anty Amarya don inji abinda zata fada min, kinga naga kamar hakan zai fi,
Ta,ce eh gaskiya ki fada mata din, Muji may zata ce akai, nace OK ,,
Mu ka dan taka zuwa gurin motar mu, ida su Baba Wadda ke ciki suna shan kira,a
Tun wanan lokacin sai na ke jin wani kasala yana rufe min ido na a hankali,
Mun biya gurin Anty mai Saloon mun gan ta mu ka dawo, a gajiye gida inda nai sa,a har lokacin Anty Sadiya tana gida basu tafi kauyen da zasu ba,,
A gagajiye na is dakina duk jikina yai min wani irin nauyi, a lokacin tankar nai wani aiki mai yawa,
Sai da na dan samu guri na kai kwance a hankali idona a lumshe ,
Ina tunanen yadda zan bullowa al,amarina akan bed rest din da aka bani
Wayana call ke shigowa don haka na mike zaune ina lalube a cikin jakana,da nadawo dashi na aje saman mirror na
Yaya Abubakar ne ke kirana a lokacin na dauka cikin kokarin sake ajiyan, zuciya ta,
Assalamu Alaikum yaya, yace Amin wa,alaikis salam,
Meenat kuna ina ne yanzu, ?
Na,amsa a cikin dan lumshe idona da cewa ina gida, Yaya,
Sai naji ya sauke yar ajiyan zuciya wanda ya sani jin wani irin sanyi a raina,
Har kun dawo ke nan ko a she ba wani dadewa zakuyi ba ke nan. ?
Nace eh Yaya daga can na dan biya gurin Antyn Saloon na karbo sakon turaren da na ba ta,
Yaya Abubakar yace ya naji muryan ki kamar you are wick ?
Nai murmushi mai sauti na ce ina dai jin wani irin kasala da nauyin jiki ne yaya,
To may ke damun ki ne haka na ce ba komai yaya may be ko period zaizo min killa,
Sai naji yace OK a cikin murya mai nuna rashin naam akai,
Ya ce dama na turo Bado driver ne ya dauko Sadiya shine nake tunanen cewa ko ba ku dawo gida ba har zuwa yanzu kada abar gida babu kowa,
Na amsa da cewa na dawo tun dazu ai Yaya ya ce kin kyauta ashe gobe kina son ki fita,
Murmushi kawai nayi ban ce mai komai ba yace ok sai mun dawo ke nan
Nace Allah ya tsare a je lafiya adawo lafiya yaya ,
Na kashe wayan na kwanta ina tunanen barkatai a cikin zuciya na,
Ba komai na ke tunane ba sai cikin da akace wai ya kai kusan wata uku, three months,
Na kai hannuwa a hankali a sama cikina tare da lumshe idona a hankali a cikin jin dadi,
Na shafa cikin tsoro naji don wani motsi da naji kamar wani abu ya canza position din zama,
Da sauri na sauke hannu na ina mai dagowa daga kwance har daurin dankwalina yana faduwa a saman filo,
A rai na nace ke nan akwai abu mai rai a tare da ni yanzu ke nan
Don dai ban taba jin irin haka ba, atare da ni, Allah Akbar mairai acikin mai rai ke nan sai Allah
Addu,an da malam tsoho ya taba ba ma anty, Rukaiya a gaba na lokacin ina yar matashiya,
Ya ce ta dinga yi tana shafawa, a saman cikin ta, duk lokacin da ta samu time, din yin hakan,
Lahaula, wala quwati ina billahi aliyal,azeem, 7 time's,
Ko kuma hasbunallahu wani,imal, wakeel shima kafa bakwai,
Da sauri na karanto, wanan adduan kamar yadda naji ya umarce ta da yi, na shafawa cikin na,wa daga sama zuwa kasa
Daidai gamawa, wanan addu,an nawa naji muryan Bado driver yana sallama har tsakiyan falon mu,
Na jawo mayafina na nufi kofan daki ina cewa ya bari a kirata tafito,
Nasamay ta tana kokarin aza mayafi a kanta ina daga tsaye kofa nace mata ga Bado driver ya iso ,,
Tana fitowa na jawo kofan dakin ta nasa mata key kamar yadda naga tana kokarin yi na kada mata a cikin hand bag din ta,
Har gab da fita falon na rakata inda na tsaya ina mata adawo lafiya Allah ya tsare hanya,
Batare da ta juya ba tace Allah ya sa,
Ban koma daki ba bayan wuce,wan su sai na dan tsaya don neman abinda zanci,
Na koma daki nai alwala don lokacin sallah ya gaba to,,,
Ina zaune a gurin da na idar da sallah wayan Anty Amarya yashigo take tambayana ko na samu zuwa asibitin, ?
Na fada mata duk yadda akayi a sibitin da abinda likita ya umurce ni dayi,
Anty tace min babban magana Meenatu,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login