Showing 264001 words to 267000 words out of 388021 words

Chapter 89 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8220

Amsan farko da yafara zo min arai shine irin yadda suka zuba soayyan su yayin samartakan shi da ita,
Saboda son da take mai ko mu yan uwan shi mun sha gata a gurin ta sosai a lokacin,
Don haka mukan tafi gurin ta da sunan yini don kawai ta dafa muna taliya da jajage mu ci, muna jin dadi muna murna,
A hankali na sauke a jiyan zuciya ina cewa insha Allah bazan sake sawa kaina damuwan da zai wahal dani ba a rayuwata,
Wanda nake yi a kansa bai ma san ina yi ba shi don abinda yai niya ba fasawa zai ba,
Bayan Anty Samira ta fada min cewa duk iyayyen mu sun halarci daurin auren da su akayi,
Kenan duk suna bayan Yaya Abubakar gaba dayan su babu wanda ya damu da damuwana ke nan,

****** ********** ******
Hajiya Mama ce ta kawo shawaran ce wa a kai ni gurin Sa,adatu mai kwalliyan mata, dake garin sokoto a Sama Road,,
A can gurin wanan matar na ga abin mamaki sosai don mata na samu yan gayu group group ana masu training din abubuwan rayuwan yau da kullum,
Ko wace da abinda tazo yin training a gurin wasu
don girki, wasu dan gyaran gida masu koyon dressing daban, sai kuma wani group dana ga mata a zaune ana masu lacture akan zama da kishiyo yi,
Tirkasa ni da yake matar yar uwar Hajiya Mama ce,, sai na samu training din abubuwa da dama, agurin ta,
Ni kaina nasan cewa na samu canji sosai a gurin wanan training din da nai sati guda ina zuwa sauraro,
Da yake ina da ciki sai aka kara min haske akan zaman mace mai ciki da mijin ta,
Tun da daga cikin wata daya, har zuwa wata tara akwai wani hikima wanda mace zata dinga yi wanda zai sa mata kara shakuwa da kula agurin mijin ta,,
Wani irin mamaki naji a yayin da take min lectures tare da fada min irin abincin da ya kamata na dinga yi da kuma ci,
Tsaba na koma wata irin first class, ni kaina nasan cewa na canza sosai
Ga dinkuna irin na alfarma da akai min wanda Anty tabayar daga cikin kayan lefe na aka dinko min,
Kitso da lalle mai kyau ba bijin ba na siffa shi aka tsara min a kafa da hannaye na ga kitson an yarba min su tsab a kaina,

Kamar yaddayace zai shigo haka din ne kuwa don sai da marance lis ya iso garin sokoto,
Saboda sun dan tsaya kai ruwa rana da Salawatu wace ta aza mai fitina da jidali agida tun daren jiya
Da Antakty Sadiya suka farayi don saida taga cewa yai nisa sosai baya jin kira dole ta kyale shi ta sa mai ido
Da farko mun dauka cewa bazai samu shigowa gurin mu ba, don munga yamma tayi sosai a lokacin
Amma sai gashi duk da yamma yayi sosai a lokacin bai wuce ba sai da ya karaso gurin mu,
Ina saye a cikin wani dogon riga dinkin Dubai gaban rigar jallabiya ce bayan ta atamfan super,
Gaban an daza mai stones har kasa, sai daukan ido su keyi, inda akai dan wani design din wuta da silver akan shi aka daza stones din akai,,,
Takalmana plat shoe's masu kyau suma da daukan ido,
Turaren kamfanin Oud, sune na fessa da murzawa tako ina sai kamshi ke tashi,
Daga gurin da yake a zaune a falon mu bayan Anty ta zagaye shi da kayan abinci na alfarma,
Na tako a hankali nake tafiya tun fitowana mukayi arba da shi nava ya sauke wani irin ajiyan zuciya tare da lumshe idanuwan shi a hankali,
Ya laso leben shi da harshen shi tare da dan shafa fuskan shi,
Gaba daya yaga na canza mashi a idon shi ga kuma cikina wanda ya turo rigana yaba da style shima din,
Direct gurin shi na nufa kamar yadda Hajiya Sa,ade tai min umurnin da inyi mashi, idan yazo ko ya dawo daga wani guri, either aiki ko tafiya,
Tace hakan yana kara wani irin kusanci mai girma a tsakinin miji da mata wanda sai Allah kawai yasan wanan sirin,
Tafiya nake yi kamar kifin, tarwada ta samu ruwa, ni kaina ban san cewa zan iya wanan tafiyan ba sam,
Ina zuwa gurin da yake zaune sai na dan rakwafo duk half part din jikina a na sa ,sai na dan rungumo shi tare da kai mai kiss a kumatu irin na matan larabawa ina cewa cikin wani irin murya,
Sannu da zuwa Sadauki yaya hanya ya aiki da sauran jama,a,
Kamar rada na rada mai a kunnuwan shi, a hankali nake kokarin zare jikina daga jikin shi,
Wani irin shock yaji yayin da ya hankalta ina dan janyewa daga jikin nashi,
Cikin lumshe ido yake cewa is that you Meenat ?
Nai murmushi tare da dan kara juyawa da kyau cikin style, ina cewa ni ceman Saudaki,
Ina jin lokacin da yai wani sauke ajiyan zuciya, tare da lumshe idanuwan shi yana shakan kamshin jikina da tufafina,
Da hannun shi yai min alaman cewa inzo zuwa gare shi inda ba musu na juya a hakali zuwa gare shi din, cikin wani irin tako da rausaya,
Yana daga, zaune na nufe shi inda a hankali ya mika min hannuwan shi, yai min mazauni a cinyar sa tare da dora hannayen shi saman cikina, yana dan shafawa
A hankali naji cikin yai wani irin motsi kamar wanda yasa may akeyi hakan ya nuna min cewa shima da ya dora hannaye, a saman cikin yaji motsin ke nan,
Sai naga a hankali ya kara kai hannuwan shi a gurin da abin ya koma yana cewa
No, no no my friend don't run away , from me,
I want to hear much about, you,
Murmushi nayi tare da kara man,na jikina anashi muna saukewa junan mu numfashi a hankali,,
Mun danyi nisa acikin irin yanayin da muke ne, sai na tsinkayo tafiyan mutum zuwa falon,
?nty Amarya wace ta nufo falon kawo mai sako ya kai wa Mama na da saurin ta juyawa komawa ciki don ka da mu ganta
Saidai bata sani ba cewa har mun gata ko don haka da sauri na sauka saman ciyan shi ina dan murmushin jan aji,
Cikin dan daga murya na ke cewa Anty iso mana tace, a,a zo ki karba don Allah ki bayar akaiwa yayan BK,
Namike a hankali daga saman kujeran da na koma na zauna zuwa karban sakon,
Yayin da Yaya Abubakar yabi bayana da kallon sha,awan da ya addabe shi nawa,
Hakan yayana duk ya bi ya, sukurkuce har sai da dare yai masu a kafin su tafi ga hanya, ba kyau sosai a lokacin,
Na gane nufin shi so yayi ya kwana amma sai nake ce mai ai yanzu mutanen gida zasu damu kuma ya fada masu cewa yana hanya nasan cewa anyi mai girke girke yanzu haka,
Sai yake cewa to na shirya mu tafi tare Birnin Kebbi ko,
Nazaro idanuna waje ina cewa haba dai Sadauki ai sai mutane suce banda hankali ko ban san ciwon kaina ba,
Ango zai je gun amaryan shi sai angani kishiya gotai gotai dani na biyo shi a baya,
Hmm yace tare da girgiza kai ya mike a kasalance yana cewa na dai gane cewa yanzu Anty ta kara canza min ke again,
Nace saboda mai babu wani canzawa da nayi idon shi daine ke ganin hakan,
Amma ba wani canzawan da nayi murmushi kawai yayi min bai iya futa komai ba abakin shi, amma,
Yanayin shi ya nuna min cewa Allah kadai yasan abinda ya keji a cikin ran shi gamay dani, a lokacin,
Saidai kuma abinda na kula dashi shi ne dan zaman da mu kayi dashi a falon Fatima ta bugo mai waya ya kai sau shidda ko fiye da hakan a lokacin,
Fahintar hakan da nayi yasa na kara sukurkuce mashi duk yadan fita hayacin shi,
Haka suka kama hanya zuciyar shi fam da kewa na tare da begen ya kasance a tare da ni a ranan,
Duk da ni ma sai da na daure sosai nakai zuciya na nisa, yayin rabuwar mu dashi
Don wani irin , mugun
Kishine ya turnike ni a lokaci guda har nake jin a raina dama na sani nabi shi kawai kamar yadda ya bukata zuwa Birnin Kebbi din
Badon komai ba don dai kawai na barkata wa Fatima amarcin ta, a ranan,

****** ********* ******
Sai after nine suka shiga garin Birnin Kebbi duk kawo lokacin sakon kamshin jikina da yaya ya shaka, dan zaman da nayi a jikin shi ya hana shi shakat a lokacin
Sai fama lumshe idon shi ya keyi idan ya tuna da irin yanayin da ya barni a ciki,

A gidan mu su ka fara zuwa yayin da ya samu taron sosai daga duk mutanen gidan,
Wanda iyanzu ya fahinci hakan sosai sabanin da can baya da idan yazo sai dai idan sun hadu da mutun a hanya su gaisa,
Amma sai gashi yanzu har su yaya Mustapha su yaya Jibrin Ya Ahmed dun suna jiran isowar shi,
Ganin su yasa shi jin dadi tare da dan lumshe idanuwan shi, don murnan hakan,
A take ya yace acikin zuciyar shi Meenatu aikin ki yayi kyau gaskiya,
Lalai kowa ya bar gida gida ta barshi da farko da baya kulakowa baya taimakaqa dashi da babu duk daya ne,
Amma yanzu taimakon da ya keyi ya zama mai wani babban jigon da ya jawo mai jama,an gida dana waje zuwa gare shi,
Kamar kullun sai da ya gama gaisawa da mutane ya nufi part din mahaifiyar shi don su gaisa, a tsatsaye don yana son zuwaya hutu,
Ga Fatima Amarya wace ta ishe shi da kira ta wayan shi tana nuna wai ita concern ne na kulawa hakan gare shi,
Abincin da mama ta aje mai a gaban shi ya sa shi dan jefo dubara fon yasan cewa amaryan shi tana can ta shirya mai ita, ma,
Don haka yai dubaran cewa Mama ,Ladi, ai yanzu baya come n abinci sau biyu don sun ratse sokoto gurin mu sun ci abinci,
Cikin zuciyar ta tai ta surfa min zagi tana cewa wanan yarinyar mara zuciya mai kamar kaska,
Watau batai fushi da abinda yai masu ba ke nan ita don gashi har da taron shi ta bashi abunci,
Bai wani dade ba yai masu saida safe zuwa masauki a cewan shi,
Malam tsoho suka hade da ya shiga yai mai sai da safe ,
Yaje cewa a,a ango har ka fito ke nan yau ba zama ke nan
Yadan bata fuska alaman akwai gajiya a tare da shi yana cewa wallahi malam duk a gajiye nake saboda abubuwan da sukai yaiwa,
Malam yace har kullun kasa ka manta da kiran Allah ga neman agajin sa ka nemi tsarin Allah, atare da kai duk inda kake,
Wanan maganan ta malam yasa, Yaya Abubakar gane cewa shagube yake mai irin ta hannun ka mai sanda,
Sai kawai yaji jikin shi yai mai sanyi saboda ya fahinci da akwai wani abu ke nan amma malam din bai fada mai ba saboda, dattako irin na manya,
Jiki ba kwari zuciyar shi fam da tunane yabar gurin malam din zuwa gidan da aka gyarawa Fatima,
Wani dan karamin gidane na Aliyu ne ya ce ta zauna a ciki a ciki ne akai mai masauki,

****** ********** ******
Ya samu Amarya Fatima ita da kawayen ta mutum biyu sai kaunar ta, guda, a cikin amma matar aure ce,
Ya shigowa suka dauki guda suna cewa ayyuriiii Allah yayi ko makiya na so ko ba sa son yau Fatima ta zama ta Abubakar,
Sai dai ido da hangen nesa don ta Allah bata mutum ba ashiga kenan ba fita sai mutuwa,
Wanan abin yai bala,in sukar zuciyar shi don dai shi a ganin shi su waye makiyan ,
Uwar shi da tace ba zaiyi ba ko matan shi da sukai ta fitina akai,
Don haka da sauri ya sha toka ya daute fuskan shi tamau, a lokaci guda ba wani annuri a tare da shi,
Falo ne dan ma tsakaici ya sha gyara sai kamshi ke tashi a cikin sa,
Ga wani dan table wanda aka jerawa kulolin abinci a sama shi birjit ta ko ina,
Yashivo falon dauke da sallama a bakin shi yayin da yai wa kanshi masauki a daya daga cikin kujerun falon,
Fatima tafito daga kuryan dakin cikin wasu Swiss lace purple masu kyau sai sheki takeyi, walwal da ita,
Ta yafa wani farin gyale mai stones a kan ta tare da takalma masu tsina suna sake sauti kwas,kwas,kwas,
Fuskan ta yana dauke da annuri a tare da ita, kamar gonar kada,
Direct gurin shi ta nufa cikin takon yan duniya, tana zuwa gab da shi sai tai wani zubewa a kasa gaban shi gwiwa biyu duk a kasa cikin wani irin kashe murya da ido take cewa barka da zuwa maigida,,,
A hankali ya dago da ita ya mike da ita tsaye, zuwa jikin shi
Sauran kawayen ta yan duniya suka sa tafe raf, raf raf da guda,
Daga haka aka fara gaisawa suna mashi barka da hanya sai aka shiga kokarin yin serving din shi da abinci,
No, no no yace tare da dan lumshe idon shi yana cewa a koshe nake bazan iya cin komai ba a yanzu,
Dam, dam gaban Fatima ya fadi da taji furucin shi akan abinda suka bata kudin su gareshi ita da uwar ta,
Cikin dan ma rairaicewa take cewa haba dai bukar kamar yadda take kiranshi tun suna samar taka,
Ya za kace bazakaci komai ba duk wanan bata lokacin da nayi gurin girka ma abincin nan
Murmushi yayi tare da dan lumshe idon shi a hankali yana cewa gaskiya a koshe nake don naci abinci sosai a sokoto da mika tsaya,
Abu guda ta ji a jikin shi lokacin da ta rugumay shi shine kamshin oud na mata da ke tashi mashi bayan nashi kamshin turaren,
Sai gashi taji yana cewa ya tsaya sokoto yaci abinci a koshe yake bazaici wanda ta girka mai ba ya sha hadi da abubuwan mallaka dam,
Ta ce amma sokoto gurinnwa ka tsaya Bukar yana kokarin sance agogon hannun shine, kai tsaye, yake cewa gurin, Meenatu mana,
Kin san tana sokoto tana karatu ne ita ai so a gurin tane nadan dade ai,
Tirkasa wani irin mugun kishine ya turnuke zuciyan ta a lokaci guda take jin bakin ciki da kishin Meenatu ya turnuko ta,
Zuciyan ta, da shedan su ka hau zugata akan wanan yar iskan yarinyar watau tana da fada ke nan a gurin shi ko,
Watau sako tabani kenan ko, na zubin kamshin ta dake tashi a jikin shi kamar ta gurin nan,
Takara dan marairaice murya tana cewa don Allah ko one spoon ne kayi ka dan dana wanan girkin nawa,
Zancen malam tsohone ya fado mai arai yace ummmyumm watau abinda ya hango kenan yake min hannuka maisanda ko,
Ya na kokarin mikewa tsaye ne yake cewa ai na fada maki yau bazan sake cin komai ba kuma again sai da kuma gobe idan Allah ya kai mu,
Kaman ta kurma ihu don takaicin da take ji a lokacin da wani irin kishin Meenatu wace ta rushe mata duk wani plan nata,,,

****** ********** ******
Washegari da asuba yana wanka ya wanko abinda ta shafa a gabanta ,
Wanda ya gane hakan sosai tun a lokacin da suke tare, da dare da ita,
Har ya fito bayin zuciyar shi tana cakushi da takaici irin wanan zubin abin da yake gani gurin Salawatu idan ya sadu da ita
Shine kuma gurin Fatima itama again watau akwai wani sabon zance ke nan itama daga gare ta,
May yasa bai taba ganin irin haka ba ko saudaya daga gurin Meenatu ko Sadiya
A gaskiya idan har rayuwan Fatima na asirce asirce ne ba zai lamunci hakan ba sam,
Yana fitowa tana kwance a saman godo ba tai zancen tashi zuwa wanka ba balle tayi sallah asuba acikin lokaci,
Daga gurin da yake a tsaye ne yake kiran sunan ta a hankali ba tare da ya daga sautin muryan shi ba,
Da kyat ya,samu ta tashi inda yake cewa ke tashi ki yi wanka time din sallah yayi,

****** ********** ******
Ina tsaye a bakin mirror ina shirya wa don zuwa school saboda Uncle dinane ke sauke mu, kafin ya tafi gurin aiki,
Wayana yashiga ruri tankar zai tsaga muna kunnuwa a dakin , cikkn mamaki nake kallon wayan don ban san kowaye ke kirana haka ba da wanan safiyan,
A zatona Yaya Abubakar ne ke kirana don yaji ya muka tashi ko kuma ya yabar mu jiya,
Bakuwar nomba ce nagani don ban san mai ita ba,
Da mamaki nake kallon wayan har kiran ya katse gaba daya, batare da na yi receiving ba,
Wani kiran ne daga mai shi again aka kara kirana don haka nayi azu,billahi minal shedanin rajin, nadauka tare da cewa Assalamu alaikum,
Naji an karba


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login