Showing 363001 words to 366000 words out of 388021 words

Chapter 122 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8239

nakashewa kudi masu yawa wai ?
Tace a yaran ka da aka haifama da uwar su kaya haka kaman masu bude shago,
Kayafa ki kace Salawatu ?
Ta amsa a cikin kuka dace eh mana baga sun ba tare a falon Meenatu da nashiga nagan su kwali kwali,
Kashe wayan yayi don takaici don shi sam baida masaniya akan wasu kayan can da take zance akai,
Sai kawai ya dauka cewa kishin haukantane da tasaba ya motsa mata,
Sadiya duk yadda taso ta basar da zancen a ranta abin ya faskara mata don haka ta yanke shawaran ta kirashi a waya tai mai zancen,
Yana zaune a office yana over work yaji kiran Sadiya ya shigo mai,
Yai mamaki ganin kiranta don ita ba ma,abociyar kiran waya bace,
Sai dai indan mutun yana da bukata yakira ta yaji lafiyanta ko kuma yai maganan da zai yi da ita,
Ya dauki wayan yana cewa, Sadiya yadai kun wuni lafiya ?
A dakile ta amsa mai da cewa, lafiya sai kuma tai shiru shima din shiru yayi don ya fahinci muryan ta a kwai bacin rai a cikin sa,
Abubakar yanzu don Allah irin wanan rayuwan da ka daukar muna a kwai gaskiya acikin shi,
Don ban haihu ba shine kake kokarin na kasani kana mayar dani baya acikin matan ka,
Murmushi zancen ta ya sakashi don yasan itama danata korafin tazo,
Sai da yagama sauraren ta kaf yake ce mata a gaban tane ya kawo wa sauran matan nashi kayan da tace din ya saya masu,
Shiru tayi, ta rasa abinda zata ce mai akai, sai sakan zuci take yi tana ta surfa masifa a zuciyan ta tana cewa,
Don kawai, an raina mutane za ai masu bat da sau sai a ce wai ba shi yai wanan kayan masu yawa ba,
Ta wa zai masu shi tunda basu da kudin da zasu sai wanan kayan masu tsada dayawa,
Jin bata da ansan bashi yake cewa, tunda bata da abin fadi zai kashe wayan shi tun da zargi yai mata yawa,
Yana kashe waya ya furzar da iska yana cewa mata mata problems,
Kishi harda na hauka idan ba haukaba yanzu ace don yaiwa diyan shi sayayya shine har zasu nuna bacin ran su haka afili saboda son kai,,

****** ********** ******
Ina shiga bedroom dina bayan nai wanka na shirya acikin night gown dina, dakin ya dauki dumi ga kamshin turaren wuta yana tashi a dakin,
A hankali na koma saman gadona nazauna ina karewa dakin kallo, ina gani kamar ba dakina ba, ne a lokacin,
Jikina ba karfi kuma gashi duk nagaji ina son hutuwa, na dago kafafuwana a hankali na dora asaman gado, fuskana yana mai kallon silin din dakin nawa,
Saboda stress din da nake a cikin shi ya dan sakani runtse idanuwa na a hankali tare da sauke nunfashina a hankali ina ma godewa Allah ubangiji madaukakin sarki da yanufeni da dawowa dakina lafiya, bayan tsawon watanin dana dauka ina kwance a asibiti
Idanuwana suna a runtse naji muryan Asama,u kauna ta akaina tana cewa, Anty Meena ga Amira tana kuka abinda ya sani bude idanuwa na ke nan a hankali, na sauke shi gare su,
Tana tsaye a kaina rugumay da yar jaririyan acikin showel pink colour
Da kyat na iya bude baki ina cewa ta kaita gurin su gwago habbi su bata madara,
Ganin irin yanayin da nake ciki yasa Asmau dan tashin hankali take cewa kin ko ji sauki Anty Meenat na ansa da kyat da cewa, tare da gyada kaina acikin wani irin murya,
Asma,u hutu nake bukata jikina ban jin dadin shi sam, fita naga tayi da yarinyan zuwa dan wani lokaci sai gasu tare da gwagona Habbi,
Sun samu na fara barci sai sukay tsaye a kaina yayin da naji Asmau ta dan duko inda nake tana min addua acikin kunnuwa na kamar kira,a haka barci mai nauyi ya kwasheni
Ban farkaba sai gabanin asubah na farka inda naga Gwago habbi da Maman Biu kwance a kasa dakin yan jariran suna daga gefena asaman gado suna barci,,
Da yake ba sallah nakeyi ba sai na kara komawa barci na lafe,kafin barci ya kara daukana nake tunanen irin kyashi da hassadan da abokan zamana suka nuna min a duniya
Na rasa wani laifi nai masu haka da har suke gwada min kiyayya a filin Allah irin haka,
Don haka na yankewa kaina shawaran cewa zan dauki mataki akan zamana dasu gaba dayan su,
Don yanzu na gano cewa, akwai adawa da kiyayya a tsakani na dasu mai karfi, duk da nake ni yarinya ce karama a cikin su zangwada masu cewa nima mace ce na iya duk abinda suke nufi dani,
****** ********** ******
Tun daga ranan ban karabin tankan kowacen su ba sai harkokina kawai nake duk da a lokacin ba wai lafiya nake da shi ba sosai ina dai manejin rayuwata ce kawai,
Acikin wanan yanayin ma bawai sun barni bane kawai hakana a,a hassada da kyashi yana nan don ko nurse din dake zuwa gida duba lafiya ta tashigo ko zata fita sai anyi gulman ta ko a sake magana yadda wani nawa dake kusa zai iya fada min naji,
Idan an fada min nakayi murmushi don nasan cewa ciwo yasan kofan kowa,
Sauki a hankali yake shigo min tare da kara samun natsuwa, anyi taron suna amma bawani cika akayi ba,
Acan gida ma birnin kebbi anyi yan shagalin bukn, suna tunda iyayyena maza su kazo gaidani malam tsoho yace mata bazasu zo ba tunda maigidan ma baya gari sun tafi kasan waje gurin wani aiki,

****** ********** ******
Sai gab da Azumin watan Ramadam zai kama maigidan ya dawo kasan tare daga kasan waje,
Abuja yayo direct gurin iyalin shi, tun kafin ya iso kowace mun sai shirye, shirye take don taron maigida kowa tana kokarin ganin cewa ta burge shi,
Nidai ba lafiya gareni ba don haka babu wani shiri mai yawa da mukayi mundai gyara part din mu duk da dama akoda yaushe a gyare part din yake,
Sadiyace ta karbi girki kamar yadda yaba da umurni kafin isowar shi garin badon komai ba sai don kawar da fitina a tsakanin su,
Baba Ramatu duk da nasan cewa bazata haifeni ba amma don girmamawa nake kiranta da wanan synan tun tana hanawa har yakai ta kyaleni ina kiran ta hakana,
Itace ta gyara falon gidan tsab yadda yadace tasaka mai kamshi a kowani kusurwa na falon,
Hakan kuma taima nawa part din komai sai kyali yake yana daukan ido,
Yana saye a cikin kananan kaya mai baiyyana mai suran kurciyan shi,
Duk suna falo suna kokarin rugumar shi inda Sadiyace kawai ta nuna halin girma ta dan dakata daga baya kadan,
A lokacin muka shigo falon nida Asamau, da Ramatu sai Maman Biu da Gwagona Habib,
Yana rugumay da Salawa sai fatima adayan gefen rugumay da yarta a showel,
Ganin fitowan mu ya dan sake su ya riko hannun Sadiya yana cewa Uwargida rangida ya gidan yake,
Sai a lokacin tai yar murmushi tana cewa Alhamdullahi,
Cikin dan fadada murmushin ta ke cewa andawo lafiya ?
Yadan matse hannayen ta yana cewa Alhamdullahi mun shawo turai sosai,
Idanuwan su Salawa akan yadda ya matse hannuwan Sadiya yana cewa yagida,
Take wani irin kishi da bacin rai ya ziyarci zukatan su, a lokacin guda, sai murmushin su yajuye bacin rai,
Daga inda muke a tsaye muna iya hango fuskokin su ya sake zuwa bacin rai,
Hankalin shi yana gare mu yayin da muke mai sannu da zuwa acikin fara,a daga gefe guda,
Daga can kafin ya karaso garemu yake cewa, Gwago Mama sannunku da gida,
Gwago tace cikin daga murya maisunan malam barka da hanya,
Yakaraso zuwa gare mu acikin irin girmamawan da mukewa iyayyen mu yake cewa tare da durkusawa kasa gwago nasamay ku lafiya ?
Irin gaisuwan da yai wa maman biu ke nan itama kamar yadda ya gaida gwago Habbi,,
Sai kuma ya dago idanuwan shi zuwa gare ni ya na mai dan langabar da kan shi tare da cewa,
Kaunata how far ?
Ya kike ya yan three's da big man ban bashi amsa ba sai dan murmusawa danayi tare da mai signal da ido inda yaran suke a tsaye hannun Ramatu da Asma,u na,
Batare da jin kunya ko nauyin su Gwago dake gurin tsaye ba ya miko min hannuwan shi babu bata lokaci namika mai nawa tare da shigewa jikin shi,
Rugumoni yayi yana mai sauke ajiyan zuciya a hankali tare da dan shakan kamshin jikina,
Gani nayi kamar ya matanta da cewa akwai mutane agurin don haka nake kokarin jaye jikina daga jikin shi,
Amma sai naji yai min rikon da bazan zare jikina daga nashi ba,
Ji nayi ya soma kokarin dan jana zuwa saman kujera, mafi kusa da mu. ,
Zaman mu yai daidai da kiran wayan shi da akayi wanda yake kokarin fidowa daga aljihun shi
Dago fuskan shi yayi yana ma su Ramatu da Asamau inkiya da su kawo mai yaran kusa ya kuma juya inda Fatima take, itama yace ta kawo yarta,
Ganin hankalin shi, ya dauke ga yaran shi ya sakani dan sauke numfashi, a hankali na mike na bar gurin batare daya ankaraba,
Abinda yakeyi yadaka yana dubana tare da yin murmushi.
Nan na barsu a falo tare da iyalen shi na, shige gurin su Gwago na na zauna,
Sai bayan shigewa na ya dan sauke ajiyan zuciya tare dacewa Salawatu Madam work kamar yadda yake kiranta in yana nishadi,
Murmushi ta dan sauke da ajiyan zuciya, tana cewa Oga naga kana duban lafiyan iyalen kane ai, bai bata amsa ba sai yar murmushi don yasan nufin ta,
Dukkan su, sauran suka dubeta don sun san maganan ta da manufa aciki ,
Fatima tace aikowa domin shi yake a gurin nan don haka dole ko ya duba kowan mu,
Dariya abin ya bashi, tare da dan dan girgiza kai yace har yanzu baku daina halin ba ga yara kun fara tarawa a gaban ku,
Sadiya tace ai barsu kawai sai yaran sun fara rabasu fadan nan nasu dabaya karewa ko yaushe aka hadu,
Ta juya tana cewa idan ka rarage ruwan wanka yana jiran ka a ciki,
Daga haka itama tai shigewan ta part din ta inda ta fara sintiri daga part din ta zuwa nashi part din,
Bai dauki lokaci ba yadan duba agogon hannun shi tare da mikewa ya shige part din shi inda yabar su nan suna hira sai dai duk rabin hiran gulma ne duk da Fatima bata yarda ta zure da yawa ba,

****** ********** ******
Kowa yau agidan namu sai murnan dawowan maigidan akeyi yayin dashi sai kokarin yin adalci a tsakani yakeyi gurin ganin yabawa kowa hakkin ta,
Da yake shigan safe yai muna nikan danaga cewa ban da wani abinda zan gudanar sai kawai na shiga barci abina saboda yanzu wani irin barci ne yake zo min
Nasan cewa rashin barcin da ban samun yi a can baya asibiti,ne nake maimaitawa a yanzu,
Shigowan shi sau biyu daki na amma yana samuna ina barci sai ya tsaya yana dan min kallon tausayi saboda yadda duk na ramay na kara yin wani fari na koma wata fayau dani,
Koda na farka daga barcin sai naji kamshi oud din da yake amfani shi ya kauraye sakin nawa hakan ya sani fahintar cewa ya shigo dakin nawa, a lokacin da nake barci,
Bankai ga mikewa Asmau tashigo dauke da Alhasan a hannun ta duk da ba gane yaran nake sosai ba take ce min kin dai sha barci, yau kan,
Nadan dago ina murmushi nace karfe nawa yanzu, ?
Take ce min shigowan Yayan sau biyu dakin nan amna dai naji fitan shi dazun nan bada dadewa ba,
Tamiko min yaron tana cewa karbar shi yadan tsotsa don tun safe bai sha nono ba shi,
Badon naso ba na gyara nabawa yaron nono don ya sha, kafin na fita zuwa ban daki,
Yana cikin shan nonon tashigo tana ce min wai,ni Antyn mu wayan nan kishiyoyin naki kuwa suna da kunya kuwa ?
Wai yau ita Salawtu din nan har da daukan Amira hassina, a gaban Yayan mu,
Ai nake ce mata tabada ita don zata iya kuka tunda bata taba daukan ta ba,
Sai na dago da sauri nake cewa haba Asma,u kika ce mata hakan,
Tace kwarai kuwa don ita wai zatai muna kilibibi saboda tafa uban su a kusa don yace ai tana kula yar,
Nace bakya tsoron Yaya yai maki fada ko ya kunyataki agaban su,
Tace cabdi wallahi da sai na fadamai gaskiya cewa bata taba daukan yar ba dabaya gari sai yau da tagan shi a kusa,
Murmushi nayi nace kai Asmau baki da dama wallahi tace ai ina fadan haka naga sun wani kalleni gaba dayan su niko nayi mirsisu dasu na karbi diyata na bar su nan a zaune, can ta matse masu,
Dariya taba ni inda namike ina mika mata dan ina kokari tashi tsaye don zuwa gabatar da awala saboda na makara,
Bayan na idar da Sallah ina zaune ina dan jan tasbaha, naji shigowan mutum dakina inda na juto don ganin ko waye a lokacin ya shigo,
Daidai lokscin da yake karasowa nake cewa Sannu da zuwa Yaya ban samu zuwa na gaishe ka ba harnai barci sai yanzu na farka
Baiyi magana ba sai karasowa zuwa bakin gadona da yayi ya zauna,
Yana cewa, may ke damin ki yanzu a jikin ki Meenat sai naga kamar har yanzu kina jin jikin naki dai,
Batare da nace mai komai ba nadan kai zaune gefe guda daga inda yake ina cewa,,
Yaya ni fushi na keyi don tunda katafi, nake cewa kacewa likita ya sallamay ni amma yaki sai da na kara sati biyu a gurin su,
Murmushi yayi yana cewa to Allah ya huci zuciyar yar kaunata, amma babu yadda za,ayi nabari a sallamay ki acikin irin halin da kike a lokacin,
Nace amma ni a lokacin nafi son na dawo gida naci gaba da jiya a daki na don zaman kadaici ya damay ni a can din,
Yace Meenatu da ki ka yi hakkuri yanzu baga shi kin dawo gida lafiya ba,
Barinki a gida acikin wanan yanayin hankali na bazai kwanta ba musan man, ma irin fitinar da ake kai,akai agidan nan,
Don haka bazan barki agidan nan ba cikin wayan nan fitinan nun daba zaki samu wani kulawa ba ma agare su,
A cikin fahitar manufar shi yasani cewa a kasale hakanane kuma don zama acan din yai min rana sosai wallahi don nasamu kulawa sosai daga ma,aikatan asibitin,
Kusan minti goma muna zaune tare dashi a dakin ganin yadan dauki lokaci a dakin nawa gudun fitinan matan shi ya sani cewa
Bari na dan kimtsa na samay ka a falo ko,? na fadi hakan cikin dan kura mai ido, don inji may zaifada min,
Murmushi naga yayi sai naji yana cewa au yau kuma korata kikeyi ne kaunata,
A hankali na girgiza kaina ina cewa cikin dan girmamawa a,a Yaya ba hakana bane inadai gudun zargine daga matan ka,
Kafin ya kai ga cewa wani bu sai kawai naji anshigo dakin kamar a hasale babu sallama sai cewa tayi,
Asheko kana dakin ke nan don cwa nayi baka ciki abari nazo na duba don muna a falo zaune, gaba dayan mu,
Atake raina ya baci don shigo min daki da tayi babu sallama,
Nace a kufule haba malama zaki shigowa mutane daki babu sallama idan an miki haka baza kiji dadi ba ai,
Ta,ce dakata malama ba gurin ki nazoba sai ki bari wanda nazo gunshi yai magana,
A lokacin har Yaya Abubakar ya kai tsaye daga zaunen dayake rai a bace yana cewa,
Nace wanan ai rainin hankaline abinda mutum baiso aimai to kada yai wa wani shi,
Na,fahinci kawai wani hanya ne na son magana,
Wani kallon mamaki naga tana min don tai mamaki da taji yadda nake mata magana a hasale,
A hasale naji muryan shi cikin kufula yana cewa kifita kawai Salawa ban son yawan surtu haka please,
Idan na gama abinda nakeyi zan fito tunda ba,a nan zan kwana ba,
Tace to haka ma kace yace a hasale hakadin nace and so what,
Daidai zata fita daga falona sukai kayi kicibis da Asamau tana dauke da flask din ruwan zafi dauke a hannun ta
Tun daga nesa Asamau ta watsamata wani irin harara na tsana ,
Suna isowa gaba da junan su ta sake mata tsuki mai karfi,
Tare da kwasanta tawatsar gefe guda ta wuce direct gurin da muke aje flask din ruwan zafin shan madaran yaran a falona,
Tana ce muna funci dodo ta Allah dai bata mutum ba, wallahi,
Salawatu ta so ta tsaya taiwa Asamau cin mutunci amma sai ta tuna cewa maigidan yana part din kuma da alaman ranshi a bace yake da shigowan datayi masu babu sallama ,,
A zuciye naga yafita batare da yakara furta min komai ba wanan yasani sanin cewa yau Salawatu zata sha masifa a gurin shi ke


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login