Showing 168001 words to 171000 words out of 388021 words

Chapter 57 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8271

Sadiya ta farka cikin yanayin damuwa sai dai yanzu complain takeyi da cewa hannun ta, hannu ta na mata zugi da radadi,
Ganin haka yasa mijin Fattu wanda Yaya ke kira da, Lawal,
Yace wa Yaya su zo gefe su tatauna, akan zancen,
A wani kauye can kauyen Suleja suka yanke shawaran zuwa tare, har ita Sadiyan da Mama,
Basu wani dade ba suka iso gurin malamin, malami ne mai aiki da alkur,ani,
Don haka yai mata addu,oi tare da bada abubuwan da za, adinga shafa mata da kuma hayaki,
Tun anan ya bayar aka shafa mata wani abu a hannun nata,
Cikin ikon Allah sai ta dan lafa jin zafin Sosai hakan yasa malamin samun yin magana da ita,
Ta soma da cewa,
Nafito daga dakin maigida zuwa nawa dakin don ban????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? 
san may yasa ban son kwana can har safe ba,
Bayan nashigo ne sai nadan kewaya daniyar inyi fitsari,
Na duka shine naji kamar abu yana lasana koda na haska toci shine naga wani irin halitta, yana kokarin shige min a gaba,
Ganin yana son shige min yasa nai kokarin rikeshi da hannuwa na ina ihu, neman ceto,
Takarashe zance acikin kuka da neman mafita murmushi malamin yayi tare da kada kai yana cewa, cikin irin harshen su na gwari,
Allahu Akbar wanan wani sihiri ne mai karfi gaskiya,
To amma yanzu atafi a shafa wanan abubuwan da ya bata zuwa gobe in Allah ya kaimu sai su dawo harda ita don yana son yin istihara akai,
Godiya Yaya Abubakar yai wa malamin tare da bashi kudi sai malamin ke cewa su bari kawai idan sun dawo sai su bashi,
Amma sai yaya Abubakar ke cewa yadai karba ai sadaka ne ya bashi dole mutumin ya karba,
Sunkamo hanya kowa da abinda yake sakawa azuciyar shi,
A lokacin wayan Lawal mijin Fattu yai kara yadauka tare da Sallama Fattu ce a layin tana fada mashi cewa babu fa abinda zasu dafa agidan,
Yadda Yaya Abubakar ya fahinci zancen mijin da matan sai suka bashi tausayi don ya fahinci sai ya fita gurin buga bugan shi yake samo masu abinda zasu ci,
Don haka bayan sun kai su mama gida da Anty Sadiya inda muma muka bita dakin don mata sannu da jiki,
Bayan kara yiwa, Mama bayanin magani Yaya yace wa Lawal yazo su fita tare,,
Basu tsaya ko ina ba sai kasuwa nan suka sayi kayan stuff duk wani abin bukata sun saya aka loda wa mai Nape ya biyo su baya dashi,
A gidan Lawal Yaya Abubakar ya tsaida mai Nepep inda ya umurci da a sauke kusan rabin sayayan da sukayo a kofan gidan Lawal,
Mamaki sosai ya kama Lawal inda har ya kasa yin magana yakai wani lokaci tsaye a cikin mamaki,
Sai da ya ji muryan Yaya Abubakar yana ce masa lokacin sallah magrib yayi,
Yakamata su karasa massalaci don kada su rasa jam,i,
Sunyi sallah sun ka fito don zuwa gida duba jikin Sadiya,
Sai a lokacin Lawal ke cewa maigida ban sanbirin godiya da zan maka ba gaskiya,
Don rabona da, samun irin haka tun lokacin da nake aikin Banki,
Sai kwatsan wata rana aka turo muna da takardan sallama daga aiki har mu biyar,
Batare da mun samu wani sallama da ga chan headquarter mu ba,
Wanan dalilin yasa na sai da duk wani kaddaran dake gareni na dawo nan, nai muna wanan ginan,
Sai nake fita kullun kasuwa ina yawon dillanci don mu samu abinda zamu ci,
Yaya Abubakar yanisa tare da cewa ai aikin banki baida tabbas,
Don idan tsiyan su ya tashi daga sama kawai zasu ce sun sallami mutum
Ba don komai ba sai don kada suyiwa mutane sallaman barin aiki, kamaf kowa,
Don haka ni sam ban dauki aikin banki acikin aiyukan kwarai ba,
Lawal yace ai maigida mun sheda hakan sosai wallahi, don alokacin abin kamar zai tabamin kwakwalwa,
Godiya na ga Allah daya bani mahaifiya irin mama wace tasan yadda zata kwantarwa da mutum hankali,
Don da taimakon Allah da na ta har na dawo normal person dina,
Takuma aura min Fattu diyar yar uwar ta don matar da na aura da farko fafir taki wai banda komai ita bazatai zaman wahala ba, dani,
Tafi abinta tabar ni batare da ta tausaya min halin da nake ciki ba,
Nisawa kawai yaya Abubakar yayi don ya fahinci matar bariki ce Lawal ya aura,
Don haka ya ce Allah ya kyauta a ta kaice kawai, batare da ya kara cewa komai ba,
Bayan fitowan su daga Sallah suka shigo a tare don duba jikin Sadiya,
Sun samu tana zaune Mama tana shafa mata magani a hannayen ta da suka kunbura sukai wani irin jajir dasu,
A daidai lokacin na shigo dakin dauke da kulolin abincin su ahannu,
Bansan cewa su Yaya Abubakar suna dakin ba a lokacin don haka ina ganin su sai na koma baya da sauri ,
Hijjab dina na sa nafito na dawo dakin inda na gabatar masu da abincin su,
Amma sai Sadiya take cewa bazata iya ?iba don bata jin cin komai,
Nadan koma kusa da ita ina cewa ko in hado maki tea mai zafi ki sha ta gyada mun kai kawai alaman eh,
Bandade ba nadawo dakin dauke da cup din tea mai zafi da bread,
Amma sai tace inbar bread din don ruwan tea din kawai zata sha,
Gurin daYaya Abubakar yake tsaye ya kura mata ido dagani nazarin abubuwa da dama yakeyi a lokacin,
Cikin dan tausa murya nace wa Yaya Abubakar Yaya abinci fa,?
Sai da ya nisa tare da lumshe ido yake ce min Meenat zanci ,
Amma naso sai nai wanka tukun nace to barin hada maka ruwan zafi ko?
Yadan lumshe idon shi kadan yace no kibarshi kawai kin san cewa ke ma ba lafiya bane dake,
Kibi jikin ki a hankali don kada jikin ya tashi maki,don stress na iya saki kwanta again,
Nai dan murmushi na ce, ai naji sauki Yaya zan iya insha Allah,
Ya ce No ki dai bari kawai, a lokacin Salawa ta shigo dakin tana saye da wani dogon riga baka maidan karamin hannu kamar shimi,
Kanta, ya saye da fullan mai net, wanda ke nuna kitson attachment din ta daga cikin sa,
Sannu da zuwa tai masu yay Abubakar tare da jira mai zaice ba
Ta juya tana duban inda Sadiya take tana cewa
Sadiya ya jikin naki, ?
Sai da Sadiya ta dan murmusa kadan sanan tace a hankali cikin daurewa
Da sauki,
Sai kuma dakin yai tsit a lokaci tankar babu kowa a gurin,
Jin kada Salawatu ta juya yayin da zata bar dakin tana cewa Allah ya sauwaka,,
Tabar dakin abinta zuwa dakin ta ba,ai wasu mintuna ba Yaya Abubakar yabi bayan ta,
Kafin ya karasa fita nake cewa mijin Fattu malam abincin kaima sai yaya yafitone zakaci,?
Yace kai haba aini yau maigida ya wadatar da mu
Anan yake fadawa Mama irin alherin da Yaya Abubakar ya sai masu,
Har dani dake gefe dakin sai da na taya su murna tare da godewa Allah
Mun kai wani lokaci zaune mu na taya Sadiya da mama hira,
Sai wani lokaci Fattu da maigidan ta sukai muna sai da safe,
Bandade ba nima na nai masu saida safe na koma dakina sai dai zuciyata tab da tsoron abinda dare zai yi ywu,
Na rufe kofana tare da jero addu,oin da duk na iya a bakina,
Nabi duk wani kafa nq dakin na toshe da adduoin,
A hankali na kwanta saman gadona a takure ina mai jin tsoron dare,
Da haka har barci barawo yai gaba dani batare sa na sani ba,



ZEEE MAKAWA YELWA
[8/21, 10:20 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
6? 0?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH-AL- MAJEED

YA ALLAH MUNGODE MA DA KA NUFE MU DA GANIN WANAN RANAN MAI TARIN ALBAKA,
YA ALLAH KA SA MUNA CIKIN YANTATTUN BAYINKA,
YA ALLAH KA SADA MU DA RAHAMAN KA
YA ALLAH KA TAUSAYA MUNA DUNIYA DA LAHIRA,
YA ALLAH KA GAFARTAWA IYAYYEN MU,
YA ALLAH KA KARA RUFA WA IYAYYEN MU ASIRI DUNIYA DA LAHIRA,
YA ALLAH KA BAMU MAZA JE MASU MUTUNCI, ADINI SANIN YA KAMATA MASU, ALBARKA
YA ALLAH KA GAFARTAWA DUKKAN QULLUMIN MUSULMIN ALLAH MAZA DA MATA BABBA DA YARO, TSOHO DA TSOHUWA ,
YA ALLAH MUN GODE MA YA ALLAH MUN GODEMA YA ALLAH MUN GODE MA DA KAYO MU MUSULMAI
YA ALLAH KA KARBI TUBAN MU, KASA MU MUTU MUNA MUSULMAI ALLAH, AMEEN YA ALLAH =?O?=?O?=?O?=?O?=?O?

BARKAN MU DA SALLAH YAN UWA


Bayan tafiyan Lawal da iyalen shi Yaya Abubakar ya koma dakin shi don ya huta,
Sai kuma zuciyar shi ta kasa barin shi ya huta din,don tunanen abin mamakin da ya auku yau a gidan nashi,
Lalai badon da idon shi ya ga abin ba da bazai taba yarda ba ,
To may ye wanan abin ya tambaya da kan shi, daga ina yake haka,
May ya kawo shi gidan shi mau yake so a cikkin iyalin shi
Iska mai zafi ne ya furzar da ga bakin shi tare da kai ma hannayen shi naushi a,lokaci guda,
Malam tsoho ne ya fado mashi a rai don dole ne ya fadawa tsohon wanan abin saddabarun da ke faruwa a gidan shi,
Sai ya kai duban shi ga agogon wayan shi take yana sa a ran shi cewa dare yayi sosai a lokacin,
Don haka dole ne ya bari har zuwa gobe da safe ya kira malam din,
Da wanan shara ya shirin kwanciya barci inda ya bi lafiyan gadon shi,
Sai bayan ya kwanta yake tunanen cewa Meenat bai ganta a waje ba tun bayan dawo wan shi gidan,
Hakan yasa shi mikewa da nufin zuwa dakin nawa don ya duba ya ga halin da nake ciki,
Salawatu ce ta shigo dakin, ta na saye cikin, wani rigan barci mai kama da babu komai a jikin ta a lokaci,
Sau guda ya daga kai bai kara kallon ta ba,
Zagayowa tayi ta bayan shi ta rungumo shi tana cewa, Sweet Oga har yanzu fushi kakeyi danine please ?
Tana son su hada baki yai saurin ture ta yana cewa Salawa are you out of your sense ?
Baki san halin da nake a ciki bane halan ?
Har zaki shigo kina son in making love da ke a haka
Cikin wani irin juya ido takara kwanti mashi a jiki tana cewa to amma ai sai naga taji sauki ko ?
Wani mugun harara ya watsa mata yana cewa ok don ciwon ba a jikin ki yake ba ne har kike ganin cewa, zaki samu kai na a yau din,
A gaskiya ni ban gane ba dear duk kwanakin nan baka da time dina sam,
Kai ya kada yana cewa look Salawa, ban son yawan magana don ina a cikin yanayi yanzu haka ,
Sai dai duk da irin yadda Yaya Abubakar yake neman ta kyale shi Salawatu bata yarda ba don saida tai irin halin su na matan bariki ta hilance shi,
Abinda yasa Yaya Abubakar ya manta da zancen zuwa duba ni a lokacin da yai niya yi ke nan,

****** ********* ******
Malam tsoho wanda tun a tsakar dare bayan ya idar da sallah nafilan shi kamar kulun daga gurin da yake a zaune barci ya dan fisgeshi,
Mafarki yayi da wai gashi a gidan Yaya Abubakar,
Inda yaga matan shi a cikin damuwa, sai kuma shi Abubakar din wanda, yafi kowa shiga hall n damuwa,
Sai kuma aka dan nuna mashi fuskan mace tare da wata, tana, ta azabantar da ita ta hanyan sihiri,
Firgigit ya farka sai yaga har tasbahan da ya ke rike a hannun shi yana ja ya fadi kasa,,
Hankalin malam ne ya tashi inda ya kai indon shi ga mamakeken agogon bangon dake dakin don ya duba time,
Karfe uku da wani abu na dare lokaci ya nuna mai hakan yana nufin cewa tsakiyan dare ake,
Abinda ya keyi ne yaci gaba dayi tare yi wa family din jikan shi addu,an, neman tsari daga sherin shedan,

Kamar yadda wa yan da ke kwana raye gurin kokarin kai kukan su ga Allah Ubangiji Subbahanahu wata, ala, mai jinkan bayin shi,
Barci da shedan kan dan so rinjayen mutun a waau lokuta irin haka,
Malam tsoho still, barcin ne kuma yaso yakara rinjayen shi har ya dan fara mafarki
Kamar farko wanan katon da mamaki ya tashi don wace ya gani acimin mafarkin nashi a lokacin,
Hakane ya tabbatar mai da cewa lalai akwai matsala sosai a gidan Jikan nashi duk yadda aka yi,
Hakan ya kara sa malam qaimin gurin ganin yai wa jikokin nashi addu,oi,,

****** ********** ******
Ya Abubakar bai farka ba sai gabanin asuba inda ya sauke idon shi akan Sallawatu wace ke kwance rub da ciki tana barci a gefen shi,
Dan tsuki yayi yana kokarin mikewa don ya duba time,
I zuwa yan karfe biyar saura na asuba hakan yasa shi sauri mikewa da sauri don, bai zaci cewa lokaci ya kai haka ba,
Don yaso ace cikin dare ya ziyarci su Maman Bi u da Sadiya don ya ga irin halin da su ke ciki
Amma sai wanan shu,uman matar tashi ta ja hankalin shi har ta shagalar dashi,
Bathroom ya fada inda yai wanka tare da dauro awala kafin ya fita massalaci sai da ya tafi dakin Sadiya, don ga kwanan su,
Yasamu mama tanawa Sadiya fitara duk da sanyin Ac dake a dakin
Amma sai korafi Sadiya keyi na cewa ita zafi takeji sosai,
Cikin mamaki Yaya Abubakar wanda ke saye da jallabiya a jikin shi,
Yake tambayan Maman Bi,u abinda ke faruwa take fada mashi irin halin da suke ciki, tun gabanin asuba,,,
Gab da Sadiya ya nufa yana mata sannu da jiki tare da tambayan ta yadda take ji,
Bayan yasamu tai dan mashi bayani sama,sama ya yi mata addu,, a
Tare da tofa mata aruwa yabata tasha yadauko mata wani standarding fan yasa masu a dakin,
Take tasamu barci daga haka ya wuce yin sallah asuba,
Sai da gari yai haske sosai, sosai sanan Yaya Abubakar ya shigo gida
Ya samu ina dakin gurin su Anty Sadiya ina masu yaya dare,?
Ganin da yai min zaune a gefen carpet din da Mama take akai, na wani takure guri guda kamar mai jin sanyi,
Ina kwana nai masa da,ga inda nake zaune a cikin ladabi tare da girmamawa,
Gurim da nake yake duba na yana cewa to yaya jikin naki ?
Na ansa mashi da cewa a cikin wani irin murya da Naji Sauki,
Yace yanzu bakya dai jin komai ko ?
Eh nace mashi kaina yana a duke,
Sannu Mama ya maijikin bata farka ba har yanzu ko ?
Eh mama tace mai ai Alhamdullahi tun dazun barcin takeyi,
Kafin ya ce wani abu wayan shi ce tai kara alaman kira, ya shigo mai,
Saida yai tsuki don yana mamakin wanda ke kiran shi da wanan safiyan haka ?
Malam tsoho yagani a rubuce saman screen din nasa,
Yai matukar mamakin ganin kiran malam din a wanan lokacin,
Cikin mamaki yace malam tsoho
Abinda yasani saurin dago kai ina duban shi ke nan,
A take kuma naji gabana ya bada dam a lokaci guda, don jin sunan wanda ya ambata,
Gaisawa naji sun fara yi tare da tambayan lafiyan mutanen gidan
Sai da naji suna ci gaba da zance yasa hankali na yadan kwanta kadan,
Don nasan cewa, lafiya babu wani abinda ya faru ke nan a gida,
Saidai kuma ina tunanen dalilin wanan kiran da wanan safiya haka,,
Mikewa Yaya Abubakar yayi zuwa waje inda suka fara zance da malam din,

Malam ke tambayan Yaya Abubakar da cewa lafiya dai ko kake da iyalin ka?
Yaya Abubakar yarasa abinda zaicewa malam din sai yai dan shiru
Malam yakara tambaya yana cewa domin jiya cikin darai nai mumunqn mafarki a kan ku,
Innalillahi Yaya Abubakar ya ce da yaji may malam din ya ce mashi,
Cikin murya irin ta damuwa yake cewa wallahi malam abin sai a hankali domin gaskiya,
Meenatu ce ta fara samun matsalan barin ciki satin da ya gabata,
Bayan tadawo gida da kwana biyu sai kuma ita Sadiya tasamu wani matsala,
Subbahanallahi malam ya furta a cikin damuwa, tare da nuna kulawan shi,
Ya jikin ita Meenatun yanzu da sauki ko Yaya Abubakar ya amsa mashi da cewa taji sauki sosai don kwana guda tayi aka sallamay ta daga asibitin don jinin da yake zuba ya tsaya da wuri,
Allah ya kawo rabo na moriya inji malam tsoho saidai yaya Abubakar yakasa ansa mai Ameen a fili sai dai a cikin zuciyar shi,
Malam tsoho yace ita kuma dayar may ke damun tane fa,?


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login