Showing 57001 words to 60000 words out of 388021 words

Chapter 20 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8296

da take tare da su ya kallla yara masu kyau da su bulbul dasu gwanin ban sha,awa,,
Nan yake tambayar ta diyan gurin kawun ta ne wa yan nan yaran ko,?
Meenat taba shi ansa da fadin en malam duk kan su diyan amaryan shi ne da take gurin ta,,
Ya jinjina kai irin na manya tare da kara masu sannu da hanya,
Daga haka ta mike ta na rike da hannun yaran har zuwa sashin su inda takeyi tana gaisawa da duk wanda ta hadu da shi wanda ta sani,,,
Mama Saratu tai murna kwarai da zuwan diyan yan uwan ta gurin ta,
Alokaci guda aka fara gwada wa yara gata da kauna,

Meenat bayan ta huta tamike tsaye tana cewa mahaifiyar zata ta gaida mutanen gida sai taga su anty samira,
Jinan Inkyau, sunan da take kiran meenat da shi ke nan,
Kiyi nisa da maman ku Ladi don bata jin kunyar tozarta ki cikin mutane,
Balle ma mama ai nasan sai tayi babu mutane ma tai mun balle yau ga jama,a,,,
To ki dai bi sannu ban son abin magana sam a rayuwana,
To mama insha Allah

Kusan duk sashen da ta leka suna gaisawa cikin mutunci dakuma yi mata sannu da hanya,
A kofan shiga sashen mama Ladi suka hadu da Samira wace ke shirin fita daga lungun nasu,
Ihu samira ta sa don murnan ganin Meenatu alokacin
Ihun da ya jawo hankalin mutanen dake daga cikin sashen mama Ladi,
Mama ladi wace take zaune tare da yaran ta suna kokarin hada kudin sayen robobin rabawa mutane, masu zuwa walima yau,
Gaba daya hankalin su ya koma gurin su Samira da meenatu da suka makale junan, su don murna,
Wacce tta ayar can ?
Inji habiba antyn Samira sai Safiya ta ba da ansa da cewa killa kawar ta ,ta taho ko ?
Caraf mama tace wacce kawar ta Amenatu ta fa diyar baban ku Samaila,
Gaba dayan su lokaci guda suke cewa, Amina shim?
Yanzu Amina ta, ta,koma haka ?
Mama Ladi tace, badole ba tunda iyayyenta sun sake ma duniya ita,
Wai wata yar bariki karikon ta matar kanin uwar ta,
Daidai lokacin da Meenat ta karaso zuwa
gurin da suke zaune ,
Har kasa Meenat takai tana gaida su a cikin ladabi,
Sai cewa suke yi Shin Meenatu, ke ta haka ?
Yaushe rabon da mugan ki a idon mu ,
Dariya kawai meenatu tayi gami da mikewa tsaye a lokaci guda,

Rungomota Samira takara yi tana cewa gaskiya kamata yayi in fushi da rashin zuwan ki da wuri haka?
Anty Samira na fada maki test nayi jiya shi ya hanani zuwa da wuri, ok, haka ne kin kuru,
Bakomai tun da gashi kin zo yau din kinga ai ayi wasu events da ke,,
Ok Meenat barin je in fara shiri kin san yau zamuyi kauyawa day,
A gurin program din ne take jin cewa wai za,a hada Aisha ko,yar wurin baba shaibu aure da Yaya Abubakar idan yadawo,daga England wurin karo ilimi,
Meenat azuciyar ta tace aiko da mai shi ta shiga uku,,,,,
****** ******** ******
Anty Sadiya wace mijin ta ya bari Abuja zaune ya wuce zuwa England,
Daga can ya kara turo mata da kudi ta hannun Salawatu,
Wanda zata tafi birnin kebbi don halartar bukin kaunar shi Samira da sauran sisters din shi,
Inda ya bata sakon wasu kudi don ta karawa mama,Ladi idan taje, gurin bukin don buki akwai cin kudi sosai tun dai irin bukin mutanen su na hausa,
Wanda za,a kashe zarahi kamar ba gobe kuma ?
Isowar Sadiya garin nasu gidan mahaifiyar ta Hajja ta nufa direct,
Duk sha,anin da akeyi bata leka ba sai yau da za,a yi sisters day,
Ko shi bata so zuwa ba saida yan uwanta suka dinga mata korafi da cewa halin nan nata baida kyau ace mutum yazo buki a gidan mijin shi amma bai taka ba ko sau guda,
Wanan ne dalilin halarta da tayi yau a tare da yan uwan ta su biyar,
Jama,a sai wani kallon ta sukeyi, don ba wani canji a tare da ita,

Ankon din pink lace akayi da blue din goggoro ,
Baba Samaila shine ya sayawa Meenatu kuma yabawa wata matar wani abokin shi soja ta dinka mata,
Kowa kagani aranan cikin pink lace da gwaggoro blue,,
Amarene kawai aka banban ta su da sauran mutane inda suka sa Fararen lace masu kyau da daukan ido,
Meenat wace ta gyara jikin ta tsab tafito kamar wata tauraruwa,
Don ba karamin kyau shigar yaiwa meenat ba don duk wanda ya ganta dole ya yaba da shigar ta ga kyau ga diri, da zati,,,
Mutane sai zolayar ta sukeyi da tafito suna cewa wanan kyau haka meenatu sai kace kece amaryan,
Murmushi kawai meenatu take masu duk wanda yace mata kai kin yi kyau sai tace nagode kawai,,
Tun daga nesa ta hango matar yayan su Abubakar zaune tare da yan uwan ta,
Yar su habiba tana tsaye tana magana da su, a lokacin,
Gaba daya suka waigo suna kallon meenat din wace alamar hakan na nuna cewa ana yin zancen mutum a gurin,
Gurin su ta nufa kai tsaye inda ta gaishe su cikin girmamawa,
Ga mamakin Meenat sai taga Sadiya ta nuna tankar bata san ta ba,
Hakan bai wani bata mamaki ba don sanin halin ko inkula da mutane irin na Sadiyan,
Tana rike da hannun yan kannen ta suka kara gaba abin su,
Anyi ta rawa da cashewa amma sam meenatu ta ki yarda tai rawa ko sau guda acewar ta su jikokin malam ne, yin rawa gare su zubar da darajan gidan su ne,

Washegari wankin amare don haka ranan buki ne sosai,
Kamar yadda kowa yasan yadda al,adan bukin birnin kebbi yake ranan jumma,a ake wanke amare,
Asabar ayi wanka, to shi wanan yasha bambam don malam tsoho yayi tsaye yace sai dai ayi wanka Alhamis, saboda shi jumma,a zai daura auren yayan shi,
Inda yace mutane ne basu gane ba da,suke daurawa yaran su aure ranan asabar sabanin da da akafiyi ranan jumma,a,
Inda yake cewa ta ya ya zakuji cewa an hana yin abubuwa a wanan ranan asabar din sai kuma hankalin ku ya gushe shedan ya rude ku, ku koma daura auren diyan ku a sabar din,
Asabar fa wata rana ce da hatta wanki da yankan akai fa da kitso ko gyaran kai a hanemu dayi a wanan ranan don gujewa masifofi,
Amma wai shine a yanzu jama,ar mu suka mayar wai ranan daurawa diyan su aure,
Don haka shi yace jumma,a ce za daurawa su Samira da murja aure,
Dole aka maida wankin amarya ranan Alhamis, a can G,R,A za ayi wankin amaren kamar yadda aka saba,
Buki yakai buki inda jamaa yan uwa da abokan arziki aka hadu aka gwadawa wa yan nan ma,aurata gata duk kowani fannin both angwaye da amare,
Meenat wace Allah ka,dai yasan yawan masoyan da ta samu a wanan shagalin
Cikin ma tana boyewa bata faye fita fili ba sai can ba,a rasa ba,,,,


ZEEE MAKAWA YELWA
[7/17, 5:26 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
2? 5?
ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH-AL-GHAFFAAR,,


A ,kwance Meenat take tsawon wanan lokacin inda take iya jiyo hayaniyar yan kai amaren, gidan su,
Amma izuwa yanzu babu wanda ya damu da yashigo sashen nasu don yaga irin halin da su,ke ciki, ?
Daga ita har mahaifiyar ta suna acikin wani irin hali a ranan mai ban tausayi,
Gwago Habbi ce kawai da yazama ma dole ta tsaya da su take sintiri a sashen,
Abincin daren da mama saratu tasa itace ta kara shi da kanta ranan
Gwago habj ita kadai ce ke faman safa da marwa a cikin sashen hankali a tashe,
Muryan yayan ta Ibrahim ne ta ji a lokacin ya shigo gida suna gaisawa da gwago Habbi,
Can kuma ta tsinkayo suna zancen auren inda yaya Ibrahim ke cewa a gaskiya gwago da ace yau na girma na kai irin shejarun su yaya Abubakar,
Wallahi wallahi da na warware auren Amina da malam ya daura mata da makiyan mu,
Aure da zuri,an mama Ladi ko auren masifa may Meenatu zata gane ga wayan nan mutane,
Muggai, azzalumai, maketata, masu tozarta zumunci, ga kullin sheri,
Duk gidan ga babu masu nuna muna mugun kiyayya irin yan dakin mama Ladi,
Masu tozarta muna iyayye agaban idon mu a gaban kowa basu maishe shi komai ba,
Daga inda Meenat take kwance dungule take jin irin halaiyar yan dakin mama Ladi yadda yayan ta Ibrahim dama yake namiji yake jero su,
Gwago ina ga yarinyar ga Samira da akaiwa aure yau ita kadai ce sai dama,dama safiya basu taba yiwa maman mu rashin mutunci ba agaban mu,

Wani sabon ciwon kaine ya ziyarci meenatu a lokacin don duk abinda dan uwanta yafadi akan zurian mama Ladi gaskiya ne,
Wasu irin hawaye ne suka soma zuba ga ido na tarara
Wani sabon kunci da bakin ciki yazo ya tokare min makogwaro na,
Wani irin nauyi ne ya ziyarci kirjina alokacin saboda bacin rai,
Hannuna nadaga a hankali nadafe daidai gurin da nake jin wanan nauyi,
Daidai lokacin Baba Samaila ya shigo gidan yasamu yaya Ibrahim da gwago Habbi suna tataunawa,
Mahaifina jin muryan shi nayi yana cewa, haba dai Habbi ai in fada maki duk wani cin mutunci da kaskanci da ladi take ganin ta shirya akan zancen nan nafita shirin shi,
Bazan lamunci aciwa yarinya da bata san hawaba batasan sauka ba mutunci a banza,
Dama ya ya Aminatu suke da Ladi balle yanzu tana ganin ta samu kafa,
Matar da ta kwaso kiyayyan duniya ta azawa yarinya akan, ba gyaira ba dalili kwakwara,
Kawai dai ni musulumi ne nasan cewa mutum bai iya canza kaddara ubangijin shi,
Wanan dalili yasa kikaga ai ban dauki wani mataki mai kwari ba
Yanzu jira zanyi har shi Abubakar din yadawo daga tafiyan da yayi mu ga irin rikon da zaiwa Meenatu,
Sam bazan lamunci wulakanci akan yata ba Habbi gaskiya, zance,,,,,

Takon tafiya na ji zuwa inda nake nasan dai dayan biyu ne ko babana ko kuma dan uwa na, rabin jiki yaya Ibrahim,
A irin yadda ya hango yar uwar nashi daga kwance yasan cewa yau an jefata acikin wani irin mawuyacin hali, yar karama da ita,
A hankali ya karasa takowa zuwa inda nake kwance ina wani irin kuka mai fidda sautin ban tausayi,
Salati ya sa alokaci guda tare da neman taimakon sauki daga Allah,
Sunana yakira a hankali yana cewa Amina meenat fa ?
Wani sabon kuka mai kara na kara sakewa alokaci guda,
Ban an,karaba ba shima yayan nawa kukan yake yi don zan iya jin sautin shi daga gurin da nake kwance,
Sunana yakara kira cikin muryan kuka
Da kyat na ansa masa cikkin dasassashiyar murya na amsa masa
Ki yi hakkuri kibar kuka keji,
Kuka bai fisshe mu tashi zakiyi kiyo alwala mugayawa Allah kukan mu,
Muryan mahaifin mu mukaji da ga kofan dakin yana cewa kwarai kuwa Ibrahim kakawo shawara mai karfi,
Gwago habbi tace, ai yanzu dole mafita zamu nema,
Kodon irin yadda aka nuna muna bakin ciki karara akan wanan auren,
Kirikiri babu wanda ko ya kulamu yazo yace muyi hakkuri ko kuma yai muna murna inka debe wanan yarinyar Samira, da tashigo, dazun,
Wa zaizo tun da sun san cewa, wani hanyar alheri ne kila ya kara sauka muna, a hakan,
Ni abinda yasa kikaga ban tsawalawa kaina dayawa ba ke nan Habbi don dai fa komai daga Allah ne
Sannan wanan tsohon da kikaga yayi wanan hadin yasan abin da yasa yai haka a rayuwan shi
Don malam bai taba yin abinda ba zai zama alheri ba,
Meenat da ke kokarin mikewa zaune daga kwance,
Tace cikin share hawayen da ke gangarowa da fuskan ta,
Shike nan Baba da kai da yaya Ibrahim dama nasan cewa ban da kowa a duniya bayan ku da gwagona,
Zan daure Baba in yi biyayya a bisa umurnin ku kai da dan uwa na da malam tsoho,
Duk da nasan cewa yaya Abubakar ba mijin aure na ba ne ba kuma zai taba sona ba,
Zuri,an mama Ladi abin neman tsari ne a gare mu,
Amma duk da haka zan daure in zauna acikin ko wani irin hali na tsunci kai na acikki
Murmushi Baba Samaila ya dan sake a fuskan shi irin ta takai ci ya ce,
Amenatu naji dadi sosai na gode Allah yai maki albarka,
Allah ya sa wanan auren yaza maki alherin rayuwa da muma nan gaba daya,
Ameen suka karba dashi gaba dayan su da ke gurin a lokaci guda,,,
Yaya Ibrahim wanda ke zaune a gefen gadon da take ya ce to goge fuskan ki,
A hankali ta sa habar zanin ta goge fuskan ts a hankali tare da sauke ajiyar zuciya,
Yaya Ibrahim ya dan sasauta muryan shi yana cewa,
Hakan da zakiyi meenat zai sa masu jin haushin wanan abin a cikin wani sabon jin haushi da takaici,,,
Daga haka suka samu suka lalabata ta tashi zuwa yin sallolin da ke kan ta,

****** ******** ******
A cikin dare meenat a kwance tare da yaran da tazo dasu daga sokoto,
Kowa na barci Meenat sai juyi takeyi ta na dan sake sheshekar kuka, a hankali,
A hankali taji an dafa ta ba kowa bane a gurin sai mahaifiyar,
Wacce ita ma ta kasa ko da runtsawa a wanan ranan saboda tashin hankali,
Karfin kukan ta takara sawa alokacin abinda mahaifiyar ta tadade da yi mata shine yai tai mata,
Rungumo,ta ta,yi zuwa jikin ta tana mai zubda hawaye tana dan bubuga ma meenat din baya,
Mama yaya zan zauna da yaya Abubakar wai a matsayin mijin da zan aura,
Mama mutumin da naga irin yadda yake zama da matar shi,
Muryan mama Saratu ce ke fadin, kar na karajin wanan zancen haka daga bakin ki,
Kai meenat ta daga kawai, alamar ta gamsu da zancen mahaifiyar ta,,
Nasiha sosai mama tai muna a wanan ranan inda ta kara lurar da ni yadda zan zauna da iyalin mama,Ladi,
Azuciya ta nace a kwai aiki ashe, don nasan yanzu mama take ga goran ta muna ni da iyayye na,

****** ******** ******
Washe garin ranan haka na tashi jiki ba kwari don sai nake ji tankar nai,ciwo mai tsawo a lokacin,
Tun har zuwa wanan lokacin ba wanda ya shigo sashen namu daga cikin mutanen gidan mu,
Mama ta gama hada muna abin kari har kuryan daki takai min inda nake kwance,
Kirana tayi da cewa,
Inkyau, ki tashi ki sa, wani abu a cikin ki ko zaki dan walwale,
Daga gurin da take tsaye ne mukaji muryan Uncle Nafi,u da Anty Amarya suna sallama akofar shigow? Sashen namu,
Zubur gaba dayan mu muka mike don mamakin ganin su a irin wanan lokacin,
Zakace a gatin birnin kebbi suka kwana badaga sokoto suke ba,
Irin yadda suka samu yaran su tsab har mama tai masu wanka ta shirya su,
Ga abin karin,kumallo da Baba ya siyo muna,saboda zuwan yaran agaban su suna ci,
Zubur namike daga sama gadon mama na kan,kamay Anty Amarya,
Daga ni har ita sai kuka muke zubawa babu mai kama wani,
Uncle Nafi,u ne ya leko daga falon mama yana cewa assha, Sumaiyya ke kuma da nake zaton zaki bawa yar naki hakkuri zaki kuma buge ga kuka kamar ta,
Daga haka mama tabi bayan shi suka koma falon nata,
Inda mukuma muna daga cikk zaune tare da Anty amarya,
Wace fuskan ta kawai ya isa ya nuna maka irin halin damuwar da take ciki,
Daga falo muna jin yadda mamana take kokarin ba dan uwan ta labarin yadda abin ya faru,
Sai dai ta kasa karasa sai ta sa mashi kuka a lokaci guda,
A lokacin mahaifina baba Samaila ya shigo dakin,
Yasamu mama tasa dan uwan ta agaba tana kuka, cikin tausayi,
Murmushin yake baba yayi yana cewa assaha saratu ke kuma kukan ne har yanzu,
A nan suka zauna suna dan tataunawa a tsakanin su inda daga can kurya Anty amarya takan dan kado masu baki a zancen,

Hayaniya ce ya kaure daga cikin gidan mu sai dai babu wanda ya leka daga sashen mu,
Muryan mama Ladi ce tare da wasu bakin murya suna magana ,
Wai anci amanar Sadiya matar yaya Abubakar don ba,a fada mata cewa za,aimata kishiya daga cikin dangi ba,
Sai gashi kawai daga zuwa buki za,a ce wai an yi mata kishiya,
Ita ko mama sai faman basu hakkuri takeyi tana kuma mai kwantar masu da hankali akan su bari Abubakar yadawo asan yadda za,ayi,
Magan ganu


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login