Showing 129001 words to 132000 words out of 388021 words

Chapter 44 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8236

kassuwan a wani plate,
Anty ta zuba su cikin wani leda ta fita dasu waje wai zata rufe su ne a cewan ta,
Tun da na gama cin wanan naman nasha ruwa sai nafara jin wanu irin kasala yana rufe min jiki a hankali,
Kara kwantawa nayi don dama weather ranan Alhamdullahi,
Anty ta shigo dakin tana cewa hajiya Mama ce ta bugo waya take tambayana cewa, nadafa maki tantabarun kuwa kin ci?
Nace cikin wasa ni dai ki fadawa wanan tsohuwar ta barni haka dai please ?
Yar murmushin jin dadin yadda na mai da mahaifiyar ta tankar kakana tayi,,
Tace don kin samu bat sa kishiba har tana gyaraki aida tabar ki da wa yancan maguzawan kishiyoyin naki ,
Nace aiko in gudo in dawo dakin ta direct don wanan Salawan da kike gani anty nasan za a sha daga da ita,
Cikin muryan na Anty tace gwada mata cewa ke ma fa yar Kebbi ce ba Sanya don kin san mu matan kasan hausa sai wace taso zama bora agidan mijin ta,
Meenatu muda ka bude ido da hudubar zama da miji har kishishiya tun muna kanana,
Zan kai kai saman pillow in gyara kwanci wayana yai kara,
A zatona Babana ne yakira saboxa naga cewa, safiya ne rana batai wani yi ba a lokacin sosai,
Wata nombace da ban san,ta ba, na dauka ina mai kwarara sallama,
Muryan Yaya Abubakar ne naji yana amsa min cikin irin dakewan nan nashi na kullun,
Yaya ina kwana nace cikin siriri yar murya na ahankali,
Sai da naji sauke ajiyan zuciyar shi sanan ya amsa min da cewa lafiya kalau Meenatu,
Sai yai shiru, nima a nawa ban garen dan shirun nayi masa,
Sunana naji ya ambata cikin wani irin murya mai saukewa mutun kasala da cewa,
Meenatu, ina hanyan sokoto yanzu haka zan zo in dauke ki zamu tagi Niger Reporblic,
Ban san lokacin da na maimaita maganan ba da cewa Niger ?
Murmushi naji yayi yace eh Niger, ko bakya zuwa ne yai maki nisa,
Na saki a jiyan zuciya nace zan tafi mana yaya
Yace don kawai mu biyo ta nan mu dauke ki nai wanan tafiyan ta mota,
Na lumshe idona ina tunanen yadda zan tafi Niger, din,
Murya Yaya Abubakar naji yana ceea ko Uncle bazai bari in tafi mashi da yar shi wani kasa ba,
A hankali na sake wani murmushi mai fitar da sautin cool, nace ,a,a ai Uncle baida iko dani kamar kai, ko banza,
Allah dai ya kawo ku lafiya ?' Nace cikin kara lumshe idona, saboda wani irin abu da naji a lokacin,
Na sauke numfashi bayan mun kashe wayan tare da kurawa hanya shigowa dakin ido,
Ina tunanen yadda zan fadawa anty zancen tafiyan nawa,
Kayan wanki yaran ta da aka wanke ta shigo dashi dauke a hannun ta, dakin namu,
Tambayana tayi cikin son jin may yace yai maganan ranan da zaizo kuwa?
Sai da na sada kaina kasa san nan na ce a hankali cewa yayi wai yana hanya zamu tafi Niger ne,
Itama Anty acikin mamaki ta maimaita da cewa Niger shin?
Na kada mata kai alaman eh,
Ba bata lokaci naga anty Amarya ta hau shirya min kaya da kanta,
Sai zuwa karfe daya na rana yaya ya iso shi da driver shin ,
Sai lokacin da na tabbatar da cewa tafiya fa zamu yi ne hawaye yazo min tab ga ido na,
A lokacin Yaya Abubakar suna tare da Uncle dina a folo, suna dan shan drinks,
A falo inda suke zaune da Uncle na samay su inda nadan zagaya gefen Uncle din na durkusa a gaban shi idon yana fitar da hawaye,
Na kasa magana sai dan sheshekan kukan da nakeyi, kawai,
A hankali na iya bude baki ina cewa, Uncle zan tafi,
Kamshin turaren dake jikina Yaya Abubakar yadan shaka abinda hakan ua saukar mai da yar kasala a take har takai ga ya dan lumshe idon shi a hankali,
Ga kukan da nakeyi yana torching din zuciyar shi,
Cikin dakewa ya mike tsaye, tare da yi wata irin murya yai magana da uncle cewa
To zamu kama hanya sai dai in Allah ya dawo damu lafiya sai mu biyo ta dauki kayan ta,
Cikin dan kuka na juya inda su Anty suke tsaye na ce, a sanyaye anty mun tafi,
Wani iri yaji a zuciyar shi don jin abin yakeyi kamar ya jawoni zuwa jikin shi a lokacin ya rarashe ni,,
Mutanen gidan mu na Uncle suna daga min hannu kamar kullun, suna min bye, bye motar mu ta daga,,
Daidai muna fita kwanar layin mu naji hannun Yaya Abubakar a cikin jiki na,
Idona na lumshe lokacin da naji hannun shi a cikin jikina,
A tare muka sauke ajiyan zuciyan lokaci guda,
Muryan shi naji yana cewa bakya son tafiyan ne Meenat,?
A hankali nadago kai na dan kalleshi karo na farko tun zuwan shi,
Yayi wani haske fatan jikin shi sai sheki yakeyi don kyau,
Yar,Sajen faskan shi da ya bari ya dan kwanta mai lub a saman kyakyawan fuskan shi,
A lokacin da yake min maganar ashe idon shi yana a lumshe, ya kara bayan shi a makarin kujera,
Batare da na kara kallon shi ba na ce cikin tausa murya,
Kawai dai, ina jin kewan rabuwa na dasu ne da zamuyi,
A kara cewa amma kuma baki jin dadin kasancewa da yayan ki da zakiyi ko ?
Hmmm kawai na iya cewa batare dai nai magana da baki ba,
Shima din bai kara cewa komai ba sai ji nayi ya kara matse ni a jikin shi tankar wani zai kwace may ni,
Driver sai kwarara gudu yaje a saman titin dake cikin sahara, abin shi,

****** ********** ******
Sam yanzu bata ganewa dodon ta don ya dai yi mata kaman da, da farko,
Irin abinda dafarko yake kawo mata yanzu sam bai kawo wa gashi kuma sai yawan shan ruwa fiye da da,
Gurin bokan ta, ta koma tana sheda mashi irin abin da take ciki da dodon ta yanzu,
Bayan yan dube duben da yayi yadan yi gyaran murya, yace,
Abinda yake samu ga alkawarin da kikai may yanzu ya daina samu shi,
Don kin ga da farko a koda yaushe, yana samu abubuwa irin yadda ya kamata,
Amma kuma yanzu sai yai kwana ki da dama bai samu abin da kikai masa alkawari ba dashi,
Shiru tayi don ba abinda yazo mata arai sai mugun tsohon nan da ya hanata shakat
Watau malam, tsoho, wanda take ganin cewa shine wanda yai mata karan tsaye ga al,amurorin ta,
Dole ne fa tasan abin yi kafin ya kai ta ga makara don idan har tabari ya kai ta bango to asirin ta zai tonu ne ,
Malam boka yace banda wani abinda zan iya maki a halin yanzu sai dai kawai ki yi kokarin aiwatar mashi da bukatan shi,
Sosai zuciyar hajja ya sosu don hankali tashe tabar gidan boka zuwa gida don gudun kar dodo ya bukaci wani abu bata a gida,

Bayan ta dawo gidane ta yanke shawaran zuwa gidan Mama Ladi, don tun,da ta dawo bata samu zuwa, gaishe ta ba,
Sai yau da take da bukatan zuwa don jin halin da gidan na dan ta ke ciki watau gidan yaya Abubakar
Tafe take,cikin shigan zani da riga inda tai mayafi da irin zanin da ke ajikin ta daure,
Malam tsoho wanda tun shigowan hajja uguwar nasu, jikin shi yabashi cewa akwai mugun abinda zai faru,
Bala babban almajirin shine yakira yace ya samo mashi rushin wuta da sauri,
Acan cikin gida hajja na shiga kafin ta kara,sa sashen mama ladi
Sukayi kicibis da matan gidan zaune a karkashin iccen darbejiyan da ya sake masu innuwa a gidan, suna zaman hira a gurin

Atake Rakiya matar Baba Hamza taji kanta yai wani sarawa alokaci guda,
Take tafara ganin guri yana juya mata a hankali hankalin ta ya fara gushewa daga jikin ta,
Wani irin ihu, ta sake a lokaci guda tare da mikewa tsaye,
Duk wanda ke acikin gidan malam tsoho alokacin da kewaye sai da yaji wanan ihun na Rakiya,,,
Gurin hajja Rakiya ta nufa tana cewa ku yi ta kanku wallahi ga diyan macizai nan da kan kare suna lasan jikin ku,
Ai take mata suka sa ihun gida ya rude, wayyo Allah Innalillahi, A,uzubillahi,
Hajja dole ta ja tai tsaye jikin ta sai rawa yakeyi, don kaduwa,
Wuyan ta, Rakiya matar Baba ta, riko dukk idon Rakiya fito waje sai wani yare takeyi, wanda ba wanda ya taba, jin tana wanan yaren, a duniya,
Da guda aka kira mazan da ke kofan gida don su kawo a,gaji,,,
Mama Ladi tafito daga sashen ta tana ta masifa wai an wa kawar kazafi don ana bakin, da ita
Ba wanda ya kulata sai kokarin ganin an banbari Rakiya daga jikin Hajja,
Saidai jama,a duk sun kassa banbaranta daga hannun Rakiya,
Daga bayan Mama Ladi akaji kuwan anty Mariya cikin wani irin ihun tashin hankali wanda duk ya kara ruda gidan,
Sai ihu takeyi tana ?ewa wayyo Allah ga sunan suna shiga jikin ku suna lassa,
Take guri ya kara rudewa da tashin hankali,saboda, yadda Anty mariya take ihun baida dadin saurare sam,

Malam ne yau ya tako da kan shi har zuwa cikin gidan sashen sarakunan shi,
Wani abu ya yarfawa tarun jama,an dake gurin gaba dayan su,,
Wani tsawa malam ya dakawa mariya da Rakiya,
Bala daga bayan shi ya zuba wani hayaki a rushin wuta gaba daya wanda ke gurin ya fara atishawa,,
Sai a lokacin Rakiya ta dan sassauta rikon da taiwa Hajja,
Malam ya tako har zuwa garesu bakin shi dauke da addu,oin tsari,
Cikin tsawa fuska a daure yace Rakiya ku sake mata wuya nace
Ba mussau aka sake Hajja wacce idon ta duk yafito, waje saboda wuya,,
Tana batun gudu malam tsoho ya daka, mata tsawa yace dakata kiji
Cikin daure wan fuska malam ya kalleta abinda yasa hajjin cikin Hajja kadawa,
Don sai tana ganin cewa malam zai tona mata asiri ne sosai,
Ciki kadu malam yq ce ke, saurara ki ji may zan fada maki,
Kinyi babban kuskure da har kika shigo gidana da nufin sheri,
Kai Hajja ta kada alamar a,a
Malam tsoho yace bari kiji ni Abubakar Sambo Manya,
Mugu ko muguwa bazai taba shigowa gida na har gurin iyalai na ya wanye lafiya ba,
Ko ina a raye ko a mace mugu bazai taba samun nasara a gida nan, ba,
Kai ko a makwabtana balle har cikin gida, na ke ki sani cewa, ba yau ba nasan cewa ke muguwa ce ta sosai, amma da baki tabani ba sai ban taba ki ba,,
Yakara kallon ta rai bace yace, daga yau kada ki sake ki kara shigo min gida cikin iyalina,
Fice ki bamu guri muguwa kinji kunya kirasa inda zakiyi sheri wai sai wanan gidan,
Simi, simi Hajja tabar gidan batare da ta waiga ba saboda tsoron malam din,
Kafin wani lokaci har labari ya karade unguwa da gari baki daya cewa hajja mayya ce wai,
Mamaladi duk jikin ta yai sanyi saboda abinda ya faru da aminiyar ta,
Sosai yau tai nadaman zama da Hajja duk da ziciyar ta, na ce mata kazafi akai wa Hajja,
Abu guda ke sa ta gaskan ta zancen saboda tunda ta haifi Mariya bata taba sanin cewa tana da iska ajikin ta ba ,sai yau,
Wanan dalilin yasa Mama ladi ta dan yar da da sherin Hajja,
Baba Buhari ya,shigo gida yana ta masifa da Mama cewa duk gurin kwashe, kwashen ta ta hadu da Hajja da ta zama masu matsala,,
Gashi har kin yi sanadin hada zuri,a da ita yanzun haka kike son diyar ta ta haifa muna jikoki a gidan nan, ?

****** ********* ******
Sai dare muka shiga kasan Niger din,wani babban, hotel din da a kasan aka kama mu na,
Direct, can muka nufa saboda duk sauran abokan tafiyan nashi suna a hotel din,
Ko ina haske ne ya haska farfajiyar hotel din gwanin ban sha,awa,
Tafe muke muna takawa guda guda, saboda steps din da akayi gurin shiga cikin hotel din,
Duk wanda muka wuce sai yadan kara waiga mu saboda yadda mukayi kyau gashi kuma abu ga jini kamar mu guda da yaya Abubakar din,
Muna shiga dakin wayan yaya Abubakar a na kiran shi a lokacin,
Don haka yadan tsaya daga shigowa dakin, abinda na fahinta shine daya daga cikin matan shine yake waya da ita,a lokacin,
Don haka na kara,sa shigewa cikin dakin, inda a hankali na ciren gyalen abaya na da na yafawa kaina,
Saman gadon dakin na aje gyalen, a hankali nake kwabe abayan da na a,za saman kayana,
Ya Abubakar wanda ke waya ina ganin how happy he's, Is ,, a lokacin,
Tufin dana saka daga ciki wanda yadan matsen min jiki yai min kya surar jikina suka fito filli,
Daga gurin da Yaya ya,ke tsaye ya lumshe idon shi don ganin irin yadda na koma a idon shi
Mikewa nayi na jawo yar jakar da nazo da ita na fidda zanin daurin da nazo dashi da hijab,
Yaya yaci gaba da kallona yana mai mamakin yadda a lokaci guda na juya na caza zuwa wata classic lady,
Nai mashi wani irin kyau ga fuska,ko ina nawa ya ciciko a murje na yi wani fresh fatana sai sheki yakeyi,
Lumshe idon shi ya karayi daidai lokacin da na fada bathroom din dakin,
Wanka na yi don inji dadin jikina tare da dauro alwala don in gabatar da sallolin dake tare dani,
A kwance na samu Yaya saman gadon dakin yadan kishingida kafan shiguda na tokare, fuskan shi na kallon kofan bathroom,
Daurin zanin gaba nayi hannuna yana dauke dakayan da na cire a jikina,
Yaya ga ruwan zafi can na hada maka, a bathroom,
Bai amsa min ba sai wani irin kallo da yake min cikin mamaki, yana wani lumshe idon shi a hankali,
Don gani yayi na yi mai wani irin girma a idon shi harda kiba,
Duk wani abinda yake bukata ga irin macen da ya dade yana son ya mallaka a gidan sa ya baiyyana a jikina,
Ganin da nayi cewa bazai bani ansa ba, kawai sai nafara war,ware hijab dina don in ta da Sallah,
Alokacin ne naji muryan Yaya Abubakar yana cewa may yasa baki jirani mun shiga tare ba,?
Murmushi mai sauti kawai nai masa batare da nai magana ba na tayar da Sallana kawai,
Har zuwa lokacin da na kusa sallamay wa na,ga ya mike zuwa wanka,
Bayan ya gama muna Odan abincin da zamuci daren da muka iso,,,
Bayan na idar da sallah ne na mike tare da dan, gyara muna kayan mu, inda na zuba su cikin,
Wardrobe din da nagani a dakin na nufa na sa kayan mu a ciki,
Sai na fitarwa yaya Abubakar, wasu simply kaya don ya saka ajikin shi idan ya fito,
Rigace mai yar guntun hannu da wando tree quarter, na samu acikin kayan na shi
Suna fitar mai don ya saka idan ya fito daga wanka,na kuma feshe mashi su da turare,
Dago kan da zanyi ashe Yaya ya fito, yana zaune a bakin gado daure da towel, sai wani dan karami, da yake ta gugan sumar kan shi da shi,
Idon shi na akaina duk lokacin,,
Kayan da na fitar mai su ya saka ajikin shi bai wani bata lokaci ba ya ta da sallah,
Nagama gyara jikina tsaba yadda ya kama ta batare da na bari ya gane may nakeyi ba, ba,
Daga gurin da yake zaune yana addu,a yadan waigo yana ce min, ki saka hijjab dinki don ga wani nan zai shigo ya kawo muna abinci,
Bamusu da sauri na saka hijab dina akaina, na koma can bayan gefen gado nadan zauna,
Wani buzu ne ya shigo bakin shi dauke da sallama,
A binci ya kawo muna wanda ke dauke da abinsha mai sanyi,
Abincin ba laifi don tankarka kalan namu na Nigeria,


ZEEE MAKAWA YELWA,,,,
[8/10, 9:43 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
5? 0?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH- AL-HAFEEZ,,,

Jumma,at Mubarak,,,

Shafin yau na kine ke ka dai kuma bada kowa ba
SADIYA SIDI MARUBCIYAR, SIDIYA,
Nagode da irin kaunar da kike gwada min,,,,,


Bayan mun karasa, cin abinci ni da kaina na gyara gurin na kawar da kayan abincin a can gefe,
Hand bag dina na bude na ciro daya daga cikin Sweet's din da Anty ta sayo min masu kamshi, nasaka ga baki na,
Wayan Yaya Abubakar yai kar da alamar daga cikin abokan tafiyan shine suke waya,
Nikan sai


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login