Showing 258001 words to 261000 words out of 388021 words

Chapter 87 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8287

ya dauko zancen aure ba,

****** ********** ******
A zaune take tana juya wani abu acikin cup da spoon a hankali take juya abin,
Saida ya juyu da kyau ta dauka ta kai a bakin ta ciki dan rutse fuska duk ta shanye abin kamar yadda aka umurce ta,
Daga gurin da Umman ta take a zaune tana kallon yar tata cikin so da kauna irin ta Da da mahaifi ta cewa yar nata,
Kina shan abu kina wani matse fuska aiko gara ki sha don kin ga har mata uku zaki samu, a gidan,,
Kuma kin san cewa ko wacen su a tsaye take bakin rai akan wanan mijin naku,
Murmushi irin na yan duniya tayi tana cewa ni Umma duk kan su banga wace zata sha min kai ba, daga cikin su,
In don wayan nan matan nashi ne dana sani kuma ita wacan ta Abujan nasa anmin aiki akanta babu wani abinda zai sha min kai,
Murmushin manya uwar tayi tace kaiyya abin badaga nan yake ba Fati,
Ai ke dai ance idan kana da kyau to kara da wanka don ka burge,
Umma duk da nasan cewa bazawarace ni to amma nasan cewa babu wace yake dauke da kaunar ta kamar ni,
Kinga ita Sadiya hadin wanan muguwar mahaifiyar tashi ce,
Gashi yanzu auren nasu ya komawa kowa ciki kamar araba auren akace,
Ita kuma wanan fitsararan yarinya fa hadin wanan tsohon ne mai tsanani da son yin iko ga diyan shi da, jikokin shi,
Kawai ya cuna mashi ita batare da yace yana bukatar ba, don haka kin ga a dole yake zaune da ita,
Ita kuma wacan dayan ance wata yar duniyace duk ta girmay masu agidan wai kila ma har shi maigidan,
Kinga ai bazata gwada min komaiba don idan tana takama da wayewa ne sai dai mu kwata wallahi,
Don haka mama duk kan su wallahi babu wace zata fada min daya ban fada masu goma ba,
Sanan kinga yaran nan duk da su zan tafi tunda ba haihuwa yakeyi ba,
Da sannu duk zan kwashe abina daga sunan hutu in maida su gurina gaba dayan su,,,
Uwar tace kai Fatima ni har kina bani tsoro wani lokaci,
Yanzu ke duk ina kika samu wanan labarin haka, ne wai ?
Tace kai haba Umma sai kace bani bace umhum, umhum fa baibar kowa ba,
Wasu daga cikin yan uwan su muka kaiwa ziyara shine nake jin wanan labarin haka,
shiru tayi kamar mai tunanen wani abu sai kuma ta sake wani shu,umin murmushi wanda ita kadai tasan may take nufi,
Uwar tace kindai ji may yayan ki yace da zaran ya turo kada atsaya wani daukan lokaci mai tsawo kawai a daura aure,
Yace idan ba hakaba zai iya cewa ya fasa don da yawa daga cikin si basu kaunar shiganki gidan ,
Tace ko sunki ko sun so sai na shiga kuma har na hada zuria da su,
Allah yasa inji uwar ba kunya yar ta ansa da fadar Ameen Umma,

****** ********** ******
Kamar kullun yau ma agajiye nadawo daga school,
Inda na samu abinci mai zafi naci na sha ruwa don in dan kara sararawa,
Anty Amarya ce ta shigo dakin fuskan ta kawai na kalla na fahinci bata acikin walwalla a tare da ita,
Don haka sai na tattara hankali zuwa gareta don jin may ke faruwa a tare da ita,
Idon ta yakai ga plate din da na ci abinci acikin sa tare da cup din ruwan dana sha a gefen,
Kokarin zama takeyi amma kuma tana tambayana cewa kin ko koshin Meenatu ?
Nai murmushi tare da kada mata kai alamar cewa eh na ko shi ,
Sai takai zaune a daidai gefena ta sami guri ta zauna ,,,,

ZEEE MAKAWA YELWA,,,,
[9/29, 10:01 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
7? 9?

ZAINAB IDRIS MAKAWA,

ALLAH AL AHA,D

JUMMA,ATU MUBARAK TO ALL, MUSLIMS SISTERS IN ISLAM,,,,WISH YOU ALL THE BEST OF LUCK OF THESE DAY ALLAHUMA AMEEN =?O?=?O?=?O?=?O?


Ganin irin yanayin zaman da Anty Amarya, tayi yasani gane cewa da magana tazo gare ni,,
Don haka sai na dan dago daga kwanciyar balance din da nayi da farko don in saurare ta,
Ganin duk hankali,na yana a gare ta yasa ta dan tsura min ido nawani dan lokaci,
Zeenatu na ji ta kira sunana a hankali don haka na dago kai a hankali na sauke idona gare ta, cikin girmamawa ,
Shiru ya dan biyo baya tare da dan tsarguwa daga gareni,
Can naji ta ce don Alkah magana nazo da shi kusan daya zuwa biyu ko uku ma,
Da fatan zaki fahinceni a hankali ki gane may nake nufi, don haka ki kwantar da hankaliki ki facinceni da kunnen basira,
Na gyada kai cikin girmamawa alaman na fahinci mai take bukata daga gareni,
Meenatu ke dai musulmace ko nai sauri dago kai nace eh duk da,gabana ya fadi don jin may tace min ,
Don wanan kalman yana fitowa ne ga bakin bahaushe ya yin da za,a ce wa mutun yayi hakkuri da wani babban kaddara da zai samu mutum,
Don haka sai naji wani irin tsoro da fargaba ya kamani a lokaci guda,
Ta cigaba da cewa don haka kin san cewa duk namijin musulmi wanda yake da hali,
Shari,a ta yarda mai da cewa ya aje mace fiye da daya,
Idan ma yana da dama shari,a ta yarda mai, har hudu yana mai iya ajewa ,
Nace hakane, tace to don haka saboda Allah ko kadan ban son inji ko inga kin tayar da hankalinki ga auren da mijinku zai kara, kwanan nan,
Duk da naji zafin maganan amma sai nai kokarin yin dariyar yake nace wallahi Anty da farko har gabana ya fadi,
Don ina cewa ko wani babban al,amarine ya faru wanda kike son ki fada min don inji,
Kallon mamaki da tausayi take min don sai take gani ban san ciwon kaina ba ke nan,
Taci gaba da cewa, sai dai kuma ita wanan amaryan taku ta yanzu da alaman akwai aiki a tare da ita, ga yadda na samu labarinta,
Mamaki naji yadda har Anty Amarya ta samu wannan labarin haka,
Muryan ta ne ya katse ni tana cewa, kuma kinga yanzu sai mu godewa Allah, tunda har mun santa mun san takon ta,
Sai dai zamu kwanta ne gaba dayan su muga gudun su, tukun na,
Don kin san wasu kishiyoyi baki sanin suna kaunar ki ko ba su kaunar ki,
Sai miji ya kara aure zaki gane true colour din su sosai,
Don idan suna sonki kishine kawai ba zasu nemi hadin kai da bakuwar amarya ba,
Idan ko kishin ya rikida ya koma kiyayya to da zaran wata tashigo zaki ga cewa tabaki baya kwata,kwata ta koma ga waccan wai da sunan hadin kai kawai wai don a yake ki,
A tare zasu dinga kawo maki hari wai da sunan hadin kai, alhalin su kan su basu bar junan su ba a lokacin,
Don dai duk sunan kishi kisjine idan an hada miji guda zama guda mai sunan kishi,
Tace kin ga yanzu zaman ki a nan wani rufin asirine Allah yai maki don a tsakanin su zai fara fita kafin ki koma,
Ta ce sai zance na biyu shine, ina kayan lefen da kikace maigidan naku yai maki,
A hankali na dago fuska na wanda ke acikin yanayin damuwa a lokacin nace yana nan tace good,
Kin ce min ba wanda yaga kayan sai Ramatu mai aikin ku ko nace mata eh Anty,
Tace masha Allah tare da dan sauke murmushi a fuskan ta , tace, yanzu akwai yadda za,a yi kayan su fita gidan ba tare da wani yagani ba,
Shiru nayi ina nazari a cikin zuciya ta zuwa dan wani lokaci can dago kai nadube ta ina cewa akwai yadda za,a yi,
Zan kira Ramatu in fada mata tare da Babana Hamza da Baba Wadda ,sai su kai min gidan su Fattu tace masha Allah haka yayi kyau sosai wallahi Allah ya bamu sa,a nace Ameen,
Tace sai kayan sun iso zaki san ko may zamuyi da su anan nace mata toh Anty nagode tace shin godiya na may fa ?
Kinga yanzu abinda zamuyi shine kawai ki kwantar da hankalin ki don dai kinga kina cikin lalura ,
Ba,a son mace mai ciki tana yawan tunane ko damuwa don haka don Allah don Annabi kada kiyarda ki sawa kanki damuwa akan Da namiji ko kadan,
Nace a hankali insha Allahu ba zanyi ba don tun farko Mama na ta yi man nasiha sosai a kan hakan,
Tace hakan na da kyau aishi dama namiji badon mace guda akayi shi ba ,
Duk macen da Allah ya nufa sai ya aura a rayuwar shi sai ya aure ta insha Allahu,
Daga haka ta mike tana cewa, ok sai kin kira Ramatun munji mai zata iya yi akai na amsa da cewa, toh na kara cewa nagode,,,

****** ********** ******
Kamar yadda na umurci Baba Ramatu tayi da su Baba Hamza haka akayi din,
Cikin yardan Allah har su ka kwashe kayan ?nty Sadiya wace ke daki tana sana,an ta na barci, bata san anyi ba,
Baba, Hamza shi da kanshi ya kawo min kayan sokoto har gidan Uncle dina,
Munyi mashi taro na arziki don yaji dadi sosai irin yadda aka karramashi a gidan,
Wani karamin hotel Uncle ya kama mashi kwana biyu, da zai yi a garin,
Nan ne yake ce, min cewa yaga maigida yana son yayi yan gyare, gyaren gida saboda ya ga an kira engines sun zo su na duban, gida,,
Ina kallon Anty wace tai min signal da ido cewa lalai zancen auren ne, yazo kusa,
Nan yake kuma kara sheda muna cewa a cikin hiran mu, yaga Salawatu suna rikci da Oga har tana ta kuka tana cewa,
Bai kyauta mata ba don ko shekara batayi ba,a gidan shi zai mata haka may yake nufi ne wai da zai mata wanan tozar cin,
Yace ina daga bakin get tankar bana jin su naji ya bata amsa da cewa
Duk wace ke iya zama ta zauna wace taga cewa bazata iya ba hanya a bude yake mata,
Daga haka ya tafi yabar ta a gurin cikin tashin hankali da masifa,
A zotana ba ta gidan don kwana biyu ban ganta ba sai ranan da wanan tantiriyar kawar na, ta, mai shigar yan iska,
Daga inda nake zaune nayi murmushi azuciyata nace ashe ba ni kadai bace ke wa wanan matar kallon yar iska haka,
Hamza yaci gaba da cewa yana gani kamar kwanan na za,a fara aikin gyaran gidan don yaga masu aikin gidan shigan su biyu suna aunawa,
Nan dai su kai ta hiran su a tsakanin shi da Anty Amarya wanda hiran duk ya kumshi mutanen gidan mu, na can,,
Zuwa tsawon wani lokaci suka dauka a zaune kafin ya tashi zuwa masaukin shi ya huta a can tare da yi muna sai da safe,,
Yana tafiya Anty Amarya ta juyo gurin da nake a zaune tare da sauke ajiyan zuciya tana cewa,
Watau dai wanan mutumin yana nugin cewa sai ya kara wanan auren ke nan dai,
Murmushi mai kama da yake nai mata ina cewa shi yasani don shi ke da aiki a kai,
Anty tace ni farin cikina guda da yake baki tare da su can ke kadai
Azuciyana nace ai komai dadewa sai na zauna tare da su din ni kadai,

****** ********** ******
Engineers ne tare da sauran maikata a kowani part na gidan namu kowa da irin abinda yakeyi a lokacin,
Lawal mijin Fattu shine wanda ke tare da su tana kula da aiyukan da akeyi,
Fitowan maigidan daga cikin gida wanda alamata nuna a fuskan shi cewa daga barci yake a lokacin,
Sun gaisa da su Lawal din inda yake dan duba aiyukan Lawal tare da wasu suba bin bayan shi a hankali,
Daidai saitin bayan dakina inda zan zauna da sabuwar amaryan shi wace ke daga gefe na kadan dakin da Baba Ramatu take zaune da farko a cikin sa,
Lawal ne ya jefowa Yaya Abubakar zance da cewa amma maigida da wanan filin an karawa Amina shi don filin yana da yawa sosai,
Baidamu da rashin sauraren da tsayawan da maigidan baiyi ba sai yaci gaba da zancen shi yana cewa,
Kaga ita mai jama,a ce idan mutanen gida sukazi a gurin ta dole zasu sauka,
Gashi kuma amfara samun iyali a tsakani sai nake ga kaman idan an kara mata daki guda daga haka gurin zai kara yin kyau sosai,
Bai cewa Lawal wanda ya bashi wanan shawaran komai ba sai ma cewa da yayiwa ma,aikatar ku tabbatar da cewa kun sa concrete da yawa a gurin nan,
Indai miskilanci ne da rashin ko in kula irin na Yaya Abubakar izuwa yanzu da suka hadu da Lawal da shi Lawal din ya saba da halin shi sosai,
Don haka ko yanzu sai bai dauki wanan bin ba na yan zu ko kadan a rayuwan shi,
Ya tafi kara cement ne ko da ya dawo ya samu yan kara jan daki babba mai girma tare da fitar da plan mai kyau a guri,
Murmushi kawai yayi a ransa don yasan halin Abubakar sosai zuwa yanzu,
Abubuwa da dama sun taru sun rikice mai a lokaci guda don ga tafiyan su saudiya ga kuma gyaran gida da aure, a gaban shi,
Don hakane ma yanzu baida wani enough time din kan shi ko da yaushe busy yake,
A na cikin hakane zancen zuwa wani course da zai fita waje ya taso don haka ya fara shirin tafiya,
Tare da Salawatu zasuyi tafiyan hakan duk yana acikin halaiyar maza idan sun maka laifi don su dan sa maka jin relief a zuciya,
Ba karya ba kuwa don hakan yadan sa ta rage zafin kishin da take ji a lokacin,

Wanan labarin yana samun Fatima duk sai ta tada hankalin ta sosai akai,
Zaune take da mahaifiyar ta inda take cewa amma Umma sai nake ganin kamar idan aka dauki lokaci wanan mutumin zai iya cewa ya fasa auren nan,
Saboda may kika ce haka uwar ke tambayan yar nata cikin nuna damuwan ta da kulawanta gare ta,
Fatima tace wa mahaifiyar Umma ai kamata yayi ace yasa an daura wanan auren sai mu tafi tare, takarashe a cikin shagwaba,
Kai fati kin faye garaje wai may kike ci na baka nazuba ne ,,
Kwana nawane idan kin shiga da sannu, sannu komai zai dawo gare ki a hankali,
Sai kuma suka sa shewa ita da uwar kamar wasu kawayen juna,
Mahaifiyar tace ai bari gaba zamusa shi daga shi har wanan abokin nashi da wai bai son a takura mai,
Aiko hakan ne saigashi duk Fatima ta jagula wa Yaya Abubakar zuciya da kukan fili da korafi da kuma text ba kakautawa, a kullun,
Wanan abin ya matukar tayar mai da hankali har gashi Aliyu da kan shi yake bashi shawaran cewa a daura aure ya barta a gida har yadawo don hakan zai sa hankalin Fatima da mahaifiyar su ya dan kwanta,
Nauyi da kunyar Aliyu yasa Yaya Abubakar neman magabatan shi don su gabatar da zancen a wajen magabatan ,Fatima din,,,

****** ********** ******
Washegari da wuri nadawo daga makaranta saboda banda lectures da yawa a ranan,
Anty Amarya ta shigo dakin da nake a kwance tana cewa,
Meenatu ya kamata yau mu bude kayan nan muga abinda ke cikin shi kafin in fada maki dalilina na cewa azo da su nan,
Itace ke cire su guda guda sai dai ina ganin tana zaban wasu daga cikin tana ajewa a gefen ta, ni dai nawa idone a tsakanin mu,
Ta sauke ajiyan zuciya tare da cewa, tirkashi, lalai anzuba kudi wurin nan Meenatu,
Tamaida kayan a cikin kowani akwati kamar yadda suke da jere da farko a cikin akwatunan,
Sai tazauna saman gado a gefena tana mai sauke numfashi a hankali,
Tace min Meenatu kinga wa yan nan kayan dana zabe su daban
Na amsa da cewa "eh a hankali,
Sai naga ta gyara zamanta ana mai fuskantana tana cewa,
Zamu ajesu ne sai idan Allah ya sauke ki lafiya sai ,mu kara da wa yanda kika samu mu kaiwa mama Ladi a matsayin kayan goyon ki,
Da sauri na dago kai na dubi Anty ta gyada min kai tana cewa eh kwarai da gaske Meena
Don kin san cewa na fada mata cewa sai mun dafa kifi da ruwan shi anci,
Don haka sai ki barni da ita don zata razana saboda bazatayi tsanmanin cewa zamu samu tsadaddun zannuwa hakaba na gani na fada,,
Kinga ai ko bata san sunan su ba za,a fada mata,
Murmushi nayi a zuciya ta nace kai Anty hoo karan bana maganin zomon bana ke nan,
Tace sauran shiri a hankali zanci gaba dayin su,
A raina nace ni,dai Allah ya saukeni lafiya ya kawo min saukin haihuwa cikin lumana ,
Ban san har addu,an yafito a


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login