Showing 330001 words to 333000 words out of 388021 words

Chapter 111 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8301

kwana uku kenan jikin na Mama, ba dadi,
Yaya yabada Umurnin cewa azo da ita don a duba lafiyanta hakan zaifi, sauki don likitan da yafara dubata yana nan,
Anty Safiya ta karba da cewa insha Allahu zasu shigo da ita zuwa banda gobe,,
Yagama wayan hankalin shi a tashe yana cewa wanan jikin na mama yana tayar min da hankali wallahi,
Salawatu tace kila bata tsare dokokine, da likita ya fada mata ko,
Ita ko Fatima sai cewa tayi, ai ko a can Birnin Kebbi akawai likitoci zasu iya dubata,
Sadiya batace tsiki sure ba sai dan wasan da takewa Amir daga nesa tankar bata jimu ba ma
Zaune yake kan shi yana a duke sai system din shi yake dan latsawa a hankali,
A hankali na kai bayana kwance, a saman kujeran dake a kusa dani daga inda nake zaune a kasa,
Nace kawai dai gara a kawo ta nan tunda likitan ta yana garin nan ya duba ta zaifi barin ta a can don a fan fresh zasu koma ga bincike,,
Shiru sukayi don basu ji dadin zancena ba saboda gaba dayan su basu kaunar zuwan Mama Abuja, ta zauna a tare da su,,
Ni kan jin duk anyi shiru a falon ya sakani mikewa don dama duk a takure nake a gurin,,
Na dauki Amir dake zaune yana ta gwalanci a kasa nake ce masu Allah ya bamu alheri suka karba aciki,ciki da fadan Allah ya kaimu Lafiya,
Sam yazu ban son cin abinci idan naji kamshi dufuwan abinci sai naji amai ya kamani,
Yau ma ina shiga sai amai yazo min inda nashiga bathroom nadinga shega shi, wanka na yi kafin na fito
A kasalance nafito daga bathroom din na haye gadona ina maida numfashi guda guda cikin wani irin yanayi,
Ramatu tace Uwar dakina nashigo na samu Amir a godo shikadai yana kuka a she kina daga ciki kina mai,e,
A uwar dakina ba kani Amir zai samu ba kuwa don dai naga cewa, aman nan yana yawan damun ki,
Ras, ras, ras gabana ya fadi inda da sauri nakai kallona ga dana dan wata takwas,
Wanda yake goye a bayan Ramatu yana barci hankali a kwance,
Da sauri nace haba dai Ramatu, haba wanan aiba fatan alheri kike min ba,
Du, du har yaushe na haihu da zaki mun wanan fatan haka, kina son na kashe dan mutane ne halan,
A maimakon ta bana rai sai naga kawai tana murmushi acikin rashin jin haushin zance na
Kwance nake amma na kasa barci saboda nazarin da nakeyi akan zancen Baba Ramatu,
Wata zuciya dai tace min kawai irin zancen sune na manya kawai take min,
Daga haka ban kara sa zancen a raina ba sai kawai na ci gaba da harkokina,
cikin ikon Allah kuma sai, na samu saukin aman dake yawan damuna,hakan yasani mantawa da kokomai,
Ranan da Mama zata shigo Abuja ranan nice da girki don haka abinci na musan man na girka ma su abinci lafiyayye da kaina,,
Matsala guda shine ban san ko wai daki Mama take sauka ba idan ta zo, kuma sai ban tambaya kowa ba, nace a raina idan tazo zangani da idon,
Basu samu shigowa garin ba sai musalin karfe shidda na yamma sun shigo a gajiye don sun sha wahala a hanya,


ZEEE MAKAWA YELWA
[11/20, 10:00 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
9? 6?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH AR RAUF



Nai masu taro na musan man don, sai rawa jiki nake da zuwa su saboda sai nake gani tankar duk gidan mu ne gaba daya suka zo Abuja,
Kayan su naga an aje a can gefe guda bayan kujera falo,
Abu na farko da na fara yi shine nace wa Anty Mariya Anty wani daki kuke sauka nakai maku kayan ku,
Shiru ba amsa sai cewa tayi aiko a nan ma ki barsu babu damuwa,
Hakan nayi nabar kayan a guri guda nagaba tar masu da abinci,
Yaya Abubakar yashigo suka gaisa yana zaune yana tambayan yadda jikin ke mata yanzu,
Idon shi yana akan kulolin alfarman da yaga na aje agaban su, hakan yadan saka shi sauke ajiyan zuciya,
Bayan na kammal komai nake cewa Anty mariya ko zaki dan watsa ruwa kuji dadin jikin ku,
Tace gaskiya hakan zaifi don mun kwaso gajiya a tare da mu sosai, wallahi,
Nace a dakin Anty Sadiya kuke sauka aiko ?
Ta ce wata Sadiya ai tun zuwan mu na farko bamu kara sauka ko ina ba saboda kikiri Sadiya ta nuna muna cewa bata zama damu a dakin ta,
Subbahanallahi nace na dan tsaya tsaye kamar mai nazari,
Part dina na fada na gyara dayan dakin guda wanda na sauke su Dije da Mama Sa,a a cikin sa,
Na saka room fresh kamshi na tashi ko ina sai zanin gado bargo mai laushi na aje masu don rufa saboda sanyin da akeyi a garin,,
Jakan kayan su da sauran komatsen su na dauka zuwa dakin ina zaune har suka ci abinci na kwashe kayan zuwa kitchen,
Duk da irin daure fuskan da Mama take min bai sa na nuna mata wani bacin rai ko kuma nuna nagane nufin ta ba,
Kokarin kara jan Anty Mariya da fira nakeyi na mutanen gida tana bani amsa,
A cikin haka, nace Anty aida ku shiga daga ciki ko zaku dan huta ko,
Wani tabure fuska Mama, tayi tare da dan tsukewa tace aiko anan ma zamu kwanta don nan din ma ai yayi,
Yaya Abubakar wanda ke daga gefe guda zaune yace ai sanyi ba zai barku kuyi barci ba anan din, ?nty Mariya tace Mama kin san ance ki daina zama a cikin sayi ko,
Don haka ba don Mama ta so ba su ka shiga daga cikin, sai raraba idanuwa Mama su ke,yi suna kallon dakina,,
Wanka na fara sa su kayi din su yi barci da dadin,
Sai da na tabbatar da cewa na gabatar masu da komai da zasu iya buka ta na shirya zuwa part din maigida,
Amir na fara kaiwa, inda na dawo na kwashi sauran abubuwa daga ciki har da ruwan zafin shan shayin Yayana,
Shigan farko na samu yana bathroom har na shimfide Amir na fito bai fito daga wanka ba, na samay shi a tsakar daki yana goge ruwa a kan shi tare da dan combing din kan shiba hankali,
Jin motsin shigowana yasa shi dan juyawa a hankali tare da dan fara,a a fuskan shi,
Ba kowane zai gane hakan ba sai ire, iren mu matan shi, ,
Yanzu da ki kafita kibar min yaro shi kadai kwance a daki idan dodon Hajja yazo ya lashe min shi fa,
Dariya maganan tashi tabani inda nace, ai kaida danka kunfi karfin dodon ta don da ba hakaba, da baka samu dan ba har yanzu Allah yana tare da ku akoda yaushe,
Ya lumshe udon jin dadi yana cewa insga,Allah sai ta, Alkah badai mutum ba ko Aljan,
Mamakin tayi barci ke nan ko ?
Ya tambaya tare da kallon fuskana yana son jin amsan tambayan shi,
Nace ayayin da nake kokarin zuwa gaban mirror inda yake a tsaye,
Saida naga sun kwanta nafito dafa dakin don kuma nazo na karasa aikin ladana tunda na samu na Mama yanzu kuma sai na samu na maigidana, ko,
Na karashe zancen cikin dan juya idanuwa acikin sallon yanayin jan hankali,
Ina matsowa gab da shi, naji kamshin turaren da yake fesawa a hammatan shi ya, daki hancina,
Kaina naji ya wani sarawa tare da juyawan yan hanjin cikina a lokaci guda,
Da sauri na juya, na dakata da zuwa gurin shi da nai niyar yi da farko, wani irin amaine yazo min a lokaci guda,
Bathroom din dakin Yayana nashiga inda naduka sai ko na shiga haraswa baji ba gani, har na wani dan lokaci,
Da kyat na,samu na iya kurkure baki na namike don na fito daga bandakin,
Yayana Abubakar ya na tsaye a kofan hannayen shi a harde cikin dan uwa yana sakar min wani kallon tuhuma,
Kokarin nake nadan bi ta gefen shi na rabashi na wuce zuwa bedroom, don babu abin da nake so sai kwanciya a lokacin,
May yasa may ki haka ?
ina dan haki ina kokarin shigewa nace abincin da naci ne yana da sanyi shine zuciyana ke tashi,
Ina shigewa na kwanta don duk jikina ba karfi a lokacin saboda ya sake,
Amna a hakan Yayana ya bukace dole badon naso ba na daure har ya cin ma gurin shi sai dai zuwa dare jikina yadau zafi,
A wahalce na kwana ranan duk dana gasa jikina da ruwa masu zafi sosai kafin nayi barci,
Amma Allah da ikon shi sai gashi na samu lafiya zuwa safe tankar bani bace a daren jiya na kwana nishi don zafin ciwo,
Kitchen na shiga inda na samu Baba Ramatu har tayi nisa ga girki ko a tare muka karasa ina goye da Amir a bayana, har muka karasa na jera a saman dining table,
Na kaiwa su Mama nasu a dakin da suke aciki inda nabar masu Amir na fito zuwa kitsa jikina,
Zani da rigan atamface a jikina din half gown, akai min iya gwaiwa, a falo na samu Salawatu tare da maigidan suna magana,
Ganin su a tarene ya sakani, juyawa sai muryan shi naji yana cewa kitsaya, mana
Nace zan jena dawo ne amma sai naji yana cewa yanzu dai ku shirya don ko ita Meenatu tana son ganin likita ai,
Da sauri na juyo ina cewa ai ni naji sauki Yaya dama don kawai,sanyi da yai ya wane ya jawo min zafin jikin,
Kallon mamaki yake min na yadda nace mai wai lafiyata kalau bayan yasan cewa a wahalce na kwana daren jiya,
Dakin, da su Mama suke na nufa ida na samu suna shiri kamar yadda ya, umurce su da yi,
Saboda idan basuyi sammako ba zasu dauki lokaci mai tsawo basuga likita ba,
Da mama zata fita take ce min nabar mata miyan kodan danai masu pepper soup din shi idan ta dawo zata sha, nace mama idan kin dawo ai sai nai maki wani da dare ko,
Cikin dan tabe baki tace tunda kun samu abincin banza ba dole ku dinga barnar shi ba,
Don na gajarce fadan sai cewa nayi bari na dauka nasaka a cikin fridge har ta dawo sai a gyra mata, din,

****** ********** ******
An kara kwantar da mama don ta samu hutu kamar yadda likita yabada Umurni
Duk da ba wai lafiyan jikina nakeji ban yarda na kwantaba don duk wani dawai niyar asibiti nice mai yi na dafa na kuma kai, masu da kaina
Yau ma abinci na kawo masu na rana anan na samu ya Abubakar har da su Baba Wadda,, Sadiya da Fatima da Salawa,
Nai mamaki kwarai don ganin su a nan azato na du suna gida ashe gidan ma ba kowa, a lokacin,
Da sallama na shigo dakin ina mai fara gaishe su saboda su na samu dole nice zan gaida mutane,,
Aiban karasa rufe baki ba naji muryan Mama Ladi a cikin fada tana cewa daga kwance inda take,
Yanzu ke don ba Saratu bane ko Sama,ila shiyasa kikaki kawo muna abinci da wuri haka,
Tsit dakin yayi don jin abinda Mama Ladi ta fada sai anty Mariya ce ke cewa, haba Mama kin san abubuwan yawa gare su,,kuma duk ita daya,
Baba Waddana a cikin fada yace ke wallahi Ladi matsala ce yanzu ba gashi an kawo maki abincin ba,
Duk kishiyoyi na dake tsaye sai wani dadi suke ji saboda irin kojenin da mama takeyi ga kuna zagi har da iyayye na,
Shiko Yaya Abubakar wani irin nauyi da kunya ne suka ziyarce shi a lokaci guda,
Nace cikin dakewa Baba yunwa take ji kila don na tsaya hada mata fruit sald ne,
Na dan juyo fuska a sake babu wani alaman bacin rai ga zagin da Mama tai wa iyayyena ina cewa
Mama, ki fara shan fruit din zai fi kama maki ciki kafin kici abinci,
Wanan anyi yar muguwa yanzu duk da yunwan da nace maki ina ji shi ne zaki ce wai kada naci abinci insha wani abu can daban,
Murmushi bayi nacs Mama bari to na zubo maki abincin amma kadan ko,
Tsuki tayi don jin haushi takawar da kanta gefe guda saboda wai takaici,
Suko abokan zama na sai ido suke bin mu dashi babu wace tai magana daga cikin su,
Haka ya nuna min cewa ba fitowan Allah da Annabi sukayi ba killa, dokace ko umurni daga mai gidan,
Cibin farko da Mama takai a bakin ta sai cewa tayi kai abinci haka da shegen yaji ga kuma man banza an samu an tsulala,
Gaba daya idon mu yakai ga abincin da tace wai mai yayi yawa a ciki babu mai sam a sama,
?nty mariya ce ke ce min ina kikabar yaron Meena, ?
Nace cikin murmushi yana gurin Mama n Bi,u ta dawo daga garin su shine suka tafi shi da Ramatu,,
Wacece maman Bi,u Mama ta tambaya bakin ta tab da loman tuwon da ta cika,
Baba Wadda yace yau kuma tunda yar ki ta dawo baki san matar kirkin da kike cewa ba ko ?
Hararan shi tayi tana cewa kai dai ka sani yace ai kin fini sani yanzu dai nuna min abincin da kika kasa cinyewa, don mai da Yajin da su kai yawa a cikin shi,
Gaba dayan mu plate din dake gabanta muka kalla duk ta lashe abincin da na zuba mata mai yawa,
Ta dago ido a lokacin da take kai loman karshe tana cewa ai nasan kana cikin masu son in mutu,,
Yace sai in gyarawa Sa,a dakin nan da kike har zuwa nata tazauna ita kadai ba karin kishiya,
Ai ko ta dago da idon ta da suka canza ta fara ,zaga mai bala,i ya fita yana dariya,
Yaya Abubakar wanda tun shigowana yana aiki a cikin computer shine ya dago tare da rufe computer yana cewa barin shiga office in dawo ,
Fatima ce ke cewa abinci fa yana cikin mota na zubo maka fa don nasan kana nan,
Kallon mamaki akai mata tunda ta iya zuwa da abinci amma ana cewa mama tana jin yunwa batace komai ba,
Yace, bazanci ba ki koma dashi kawai, ajiyan zuciya Mama ta sauke wanda kowan mu yaji ta,
Alaman cewa Yaya Abubakar ya ku ru don da yace zaici da ta mai masifa akai,,
Ya,fita daga dakin inda Fatima mai duty a ranan ta mara mai baya suka fita tare,
Namike na zubawa Mama fruit din a cikin karamin abin shan fruit tare da saka cibi shina ta shanye daga haka na gyara, wurin ta dan kwanta don ta huta,
Sai barci ya dauke ta nan muka fara hira a tsakanin mu zinda na gane cewa fada yaya yai masu na sai sun shigo asibitin dole,
Don Salawatu ce ke cewa Sadiya mutafi ko tunda ya wuce office may zamu tsaya jira kuma,
A waje suka samu Fatima tana waya, inda suka tsaya jiranta saboda itace ta jawo su zuwa,
Sai da takarasa abinda take sannan tazo suka tafi ita da Salawatu a gaba zaune Sadiya tana zaune a baya,,
Fatima tace, a lokacin da take shan kwana, yau Mama tai maganin mai iyye,iyye,
Wake nan inji Salawatu take tambaya duk da ta fahinta da zancen,
Sai Fatima tace Meena mana yar iyayya, wai ita a dole ga yar gida,
Saida Salawatu ta dubi window take cewa kuma ai bata damu da zagin da akaimata ba,
Daga bayan mota Sadiya data dan gyara zaman ta tace, ai inda sabo Meenatu ta saba da halin Mama,
Saboda ita ta tayar da ita may zai zama mata sabo daga halin ta kuma,
Da sauri Salawatu uwar gulma ta juyo inda Sadiya take zaune tana cewa don Allah da gaske a gurin Mama Meenatu ta tashi,
Sadiya tace Allah kuwa don dai ni a nan na santa lokacin tana karama,,
Wallahi wanan yarinyar tafaye kankajelin tsiya haba dai mutumiyar kodai duk a cikin kishine,
Salawatu ce ke cewa Fatima hakana a lokacin da tace Meenatu a kwai iyayi,
Kudai kuna sakawa yarinyar nan ido amma ai Meenatu ita halintane hakana bawai wani abubane,
Don ni suna zuwa hutu a gurina duk cikin su tafisu zafin nama don ita bata da kyashin sai wani yayi abu zatayi,
Hmmmm inji Fatima dake kokarin shiga cikin wani plaza don za suyi sayayya aciki,

****** ********** ******
Shigowan shi gidan yau direct sama ya hau bai tsaya jiran komai ba ko shiga gurin wata ba,
Kasan cewa nice da girki yau yasani bin bayan shi don in mai ya dawo lafiya,,
Babu kowa a dakin sai sanyin AC da kamshi dake tashi da zaran ka sakai shigowa dakin,,
A can saman gado na hango shi yai kwance rigingine ko kafan shi bai cire ba,
Da sallama dauke a bakina na


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login