Showing 270001 words to 273000 words out of 388021 words

Chapter 91 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8232

akayi kuma kuma kun gyara kuskuren bashi ke nan sai mai girki ta dora inda aka tsaya,
Da wani irin mamaki Fatima take kallon maigidan dashi don ba tai tsanmanin jin hakan ba daga bakin shi,
Sai duban shi take yi a cikin mamaki tare da dan jijiga kai tace a ziciyar ta lalai namiji abarshi kawai,
Inda ya kara bata tsoro shine ganin ya mike tsaye yana kallon fuskokin su a cikin bacin rai,yana, kara fuskantar ta yayin da ta sauke mai,firgitattun idanun ta da suka nuna kankanci,ya na cewa, daga haka bana son inkara jin muryan kowa again, daga haka ya shige part din shi,
Jiki a sabule Fatima ta dauki, jug din drinks din ta zuwa part din ta,
Inda rayuwan ta yayi dubu ya baci a ranan saboda bata mata tsari da Salawatu tayi,
Ita kuma Sadiya ai dama sun saba kar tasan kar tun suna gida,
Tun wanan lokacin bata fito waje ba tana dakin ta tana waya da yaranta, don zuciyar ta ya kwanta,
Salawatu, ce ya kamata tai taking over, din duty ranan, don dama itace zatayi,
Amma sai tace wa Sadiya ta dauka don abin ya dawo ma su normal according to tsarin shigar su gidan,

****** ********** ******
Zuwa yanzu nayi nauyi sosai na zama wata irin cikakkan mace
Cikin jikina ya zauna min das a jikina yayi wani irin turowa sosai,
Ni dai nakan ga anty takawo min ruwan abubuwa wai insha, na rage zaki,
Bana mussawa nake karba nashanye shi a duk lokacin da ta bani din,
Sai adduan lahaula, da nakeyi kullun a cup kafa goma sha bakwai na shanye,
Ina zaune a gaban mirror muna waya da Baba Ramatu wace ta bugo min don mu gaisa,
Ban taba tambayar ta may ke faruwa a gidan mu ba a baya na,
Haka itama Baba Ramatun bata taba fada min komai daga zancen zaman su ba,
Tambayana tayi da cewa wai uwar dakina yaushe ne zaki dawo,
Murmushi mai sauti na yi mata ina cewa Ramatu ai ni da garin ku sai idan Allah ya sauke ni lafiya,
Ramatu tace kai haba dai uwar dakina naji Alhaji nacewa ai kina tafe kwanan nan ,
Nace gaskiya Ramatu ni bazan je ko ina ba don bazasu dade ba zasu wuce zuwa saudiya ne,
Ramatu ce aiko dai ga gida nan yasha gyara kowa ta shige a cikin nata,
Nai saurin katseta da cewa ai idan da rabon in shiga komai dadewa zan samu nawa na jirana,
Mun dan dade da Ramatu muna waya tana bani labarin diyan ta, da irin cigaban da ta samu yanzu,

Duk irin yadda Yaya Abubakar yaso nazo Abuja hakan baiyi ba saboda dan zazzabin da nayi yayin da mukai hutu,
Dole ba don ya so ba yabar ni a gida don babu yadda zaiyi,
Don hakane ma ya shirya zuwa dubana tare da zuwa gida.
Fatima taso ace ta biyo shi su zo tare amma saiyake ce matabai zuwa da kowadaga cikin su,
ayan yazo yaga irin yadda a lokaci kan kani na wani zama big madam sai da ya tausaya min,
Wanan ganin da yai min yasa shi ya sauko da fushin da yakeyi da farko,
Don yana ganin cewa, dan ban son zuwane kawai na kirkiro wa kaina ciwo,
Duk yadda yaga kafafuna sun kumbura da kuma jikina yadda ya koma min duk na wani hakewa,
Bai, so ya wuce zuwa Birnin Kebbi a ranan saboda yadda yaso ya kasance dani,
Ina saye a cikin dogon riga baki dan kasan Jordan, ya kara sani yin kyaun masu ciki idan na bada baya yana nuna mazauna na irin yadda suka ciko min,
Na shiga daga ciki don in dauko mai takardan asibiti na ya gani saboda yace sam bai yarda da cewa na tafi asibiti ba.
Ina juyawa yabi bayana da kallon sha,awa yayin da yadan lumshe kyawawan idanuwan shi a hankali,
A hankali idon shi a dan lumshe ya furta sunana da cewa Hmmm MEENAT,
Ya dan furza iskan da ya gunda a bakinshi ya na cewa a cikin ran shi,
Kunya natsuwa kamun kai, rikon addini, ga sanin ya kamata,,
Meenatu kin samu tarbiya ingantattace wanda ya sa maki zama kamilar mace a rayuwan ki,
Babu kwadayin komai a tare da zaman ta da ni babu zancen cewa bani nasai kaza ,zanje gurin abu kaza ,
Baikai ga karshen zancen zucin shi ba na dawo daga ciki hannuna dauke da farar takardan asibiti,
Har na karaso gurin da yake zaune idon shi yana akaina na mika mai a cikin ladabi,
Inda yakarba naji yana sauke ajiyan zuciya a hankali,
Gefen hannun kujeran da yake a zaune na samu gefe guda na zauna, da kyat tare da cije baki,
Yayi daidai da ya dago kai zai tambayeni zancen waya biya kudin maganin don yaga suna da yawa,
Ganin yanayi na sai yaji wani irin tausayi na ya kama shi a zuciya, yace a hankali may ke faruwa kuma cikin nuna concern din shi gare ni,
Saida nadan kara ya muta fuska don a gaskiya bana jin dadi sam,
Nake cewa, a hankali bakomai kawai dai ban jin dadin jikin nawa har yanzu,
Ya rasa may zaice min sai dai dogon ajiyan zuciyar da yayi yake cewa in daure mu tafi Birnin Kebbi a ranan,
Ban kai ga magana ba Anty Amarya tashigo falon bakin ta dauke da sallama,
Sun dan kara gaisawa dashi inda take cewa asibiti sun bata, Edd, cewa nan da two week ko kafin shi zata iya haihuwa,
Da sauri ya juyo gurin da nake zaune yayin da zancen su yadan sakani jin kunya sai wasa nakeyi da yan tsun hannu na, a hankali,
Dan jingina yayi da kujera yayin da yake jin wani irin zafi yana fita mai daga jikin shi,
Yace ina ganin ni zan fasa tafiyan nan don dai kada sai mun tafi kuma ta haihu ba ma nan,
Duk kan mu da Anty abin ya bamu dariya amma sai na dan sake murmushi mai sauti,
Anty ce tai karfin halin cewa ai da kana nan da baka nan duk Allah ne mai yin komai,
Allah dai ya kaiku lafiya, ku dawo lafiya ka samu bako ko bakuwa acikin yan taron ka da ti maka sannu da zuwa,
A hankali ya murmusa tare da sa hannu a cikin aljihun shi ya ciro, dan kyallen shi na goge fuska,
Yana cewa da yau naso mu tafi tare Birnin Kebbi da ita to amma kuma sai nake ga zata ma iya zuwa a hakan, naso taje suyi sallama da Baba ne wai,
Gurin da nake Anty ta duba tana cewa zaki iya zuwa, mana Meenatu kuyi bye, bye da su,
Nace zan iya a hankali don haka dole tafiyan ta kama dani ke nan,
Ban dauki wasu kaya masu yawa ba don nasan kwana biyu kila zamu yi,

Koda muka isa dare yayi a lokacin amma ba wani sai ba don haka direct masauki ya wuce dani,
Wai a cewan shi nagaji sosai kuma ba wai ba a gaskiya ranan nagaji sosai din don na dade banyi zama irin wanan din ba,
Nai wanka nayi sallah, inda aka kawo muna abinci lafiyayye a cikin kuloli masu kyau,
Ganin kyawon kulolin yasani zargin cewa daga gidan su Fatima wanan abincin ya fito,
Ina cikin tunanen naji takun shigowan yaya Abubakar wanda yadan fita da dadewa, yashigo dakin ,
Gurin da abinci yaje a cikin basket ya kalla da sauri ganin ban taba ba yasa shi saurin kalloni,
May yasa baki ci abincin ba har yanzun nan haka gashi kin san cewa bake kadai bace,
Murmushi nayi ina cewa abincin ne ban san daga ina aka kawo muna ba,
Kai tsaye yake ceea mahaifitar Fatima ce ta hada muna shi don tasan zamu zo,
Nima kai tsaye na ce mai ai ni da kai duk muna da mahaifa kuma sun san cewa zamu zo yau din,
Don haka ni ba zanci abincin gidan kowa ba tunda ba bakuwa nake ba agarin,
Mamaki sosai yaji don shi sam baiga abin cewa wani abu a nan ba don kawai an kawo muna abinci,
Ban tsaya jiran komai, ba nafara kokarin gyarawa na hau gado na kwanta, don dama agajiye nake lokacin,
Ido ya zuba min da mamaki don ganin iyakar gaskiyana ke nan zan kwanta da yunwa,
Nikan har na kai kwance don yasan bazanci abincin ba ke nan tunda har na kwanta,
A hankali na lumshe idona sai wani irin takaici dake dibana don dama nasan cewa zan iya cinkaro da irin haka ko daga Aliyu ne,
Murya yaya ji yana kiran yaya Mustaph wai yazo mai da kaji da drinks nace a raina da yafi dai,
Muryan shi naji daga bayana yana cewa, zaki dai ci kazan ko ?
Da kyat na iya amsawa dacewa ummmumm cikin bacin rai,
Idona a runtse yayin da Yaya ya shiga wanka, ina tunanen cewa ai a sashen Baba na yake cin abinci tun yana samartakan shi,
Sai yanzune zata tsiro wani tsurku cewa wai daga gidan ta za,a kawo muna abinci,

Shima yaya, a lokacin yana bayi sai tunanen wanan irin rashin jittuwan dake a tsakanin kowacen mu da Fatima yake yi,
Amma duk ace gaba dayan mu babu wace zata sha da dadi daga gare ta,
Yace kai itama Fatima akwaita da son iyayi ne in bashiba ai tasan muna da gida may na cewa a dafo mai abinci daga gidan su,
Hakana yafito rai abace saboda sai ya rasa may ke mai dadi a lokavin kawai rayuwan shi yaji ya baci gashi kuma yana jin yun wa don tin karyawan da yayi ne da zaifito daga gida ke cikin shi,
Yana gama shiryawa yaya Mustapha ya bugo mai waya gashi waje a lokacin,
Baidadeba yadawo dauke da ledoji a hannuwan shi yana cewa ki tashi kici tun bai yi sanyi ba fa,
Bamusu don dama ina jin yunwa sosai don bazan iya barciba banci abinci yadda nake ji,
Sosai na ci abincin hankali na a kwance, na gama na samu guri na Kwanta don inyi barci,,
Sai can zuwa dare naji bin da Yaya ke min abinda yasani bude idona kenan, a hankali tare da dan sauke numfashina a hankali,,,


ZEEE MAKAWA YELWA
[10/8, 1:36 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
8? 2?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH- AL- MUQADIR


Yan uwa muslmai, fatan alheri gare ku, a koda yaushe, kaunar ku da addu,an ku a gareni tankar wani taki ne, mai kara min girma da albarka ga al,amarina,
Nagode nagode nagode kwarai da irin kulawan da kuke gwada min,,,,,,



Fuskan Yaya Abubakar yana dauke da murmushi har barci ya kwashe shi a haka, yana tunanen irin bawai war da Allah yai ma wanan yarinyar haka,
Natsuwa gamsuwa da kwanciyar hankali inganttaciya sai idan ya kasance da Meenatu,
Gashi kuma yau yaji ta kara canza mai a fiye da kullum da yasan ta,
Duk da cikin ta ya tsufa amma sai ya samu gam suwa ta daban daga gare ta wanda ya sa shi farin ciki da annashuwa,
Ya tambayi kamshi da kamshi cewa kenan wanan yanayin ya mayar da Meenatu haka ko ya dai,
Nikam ban san may ya ke ciki ba sai kwance nake ina barci na a hankalina kwance,
Sai jin hannuwan shi nayi ya kara rungumoni zuwa jikin shi yayi da naji ya sauke wani irin ajiyan zuciya da karfi,
Tare da kara rungumo ni zuwa jikin shi ya dan matse ne a hankali yana sauke numfashi a hankali,
Abinda ya dan sani bude idona a hankali daga barcin da yadan fara dauka na saboda duk a gajiye nake a lokacin,
Kiss naji yakai min a daidai kumci na alaman godiya da sai da safe ,

Washe gari mun tashi duk a gajiye ban san ya akayi ba ina ganin ankawo breakfast a gidan su Fatima,
Amma sai naji yana cewa a fita da shi, aba yan ma,aikatan gurin masaukin,
Ina ganin haka nace a raina tare da wani irin lumshe idona ina cewa yan raini hankali kawai,
Naso na koma barci amma sai kuma cikina dake bukatan na sa mai wani abu saboda wani irin yunwa da nake ji,
Don haka sai ban tsaya ba na mike na kara shiga wanka ida na fito na fara shiryawa,
Yaya Abubakar, ya shigo dakin yana min kallon mamaki ganin cewa ina shirin fita,
Ina kokarin rolling a kaina nake cewa cikin dan bata fuska wallahi yaya gida zan tafi yunwa nake ji sosai,
Dariya naso bashi ganin irin yadda har jikina yake rawa a lokacin,
Inda nake tsaye ya kara yayin da ya tallafo cikin nawa a hankali yana cewa
Oh, I am,so sorry dear, laifin Daddy ne ko yasa ka wahala last night,?
Murmushi nayi don jin may Yaya Abubakar ke cewa,
Nace a hankali ai, baby bai fushi da Daddy, shi, kawai dai yunwa muke ji,
Dariya yayi mai kama da yake don shi ba muyltum bane mai washe baki a gurin dariya,
Yana cewa an kawo maku abinci kun ce bazaku ci ba ,,

Mun shiga gidan mu lokacin rana yadan tasa mutane sai hada,hada dan su, su keyi na yau da kullun wanda haka al,adan rayuwan dan Adam yake,
Saida na shiga part din mahaifana inda na aje handbag dina, na nufi sauran part din gidan namu,
Mutane sai sannu da zuwa suke min da kara yi min kallon kurullah,
A part din su Mama Ladi gurin gwago Sa,a kishiyar ta na fara zuwa gaida ita,
Daga baya na dawo gurin Mama Ladi, inda na samu har yaya Abubakar ya shigo suna zaune tare da ita,
Tun da ta hangoni naga ta daure fuskan ta tamau daga yar fara,ar da takeyi da farko,
Saida na dafa dan kujeran dake dakin ta wanda Yaya, Abubakar yake zaune, akai,
Na samu na kai zaune saman tabarman dake shimfide akasa dakin
Nai mata ina kwana da mun samay su lafiya ?
Yau abinda mamaki don na samu amsawan kwarai daga gare ta ba kamar kullun ba,
Amma sai na dan ganta hakan da cewa ko don dan ta ya na zaune a gurin ne, zato dai (zunubi ne, )
Muryan ta naji tana cewa kamar da gaske amma dai, yanzu ke kusa hauhuwa ko ?
Ban amsa mata ba don amsawa rashin kunya ne ga manya don haka sai nai shiru kawai,
Yaya Abubakar ne wando idon shi yana ga wayan dake hannun shi ke cewa insha Allahu kila kafin mu tafi ta haihu,
Wani irin naga Mama Ladi tayi tana cewa, to aiko gara in haihu tun kafin su wuce din,
Nidai ban ce komai ba sai dan wasa da gefen tabarman da nake zaune na keyi,kawai,
Dashi da mahaifiyar shi ce kawai suke tahiran su suna magana akan Safiya da mijin ta yanzu bai aikin komai kamar da can baya,
A hankali na yunkura na mike don komawa part din mu gurin Mama Yaya Abubakar ya bini da ido a hankali, yana cewa, ina kuma,zaki
Nace cikin dan ya mutsa fuska gurin Mama sare zanje ko da fura a fridge na sha,
Ok kawai yace sai bayan fitanane mama tai wani irin ta dubi dan nata tana cewa
Allah mai iko yanzu ni jikana na farko da zangani a gurin ka ta wa yan nan munafukan mutanen zai fito min,
Mutanen da ko mutun yafi aula dubura baya taba gane cikin su sun iya, kisisina kamar yunwar cikin su,
Dubi yadda take wani karairaya kamar diyan wani da wata can sai mutum yace ba diyar Samaila da Saratu bane tallakan banza da wofi,
Haba haba Mama wanan ba kyau fa ina dai yarinyar nan diyar ki ce itama,
A,a wallah, mi add hadin kifi da kaska
Babu abinda na hada dasu don dai ni wallahi tallahi kaina kadai naga kana ra,ayin zama da wagga diyan in bashi ba da tuni na kakabe ta cikin kayana,
Mi akai da babbakun iri irin diyan Fuldenu masu gaje guri yazam nasu,,
Yaya Abubakar wanda zari ya ishe shi yace, waima ina son ganin Safiya don mu san abin yi a kan zancen haihuwan Meenatu,
Da sauri Mama tace mi zakayi har wani shiri na zakayi su mi aggaresu da zasuyi wanda har za,a kashe masu garali irin haka,
Ya mike tsaye yana cewa mama ni ban damu da zancen suna da shi ko ba su dashi ba,
Meenatu dai ko banza kaunata ce ita, ina da ikon yi mata irin yadda zanyiwa Safiya ko Samira, a rayuwa,
Don haka ni bance sai sunyi min wani dawainiya ba mai yawa can,,
Sannan kuma abinda ke cikin cikin ta ai dana ne jinane jininki ne kema don haka babu zancen yi dole,
Daga haka yasa kai yana cewa hello, hello a cikin wayar shi,

****** ********** ******
Zaune ni da mahaifiyata itama babu zancen da take min sai na yadda za,ayi fitar kunyar haihuwana,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login