Showing 63001 words to 66000 words out of 388021 words

Chapter 22 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8237

lafiya,

Wani iri zuciyar shi yai mai a lokacin ji yake kamar zai kama da wuta,
Don bakin ciki, wanan ai shine adake ka a hana,ka kuka,
A lokacin ji ya yi tankar kada ya dawo gida Nigeria saboda takaice,
Mata biyu duk kunjun babu mai tada wani daga cikin su,
Daga gurin da yake ya kwana atakure batare da yata shi zuwa bedroom din shi ba,
Abubakar mutum ne wanda bai iya boyo ba sam a rayuwar shi
,Don haka yakira sahibar shi Salawatu don su gaisa,
Bayan sun gaisa da ita sai tadan fara mai irin sha,gwaban da ta saba yi mashi
Sunan ta ya kira awani irin yanayi wanda har sai,da salawatun ta natsu,
Yace mata maganar dazan fada maki yanzu ban son ki tayar da hankalin ki,
Nayi auren last month, da water, blood sister dina da muke kaka guda,
What tace cikin wani karaji,,,,
Ba bata lokaci tafara sheshekar kuka kamar wata karamar yarinya,

,
ZEEE MAKAWA YELWA
[7/18, 10:06 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
2? 7?

ZAINAB IDRIS MAKAWA


ALLAH- AL WAHHAAB,,,,



Acikin dare ya dawo daga, don haka abokin shi ya dauko shi daga airport zuwa gida,
Mamaki kwarai ya kama Lawal abokin shi ganin irin yadda suk samu gidan a hargitse,
Sai dai bai ce komai ba don ba yau ne farkon zuwan shi gidan ba da har zai yi mamaki,
Mamakin shi guda ne shine, mace tasan cewa mijin ta yai irin wanan tafiyan mai muhin manci har wata kasa yadawo amma babu wani canji daga gare ta,
Wai wanan matar wata irin mace ce, ita
Agaban shi yana kallon shi Abubakar da kan shi ya nufi gurin da fridge yake ya dauko goran ruwa yakafa kai ya sha,.
Kallon gidan yayi da kyau bayan tafiyan Lawal abokin shi yana nan kamar yadda ya bar shi tun tafiya shi,,,,,
Tun bayan dawo, wan Abubakar Nigeria yau kwana biyu ke nan yana gida yana hutawa,
Sai dai zuciyar shi a cike take da maganganu da yawa,
Da yam, Abubakar ya shirya acikkin wasu yadi milk,colour,
Dinkin rigar mai gajeren hannu, ne ,anyi wa wuyar rigar dan aiki kadan daga sama,
Takalmin da zasu shiga da kayan yasa inda kuma ya kara feshe jikin shi da turare,mai kamshi,
Motar shi guda ce ya fitar wace tasha wanki gurin masu wankin mota,
A tafe yake yana tukin motar a hankali saboda zuciyar shi da ke cikin damuwa kala,kala,
Abubuwa izuwa yanzu sun mai yawa acikin rayuwar shi, a lokaci guda,
Gidan Lawal ya nu fa a,lokacin don can ne yake jin zai iya tun,kara, don yaji sanyi,
Motar ya samu gefe guda a kofan gidan Lawal din ya Parker, ta,
Sai da ya tabbatar da cewa ya kulle ko ina na motar,
Ya wuce kofan gidan direct yana mai kwankwasawa,
Juyawa yayi yana kallon irin yanayin uguwar a hankali irin gurin da yake son ya,samu gurin da babu yawan haya niya,
Karan bude kofan Lawal ne ya sashi jiyowa a lokaci guda daga irin kallon da yakewa nahiyar da abokin aikin nashi yake,
Hannu su ka bawa junan su don gaisawa kamar yadda sunna tace,
Sanin cewa da yayi Lawal ba zaune yake da iyalin,shi ba a Abuja don mahaifiyar shi tai mai TARKO, akan sai ya bar matar a gidan,
Saboda idan yazo da ita birni zai dade baizo gida bane,
Shiko sai ya samu wata kafa ta holewa agarin Abujan abin shi,
A tare suka shiga gidan Abubakar na cewa yakama fa ace zuwa yanzu madam ta dawo hakana,
Lawal din yace wallahi nima yanzu naso haka kodon karatun yaron nan don ya girma yanzu,
Fadawa saman kujera Abubakar yayi , da ga gurin da yaje zaune, kallo guda za kai mai kasan cewa, rayuwar shi babu dadi,
Daga inda Lawal yake zaune ya tsurawa abokin nashi ido,
Saboda yasan cewa akwai abinda yau yake damun abokin nashi,
Don ba haka ya saba ganin shi ba Abubakar mutun ne dama wanda baida yawan surutu kuma, bai faye nishadi ba,
Sai dai yanayin na yau yafi na kullun don alamomi sun nuna sosai,
Gashi dai ga ido wanan tafiyan da ya yi kasan turai tasashi yakara fari ga dan jiki da yakara yai wani fresh da shi,
Muryan Lawal ce tadan sa shi dagowa kadan a,lokacin da yaji Lawal na cewa,
Wai ko lafiya na gan ka kazama wani irin so weak, ?
Jikinka duk a mace mana ?
A hankali Abubakar yadan dan dago kan shi daga jikin kujera yana mai furzar da iska daga bakin shi tare da lumshe idanun shi,
Ido Lawal ya tsura mai tate da tattaro hankalin shi ga Abubakar din,
Shiru sukayi gaba dayan su ba mai magana daga cikin su,
Shi Lawal ido kawai ya tsura mai don yasan zuciyar shi ce ke suya,watakila?
Sai da ya dan nisa kadan sannan yafara magana kamar wanda bai son bude baki,
A cikin yan dakikoki Abubakar din ya jerowa Lawal irin danyen hukuncin da iyayyen shi musan man kakan shi ya yanke mai na yimashi aure da yar uwar shi ba,tare da sanin shi ba,
Lawal ya ce cikin dariya kai amma kai dan gata ne Abubakar,?
Wani kallon kai wawane ya manno wa lawal a lokaci guda,
Yanzu ashe ma abin alheri ne ya samay ka shi ne har katayar min da hankali haka,
Wallahi na dauka ko wani babban matsalane kake ciki,
Abubakar yace kasan da alkawarin da naiwa mutumiya ta ko ?
Fuska Lawal ya daure a lokaci guda yace wakenan ?
Badai wanan tsohowar Salawa ba da ban san may kagani a jikin ta ba,
Wai ko dai wanan big breast din nata ke rudin kane man ?
Cikin wani irin yanayin murya Abubakar yace kaji ilar ku masu sa ido, ni yanzu yadda zan fadawa Salawatu na kara nake tunane
A fusace Lawal ya ce ina rukan da wata Salawatu can,
Tunda har Allah ya rufa asiri ya baka yar uwar ka agida,
Shima Abubakar cin wani murya kamar zaki yace na fada maka cewa ina son abina haka zan aureta,
Kallon shi a,cikin mamaki Lawal ke yi, ya tako zuwa har ida Abubakar din yake zaune cikin rudani
Lawal yace ka kwantar da hankalinka abokina wanan abu mai saukine ,,
Ni a gani na wani babban wahala ne ka,ke son jawowa kanka,
Salawatu zaman ta a cikin irin matan mu na kasan Hausa,
Idon shi ya rufe gaba daya wanan karon tare da kwanta da bayan shi a saman kujera,,,,
Lawal yace ka rufawa kan,ka asiri ka kama yar uwar ka kamar yadda iyayyen ku su kai maku gata,
Shin wai kana ganin ita ma yarinyar ba ta,da wanda take so ne ? amma tai hakkuri tai biyayya ga , iyayyen ta,
Haka kai,ma dole ka hakkura ka yi biyayya don gamawa da duniya lafiya,,
Har zuwa yanzu shiru, ya,ke idon shi a rufe tankar mai barci,
Zuwa can ya dan yi huci kamar kosasshen doki,
Ina zan samu gida mai girma don in sake wuri,
Don wanan da muke a ciki bazan iya zama da mata biyu a wanan gidan ba,
Kabari za,a samo maka idan nai magana da Musa, dillali,
Ok kawai yace tare da mikewa ya kwashi keys din motan shi da wayoyin shi ya nufi hanyar fita,

****** ******** ******
Cikin yan watan nin da akayi Meenat ta soma mantawa da zancen da ke damun ta a lokacin,
Jikin ta ya soma wani irin, can,zawa a lokaci guda,
Saboda irin kyakyawan kulawan da Anty amarya ke bani a lokacin,
Jikina ya fito yanzu sosai, har da dan tsayi nakara, mazaunan bayan na da kirjin na sun ciciko, yanzu ya fito da kyau,
Yanzu Anty amarya ta koya man gyaran kai, da amfani da man,gyara gashi, kala,kala,
Hakan yasa gashina ya kara tsayi da taushi har da,wani santsi, ya sauko har zuwa kafadu na
Kamanni, na, na jinin fulani ya fito yanzu da kyau,

Izuwa yanzu duk na cire wani damuwa a tare da ni, na manta da zancen wai wani aure,
Izuwa yanzun duk wani girki na zamani da yai suna Anty ta koya min,
Kwalliya yanzu nasan yadda ake sa kaya irin yadda yadace
Yadda Anty Amarya ke kula da uncle tun daga tatali, nu na mai so da kauna, tsafta kissa tarairaya mutanen gida da na waje,
A lokaci lokaci mu,kan yi waya da mahaifina ko mama na da yan uwa, na
?nty Samira takan kirani mu gaisa wasu lokutan,
Sai dai kiran nata kamar duk zolaya ce nake gani don sheri takan min sosai a hiran,

****** ******** ******
Kamshi kawai ke tashi tun bai fito daga dakin ba gidan ya kaure da kamshi mai dadi,
Ya fito falon yana ko,karin daura, agogo a hannun shi,
Key din motar shi ya dauka asaman TV stand, gurin da yake yawan ajewa,
Sadiya wace ke zaune tana waya tabi shi da idanu,
Alokavin ne shima ya gama daura agogon shi ya dago kai ya kalle ta,
Zan dan fita sai na dawo,
Har ya fara hanya yadan juyo yana ce mata ina ganin zamu tashi daga gidan nan bada dadewa ba,
Maimakon Sadiya ta nuna farin cikin ta ko rashin jin dadin ta sai kawai tai tankar bata ji may yace ba sai dan dakalar wayan ta take yi,
Yana tafe, yana dan dube dube, a cikin motar shi,
Tsaraban da ya sayo mata yake kokarin dubawa gurin da ya aje,
A can kasar case ya hango dan kit din da ke dauke da sarka,
Wayan shi yadauko don yasheda mata cewa yana kan hanya zuwa gurin ta
fa,
Kira daya ga na biyu ta daga wayan a cikin jin dadin rashin barin ta da Abubakar bai yi ba, har izuwa yanzu,
Tsaye yake inda ya jingina jikin shi a motar shi,
Wayar shi ya dauka ya kira ta don ya sheda mata cewa, ya iso,
Fararen kujerun roba guda,biyu ta bayar akawo masu waje don su zaune,
Komawa yayi mota, ya dauko dan kit din nan da ya zo mata dashi tare da sauran tarkace,
A lokacin ne Salawatu tafito acikin wani shiga ta matsastun kayan, ajikin ta sai dan gyale da, ta, ya fa a kafadar ta,,
Cikin wani irin murya tana kararaiya take mashi oyoyo,
Bayan sun dan gaisa ne sun yi ya bayan rabo tare da tambayar shi jama,an shi,
Can tai shiru yayin da Abubakar yake dan duke da kan shi yana dakilar wayan shi,
Tambaya ta jefo mai da cewa yanzu shi ke nan ba zai aure ta ba yake nufi
Tambayar ta ya,yi da cewa waya fada mata hakan ?
Wani dadi ne ya kamata don jin may yace?
Shi ma tambaya ya jefo mata, a,lokacin yace,
Zaki yarda ki zama ta uku, ko ?
Shiru tayi can tace, indai har da kai zan zauna aiko ta hudune zan zauna,
Good to ki,bari idan na tafi, gida garin mu, zamu zauna da yan uwa na, a gida,
Zan dawo da zan mu insha Allah don musan idan zamu kwana,
Dadi sosai Meenat taji a lokacin don dai har yanzu alama ya nuna cewa yana ra,ayin ta,

****** ******** ******
Ranan Alhamis ya bakunci garin birnin kebbi don ganin lafiyan iyayyen da yan uwa,,
Daganin shi kasan cewa ya zama wani babba i,yanzu mai cin gashin kan shi,
Kwarjinin shi yakara haskawa, hasken shi ya fito sosai,
Ya aje saje a fuskan shi yai mashi kyau, kamar wani balarabe,
Tun daga nesa Malam tsoho ya hango irin yadda jikan shi Allah yai masa daukaka a lokaci guda,
Godiya yaiwa Allah ubangiji subbahanahu, wata,allah,
Yakara godewa Allah da ya nuna mai wanan baiwar daga zurian shi,,,
Da murmushi a fuskan shi yake taron jikan nashi tun daga nesa,
Amma sai ya ga yau Abubakar din ya dan daure mashi fuskan shi ba kamar kullun irin yadda suka saba taron junan su ba,,
Kara murmusawa ya yi a cikin hikima don yasan cewa har yanzu, jikan nashi yana fushi dashi ke nan
Duk da haka bai nuwa Abubakar ya fahinci may ya,ke nufi ba,
Da murnan shi kamar kullun yake cewa bakin England, ne tafe a wanan lokacin,
Eh malam nine,
Yayin da yake ta kokarin cire takalmin kafar shi kamar kullun don girmamawa,
Malam mun samay ku lafiya, yace a yayin da yake kokarin zaunawa,
Kafin su gaisa da malam jama,a har sun fara, taruwa don mashi sannu da zuwa,
Hakan yasa yadan dakata da malam din ya fara gaisawa da mutane,
Motar da yazo da ita, ta dauki hankalin jama,a da dama saboda girman Jeep din,
Bashi ya samu kan shi ba sai gab da magribba a lokacin har malam tsoho yafara alwala ko,
Don haka shima ya mike ya suri butan da ke kusa dashi, don dauro alwalan,
Malam na cikin massalaci yana sallah don haka ya wuce zuwa cikin gida gurin Mahaifiyar shi,
Wace tunzuwan shi tankar tayi tsuntsuwa ta fito gurin da suke zaune da Malam don kar ya zuga shi ya karbi auren da suka lakakka mashi na Meenatu,
Ta aika yan leken asiri sun fi mutum uku don aga ko suna wani zancen siri da kakan nashi,
Amma sai yaran su koma suce mai basu ma tare da malam din,

Zaune yake a sashen Mahaifiyarshi, a saman tabarman roban da ta shimfida mai,
A hankali yake bin dakin da kallo yana kallon mamaki,
Don sai yaga ai babu komai a dakin sai dai kuma ya dan juya yana fuskan tar Mama Ladi,
Wace, ta,koma saman gadon katakon dake dakin nata,
Kamshi Abubakar duk ya gauraye dakin sai tashi yakeyi,
Mama mun samay ku lafiya,?
Yaya jama,a ?
Ya wajen su yaya Mariya ?
Da sauran yan uwa, ?
Duk lafiya lau suke,, ya aiki ?
Kadawo lafiya ?
Wallahi lafiya kalau Mama,
Yaya wajen iyalinka tana lafiya ko ?
Lafiya lau Mama,,,
Mama tace to madallah,
Dan shiru yayi can yadago kai yana fuskantar Mahaifiyar na shi,
Yaya gajin buki da kuka sha ?
A take fuskan ta ya canza a lokaci guda,
Kana can kaji yadda tsohon nan ya gwada muna son rai, da son zuciya ko ?
Murmushi ya sauke tare da ajiyan zuciya yace naji yadda abin ya faru ai Mama,
Na fada masu gaskiya wanan zancen ba mai yuyuwa bane, sam,
Ai kana da yan uwa da mahaifan su suka fito cikki guda da naka mahaifin ,
May yasa ba, hada su da kai ba sai wa, yan nan bakin irin nagidan mu za,a laka maka,
Don a mallake min kai in kasa gane maka kamar yadda uwar ta, ta hana ubanta kara aure,
Wani iri yaji a cikin zuciyar shi don yasan cewa a,kwai fitina ke nan a tsakanin mahaifiyar shi da shi akan wanan zancen,
Don dai shi a gaskiya bazai iya tozar ta wanan dan tsohon mai mutunci acikin fadin shiyan su ba,
Murmushi ya sake tare da ajiyan zuciya ya ce watau al,amarin ne ba shawara aciki wallahi,
Amma aini ba auren gida naso in kara yi ba,a yanzu,,
A,to, na,dai fada masu su san yadda za suyi da yar su maikama da zubin yanyawa,
Mama barin je in dan ga su Baba a waje don ba mu gaisai dasu ba na shigo,
To abinci fa?
Ko, sai ka dawo zaka ci ?




ZEEE MAKAWA YELWA
[7/19, 8:37 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
2? 8?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH-AL-RAAZZAQ,,,,

FATAN, ALHERI GAREKU
Duk masoya Novel,s din ZAINAB MAKAWA
JINJINA GAREKU
Mamana, Aishatu Shehu, Maimoto Zaria,
Antyna Nafisat Aliyu Harzami Kano,
Anty Safinatu Mahmud Maiduguri, (Abuja),
Anty Safiya Abdullahi Huguma
Maman Farida,
Anty Mariya SB
Besty na Jamila Sufiyanu,
Da duk wace ya kamata in rubata ban samu tubutawa bs,
Nagode kwarai don da taimakon ku na kai a hakan,


Tafe yake maganganun Mama Ladi yana mashi yawo a kwakwalwan shi
Daidai fitar shi kofar gida yai daidai da dawo wan Baba Samaila daga gurin jigilar shi,
Yana kokarin dauko leda daga gefen shi, ledace da ya siyo tsaraban kauye daga ciki,
Baba Samaila mutun ne wanda bai zama, a cikin gari sam yana daji gurin bidan kudi koda yaushe,
Ganin


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login