Showing 111001 words to 114000 words out of 388021 words

Chapter 38 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8279

cikin wanan lokacin ne ya bani mamaki,
Nomban yaya Abubakar ne kiran yai matukar ba ni mamaki sosai don baya kirana da rana sau dadare lokacin da yasan cewa ina free,
Bayan na dauka mun gaisa yake sheda min cewa yana hanya ya kusa shigowa sokoto, zai tafi Birnin kebbi,
A hankali na ke tambayan shi ko lafiya zai yi tafiya haka, shine ya ke tambayana acikin mamaki banda labarin mama tana asibiti kwana biyu kenan,
Cikin wani irin murya nake cewa subbahanallahi,
Banda labari gaskiya, ban san da zancen ciwon mama ba haka, gaskiya
A take na nu damuwa da kullawa na ta hanya ce
O ni Allah mama may yasamay ta haka, ?
Allah ka dube mu da idon rahaman ka ya Allah,
Sosai yaji dadin jin yadda na nuna concern di na akan mahaifiyar shi ,
Batare da na nuna bata kauna in nuna jin dadina akan ciwon ta ba
Muryan yaya Abubakar ne naji yana cewa ban san ko kina free ba don ina son in tsaya indauke ki don mu je tare
Ina school ne yaya amma zan kira Anty Amarya ta fadawa uncle dina,
Ok zaki samu zuwa ko in wuce kawai ya fada cikin nuna dan bacin rai,
Amsa na bashi da cewa zan tafi,
Sai naji yai wani yar sanyayar ajiyan zuciya lokaci guda tare da cewa sai na shigo zan kira ki,

Bayan kashe wayan ne nai shiru sai kuma naga banda enough time na tunane don haka na kira Anty Amarya na shedawa yadda mukayi da yayana,
Murmushi naji tayi tare da cewa Meenatu akwai ki da shirmay,
Uncle din ki yanzu yana da iko a kanki ne dazai ce bazaki bi mijin ki ba
Balle gida zaku gurin mahaifiyar shi wace ke fama da jiki,
Ki yi sauri duk inda kike ki dawo gida, ki shirya kanfi ya iso,
Sosai Anty Amarya ta min shirin gagawa na ban mamaki,
Don ina kallon yadda tai ta min jike jike da kuma yan sauran dabarun mata,,
Sai bayan biyar ya shigo garin sokoto inda nai mashi kwatancen gidan uncle din mu, suka karaso,
Driver ne ke jan motar shi kadai zaune, a bayan motar,
Masha Allah, kalman da su Mummy suka furta ke nan
Yayin da yaya Abubakar yasamay su waje tayowa yan uwan ta rakiya,
Nan take sheda masu cewa ai, tana ganin shine Mijin meenatu,
A lokacin anty Amarya tafito, daga cikin gida don tai min rakiya,
Kafan shi wanda yasa wasu bakaken takalma sai wani irin walkiya yakeyi,
Yafar fitarwa, daga cikin motan a hankali, sanan ya fito da gangan jikin shi wanda, ke saye cikin wsu yadin silky mai laushin da sulbi,
Annurin shi duk ya cika gurin ga zatin shi mai daukan idon al,umma,
Cikin wani irin tafiya na kasaita wanda bawai da gangan yakeyi ba halitta,ne hakana din, kawai, ya karaso gurin su mummy din,
Ya gaisa da su Anty da mummy cikin mutunci da girmamawa,
Muka kama hanya, zuwa gida garin mu Birnin Kebbi,
Tun shigana motar inda yake zaune a baya cikin dan gyara zaman shi,
Batare da ya kalli gurin da nake zaune ba naji hannu yaya daidai saitin kunkuruna,
Ya kamoni zuwa jikin shi tare da sauke wani irin ajiyan zuciya,
Ya kike yace yayin da yake kokarin sunsunar wuya da hancin shi,
Ganin a kwai driver a gaban motan yasa ni dan kara kama jikina kadan daga abin da yaya ke min,
Zance Anty Amarya ne ya fado min a raina cewan da tayi yau sai na daure, don zan ya bawa aya zaki, gurin yayana,
A hankali nacewa yayan nawa ya hanya?
Ya labarin jikin Mama kuma,?
Hannu na ya damke a cikin nashi tare da dan matsewa a hankali,
Sai ya dan ja ajiyar zuciya a fili yace Alhamdullahi cikin kada kai,
Kafin muyi wani magana kuma wayan shi ce akakira,
A yadda nake tsanmani daga gurin aikin sune wanan kiran saboda irin bayanan da naji yanayi da mai shi,
Dankali da su tumatari din hanya danagani anasayar wa na saba dama idan zan tafi gida in tsaya insaiwa malam tsoho,,,
Wanda shi a rayuwar shi baida abinda yafi mai cin dafafen dankalin hausa, da kulikuli dakakke,
Ganin Dankalin fari fet saman hanya yasha wanki yayi wani irin kyau gasu manya manya,
Ban san lokacin da na cewa yaya wanda ke waya har zuwa lokacin,
Nace mashi cikin murya maikama da shagwaba, yaya don Allah, zan sayawa malam dankali please?
Dakatar da wayan da ya keyi, a lokacin yayi cikin bada umurni yana cewa driver stop there please,
Cikin wani irin jan burki driver ya taka burkin motan a gaban wani dan yakwamamay tsoho mai farin gemu, duk rigar shi ta mutu saboda tsufa,
Yaran dan tsohon naganin mu suka taso suna cewa,
Dankalin mu yana da zaki da gari ga gardin ci , na,nawa zakawo maku,
Kokarin bude zip din jakata nakeyi, amma sai naji,
Yaya Abubakar nacewa dan saurayin mai dankali kowa wancan kwanonin dukka gaba daya,
Sai da ya shake bayan buth da dankalin manya,manya masu kyau sanan muka,wuce,,

Mun shiga garin lokacin dare, ya soma don haka muka wuce direct asibitin Sir yahaya, inda mamatake kwance, cikin jin jiki,
A mota muka dan tsaya yaya yakira abokin shi Aliyu, yana sheda mashi cewa mun shigo garin,
Wani Ward mama take kwance, ne wai ?
Females Ward take zakuga su Wadda ai a haraba asibitin idan zaku shiga,
A,nan nake jin yaya na ba Aliyu umurnin ya kama mashi hotel mai kyau kafin ya karaso,,
A cikin girmamawa naji Aliyu, na karbawa yaya Abubakar umurnin shi,
Females Wards muka nufa, atafe muke tare da yaya Abubakar sai, Baba Wadda wanda ke gaba yana muna ja gora zuwa dakin,,
Dakin su kadai ne aciki dakin kudi, aciki ba na taro bane,
Duk ilahirin diyan Mama suna dakin a lokacin gaba dayan su,
Tare da wasu sauran yan uwan mu yan mata da su ka zo gaida mama din a,lokacin,
Jikin nata ba laifi don da dan dama amma akwance take rijib,
Sallaman da yaya yai masu yasa gaba dayan su juyowa suna fuskantar kofan, dakin,
A cikin mamaki su ke kallon mu suna muna sannu da zuwa,,
Duk da dare ne amma gaba daya idon su na a kai na,
Kowan su na kokarin ya ga yadda na koma, kamar yadda suka,ji labari
Duk da a fuskan su akwai murnan ganin mu amma akwai kyashi ga zukatan wasun su,,
Saboda irin kallon kurullah da suke min a lokacin, da na shigo,
Ni dai ina bayan yaya Abubakar sim, sim dani kamar zan shige cikin sa,
A bakin gadon da mama take a kwance muka, tsatsaya muna kallon yadda take barci numfashi sama sama take fitarwa,
Ido na kafe mama da shi sai ruwan da ake kara mata wanda ke shiganta kamar digo,
Jikina duk ya dauki rawa saboda tsoro da tausayin yadda mama ta koma acikin lokaci guda,
Da baya baya na koma ta kofa, ina mai zubar da hawaye, hankali na a tashe,don bazan jure ganin wanan abin ba mama ce haka a,kwance kamar ba ita bace hakan duk ta ramay ta canza halitta,
Daga gurin da yaya Abubakar yake tsaye idon shi kyar a kan mahaifiyar shi,
Ganin ina kuka ya,dan sa shi, dago kai tare da juyawa yana kallon gurin da nake tsaye,
Fuskan shi da gani babu dadi acikin ta ko kadan don shima hankalin shi a tashe yake,
Irin halin da ya riski mahaifiayar shi a ciki, kwance,
Anty Samira ce da dan karamin, cikin ta, da ya fara turo rigar ta, sai faman zubar da miyau,takeyi,
Ita ce ta biyoni inda nake ta dan ja min hannu mu ka fito wajen dakin, tare da ita,,
A hankali take ce min Meenatu ai kun samu Mama taji sauki, sosai inda ga kwana biyu da ya wuce ne ai baza ki iya ganin taba ashe, ?
Subbahanallahi na furta a hankali ina mai yiwa Mama addu,an samun sauki ,
Sai kuma Anty Samira ta dan kara kallo na wanan karon fuskan ta da guntun murmushi makale, tace,
Meenatu wai da ke da mijin naki may kuka ci ne haka wai?
Kun wani sake kun canza a lokaci guda gaku kamar wasu larabawa, can,
Sai lokacin na dan yi guntun murmushi na ce kai Anty Samira ho,
May ko mu kaci idon ki dai ne ya nuna maki mun canza,kawai,
Hararan, wasa ta jefo ni da shi, tana cewa tunda makauniya nake ba, koko in ce muke ba,,
Meenatu kin yi wani irin girma ga haske, ga kuma waye,wa atare da ke duk a lokaci guda,
Kai haba dai Anty Samira duk a lokaci guda haka gaba daya abinda kika lissafo min,,
Baba Wadda ne ya leko daga kofan dakin yace in zo Mama ta farka daga barcin,
Mum samu ita da yaya Abubakar suna magana haka na kutsa kai zuciya na tare da fargaba, zuwa har bakin gadon da take kwance,
Mama sannu da jiki ya karfin jikin, ?
Shiru Mama tayi tankar bata jini ba sai kuma dan annurin fuskan ta da ya gushe, a lokacin da ta ganni,
Dakin yayi tsit ana sauraren mu gaba daya an sako muna ido a dakin, a ga yadda zamu yi, da ita,
Yaya Abubakar ne yake cewa mama Meenatu na gaishe ki,
Mama tai wani irin lumshe idon bakin ciki tace, lahiya, a takaice,
Na ce Allah ya sauwaka ya bida lafiya daga haka na juya da zuman komawa gurin da nake tare da Antyna Samira,,
Kujeran da Anty Mariya ta dauko mashi ya zauna ya nuna min yace zauna nan,
Wani irin nauyi da kunya ne ya kamani don ganin yadda yayyene yan uwan haihuwan yaya su ka sako muna ido gaba dayan su dakin,,
Kai na dago daniyar in,cewa wa yaya Abubakar ya bari in fita waje amma sai annurin shi da kwarjinin shi ya hanani iya bude bakina alokacin,,
Still dai kujeran ya dan kara, matso min da ita gabana inda nake a tsaye gab da shi don in zauna da kyau,
Ba mussu na zauna kamar yadda ya umurce ni da yi,
Daidai zan zauna naji daga bayan mu daya daga cikin su Antyn nawa wata ta sauke wani irin ajiyan zuciya,
Dakin gaba daya yai wani tsit a lokaci guda inda kowa mu yake kallo,
Mamaki ne karara a tare da yan uwan mu wai yau ni Meenatu mutum kamar yaya Abubakar kebawa gurin zama,
Hmmm,umm wani abu sai mace, kaina duk yai wani nauyi don nasan cewa akwai magana ke nan, agidan mu,,
Shigowan Aminin yaya watau yaya Aliyu makwabcin mu ne shima, uguwar mu guda dashi
Acikin shiyan Sarakuna tare sukayi tundaga primary har secondary da yaya Abubakar,
Zuwa gaban secondary ne suka rabu, don shi yaya a lokacin gwaunatin jahar sokoto na lokacin ta dauki nauyin karatun yaya Abubakar din,
Yasa hankalin kowa komawa gurin shi, don agaisa da shi,
Sun gaisa da yaya ta hanya bawa juna hannu tare da tambayan gajiyan hanya,
Sai lokacin yaya Aliyu yan da kula dani a zaune, cikin mamaki yace,
A kace min tare kuke da Madam ashe,?
Mama Ladi wace ke kwance tana bautan Allah ta ji wani irin haushi a ran ta hakama sauran yaran ta masu mara mata baya, haushin abinda yacd ya kama su,
A cikin mutunci fuskana dauke da yar murmushi na gaida yaya Aliyu da cewa ina wuni yaya Aliyu,
Ya ansa min cikin fara,a da jindadi ta hanyar cewa lafia kalau Meenatu,,
Kun taho lafiya yaya hanya ya, karatu shin ko kina Abuja ,har yanzu ?
Ban bashi ansaba sai murmushin dana dan yi kawai,
Yaya Abubakar ne ke cewa yaya Aliyu da motan ka kazone,
Ya amsa mai da cewa eh tana waje, yace ok bari Baba Wadda ya tafi da driver mu can gida, ya sauke ma Meenatu tsaraban ta,
Ka kai mata sashen Baba Samaila, don kar ya lalace,
Saboda na gaji baza mu iya shigowa gida yan,zuba dare yayi daga nan masauki zamu tafi,
Yakara fuskan tar gurin da Baba Wadda yake yana cewa, idan an sauke kayan sai ka,kai driver inda Aliyu yai mashi masauki don ya huta, ko,,,
A yake yan uwan mu dake a zaine sai suka fara kallon,kallo a tsakanin su don jin may yaya Abubakar yafadi a gaban su,,

Ina zaune saman kujera idona kur akan Mama wace ke kwance shamay shamay saman gadon asibiti cikin ban tausayi,
Sai dai har yanzu da alamar bata saduda ba ga al,amarin Ubangiji, don irin halin da alaman yanayin ta ya,nuna,,,
Yaya Abubakar sun fita waje da yaya Aliyu, don haka ni da yan uwa na matane,a zaune dakin,
Daga inda Anty Safiya take zaune tace min Meenatu mutanen Abuja dada kin tahiyar ki ke kyale kowa, ko?
Murmushi nayi ina cewa Anty Safiya ba hakana bane,,
Nomban wayar ki ta ban dashi ai da keji kira na,,
Daga can bayan ta Anty Mariya tace a,a wallah ina taka kiran mutane ta samu maisunan malam ta kalalamay,shi
Baki ga wadda shika rawan kafa akanta ba na?
Daga baya kuma Anty hafsat tace to ko ke ce, aka rike ma kan maciji mika hanaki wasa da bindi nai,?
Yanzu fa da kunnuwan ki kin kaji yace, tsaraba da yattaho da ita wai ta Meenatu ta,
Lungun Baba Sama, za a aje mata suwa,,
Samira ce tace kai jama,a asibitina fa muke ba gurin dadi rai ba,,,
Shin mikkawo wagga magana wai,?
Babane tare da Mama Sa,a su kazo akan babur din makwatan mu da ya aro,
Cikin murna da jin dadin ganin mu gaba dayan su sai murmushi su keyi,,
Amenatu ashe kuna hanya bamu da labari, na dan mike tsaye ina Kokarin ba Baba Buhari kujera,
I zaman ki Aminatu ke ji, da kun ka kwaso gajiyan hanya,
Na kai kujeran har gaban gadon da mama take dai inda Baba yake tsaye,
Durkusawa, nayi har kasa na gaishe su shida matar shi na mike zan fita waje,
Anty Safiyace ke tambayana ina zan tafi,? nace mata sallah zanyi don ba muyi sallah ba, daman,,,,
Ita ce da kan ta ta taso tabani buta da sallaya sai kuma ta rakani tana nuna min inda zanyi tsarki,

Gurin da na idar da Sallah muke zaune da Anty, Safiya da Samira, muna kara zance akan ciwon Mama,
Samira ce ta kara jefo min tambaya cewa har yanzu ina Abuja ne ko na dawo sokoto,
Nace mata ina Sokoto ai tun sati kusan uku, da suka shude,
Sai naji ta nisa tana kallon yar uwar ta can dai tace,
Gaskiya Anty Safiya idan har Meenatu bata Abuja za,a samu matsala sosai idan ance Mama zata can jinya,,,
Anty Safita tana kallon yar uwar ta tace, matsalar may,
Ai baza a samu matsalar komai ba kin manta cewa Sadiya diyar Mama ce,
Ni Samira ta kalla amma sai nai kamar ban fahinci may take nufi ba don haka sai mukabar zancen kowa yai shiru a cikin mu, duk kan mu uku kowa da abinda yake kiyastawa a zuciyar shi,
Daga inda muke zaune muka hango yaya Abubakar shi da Aliyu tare da wani doctor, sun nufi dakin da mama take kwance a ciki,,
Ba,a dauki lokaci ba sauran yan uwan mu dake cikin dakin har mama Sa,a su ka fito waje daga dakin,
Gurin da muke zaune, su ka dawo suna cewa likita zai duba Mama, ne,
Nan kuma gurin aka sake hada wani sabon daban hira sai kace ba jinya a,kazoyi asibiti ba,,,
Sun dauki lokaci adakin tare da likita ciki zuwa can likitan yafito yabar su yaya da Baba acikin dakin,,
Sun dauki lokaci a ciki saiga su sun fito har Baba Buhari,,
Gurin da muke a zaune,da yan uwa nan suka nufo mu gaba dayan su,
Yan bayanai yaya ya kewa su Anty Mariya da cewa zasu bari zuwa gobe sugani idan mama ta dan kara samun sauki,sai su wuce Abuja da ita,,
Ina daga can zaune tsakiyan anty,Safiya da Anty Samira,
Yaya Abubakar ke cewa kizo muje ko zan samu indan huta, hakanan,
Wani irin nauyi ne da kunya suka rufeni a lokacin don duk wanda ke gurin ya girmay ni don nice karaman su,
Anty Safiya ce da Mama Sa,a suke cewa alokaci guda,
Meenatu tashi kuje kinji yace duk ya gaji don Abuja ba kusa bane,
A hankali na mike tsaye daga inda nike zaune saman sallaya,
Barin raka matar yayana inji anty Safiya, anty Samira kuma cewa tayi barin bisu su sauke ni gida nikan ,,
Bayan shigar mu motane, naga zamu tafi yqyq bai bar masu komai, ba,
Daga can bayan motan nake cewa yaya ya kamata fa kabar


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login