Showing 228001 words to 231000 words out of 388021 words

Chapter 77 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8196

gurin da nake kwance,
Muryan Babana ne naji daga kofan mama yana tambayan cewa na tashin,
Nace na tashi Baba mun samay ku lafiya ko ?
Yayin da shi kuma Baba yake cewa Yaya jikin naki meenatu na ansa da cewa Alhamdullahi Baba naji sauki,
Mikewa nayi zuwa ban daki nai alwala tare da zuwa tadda sallah
A gefen barandan dakin babana na hango kayan tsaraban mu an jibga su agurin,
Mamakin ganin su a gurin nayi don ni a zatona ai part din Mama Ladi za a kai su,
Na fito muka kara gaisawa da babana wanda yake ta nuna
jin dadi gani
Sai tambayana bayan rabuwan mu yakeyi tare da tambayana labarin mutanen gida Uncle dina,mun dauki lokaci da mahaifi na muna hira, sai na
Namike tsaye na jawo mayafina ina sabawa akaina nacewa yar kaunar ta, tazo ta rakani cikin gida in,gaida mutanen gida,
Baba yace baki bari har zuwa safe idan kinji sauki sai kije ku gaisa da su,
A,lokaci???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?n guda ni da mamana har muna hada baki gurin cewa bari dai in tafi ingaida Mama Ladi don gudun laifi,,
A cikin wani murya a hasale don jin haushi da takaici Baba na yace
Ladin may can inji babana ya fadi acikin fada bata da lafiya dole ne, sai ta tafi gaida ita a hakan,
Mama tace ance tun dazun fada takeyi wai yar Baba taki zuwa gaida ita,
Ita ta dade bata kai safe tana fada ba inji baba ni dai bance komai ba jiki ba kwari na kama hanya,,,
Ina jin Mama na nacewa duk fa wanda yazo dubata sai yace ashe ma jikin sosai ne shine, Mama ke cewa ta can kwance don ta zama yar mulki yanzu wai har wullakancin da nake wa Yayana shine zan kawo gare ta,
Nidai murmushi kawai nayi don jin may mama ke fada wa Baba abinda mama ladi ke fadi,

Tun daga nesa na gane cewa akwai mutane a part din na, mama Ladi saboda hayaniyan da na keji na mutane,
Tun daga farko shiga part din nake ta faman kwada sallama amma sai hayaniya suke yi ba sa jin na,,
Da Sallama na shiga har kofan dakin wanda tun kafin na kaiga karasowa nagane cewa ita da diyan tane adakin, lokacin,
Sakon kamshin dana aika masu ne ya daki hancinan su a lokaci guda duk sai suka juyo kofan dakin, su na kallo na,
Na kutsa kai dakin bakina dauke da sallama a cikin sa,tare da jefa masu kalman shahada,
Gaba dayan su idon su yana akaina sunyo min caaa dashi daga uwan har yayan suna kokarin ganin ya nake, ?
Wasu kuma suna son ganin suturan dake ajikina halinsu ba bako bane gareni don haka sai ban damu ba,
A can saman gadon dakin mama na hango ?nty Sadiya kwance ta basu baya tana waya,
Na gaida su inda wasuke min ya jikina sai dai ita mama ban tsanmani ta karba min gaisuwan ba ma,
A,a Meenatu ta shin Meenatu mutan Abuja ke tashi?
Ace kina can kwance jikin ya tabu maki tun hanya ?
Murmushi nakwyi yayin da nakai gurfane a saman tabarman da suke zaune akai na gyara zama a gefe guda,
Sai nashiga gaisawa da su duk da na fahinci irin mugun kallon kurullah da suke min,
Na jajanta masu akan abinda yafaru da anty tare da fatan Allah ya bata lafiya,
Daga gurin da mama take takecewa ai abin farin cikina don karuwa tasamu gashi ta aje min yar jikayan
Mijin ta bai ciyar da ita ga banza ba aitunda yaci riba zama da ita,
Bata zauna tai ta raruma nai ba tana aikowa iyayyen ta dasuwa,
Wayana dake a hannu na yai kara gaba dayan su suka kara zubo min idonuwan su ,,suna saurare na,
Don su gane wanda nake magana dashi yasa ban fita daga dakin ba ,
Muryan Yayana ne yake magana,
Tambayana yayi cewa ina ina ne nace gani nan nazo gaida mama,
Sai yake tambayan naji saukine dana fito sai cewa nayi naji sauki yadan lafa min yace inzo yana part din malam tsoho a sanyaye na amsa mashi da fadar to ,,
Ina gama wayan anty Mariya tace Meenatu sai kace mai laluran ciki, haka, ?
Mama ba nauyi ko kunya tace ciki ina matan kwarai ma basu yi ba balle,,
Ai sai dai ai takaryan shi amma karyan mutun yace zai hada dani ban gaiyyace shi a cikin zuria na ba,
Haba haba mama ina wanan zancen kuma yafito daga bakin ki inji anty , dake kokarin dauke plate da alaman wanda su anty Sadiya su kaci abinci ne dasu,
Murmushi kawai nayi daga gurin da nake tsaye ban nuna ma dani take zancen , ba
Ganin da mama taga nayi na mike da alaman fita zanyi a lokacin, yasa ta cewa,,
Ke Sadiya ai gara ki shirya ki bi mijin ki ku tai zuwa masauki,
Don kin san iya duniyanci na iyasa a tafi abarki a nan, don ba kunya anka gada ba
Murmushi kawai nake yi tankar bada ni Mama kezancen ta ba ,
Nai masu sai da safe nafito daga dakin jiki a sanyaye saboda irin kalaman mama agareni
Ina tafiya ina tunanen yaushe wanan kiyayyan zai gushe a tsakanina da ita,,
A iya tunane na ni dai banga abinda muke mata ba wanda yai zafi haka,
Gashi kuma Allah da ikon shi har zamu hada jini da ita yadda bata so,,
Har na kai part din malam tsoho ban kai karshen tunane na ba nan na fara gaisawa da matan malam tsoho ida n su ke min sannu da zuwa da kuma yaya jiki don zuwa yanzu kowa nagidan yasan nazo ba lafiya
Nasamu gefen tabarman dasuke zaune nazauna ina mai kara gaida malam tsoho shima anan yake min ya karfin jikin na,ansa acikin kamala dacewa naji sauki,
Tausayin yaddanake malam ke ji don haka yake cewa Yayana kutashi ku tafi don ta huta ,,,
Yace wa Yaya Abubakar Kasan irin yanayin da take ciki may yasa ka zo da ita ai da sai ka barta gida, ku kuzo kawai,
Tafiya da mace mai ciki irin haka ai hatsarine sosai,
Cikin mamaki Yaya Abubakar ya yace ciki malam tare da daga kai ya dubeni,
Ni kuma sai nai saurin dukar da kaina kasa tare dan wasa da gefen tabar da nake a zaune,,,,,,,


ZEEE MAKAWA YELWA
[9/13, 4:54 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
7? 2?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH AL MU,HYI,,

A cikin tausaya murya da marairaicewa, nake cewa Yaya Abubakar, don Allah su tafi da Anty subar ni in dan gana da mahaifana, har zuwa gobe idan naji sauki,,
Sai da ya dan zubo min ido wanda duk da a cikin duhu ne amma sai da nasha jinin jikina sosai, don tsoron may zaice,
Sai can naji yace OK hakan kuma fa yana da kyau don haka mu zamu tafi ,
Malam tsoho wanda ke daga gefen mu tankar baya jin may muke cewa saboda yadda muke maganan ba lalai ne yajimu ba,,
Cikin mikewaa irin yanayi na wanda ya gaji yake cewa yayin da yake mikewa,
Tau malam ni zan tafi masauki ke nan sai dai da safe idan Allah ya kaimu zan shigo,
Malam ya amsa mai da cewa to maisuna Allah ya,bamu alheri a huta gajiyan hanya ko,,.
Zuba mai ido nayi daga gurin da nake zaune saman tabar man malam,
Malam tsoho ne ke cewa ita anan zata tsaya ko don naga bata tashi ba,
Yaya Abubakar yace bazata ba zata tsaya su gana da yan uwane,
Nima mikewa nayi don in taka mai daga nan nashige part din mu,
Kamar yadda ko wani babba gida irin na hausawa yake sassa daban daban wani akewaye wani kuma a bude haka gidan mu yake don yawa sassa shima,
Saboda nazo ban jin dadin jikina yasa ban leka kowani sashe ba sai namu dana Mama Ladi, kawai ko ita daurewa nayi don gudun fitinan ta,
Sai kuma yanzu da na shigo na malam tsoho don ansa kiran mijina,
A hankali nake bin shi a baya a lokacin da yake tafiya,,
Saida safe iyalan malam ke muna a lokacin don sanin cewa tare zamu tafi, azaton su,
Mun kai kwanar da zai shigar da ni sashen mu Yaya ya ja ya tsaya tare dan juyowa yana cewa tau kikoma ki kwanta nasan cewa yanzu Baba ya dawo amma bazan shigaba saida safe idan Allah ya kai mu,,
Nace zan fada mai insha Allah saida safe ke nan, in Allah ya kaimu,
Nikan daga haka na shige abina part din mu idan na samay su zaune suna kallon TV a yar varander sashen mu,
Nai masu sannu na shige dakin Mama a zaton su zan fito ne ayi fira amma sai naji sanyi nakeji don haka kawai saina samu guri na kwanta kawai,
Idona biyu amma zakace barci nakeyi nan ko tunane na keyi yadda malam tsoho ya fahinci cewa ina da cikki wai,
Muryan mamana naji a dakin tana cewa, bazaki kara cin komai bane kuma,
Na bude idona da su ke a lumshe nace ban jin yunwa yanzu Mama kila sai zuwa dare, kadan,,
Yanzu banjin ci komai a raina ,zama naga mama tayi kusa dani tana mai tsura min ido abinda yasani kokarin kai wa daga zaune ke nan,
Kwanta abinki nima fita zanyi Mama tace min sai kuma naga tadan maida yanayin fuskan ta a dan daure tace,
Yar Baba yanzu cikin ki wata nawa ke, nan ?
Da sauri na dan juyo na kalli Mamana sai kuma nai saurin dukar da kaina kasa,
Bance komaiba sai itace ke ce min ya kai wata biyar ga yadda nagan ki ko ?
A hankali na daga mata kai na bude bakina da kyat nace a sanyaye kila zai kai haka din , ko yafi,
Kamar zata wuce sai kuma ta dawo ta tsaya ta jefo min tambayan cewa,
Ya akayi kowa bai san zancen cikin ba don banji a na maganan hakan ba in ba da ki ka zo kowa ya gani ba,,,
Da kyat na bude bakina nace ni ban fadawa kowa ba cewa ina dashi,
Da sauri mama tace har da shi mai sunan malam din baki fada mai ba kike nufi, koko shima ya boye muna ne kamar yadda kika boye ke,
Nadan marairaice murya a hankali nace mama ni ban san yadda zan gaya mashi bane ai, na fada tare da dan turo bakin shagwaba,,,,
Ido na ga ta tsura min kamar zatayi magana sai kuma tai shiru yayin da tafara tafiya tace Allah ya Rabaku lafiya,
Ban ansa a fili ba mama taji ,,amma a can cikin zuciya na na ansa da cewa Ameen ya Allah,
Na koma a hankali na kwanta zuciyana cike da tunane da kuma fargaba,
Don nasan cewa kafin mu koma sai Yaya Abubakar ya samu labari kilaa,
Aikuwa ban san yadda zan kalleshi ba don gaskiya, ban san abinda zan ce mai ba,
Da irin wanan tunanen barci yai awon gaba dani ban sani ba sai kusan asuba na farka da wani irin yunwa a tare da ni,
A hankali na bude idona inda na fara raraban ido a cikin dakin ,
Wanda hakan ne ya sani tuna cewa, a gidanake kuma a dakin mahaifiyana,
Hankali na dan yunkura nakai zaune, tare da lalubo wayana na kunna don inga haske a lokacin,
Flask ne nagani a kusa dani da bread da sauran kayan hada tea, har da cup, da ruwa leda biyu,
Na sauko a hankali na fara kurkure bakina sannan na zauna na hada tea din,
Zan fara sha ke nan naji muryan mahaifina ta window dakin mu yana cewa kin tashi Meenatu ya jikin naki nace naji sauki ba,
Yace to ki sha tea din sai ki kwanta kinji Allah ya sauwaka,
Nace Ameen Baba nagode,
Yana wuce, wa na sauke, ajiyan zuciya Baba na ya bani tausayi don Alama ya nuna min cewa ya kwana yana gadina ke nan,
Mamana ce ta shigo dakin a lokacin jikin ta yana saye da hijab har kasa,
Tace kin farka yar Baba kin hada tea din ne ko nace a hankali eh Mama nagode,
Tace ai kamar Baban Baban ki ya sani cewa zaki bukaci shayin fiye da abinci da dare shine yace a sayo maki, ,
Na kai cup din tea a bakina na dan kurba a hankali, sannan nace haka nake a gida wallahi,
Ko naci abinci bana koshi sai wani irin yunwa ya dinga damuna tankar banci komai ba,
Cikin murmushi Mama tace badole kici abinci ba tunda bake kadai bace,
Sai na maida kallona a gurin Mama na don jin may tace,
Sai kuma naji tace gaskiya yar Baba banji dadin rashin fadawa mijinki zance juna biyun ki ba,
Idan har zaki samu abin alheri haka baki fada mai ba towa kike ganin cewa zaki fadawa,
Fuskana acikin yanayin damuwa nace mama ni bawai naki fada mai don wani abu bane sai kawai don irin mutanen da nake zaune da su,
Sam mama wallahi babu yarda a tsakani na da su,
Idona ya kawo kwalla na ci gaba da cewa, mama duk irin halarcin da nake kokarin yi masu sai sam babu yarda a tsakani na dasu,
Murmushi naji tayi tare da zama a gefen gadon da nake tace,
Laila kurciya, ke da har kike ganin cewa zasu yarda da ke,
Ai kamar yadda kikasan cewa babu yarda a tsakanin ki da su
To hakanen ma suma babu yarda a tsakanin su dake don duk abinda kikayi masu na alheri sai su dauka cewa da munakissa kikai masu shi badon Allah bane,
Tace Allah dai kawai ya kare muna ke daga duk wani sheri mutum ko aljan
Mama tace balle irin yadda naga mijin ku yana nunawa abinsa kanki babu ko boyo a cikin sa,
Tsaraban da kukazo dashi fa dazun duk gaba daya cewa yayi wai a kawo nan na ki ne wai don shi bai zo da tsaraba ba tunda ba mace yake ba,
Kin san halin Mama Ladi wurin fitina ance tsaye tayi tanacewa wai akawo komai a part din ta shi kuma yace tunda bashi ya sayo maki ba dole a nan za,a kawo,
Wadda dayake shima ya fita iya fitina yace baza a kawo mata ba tunda an fada mata mai su,
Dole tana gani Wadda ya sa yara suga shigo muna dashi nan a katara su kin gan acan kofan dakin babaki a ajiye,
Ga shi ba ke kadai ce yazo dake ba balle yace akawo maki a nan, ai ko tunda da uwargidan shi yazo ita kuma din yar gari ce ai,
Kinga hakan ne yasa surutu duk ya zagaye gidan nan da daren nan cewa wai kece yar gaban goshi sa ke nan,
Nace indai Yaya ne kowa ar gaban goshin sa ce akwai dai wani dalilin da yasa yai hakan
Na kurbi tea na nace Mama ni azatona ai akwatina kawai za,a kawo min nan din,
Ai da da,fa yanzu ance Mama Ladi tace wai ai don sheri ki ka ki sauka a dakin ta daga yanzu a dakin ta zaki dinga sauka,
Murmushi nayi nace ai babu damuwa dama uwatace ai,
Mama tace zancen mu yazo daya da ke ke nan don nima hakan nace
Mama tace, dama ta daine cewa bata son zaman shi da ke don dai ga shi kuma Allah ya kawo alheri a tsakani sai muga yadda zatayi,
Don har gobe tana bakan ta na cewa wai sai ya sako muna ke, kin dawo, gida, da takarda
Naga mama na ta sake wani dan guntun murmushi tace da farko har shedan yaso yasa mu biye mata dagani har mahaifinki,
Amma tunda malam yai muna nasiha akan cewa mubar wa Allah al,amarinsa,
Kinga ashe da mun bi ta kan,ta da duk mun zama shedanu akan hukuncin ubangijin mu,
Don wanan rabon da yaya zamuyi da alhakinsa tunda har akwaishi,
Murmushi nayi don jin may mama tace don nasan tadai fadi ne ina Yaya Abubakar zai iya sakoni,
Gashi kuma da ga baya duk irin kaunar da mijin ki ke maki duk yana a kunnuwan mu,
Bamuba ma duk wani wanda ke gidan nan yanzu ya fahinci, hakan don kinga ai da can mai sunan malam bai damu da kowa ba, daga cikin iyayyen sa,
Amma yanzu gaskiya kowa agidan nan yana alfahari da shi babba da yaro,
Don yanzu haka baifi sati uku ba da ya turowa kowa da dubu dariri wai su sayi abinci,
Kinga shi mahaifinki da hamsi yabashi,aiko kinga dole su san cewa kin zamo wata babban hakankan TARKO agare su,,
Sai naji tayi shiru tare da girgizan kan ta acikin takaici,
Tace Yar Baba nida mahaifinki ka dai sai gwagon ki muka san irin halinda muka shiga a lokacin auren ki,
Nayi kuka sosai akan wanan hadin da malam yayi a tsakanin ku, da mai sunan shi,
Ba,don komai ba sai don sanin cewa mai sunan malan dan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login