Showing 81001 words to 84000 words out of 388021 words

Chapter 28 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8289

yin girki, ?
A hankali ya kara kwantar da ni gurin da nake a kwance, da farko,,
Falon ya koma ya hado tea mai zafi tare magani pain relief
Sai da ya tabbatar da cewa nasha shayin da ya hado min,
Sai ya, miko min magani tare da dan yimin addu,oi a saman kai na,
Ido ya tsura min duk da a rufe idona su ke amma sai da na gane hakan saboda yadda naji a jikina,
A hankali ya mayar min da kaina saman filo tare da gyara min kwanciya ya jawo min bargo a hankali,
Falo ya koma inda ya kwashi kalacin shi hankali kwance,
Dakin Sadiya ya nufa ya tura kofa a hankali tana kwance saman gadon ta kaya ne ko ina a yashe a kasan dakin da saman kujeran dake daki,,
Wani tsamin dauda ne kamar kullun ya daki hancin shi don bayau ne farkon jin haka ba adakin na ta,,,,
Kwance take rub da ciki ta sake ko ina nata wai tana barci,
Cikin takaicin wanan kwanciyar ya kalle ta
Sunan ta ya ya ke kira a,cikin yar hasala
"Ke; Sadiya manene haka wai, dallah gyara kwanciyar ki mana,
Mika tayi tare da yin wani irin nishi sai kuma
tafara yar soshe soshe,
Ta dan dago kai tana kallon shi sai cewa tayi katafi kawai idan na tashi zan rufe gidan,
Ke dan Allah tashi kin ji , cikin bacin rai, yace hakan a kuma hasale,
Mika takara yi tare da mirginowa tana fuskantar shi,
Har zaka tafi ke nan?
Ke tashi ki rufe kofa ban son yawan surutu please ?
Mikewa tayi dan sanin cewa ba wasa azancen shi ta ,mike ba don taso tashi zuwa rufe gidan ba,
Tafe yake ta na bin bayan shi har zuwa falo ida kamshin girkin da ya kwasa ya shige hancin ta,.
Gurin dining ta juya ta dan kalla a hankali inda ta hango kulolin abinci a saman table din,
Har yasa kai zuwa fita waje, sai kuma ya ja ya tsaya, yana ce mata,
Wanan yarinyar bata jin dadin jikin ta please ki dan kula da ita kafin na dawo,,
Wani kallon raini tai mai batare da ta yi magana ba
Ta koma daga gefen alamar tana jiran shi ya fita ta rufe kofan, gidan,,,

****** ********* ******
Tasha kwalliya kamar mai zuwa unguwa, ga makeup da taiwa fuskan ta,,
?nty Amarya ta na daga kwance a dakin ta bayan barcin da ta sha har ta gaji, ta tashi,,
Wayan ta da ke saman side drower ta jawo, tare da duba sakon ni, da take da su,
Sai kuma ta koma gurin contact din ta, don ta duba sunan wata yar uwar su,
Sunan Meenat din ta ne, ta gani kusa da gurin sunan maimunan,
Sai taga ai ya kamta ta, kira ta taji lafiyan ta, zuwa yanzu don tun dawowar su basuyi magana ba,
Kamar ta kirata sai ga uncle ya shigo dakin ta cikin jin dadi da ganin irin yadda Sumaiyyan shi mace mai kwazo da kuma hankali uwa uba tarbiya ga tsabta da sanin ya kamata, ya caba ado badon kowa ba sai saboda shi,,
Zaunawa, ya yi a bakin mirror suna fusk???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?antar junan su shi da ita,
Yace cikin murmushi, wanan kwalliyan ya kama ta a ba tukwuicin sa fa,
Wani far tai mashi da idon ta tace aiko ba tukwaici tunda ka yaba shike nan,
Tambaya ya jefo mata da cewa,
Kina kewan yar ki ce halan,?
Naga kin wani kwanta kin lafe kamar mai tunanen wani Abu a zuciyar ta,
Murmushi tayi tana kokarin mikewa zaune tana fadin,
Ai dole ne inyi kewan Meenatu, yarinya ce mai kirki ga ta da mutunci sosai,
Amma kuma sai naga bata samu abokan zaman kirki ba daga matar har mijin,,
Murmushin Uncle yayi don jin may tace mai a lokacin,
Aganin ki ko ?
Ni kan a bangare na ban ga matsalar komai ba gaskiya,
Indai don ganin da ki kaiwa mijin ta ne haka na ai, ko ita Meenat din haka take,
Kallon Uncle Anty tayi don taji yace haka Meenatu take ita ma,
Uncle yace yes hakan
Daga jinin, jikin yan gidan su, ne haka na din zaki gan su kamar ba su da sakewa, da mutane
Amma sai idan ka zauna dasu zaka gane cewa, suna da sabo, so,sai
Don kinga mun dan
zaman da muka yi dashi na lokaci kadan mun fahinci juna dashi sosai,
Anty Amarya ta nisa tana cewa tau ni dai, Allah ya, dau,kaka min diya ta, akan su,
Uncle yace kaji masu diya ba son kai dai ba kyau,
Cikin murmusawa da kallon irin na ya nayin kissan mata, tace mai,,
Ai kai,ma, addu,an, zaka ta ya mu yi please,,,,

****** ********* ******
Zufa na diga jin yana tartso min daga cikin barcin da na keyi,,
A hankali na yaye bargon da nake a cikki lulube, tun da safe,
Ido na, bude a,hankali, inda
nafara kallon silin din dakin a hankali,
Launin silin din daki ya sa ,ni saurin tuna inda nake a halin yanzu,
Ido,na na dawo dashi ga dakin a hankali ina kallon ko ina,
A lokacin fankan Sama ne kawai ke dan aiki a hankali, cikin dakin,
Karan waya na Nokia naji daga gefe na tana dan tsuwa,
Hannu na mika daga cikin bargo na dauko wayan a gefen filo na,
Bakuwar noba ce na,gani ke kirana, ban daga ba har kiran ya katse,
3 miss called na gani a wayan kuma duk dsame noba, ke kirana,
Ina cikin tunanen ko laban waye ke kirana' haka ,?
Sai naji an kara kiran na dakuma, wanan bakuwar, nobar dai,
Dauka nayi batare da na ansa ba ,
Muryan namiji ne ,ke magana,
Kin farka daga barcin ke nan ko ?
Zazzabin ya bari ko ?
Kin ci wani abu kuwa da kika tashi,?
Tambaya uku a lokaci guda abinda yasa idona ya watsake har na gane mai magana alokacin,,,
A cikin dan daburcewa na mike daga kwancen da nake ina kokarin mayar mai da ansa a cikin girmamawa,,
Idon shi ya lumshe tankar ya na a gabana to ki,yi kokari ki ci wani abu a bakin ki,
Na ansa da cewa to na gode,
Mamaki yayi daga magana sai nagode,?
Kashen wayan yayi inda ya mai da kan shi saman marikar kujeran shi yana dan juyawa a hankali, a cikin wani yanayin jin dadi,
Irin abinda ya faru a daren jiya ya,sa shi lumshe idon shi,
Malam Mudi ya shigo office din yana kokarin rufe kofan office din,
Shugaban nashi ne yasa mu, a cikin wani irin yanayi na shaukki,
Sai da ya kara sallama ya bude idon shi da yai ja kamar mai jin barci,,
A hankali ya ce malam Mudi lafiya dai ko ?
Cikin girmamawa da kallon yana yin ogan nashi, ya sashi dan tunane,
Akwai wani sabon yanayi da shugaban shi yau yake ciki,
Tun safe yake ganin shi cikkin cool action,
Takardan da ke a hannun shi ya tura mai a gaban shi yana cewa yanzu, a kabani in kawo maka,
Tarone watau, meeting na gagawa daga office din shugaban su,
Acikin su uku da aka tura kasashen duniya karo ilimi ana da bukatan mutum guda wanda zai zama masu babban a counter,
A karshe taron Allah ya bawa Yaya Abubakar sa,an cin wanan interview din
Nan aka bashi wanan mukamin na a,counter din su na N,N,P,C,
A take guri ya dauki murna da ihu cewa mukami ya dawo gurin dan arewa,
Dama wani IBO ne ke rike da wanan mukamin tsawon shekaru masu yawa,
Daga gurin meeting din ya na fitowa ya nufi Mosque din ma,aikatar su,
Inda yai sallolin da ake bin shi,
****** ********** ******
Ban jin komai a jikina sai dai nauyin da yai min tun wayewan garin,
Kitchen na fada inda nai muna abincin rana, sai dai kuma still akwai na daren jiya saura da kuma na safen yau da ya dan rage,
Gashi babu wanda zan sa ya kira min almajiri abashi, sadaka,
Kuma ban san ya zanyi da wanan abincin ba don gudun kar ya baci,
Hijjab na dauko daga daki na sa na dan tsaya daga cikin garejin mota gidan,
Daga ida nake tsaye ina jin motsin samarin nan, masu zama gaban gidan
Wa yan da muka gani a kofan gida ranan da mukazo,
Kamar an jefo wani daga cikin su ya dan zo ta kofan shigowa gidan namu yana dariya ,
Gani na yayi a tsaye abinda ya dan sashi cewa a,
Ina wuni na ansa da lafiya,
Tambayar shi nayi da cewa,
Don Allah almajiri nake nema in abashi wanan abincin,
Kallon kulan abincin yayi sai ya ce ok barin karba in fita da shi,
Na mika mai na nufi cikin gida inda naci gaba da ai,yukana, don hada abincin dare da wuri tare da gyaran gida,,,,,

****** *********** ******
Wanan Saurayin yana fita da kulolin abincin duk sai sauran, suka zubo mai ido, har ya iso gare su,
Abinci,ne inji, Amaryan gidan nan wai abawa almajirai,,
Kulolin suka shiga budewa a hankali abincin dake cikine yasa su kallon junan su,
Sai daya daga cikin su yace waiko kasan cewa tun safe rabon da in ci wani abu ,,,
To ai kuwa yau gashi Allah ya tsaga da rabon mu ba bata lokaci suka hau abinci da ci,
Gaba daya har na jiyan suka tashi dashi tas tare da zuwa gurin famfom gidan namu dake ta cikin gareji suka sha ruwa suka kuma wanke min kulana tasa,
Bugun cikin shi ya yi yana cewa yau wanan matar ta ceci gayu wallahi,
Allah ya saka mata tare da maigidan ta da alheri sauran suka ansa da fadim Amin
Ina daga kitchen naji ya na kwada sallama yana cewa ga kula ya dawo dashi sun gode fa,,
Karba nayi nakara wankewa na kife,

Tun safe ban ga Anty Sadiya waje ba don haka na shirya cikin atamfa dinkin zanin rapper,
Da Sallama na shiga sashen nata wani irin tsamin dauda yadan daki hanci na,
Tana kwance a three seaters, ga plate din da ta debo abinci da ga falo har ya dan bushe,,
Da cup din da tasha tea tun na safe,
Ina wuni Anty ?
Lafiya ta ansa a,takaice
Shiru mukayi batare da wani yai wa wani magana ba,
Ganin da nayi cewa shirun yai yawa ga kuma tsami na dukan hancina yasani cewa sai anjima,
Ban tsan manin cewa ta ansa min ba a,lokacin don duk hankalin ta naga kallo, tv,,,
Sai dai kuma tayi hakane don ta wulakanta ni,
Saboda ita gani takeyi wai na aure mata mijin ta don rashin mutinci
****** *********** ******
Ko karin yake ya sa takalman shi a kafan shi, a daidai,kofan massalacin,
Wayar shi tai kara inda ya dan dago yana karasa ,sa takalman nashi daga tsaye,,
Sweet Mum ya,gani rubuce, a screen din wayan shi cikin murna da jin dadi ya dauki wayan don su gaisa,da mahaifiyar shi,
Amma sai yaji muryan mahaifiyar nashi babu ko gaisuwa balle yaji dadin fada mata, alherin da ya samay shi,, yau,
Muryan Mama a cikin fada, ya tare shi da cewa mai sunan malam ka bani mamaki,
Yanzu ace an dauki wanan yarinyar har an,kai maka ita, gidan ka ba tare da na sani ba,
Mama baki sani ba fa ?
Yaya ko za,a bari in sani tunda ba alheri bace,
Gaskiya mama na zata kina da labari saboda na ai mutanen gida ne suka kawo ta,
Mama Ladi takara cewa cikin hasala mutanen gida muna fukai ko ?

Saurare ni kaji da kyau ina son katurowa wanan tsohon da munafukin uban ta da yar su kafin jibi,
Da karfi yace Jibi mama gaskiya sai kuma yai shiru don yasan maganar shi ma fitina ne, a gurin ta yanzu yadda ta hassahaka?
Nafada maka cewa kada ka fara ka taba yarinyar nan,
Ka turo ta gida ta dawo gurin iyayye ta, su kama abinsu



ZEEE MAKAWA YELW@
[7/24, 9:48 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
3? 4?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH-AL-KHAAFID


Mamaki da,tashin hankali suka sauka mai a lokaci guda,
Da farko yana mamakin,irin rayuwar mahaifiyar su,
Wace, a,koda yaushe cikin fit?n? take da tashin hankali da kowa na gidan,
Bakamar Mama Saratu ba,wace take saliha da kowa mutunci takeyi a gidan, dashi,
Ga halin alkunya irin na diyan fulanin asali, ko ba ka kaunar ta zata iya yi ma alheri ita,
Sabanin mahaifiyar da har makwabta hakkuri sukeyi da ita a shiya,
Wanan kalaman da mama tai mai sun matukar girgiza shi, ainun,,
A hankali ya taka har zuwa office din shi inda jama,an ma,aikatan su ke ta zuwa yimashi murna,
Sai,da aka dan rarage ne ya dan fara dawo da tunanen shi,
Akan irin sharadin da Mama ta gidaya mashi akan Meenatu,
Ya zai yi da umurnin da su Baba suka bashi akan yarinyar,
Ya zai yi da alkawarin da ya dauka akan wanan auren,
Waiko Mama tana tausaya mashi akan bukatocin ta
Shigowa Salawatu tare da yan gungiyar ta mata ma,aikatan gurin aikin nasu,
Yasa shi dakatar da tunanen da yake yi akan Mama,
Murna sosai sukai mai tare da nuna fatin cikin su akan samun cigaban shi,
A nan su ke gaya mai cewa zasu hada mai yar party don nuna farin cikin su,
Tafiyan su bada dadewa ba shi ma ya shirya zuwa gida,
Mamaki malam Mudi ya,yi da yaga cewa, yau zasu rufe da wuri zuwa gida,
Sai da ya tsaya hanya yasai masu kayan da yasan za,a bukata a gida,
Shi da kanshi ke kokarin shigo da kayan da ya siyo a hanya,
Yaron da ya bude mai get na gani ya zo da sauri ya kama mai kayan zuwa cikin gida, da su,,,
A gajiye ya karaso zuwa cikin gida yana dauke da case din shi,
Zubewa yayi saman kujeran dake kofan shigowa falin shi,
Yayin da yake ko,karin sauke Nick tie da ke daure a wuyan shi,
Makullin buth din shi yaron da ya kwaso mashi kaya, ya mika mashi a cikkin ladabi,
Minti kamar biyu yayi a zaune sai kuma ya mike tsaye, zuwa ciki, don bai ji motsin kowa ba acikin gidan,
Ruwa ya watsa majikin shi don yaji sanyi, daga nan ya dan gyara dakin kwanan shi kamar yadda ya saba yi idan ya dawo daga office,
Zaune take tana waya a saman kujera, kayan da ya barta da,sune a jikin ta tun safe har zuwa yanzu a jikin ta,
Ba gaisuwa ko wani zance sai daga kai tayi takalle shi yayin da ta ci gaba da maganan ta a waya,
Ganin irin yadda tai mai yasa juyawa ya koma falon shi duk da dai ya saba da halin ko in kula na Sadiyan,

****** ********** ******
Tsaye nake ina kokarin gyara filolin saman gadona duk da bawai sun yi wani abu bane,
Jin shigowan mutum dakin yasani saurin dago kai,na da ke duke,
Tsaye yake jingine da ban gon kofan dakin idon shi na zagaye dakin da kallo,
Yana saye da wani farin jamfa, da wandon shi mai budaden hammata, kafan shi saye da wasu plat shoes,
Idon shi ya sauke a kai na gurin da nake a tsaye bakin gado rike da filo a hannu na,
Har kasa nakai, tsugunne ina mai cewa cikin sanyin murya sannu da dawowa ?
Ansa yabani a takaice da cewa barka da gida?
Wani irin nauyi da kunya sa ne suka lullubeni a lokacin,
Bakina naji ya na cewa akawo maka ruwa ne, saboda yadda naga a gida idan iyayyen mu maza, sun dawo ake kawo masu ruwan sha,,,
Cike da fara,a fuskan shi ya ce Alhamdullahi nasha ruwa don har wanka nayi, ko,
Kaina yana duke a kasa har zuwa lokacin da naji muryan shi yana cewa,
Ya jikin naki yayi sauki ko?
Ban samu dawowa da rana in dubaki ba don yau meeting mukayi har zuwa wani lokaci,
A dan kunyace cikin satan kallon shi nace ai ba komai naji sauki,
A, hankali kamar wanda ya gaji yace Alhamdullahi, sai,dai ki kara shan maganin ki pls,
Cikin kwantar da murya na ansa mashi da toh,,,
Ido ya zuba min tare da cewa Meenatu kunyi waya da malam ?
Damm naji gabana ya bada ,
Amma a cikin dakewa tare da boye razana na nace bai kirani ba,,
Ok kawai ya iya cewa sai naga ya juya zuwa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login