Showing 114001 words to 117000 words out of 388021 words

Chapter 39 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8283

masu dan wani abun kashewa,
Bai yi musu ba ya ciro kudi daga aljihun shi yace wa Anty Safiya da batai nisa da motar mu ba tazo takarban masu,
Anty Samira wace ke tare dani a bayan mota tace wa dan uwanta,
Yaya shima Baba fa da mashin suka zo shi da mama Sa,a,,,
O,o Allah na nace, daga gefen da nake zaune, nace Allah ya yaye muna wanan halin da muke ciki
Anty Samirace takarba da fadin Ameen ke dai Meena,


ZEEE MAKAWA YELWA,,,
[8/4, 9:13 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
4? 4?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH- AL-HALEEM,,,,

Wanka na fito ina daure da tawul, fari na hotel din a jikina,
Yaya Abubakar yana daga bakin gado zaune cikin wani dan wandon boxes na maza,
Kokari nakeyi in daure kaina da ribon fin da na dauko daga cikin jakata,
Muryan shi da abin da yake fadi yana kawowa daga gurin da nake a tsaye bakin mirror,
Hakan ne yasani gane cewa da mace yake magana kuma ba Anty Sadiya bace,
Saboda irin yadda naji yana bada amsa cikin shauki da so,,
Wani irin abune naji yai min tsaye a zuciya ta,har naji kamar idona yana rufewa,
Amma abinda yafado min arai shine zancen Anty, Amarya, alokacin da nai mata hira lokacin da Salawatu tazo gidan mu a Abuja,
Anty Amarya tace min,Meenatu koda mata biyu yayan ki zai auro yanzu a lokaci guda babu ruwan ki don ba yadda zakiyi,,
Don auren ki dashi aure ne na mutu ka raba ban ga dalilin da zai sa ki tayar da hankalinki ba,.
Abu gudane yanzu agaban kishine kisan yadda zaki tafiyar da rayuwar ki dana Mijin ki ta yadda duk wace ma zai auro bazata iya dake ba sai dai ta barki, da shi,,,
Ajiyan zuciya na sauke tare da dan kirkiro farin cikina a fili,
Ban san zuwan yaya Abubakar kusa da ni ba sai dai jin hannun shi nayi a baya na,
Daga haka muka dan yi tafiyan hazo a tare ba tare da na kara, tunazancen wata Salawatu can ba,

****** ********* ******
Karfe takwas na safe muna a haraban gidan mu kofan gidan malam tsoho dake uguwar shiyan Sarakuna cikin garin, Birnin Kebbi,,
Idan na tsaya baiyyana irin farin cikin dake dauke a fuskan kakan mu malam tsoho da wasu daga cikin iyayyen mu dake gurin,
Babu wanda yakai mahaifina farin cikin ganin mu a lokacin don dagani har yaya Abubakar ban san wanda yafi jin daddin gani ba a tsakanin mu,
Nafito daga bayan mota tare da ni da yaya Abubakar cikin murna yau gani a gida, bayan dan dadewan da nayi batare da na shigo ba,
Yaya Abubakar yana gaba ina biye dashi kamar yadda yake a gidan mu,
Don kusan doka ne hakan don duk wani dan gidan idan har yai tafiya yadawo dole ne sai ya fara zuwa rufar malam tsoho ya kai gaisuwa da neman albarka,
Sosai malam ya kasa boye irin farin cikin da yake ciki yau don ganin yadda TARKO shi yai kamu,
Mun gaisa da shi cikin wasan jika da kaka inda yake cewa watau Abubakar wayau da kai min ke nan, ?
Ka karbe min mata katafi da ita birni, kuka barni nan a cikin rumfa ko,
Dariya sukayi atare inda yaya Abubakar yana zama yace mai, ai, kai ba jarumi bane sunan kawai muka ara maka,
Don haka kaga da ni jarumin maza tadace shiya sa ka,sadaukar kabar min kawai,
Atare suka kara sa dariya malam na cewa to haka zaka ce min yanzu ko,
Tun da nai maka wanan, halarcin kake ganin kamar ban kai jarumi ba ko,
A hankali yaya Abubakar ya dan sasauta muryan shi kasa kasa yace bance ba tuba nake, malam tsoho mai ran karfe,
Nan nabarsu zaune a tare da malam din suna kara tataunawa a tsakanin su,
Direct sashen mahaifana na wuce kai tsaye,,
Na samu Mamana tana kokarin hada muna breakfast,,
Da dan gudu na nakarasa gurin ta na rugumay ta, ta baya, nadade rungumay da mama ina jin dumin jikin mahaifiyata,
Sai kuma ga hawaye sun zubo min shar ga ido na subbanallahi
Yar Baba may ye haka kuma farin kisa wata tashigo taganki kina kuka ace ai, wani abin ne ya faru, dake kuma,
Cikin muryan kuka nace mama naji marmarinku ne wallahi,
Tace to yanzu ba gaki ga muba sai ki cinye mu tunda kinji marmarin mu,
Kaina nakara nutsarwa a jikin ta nace, mama idan na cinye ku ingawa kuma,
Muryan mahaifina ne mukaji daga bayan mu yana shigowa gidan, yana cewa,
To ke Saratu tunda sun zo ai sai abarshi su karya anan ko?
Anan kuma malam mama ta tambaya cikin mamaki, da fargaba,
Nan muka zauna gaba dayan mu a yar barandar tsakar gidan mu ana hiran yaushe rabo,,
Babana yakalleni yai murmushin jindadi yace, to ya wajen kawun naki, ina fatan duk suna lafiya ko,?
Na ba Baba ansa da cewa duk lafiya suke suna gaisheku,
Baba yace , Nafi,u dan rigima,saiga shimkafa da su mai, ya turo min dasu wai, muyi anfani da su,
Shigowan yaya Abubakar a sashen mu yasa ma sauri dauko hijabin ta tasa,
Wai kada suriki ya ga jikinta,surukin da tun ba mu zo duniya ba yake ganin ta a hakana,
Shima afaninyaya Abubakar din yau sai yake jin wani irin nauyin Mama da Baba,
Don haka sai ya kasa sake jikin shi kamar yadda ya saba,
Baba ne yai mai umurni da ya zauna su karya a tare dashi,
Bai fi minti biyar da zaunawa zai yi breakfast ba sai ga Baba Wadda yana sheda m?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? ashi cewa, wai ana sallama dashi a waje,
Har zai mike sai baba yace dakata ka tsaya kaci abincin ka kafin ka fita,
Don yanzu haka da ka tashi bazaka kara dawowa ka zauna ci ba,
Masa ne da miya, sai, kunu koko, da kosai, da sugar,
Sosai yaya yaci masa da miyan da aka siyo muna gudan mai yawa, sosai,
Kafin ya kai karshe,sai ga yaya Aliyu ya shigo yana ce mai wasu daga cikin abokan su ne su kazo mashi murnan samun girman da yayi,,,
Daga wanan fitan ban kara ganin yaya Abubakar ba har zuwa, wani lokaci,
Nikuma ganin haka yasa nasamu sakewa da mahaifiyana da yan uwana munata hirar mu gwanin ban sha,awa,,
A dakin mamana in kwance saman gadon ta mana tana zaune saman kujera,
Mamana tace yar Baba naji dadin ganin kuna zaman lafiya da maigidan ki fiye da yadda muke tsanmani,
Da farko zancen auren ku hankalina ya tashi sosai wallahi sai nake gani kamar zai wullakanta min ke,
Amma tunda mahaifin ku ya ce min mubar wa Allah al,amarin sai kawai naji hankalina ya kwanta sosai
Don haka nashiga rokan Allah da ya kara sanya alheri fa wanan al,amarin,
Yakawar da duk wani sheri ko kulli dake tattare da wanan auren naku,
Tambaya najefo mata da cewa amma Mama Ladi ta daina wanan irin zagin da take muna ko,
Murmushi Mama tayi wanda ya nuna min cewa bata daina ba, har yanzu tana yi,
Sai Mama tace inma har bata daina ba ai sai tayi da wanda ya kulata,
Yanzu ai wanan ciwon kawai ya isheta ishara in tana da hankali,
Haka mukai ta hira da mahaifiyata mu na yi muna girkin abincin rana, tare,
Sai bayan Sallah azahar yaya Abubakar yabugo min waya yana cewa daga gida suka wuce, gaida mama sai kuma wani abokin su da gidan shi ya kone suka tafi mai jaje,
Akarshe yake tambayana da cewa ba dai matsala ko ?
Murmushi nasake ina cewa saidai na rashin ganin yayana a kusa dani, ba,
Yaji dadin may na,ce haka yasa shi dan murmushi jindadi,
Yace ai, gani zuwa don nasan mama tai min abinci rana, yanzu haka ko ,
Nace kaman kasani yaya amma dai tuwon shimkafa nace tai maka shine ta hada ma harda dan wake wai tasan kana son cin danwake da,
Murna sosai naji yanayi yace wa kifara min godiya kafin in zo, don ban san yaushe, rabona da cin dan wake ba,
Kafin yazo na dan tashi na shiga wasu sassan gidan mu ina gaida su,,
Sai zuwa dare na samu shiga asibiti,gurin gaida mama,
Gaskiya yau jikin ya dan yi dama sau don da alamar taji sauki,
Tun shiga na mama wace ke zaune tana shan kunu acikin cup,
Mu kayi arba da ita, sai naga ta kauda kai gefe guda, kaman bata kaunan gani na,
Har gaban ta na karasa ina gaishe ta da jiki,
Kamar bata son ansawa ta nsa min tare da kauda kanta gefe guda,,
Nagane may take nufi amma sai naki gushewa daga gaban ta naja na tsaya, mata,
Da ta gaji da aje kanta a gefe guda sai takai kwance ,
Anty, Safiya ce ke min magana daga bayana, tana cewa,
Matar yayana jiyafa munga sako, daga yayan mun gode,,
Da mamaki na juyo ina kallon Anty Safiya ina murmushi nace nikan anty ai wanan zancen kune ba nawa bane,,
Sai da dare yaya zo dakin inda yake tambayan yan uwan haihuwan shi, koda wace cikin su za,ai tafiyan,
Inajin yadda suke muhawara a tsakanin su, don anty ,Samira ce tafara magana tana cewa nidai kar ku sani don kun ga halin da nake ciki,
Haka dai sukai ta cecekuce, inda anty mariya tadage akan cewa itace zata,
Dole kowa ya kyale ta, ta tafi din su zasu zo daga baya suga jikin mama din insha Allah,,
Motar asibiti ce yaya yai haya zata kai, Mama Ladi har Abuja, tare da baba Wadda da Anty mariya,
Washe gari badon naso ba mukayi sallama da iyayyena da yan uwa da abokan arziki,
Mun kusa shiga sokoto,ne na dan matsa kusa da yaya Abubakar,nadan kwantar da kaina ga kafadar shi,
A hankali naji yana sauke ajiyan zuciya mai yar nauyi,
A hankali nace mashi yaya Allah yaba wa mama, lafiya
Ya ansa min da amin a hankali,,
Inda naji ya dankara matse ni zuwa jikin shi yana cewa, kici gabada kula da kanki pls,
Kudi ya mikomin don zasu kai kamar dubu hamsin, zanyi magana ya kada min kai dole nayi shiru bance komai ba sai dai ina rike a jikin shi,,,
A sokoto yaya Abubakar suka saukeni a gida tare da tsarabar da nazo ma su da shi,
Mun rabuzukatan mu babu dadi acikin ta don ga zancen ciwon mama ga kuma kewan rabuwa da junar mu da zamu kara yi,

****** ********* ******
Masu tafiya sun isa Abuja lafiya inda ba bata lokaci ya kai,ta Turkish hospital,
Inda kwararu likitoci suka diba mashi ita, Baba Wadda tare dashi aketa faman wanan zirgazirgan asibitin,
Salawatu tare da abokan ta sun zo gaida mama da abin arzikin su fam a leda,
Sun dan zauna jim kadan sanan su kace zasu tafi,
Kufi lubuna ta mikowa, Anty Mariya, tana cewa su zasu tafi Allah ya sauwaka,
Anty Mariya tabi bayan su don yi masu rakiya, suna cewa ta tsaya amma saida ta bi su har bakin motan su,
Sai da zasu tafine Anty mariya ke tambayar wace amaryan tasu ne daga cikin su,
Lubuna ta nuna mata Salawatu, wace take kokarin shiga mota, daga dayan bangaren,
Addu,an, Allah ya nuna masu anyi wanan abin arzikkin suke fata, kamar yadda tace,
Ai mu mun fi son ki shigo ko gidan dan uwan mu zai gyaru,
Bayan ta koma daki ta zaina kirga kudin da Lubuna ta miko mata dubu ashirin ne cif,
Tace cafdi mace ke kyautar kudi haka masu yawa, don aso ta kawai,,
ta maida kudin acikin aljihun bujen ta taja zip, ta rufe,
Sun kwana sun wuni Sadiya bata lekasu ba, tun zuwan da tayi da dare ranan da akabawa mama gado,
Tun abin bai damun Mama wace tafar murmurewa zuwa yanzu,
Har takai ga cewa su Anty Mariya, da Baba Wadda,
Shin Sadiya ko tazo ne tana barci?
Anty Mariya tace tun ranan da mu kazo tun ranan tazo dubaki tare da yaya,
Kagin su tafi duk ta ishe mu da tsaki tana tacewa yaya wai a kai,ta gida, ina jin sai da yai mata dan fada ta daina damun shi
Mama tace ke Mariya, badai, Sadiya ba sai dai in akwai wani matsala da ya hanata zuwa kawai,
Shiru Anty Mariya tayi don tasan cewa mama bazata taba yarda ai maganar Sadiya ba agaban ta,
Don ita Sadiya bata laifi agurin ta, sai dai yaya Abubakar yayi laifi,,
Sai bayan kwana biyu anty Sadiya tazo duba Mama yadda take wani ya tsune fuska tankar mai jin, warin su,
Shigowan yaya Abubakar dakin ya sa hankalin su dawowa gareshi,
Dauke yake da ledojin take away, din da ya sayo masu abinci,
Daga gurin da mama take kwance ya karasa yana cewa mama tashi kidan ci abinci ko sai kisha maganin ki ki kwanta,,
Mama ta ya mutsa fuska tana cewa, nagaji wanan shimkafa shimkafan maisunan malam, kace ma matarka tai muna tuwo mana haka,
Gurin da Sadiya take yadan kalla yana mata wani kallon ke kin ji ko ?
Ita ko Sadiya ko a jikinta don bata damu ba sam, don ba matsalar ta bane,
Yan office, din su yaya Abubakar da kuma abokan arzikin shi haka suke zuwa, gaida Mama, Ladi tare da mata abin arziki,
Wanda ganin haka yasa Mama Ladi kara mikewa saman gadon asibiti,
Don ita bata da niyar tashi, zuwa gida sam, ranan da yaya Abubakar yazo fada mata cewa za,a sallamay ta sai cewa tayi,,
Kada akawo mata bakin ciki a filin Allah don anga ta na samun abin arzikigurin mutanen arziki za aimata bakin ciki haka,?
Sai da lalashi da ban baki aka samu mama tayarda zata koma gida,

****** ********* ******
Yaya Abubakar bai samu kwaso su, ba da kan shi zuwa gida,
Don haka ya tura malam Mudi da driver don su kwaso su mama zuwa gidan shi bayan an sallamay su daga asibitin,
A falo su ka yada zango don basu san inda zasu shiga ba,
Ga yunwa na cin su don ba akai masu abin karin kumallo safe ba
Tun da sallamar safiyane akai masu,daga asibitin,
Tunda su ka shigo gidan ba kowa a falo malam Mudi, yai ta kwada sallama kamar tashin hankali,
Bashiri Anty Sadiya ta fito falon don ganin mai wanan sallaman haka,
Ganin su ne tai wani shekeke tsaye tana masu wani irin kallon,
Sai, cewa tayi O,wo kune ashe,?
Mama ya jikin naki,?
Mama tadan ansa da kyat tana cewa taji sauki,
Tun wanan lokacin da ta shige bata kara fitowa ba,su kadai ne zaune a falon sai kalle, kalle su keyi,
Ganin yuwa zai halakasu Baba, Wadda ya fita waje, cikin Sa,a ya hadu da Hamzan maman Bi,u,
Dama tun zuwan da sukayi da su Baba musa sun san juna,
Nan Baba Wadda ke sheda mashi yunwa su keji, sun dawo daga asibiti matar gidan bata taresu ba,
Gida ya koma ya fadawa Maman Bi,u da, Fattu
Anyi sa,a angama abincin rana shi aka kwaso masu sukaci har suka bari,
Sai bayan karfe uku yaya Abubakar ya fito daga meeting din da suka shiga na gagawa,
A likacin ya bugowa Anty Sadiya waya ko ta,yiwa su mama wani dabara,,
Saicewa tayi au suna nan gidan ne dama ?
Wani irin abu ya ji a ran shi baisan lokacin da ya fisgi mota ba sai gida dauke da abincin take away,
A lokacin suna zaune fali suna sallah la,asar bayan sunyo alwala can wajen get, din gidan,
A falo ya samay su tarshe da kayan su zube duk sun gaji,
Daki ya fada daga inda su ke suna jin, yadda yaya Abubakar wanda bai magana yau yana daga harshe gurin sababi,
Dakin dake gefen na Sadiya yasa key ya bude masu dakin na bukatan gyara,sosai,
Hamza ya kira awaje ya sheda mashi cewa, yazo ya taimaka mashi da aiki,.
Kafin wani lokaci da Hamza da Baba Wadda sun gyara dakin nan tsab sun kwashe kayan su mama sun kai, ciki,
Wanan abin ranan yabawa Mama Ladi mamaki matuka,
Da yamma sai ga Maman Bi,u da Fattu dauke da kulolin abinci lafiyayye sun kawo wa mama, ladi,
Lokacin da yaya Abubakar yadawo daga massalaci ya samay su zaune suna cin abincin da su Fattu suka kawo masu,
Duk nauyi da kunya ya kamashi, mama cikin muryan mai ciwo take ce ma yaya Abubakar ya zauna yaci abinci, mana yace ya koshi,,
Tausayi yaba mahaifiyar nashi don ada da bata gani ba sai take ganin ka,zafi ake wa Sadiya don ba,a kaunar auren shi da ita
Amma sai gashi ta gani da idon ta, sam Sadiya bata wani damu da zancen,

Basuga Sadiya ba


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login