Showing 12001 words to 15000 words out of 388021 words

Chapter 5 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8231

gida idan ya isa,
Yace ba don sakon mutane da Abubakar ya bashi da bazai fadawa kowa cewa ya tafi har Lagos din ba,
Shigan su garin Birnin kebbi da misalin magriba mota bata tsaya da shi ko ina ba sai uguwar su watau, shiyan Sarakuna,,,,
Mutane suna alwalan sallah magrib suka ga tsayawar mota a sheke da kaya cikin ta,,
Kowa idon shi na kai har malam wanda bai san ko wani bako ne ba a wanan lokacin, na huturo,,,
Wada ya bude mota tare da ahi da driver suka fito a lokaci guda,
Daga shi har driver haraman alwala suka fara yi duk da dinbin gajiyan dake a tare da su,,,
Sai da ya karanto, yan addu,oin da ya iya wai kada malam yai mashi fada, a kan tafiyan shi,
San,nan, ya tunkari gurin da malam yake a zaune ya jan casbi,
Ganin yana lazimi yasa shi komawa baya a lokacin har driver ya fara sauke kanyan motan,
Nan Wada ya kira yaran dake gurin don su kwashi kayan zuwa cikin gida,
Mahaifiyae shi da tun isowar shi yara suka sheka suka fada mata tana cen cikin farin cikin ganin dan ta ya, dawo gida lafiya,
Ganin irin kayan da ake ta faman shigowa da shi wai duk tsaraban Baba Wada,
Shi yasa har matan wani lungu zuwa ganin gulma da sunan sun,zo taron Wada ne,
Abin "da mahaifi, har mahaifiyar shi ta gabatar mai da abinci da su ruwan sha a daki,
Sai daukan abincin yayi yace bari ya kai, waje su ci da driver,
Sai a lokacin mahaifiyar shi wace jin dadi ya hana ta tun farko tambayan Dan, nata inda ya tafi,
Kai tsaye batare da wani shakkunta ba ya ce mata, Lagos gurin Abubakar,
Lagos Wada ?
Da kai dawa shi katafi ?
Ni kadai ya bata ansa a takaice,batare da jin wani darr, ba,
Kafin tai wani magana ya sukkuci kolan abincin nashi zuwa waje gurin driver da ya ce,
Ya samu har yana niyar tafiya alokacin amma sai wada ya tsaida shi da magiya don ya tsaya suci abinci,
Da kyat driver ya tsaya inda sukaci abinci da abokin tafiyan shi na wanan ranan,,

Wada ne a gaban malam kai a sunkuye, cikin tsananin tsoro malam karo na farko a rayuwan shi,
Don haka ya yanke wa kan shi shawaran fadawa malam cewa Abubakar ne ya bukaci ya zo inda yake,
Wanan zancen ya batawa malam rai inda yace a harzuke yaushe har ka ga Abubakar din yace kazo,
Kai a sunkuye Wada ya ce tun lokacin da zai koma da yazo ,
Wanan zancen kawai ne inji malam watau kai ka girma har ka kai lokacin da zakai bugun gaban kan ka, ka ai,watar da abin da kaga dama,?
Wada yai maza ya kara sunkuyar da kan shi a kasa,,
Don jin may mahaifin shi yace, da kyat ya iya cewa ayi hakkuri malam,
Malam yasan idan yace zaiyi magana rayuwan shi zai ci gaba da baci sai kawai yaja bakin shi yai shiru,,,
Tsawon wani lokaci Wada ya na duke a wurin, malam bai ce komai ba sai can yaji muryan malam ya na cewa akira ma shi Samaila,
Hakan ya sa wada gane cewa ba zancen shi malam ke yi ba,a yanzu, kuma, bai da halin yin maganar,
Don haka ya mike a hankali zuwa dakin mahaifiyar shi,cikin sanyin jiki,, duk sai bai ji dadin abinda ya aikat ba,
Dan sako yadawo yana sheda,wa Malam cewa Baba Samaila wai tun safe bai da lafiya,
Cikin murya mai kama da fada Malam Manya yace,,
Samaila yaro na ? da zai zauna da ciwo daki bai fadawa kowa ba,
Baba Buhari malam yasa a kira mashi don ya je ya dubu Baba Samaila, ya ga ya jikin na shi, ya ke,?
Sosai Baba Buhari hankalin shi ya tashi don dama duk yinin yau baida kwanciyar hankali,
Rayuwan shi yau a,bace yake don bai ko son yaga mama ladi a fuskan shi yake ji,,,,

Yadda Baba Buhari ya samu Baba Samaila yasa hankalin shi tashi a lokaci guda,
Don a rufe yake tun daga kan shi harzuwa kafan shi cikin wani katon bargo,
Take abinda yafaru da safe dasu ya fado mai a rayuwan shi,
Cikin wani irin tausayi da kuma tsoron halin da dan uwan shi ya ke a ciki,,,
Cikin sauri ya juya zuwa gurin Malam Manya mahaifin su don ya sanar da,shi abinda ke faruwa,
Tsugune Baba Buhari ya ke agaban mahaifin su yana sheda mashi abinda yafaru dashi,
Subbahanallahi inji Malam yace ya akayi baku sanar da ni ba tun farkon faruwan abin,
Daga haka ya mike shima yau da kan shi har cikin Sashen Baba Samaila,
Kamar yadda Baba Buhari yabar shi tun farko hakan suka samay shi,
Kira biyu zuwa uku Baba Buhari yai ma Baba Samaila amma bai iya ansawa, ba,
Hakan ya kara tayar masu da hankali sosai don haka ba bata lokaci malam ya,juya,zuwa Shiyan shi,
Bayan wasu lokota,sai ga malam ya,dawo dauke da wani roba mai, ruwa aciki, shi,,
Malam, yasa Baba Buhari ya kware mai bargon da ya ke a ciki,
Kwance yake idon shi a kafe sai, rawan dari da yake yi,
Daidai gurin kan shi malam ya nufa inda ya dafe goshin Baba,Samaila, a hankali,
Adduoi, yafara jefo mai ya na tofa mai a goshi, sai kuma, ruwan da yake yayafa mai a duk kan sassan jikin shi a hankali,
Ba,a gushe ana mai haka ba ya sake wani irin ajiyan zuciya mai karfi, tare da kokarin dagowa,
Cikin sauri Baba Buhari ya dan danne shi ta mai da shi saman gadon,
A hankali ya ke bude idon shi acikin wani yanayi na rashin fahinta, inda yake sosai yake kallon su,
Ganin haka hankalin Baba Buhari yai matukar tashi, a take idon shi ya fara silalo da hawaye,
Nan take gaba dayan su suka shiga karanto addu,o,i iri iri don neman tsari a gurin ubangiji mu,
Sannu a hankali ya koma barcin da yake yi sai dai wanan karon numfashin shi yana sauka,a hankali ba kamar farko ba,
Ganin ya samu barci kuma alamar da yar sauki a zancen
Yasa malam yasa Baba Buhari ya debo mai garwashin wuta a waje,
Cikin sauri baba ya nufi gurin samo garwashin, wutan da aka umurce shi,
Wani dan kulli malam y bude ya debo hayaki aciki,
Nan aka zuba duk da barci yakeyi amm sai da ya dinga sake atishawa, mai karfi har sau biyu,
Malam manya da Baba Buhari dake gefe suka, sauke ajiya zuciya a hankali,
Sai a lokacin malam ya juyo inda Baba Buhari yake a tsaye, ya ce,
Ya samu sauki insha Allah, amma idan ya farka a bashi wanan ruwan ya sha,
Har malam ya taka kamar zai bar dakin sai kuma ya juyo, inda Baba Buhari yake a tsaye
Yanayin fuskan malam yasa gaban Baba Buhari ya yanke ya fadi,
Malam yace,cikin wani irin yana yi wanan zancen yazama siri a tsakani ku da dan uwanka har matar ka,
Cikin karfin hali Baba Buhari ya,ansa da kada kai gami da cewa to, a fili,
Daga haka malam yabar shiya cikin sauri batare da ya kara furta wani abu,ba,,,,,,

Mama Ladi wace tin safe ta kasa zaune ta kasa tsaye don maigidan nata bai ce mata kalla ba akan wanan mumunan halitan da suka dauka a dakin ta, wada za aiy da dodon kwallah a takaice,,,
Ga sako tun da rana da Hajja ta damay ta da,shi wai tazo malam na San,inna na son ganin su,
Wanan aiken ya kara tayar mata da hankali sosai don tana tsan,manin ko, dodon kwallah ya koma gurin shi ne,
Amma ta san yau duk abinda zai faru sai dai ya faru don dai ba ta da wani kafa da hae zata samu fita zuwa Anguwa,
Don a yinin ranan ba abinda takeyi sai rokon ubangiji Allah sauki,,,

Ba karamin kidemawa mama Ladi tayi ba, don ganin irin aiken da Abubakar dan ta wanda suke kira da mai sunan malam, ya yi ba,
Hakalinta ya tashi kwarai duk da tana cikin tashin hankalin dama,
Sam bata taba tunanen cewa yana da irin wanan arzikin ba,
Sai gashi zuwan Wada gurin shi yai ma kowa aike da ya tayae mata da hankali,
Mama bata san lokacin da ta manta wancen zabcen Dodon kwallah nata ba,
Sai ta hau sake maganganu kawai tana cewa wai anfara zuwa gurin dan ta yawon maula batare da sanin ta ba,
Sai kuma cewa da takeyi ita bazata yarda a mallake mata "da ba har ya dinga abu batare da shawaranta ba,
Hakan yasa tun tana yi ba wanda ya tanka mata har saida Baba,Buhari ya taka har kofan nata duk da haushin ta da yake ji,
Daga labulen dakin yayi ya ce mata cikin fada, Ji mana Ladi,
Kin dai san cewa dama ina da,ke a raina ko? Ba wai na manta da zancen bane,,
Don a,sanadinki ga dan uwana can a kwance tun jiya,
Don haka ki san zaman ki a gidan nan tun yanzu don ba, zan yarda ki zubar muna da darajan gida ba a cikin shiya,,,
Tunda Baba Buhari ya fara magana sai mama ladi tai tsit don ta hango zancen gaskiya ya ke a idon shi,,,,
Ganin bazata tanka masa ba yau ya sa shi kumtawa da karfi alamar zaki sani,,,
Can cikin gida kuwa sai murna da farin cikine ya mamaye kowa don ba lungun gidan da,ba aiwa alheri ba,
Abinka da babban gida kafin wani lokaci labari ya karade cewa mama Ladi batai farin ciki ba da,wanan baiwan da Allah yai mata,a dakin ta,
Don dai ka haifi da yana wa mutane alheri wani abu ne na musan man,,,,

Yau kimanin sati uku ke nan da komawan Baba Wada gida daga Lagos,
Zama tsakanin Abubakar da matar shi ana dai yi ne kawai don kowa ma miskilin kanshine, ba mijin ba ba matar ba,
Babu wani abinda ke burge shi daga halaiyan Sadiya din,
Duk ta kowani gefe Sadiya bata da gurin da za,a yaba mata akai,
Don haka, yau tun wayewar gari Abubakar ke son yiwa Sadiya magana akan ta je gurin gyaran kai ko kitso,
Sai dai kuma yana dan shakkan yi mata zan cen don baya son ta fassara mai zancen shi,
Don inhar son samu ne itace da kanta ya kamata ta san kanta yana bukatan gyara,
Gashi kuma agaskiya dole ne yau ya daure ya fada mata ta gyara kan nata,
Sai da ya dauko goran ruwa a fridge ya dawo inda ya ke zaune da farko,
Muryan shi Sadiya taji yana cewa Ni kan dai Sadiya nace yau ya kamata ki shirya in kai gurin gyaran kai ko kamar yadda naga mata suna yi,,
Abinda Abubakar ya fahinta shine tunda ya fara magana
Sadiya tai yi kicin kincin da fuskan ta alamar maganar bai mata dai ba,
Sai cewa tayi gaskiya ni ban son fita ban san kowa ba a gari
Ai,kuma gashi, nakan iya kamawa na gyara da kauna,
Murmushi yayi irin na takaici yace Sadiya ke nan
In banda abinki ta yaya mutum zaiwa kan shi gyara kamar yadda wani zai mai yayi kyau,
Ka???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ra bata rai tayi alamar yanzu bata yarda da zancen zuwa gurin gyara ba,
Daga karshe sai cewa tayi ni banga rashin kyaun wanan din da nake lalabawa kaina ba,
Galala ya yi ya saki baki yana kallonta don kuwa tagama bashi mamaki,,,,


ZEEE MAKAWA YELWA=?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
7?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

IYYAKA NA,ABBUDDU WA,IYAKA,NAS,TA,INN,


SADAUKARWA
Sadaaukar da wanan pages din a kullun gare ku yan family mu na ALIYU HARZAMI KANO

FATAN, ALHERI GARE KU MAKARANTA WANAN NOVEL DIN MAI FADAKARWA,


A kan wata katuwar shifidaddiyar tabar suke zaune, a sashen malam,
Kallo guda zakaiwa Baba Samaila kagane cewa yai ciwo mai karfi a cikin yan kwanakin nan,
Duk wanda yaga irin yadda aka shimfida wanan tabarman yau in dai har a gidan kake ba wani abin mamaki ba,
Don duk wata maga tasamu mai muhinmanci za,ayita haka ake shimfida,
Sai har matan sashen na malam dole a lokacin subar sashen har zuwa lokacin da za,a gama zancen,
Zaune suke da alamar suna jiran wanine a lokacin,
Mama Ladi ce tafe cikin tsoro da fargaba take tafiya don jin da tayi cewa malam ne yau da kan shi ke kiranta,
Wasu zannuwa masu ruwan zuma da yan adon flowers kore da ja ne a jikin ta,
Ta daura guda da dan kwalin shi da riga sauran sanda biyu kuma ta yafa a jikin ta har zuwa kai,
Azaton mama ladi tunda taji shiru har kwana kusan goma ta dauka zancen ya wuce ne,
Amma kiran da malam yai mata yau ya sa ta jin nauyi da fargaba don bata san ko may zai faru ba,
Wani iri tsuki Baba Buhari ya ja tunda ta tunkaro gurin,
Cikin tsawa ya ce mata ke dai san ke mu ka zaman jira tun dazun shina ki ka wagga tahiya,
Malam Manya ne cikin murya irin ta manya ya ce mashi koni, "an, bita sannu, tunda ta taho,,,
Can gefe guda,mama Ladi ta samu ta zauna ta gaida malam a hankali,
Addu,a akafara bude taron dashi,, tare da neman wa zurian su gamawa lafiya, da fatan alheri ga ko wani musulmi,,,,

Gyaran murya malam din yayi wanda ya kara dawo da hankali kowa zuwa gare shi, don sauraren abin da zaice,
Malam ya fara da kiran sunan mama Ladi, da cewa,
Ladi,
Mama ta ansa kai a sunkuya da cewa naam Baba,
Wanan zaman da ki ka ga mun,yi don ki muka yi shi badon komai ba sai don, mu tatauna mu ji yaya ankayi haka ya hwaru,?
Shirune ya biyo baya tankar babu wani mahaluki a gurin zaune,
Ganin baza tai magana ba yasa Baba Buhari cewa cikin bacin rai ko ni an malam bari dai in yanke alakata ga wagga bakin irin ,
Yar nema mugguyar shiya,
Dibo wadda kinka mayar min da dan uwa saboda bakin kwadan ki,
Mi kin ka rasa duniya ? da,,,,,,,
Malam ne ya katse Baba Buhari cikin daga hannu tare da kiran sunan shi da karfi,
Wanda hakan yasa baba saurin yin shiru don bin umurnin mahaifin shi,,,
Malam ya ce Ladi an, magana zakiyi don musan ta ida zamu bullo ma,wagga zancen,
Don ba karamar magana ta, ba ke ga aikina ta sihiri,
Ko yaushe yana iya dawo wa,
Gaban mama Ladi ne ya fadi ras don jin cewa wanan dodon kwallah zai iya dawo wa ko wani lokaci,
Zama ta dan gyara tare da kara dukar da kan ta a kasa inda tafara cewa,,,
Malam, walle sherin shedan na da kuma Hajja ,,,
Gani ni, nayi ina zaman banza bani sana,a shina na tai inda Hajja, ni ce ta taimaka min,
Walle bata fada min cewa sihirina za,a yi min ba sai dai bayan kwana biyu ta aiko min cewa in aiko da, kwalin, Lipton shayi guda uku,
Sai na saye na aika mata dashi takara aikowa tace in dan bayar da ko nawa gare ni,,
Sai na aika mata da dari biyar, bayan kwana hudu ta aiko cewa ranan laraba mai zuwa in taho da kwallah akwai inda zamuna
Sainace mata banda kwallah mai dan kyawo tace min in bari tana dubawa cikin nata,,
Sai kuma ta kasa karasa maganan tai shiru tare da dukar da kai,
Muryan malam ce da ya jefo mata tanbaya yasa ta saurin dago kai,
Wane malamina ko in ce boka kun ka tai wuri nai ?
Nan ma shiru mama Ladi tayi saida Baba Buhari ya daka mata tsawa,
Cikin dan i,iniya tace malam na San,Inna munkatai wuri nai
Wa, akacewa hakana inji malam ke tambaya tace shina can kasan yar mayan ka shike da zama,
Salati sukayi gaba dayan su yadda akayi tun daga shiyan sarakuna ace mace ta tashi har mayan ka,,,
Malam ya ce Ladi baki kyauta ba gaskiya, ke manta da gidan da kika aure na,,
A ce yau macen da ke gidan ga na, ta tai gurin Boka don dai rashin tawakkali,
Ladi rashin tauhidi na har ya kai,ki ga wagga harkan,
Yau idan kaga mutum na sha,ani nai iyakan ka dashi ijjiya,
Amma tambaya ba shi shuka ma alheri ga wagga zamani da muke ciki,
Ke de ga halin da dan uwan mijinki ya shiga ciki sanadiyar wagga abin,
Sai a lokacin mama ladi ta daga kai ta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login