Showing 201001 words to 204000 words out of 388021 words

Chapter 68 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8243

Shi dai ina nuna mai sai bai karbi takardan ba ma tun da ya gane dai cewa na tafi asibitin har ga sheda,
Allah ya saika yai min tare da jadda da min cewa in kula da shan magani na please,
Tare da kula da jikina kamar yadda aka umurce ni da yi asibitin
Nai hamdallah ga Allah don bai sa Yayana ya fahinci plan di na ba,
Abu guda nake dan fahinta irin yadda na ke ganin kaman cewa akwai matsala a tsakanin Yayana da Sadiya, Saboda irin yadda take mai abubuwa da bai dace ba, agidan,
Ni dai sai nake ta kokarin nuna cewa ban fahinci komai ba akai,

****** ********** ******
Tsuki taja tare da kauda kai gefen window da take a zaune inda driver sai faman sharara gudu yake da su a titi,
Lubuna tace gaskiya Salawatu inda nasan haka gurin nan yake da nisa sosai da banzo wallahi sai dai kizo ke kadai,
Ita ma Salawatu a cikin nuna gajiya a fuskan ta tace, ban taba zaton cewa gurin yana da nisa haka ba wallahi,
Lubuna tace ni wallahi mamaki kike bani Salawa ace kamar ki duk kin tsaya kin susuce a kan namiji guda haka wai har ya ke ta juya ki irin yadda ya so,,
Ki duba fa har aikin da kike yi yanzu kin daina gaba daya da sunan ki na hutun aure har yanzu banga kin fito ba,
Kina gida kina ta kwasan masifa da karamar Yarinya, inda ace kin koma ga aikin ki ne ai da duk wanan fitinan bakiyi shi ba,
Yaushe ma kike da time din tsayawa wani fitina irin haka ?
Murmushi kawai Salawatu tai mata tare da lumshe ido irin na takaici,
Ta ce adaidai lokacin da take kokarin gyara zaman ta daga gajiyan da tayi da zama,
Cikin murya mai kasala tare da lumshe idon ta a hankali,
Lubuna shi fa Oga habit din shi is different from the others,,
Dariya Lubuna tayi tare da itama gyara zaman ta acikin gajiya yana kokarin jawo gyalen ta da ta zauna akai,
Ke dai kawai kin mutu wa wanan guy din bakya ganin laifin shi ko kadan
Murmushi Salawatu tayi mata cikin jin zafin irin son da takewa mijin nata,
Sai bayan Sallah la,asar lis suka isa garin birnin Kebbi, agajiye suke gaba dayan su har driver su,
Mai yar mashin suka samu suka bukaci da yai masu jagora zuwa Shiyan Sarakuna,
Har cikin shiyan mai yar mashin ya kaisu suka bashi dubu daya yana ta godiya da mamakin su,
Kwatancen da Bado driver yai madu shi suka inda suka kai har k???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ofan gidan mu driver ya kawo su,
Tun suna zaune a cikin mota su ka hango, bawan Allah malam tsoho zaune tare da dattijan suna karatu,
Yana saye da farar shadda anyi mai babban riga da yar cikin sa,
Kanshi da hulla wanda hullan a daura mai rawani akai,
Ksan duk wanda ke a kofan gidan ya na kallon motar don suga wanda zaifito daga cikin motar,
Banda malam tsoho wandai baima san da tsayuwar motar ba agurin
Sai biyawa wani dan matashin saurayi karatu yakeyi hannun shi yana rike da bulalan fata,
Lubuna tace see the wicked old man ,
No,Wander ashe babban malami ne shiya sa duk abin da mukayi bai kama shegu,
Salawatu tace I beg make we, live dis place first before you talk,
You know he's witch man,
Daga haka suka fifito daga cikin motan inda ake ta mamakin ko wurin wa wayan nan matan kabilan sukazo haka,
Wasu yan mata da ke kokarin barin gurin karatun don an tada su suka biyo suna kallon su Salawatu ,
Lubuna ce tace sannun ku yan mata don Allah muna tambaya ne please ,
Sai yaran dukkan su su biyu suka dan tsaya daga nesa su na kallon su,
Lubuna tace muna son ku kai mu part din mahaifiyar Abubakar wanda ke aiki a Abuja
Sai Yarinya tace mijin Meenat din gidan ga ?
Duk da maganan ya soshi ran Salawatu amma sai suka daure suka amsa mata da cewa Eh shi din,
Su ka ce zo mu kai ku, ba bata lokai su kafara tafiyw su Salawa sukabi bayan su
Babu wani mayafin kirki mai nuna cewa akwai macen aure daga cikin su,
Hankalin mazan gurin duk ya gare su ganin zasu shige basu gaida kowa ba yasa Baba Buhari dakawa yan matan dake masu jagora tsawa da cewa
Ke ina zaku kai su ?
Kun san su na halan ?
Yarinyan ciin dan rawa murya tace ,a, a cewa sun kayi wai mu nuna masu inda Mama Ladi,
Baba Buhati ya kara nanatawa da cewa Ladin shin su suwa na shim ?
Walle baba bamu san su ba mudai abinda dai sunka tambaye mu ke nan,
Cikin mamaki Baba Buhari yace, daga ina kuke tafe ne ?
Lubuna ce cikin karfin hali take cewa, muna neman Mama ce,
Matar Abubakar, ce daga, Abuja, ke tafe yanzun nan,
Wani, irin kallon ke din a haka din ?
Sai da duk suka ji wani irin nauyin kallon da Baba Buhari yai masu,,
Shiko Baba wani irin bacin rai ne yaji a lokacin ganin wanan macen wai ita ce matsayin sarakuwar shi matar mai sunan malam,
Ganin yadda ya dawo gurin su rai a bace yasa kowa ke tambayan shin su wana ?
Cikin wani irin murya ya juta ya na daukan buta don yin alawala ya ce wai ita ta amaryan maisunan malam,
Baba Samaila daga gurin da yake ya zaune yana kallon duk abinda ke guda na, tun farko,
Yace ke ku tai ki kaisu sashen Ladi din kice bakina, tayi daga gurin mai Sunan malam,
Sannu,ku da zuwa sannun ku da hayan a,a kuna tafe, ?
Ko,wa yabi su da kallon, mamaki,
Yau anyi baki a gidan malam da har zasu wuce, malam zaune a kofa ba su gaida shi ba
Lailai ko zamani ya zo da canji sosai, da har an samu sarakuwa agidan malam da bazata iya tsayawa ba ta gaida shi,,
Sai faman haraman sallah magrib suke yi a lokacin don, lokaci ya gabato,,

****** ********** ******
Sarama Alaikum, cikin hausan yaren da addini bai wani zauna a zuciyar su ba,
Wa ka wanga irin sallaman haka inji Anty Mariya wace tazo gaida mama Ladi,
Ganin yan matan nan suna cewa ga sashen nata mu,mun tafi suka juya din wucewa,
Lubuna ta ce su tsaya tabasu five hundreds naira, tace su raba,
Sai suka ,a a wallah ki bar shi don dai mun gwada maku sashen Mama zaku bamu kudi ?
Suka wuce abin su batare da,sun karbi kudin ba da aka ba su,
Sallama suka karayi daidai suna shiga cikin part din na Mama Ladi Anty mariya ce tagane su tace kamar Amaryan mai sunan malam,
Mama Ladi wace ta dawo daga ban daki tana kokarin zama saman wani dutse da take alawala akai,,
Tace suna shin kin kace ?
Har kasa Salawatu takai gwiwoyin ta tana cewa Mama sannu da gida mun samay ku lafiya,
Tabarma Anty Mariya ta dauko masu daga cikin daki tana masu sannu da zuwa, ta shim fida masu a kofan dakin Mama Ladin,
Ta wuce da gudu zuwa sashen baba Hamza don sayo masu ruwan sanyi su sha,
Sai wani kalle kalle sukeyi suna wani mayde baki kamar masu jin kazanta ko wari,
Anty Mariya wace ta shiga sashen Baba Hamza a rude tana cewa matar maisunan malam ce suka zo yanzu,
Matan Baba Hamza su kace wace tace ta karshen mana wanan ma,aikaciyan,
Da sauri ta karbi ruwan leda tabar part din zuwa na Mama Ladi,
Kafin wani lokaci duk labari ya karade gida cewa matan Yaya Abubakar amaryan shi babban ma,akaciya tazo,
Sai tururuwan zuwa gaida su akeyi da kuma ganin kwam irin na mutanen babban gida,
Mamakin irin yawan gidan mu, suka farayi shi babban gidane,
Sai dai suna ta kokarin gane ko wacece mahaifiyana daga cikin su,
Mamana batazo ba saida kwanonin abincin da ta kwashe wanda tasawa Baba shi ta sa a wani sabon kula ta kai masu,
Amma basu gane ta ba don duk basu yi tsan manin cewa mama ce ta haifeni ba,
Sai da sukayi alawala su kayi sallah kamar kowa,
Sannan suka dan zauna cin a binci sai bayan wani dan lokaci maza suka fara zuwa gaida su suna masu sannu da zuwa,
Kowa sai kallon mamaki akewa Salawatu don sun ce ta girmay yaya Abubakar nisa ba kusa ba,,
Salawatu tace tana son ai masu iso su gaida malam don gobe tun da safe zasu koma insha Allah,
Daidai malam din ya shigo gidane aika masu iso gurin shi,
Yana zaune ya gaman cin abincin dare tare da matan shi,
Suka iso sai wani irin kamahi da karnin man bleaching ke tashi,
Bayan sun gaisa ne Salawatu take,cewa dama Yaya Abubakar ne yace tazo ta gaida shi takuma ga yan uwan shi,
Daga cikin duhu gurin da malam din yake zaune suka kura mai ido inda suke kallon irin kaman da tsohon yayi da Yaya Abubakar sosai,
Waya ta jawo tafara kiran layin Yaya Abubakar din don ta sheda mai ta iso,

****** ********** ******
Dining ya fara zuwa inda ya bude kulan abinci yaga cewa babu wanda ya ci abinci a lokacin,
Sai ya rufe ya nufi part din anty Sadiya ya samu suna shafa magani sai faman cewa takeyi wa Ramatu kada fa ki danna min kwarai don da sauran zafi a gurin,
Yai masu sannu tare da tambayan ko sun shafa maikama da man shafin da aka bayar ta dinga shafawa idan zata kwanta,
Anty Sadiya acikin dan daure fuska tace ai na fadama bazan kara amfani da abinda ya bayar yanzu ba,
Don na gane cuta ya shiga cikkin harkan nashi saboda son kudin dan adam,
Yaya Abubakar yace duk da na fada maki cewa, kiyi amfani dashi tunda wanda ya bamu da farko munga amfanin sa ina ruwanki da sherin sa ke, badai lafiyan ki akajawa ba kawai,
Tace ai nace bazan yi ba don ban mason inji zancen shi sam wallahi,
Ramatu ta jefa masu baki a zancen su da cewa haba hajiya kiyi hakkuri da kiyi amfani dashi kamar yadda ya umurce ki da kiyi,
Wani tsawa ta dakawa Ramatu inda cikin murya kamar fada take cewa ke Ramatu kada ki soma kice zaki tsoma min bakin ki ga zancen mu, nida mijina,
Allah ya baki hakkuri Hajiya dama don naga yana cewa ashafa maki ne shiyasa nace kiyi hakkuri ki bari a shafa maki din,,
Ke Ramatu naga fa al,amarinki irin na munafukaine don haka ni ban yarda da ke ba ma sam, wallahi,
Innalillahi wa,ina alaihim raji,um,
Hajiya mai yai zafi haka har da wanan shedan haka subbahanallah inji Ramatu sai hawaye, masu zafi shar, shar shar, suka zo mata,
Ganin haka Yaya Abubakar acikin bacin rai yabar dakin na Sadiya rai a bace batare da yw kara cewa uffan ba kuma,
Ina kwance a lokacin ina jin wani irin tashin zuciya na damuna kamar amai zai zo min,
Jin shigowan shi a dakina yasa ni gane cewa shine ya shigo a wanan lokacin,
Ganin irin yanayin kwanciyan danayi yasa shi, cewa tun kan ya karaso May ke damun ki kuma haka Meenat ?
Gab da zai iso gare ni na mike da sauri jikina har yana ciri na nufi bandaki,
Na dinga kwarara amai tankar zan shude, a lokacin don sai nake gani kaman zan amaye komai na cikina,
Na mike tsaye bayan na dan wanke baki na daniyar in koma daki,
Sai na ji wani iri jiwa ya kara kwasa na kan zan fadi,,
Ban san cewa Yaya yana tsaye a bayana ba duk aman nan da na keyi sai da nai kamar zan fadi naji ya riko ni ta baya,
Dauka na yayi cak a cikin damuwa zuwa saman gado na,
Yana jin yadda nake cewa wayyo Allah wai wai ina dafe kaina,
Yana tsaye ya tsura min ido yana kallo na a cikin mamaki,
Bai min magana basai naga ya juya yafita ya bar dakin ina ta kai na don haka ban tsaya mamaki ba,
Bai wani dade ba ya shigo dakin ya na ce min ina card din da kike zuwa asibiti,
Duk da ciwon da nake ji sai da gabana ya fadi don nasan yau asirina zai tonu ke nan,
Ba musu dole na dauko katin acikin hand bag dina na bashi ya kama min hannuwa na tare da rufo min kofan daki muka fita,
Daidai zamu bar get din gidan mu su Baba Wadda dasu Baba Hamza suna zaune suna hira,
Suka ga fitowan mu hakan ne ya nuna masu ba lafiya don sun san cewa shi bai fitan dare,
Duk suka taso zuwa gurin motan mu suna cewa lafiya dai ko ?
Cikin rashin sake fuska kamar yadda ya ke ce masu bata jin dadin jikin tane , zamu tafi asibiti ne Baba Hamza' yace asha
Bari mu tafi tare ya bude motan shi da Baba Wadda muka wuto da su zuwa asibitin,
Kafin mu bar uguwan Hamza ke cewa Usman don Allah ka kai muna kayan mu cikin gida ko,
Yace to yayi yanzu zan kwashe ashiga ma ka da su don muma zamu tashi ke nan,
Wayan Yaya Abubakar tai kara ya dauka sunan wace ya gani yaso ya share amma kuma yadda wayan ke ta kuka yana neman agaji yasa shi dauka acikin muryan dakilan ci yace,
Hello,,
Ta amsa da cewa hello sweet Oga gamu nan tare da Old man zaune,
Ki bashi phone din ya ce acikin mamaki,,
Sai yaji muryan malam tsoho yana cewa maisuna muna zaune sai ga baki mun gani bamu da labarin zuwan su,
A dan dadare yace eh tafiyan nata babu shirine shiyasa baku sani ba,
Malam tsoho yace to madallah nan yake cewa
Nagode sai ayi ta hakkuri da jama,a da iyali Yaya Abubakar yace ba komai,
Salawatu ta karbi wayan tana cewa ok sai mun dawo ke nan,
Bai bata amsa ba sai cewa da yayi Ok kawai, ya fara kashe wayan ta bangaren shi kanfin ta kashe,
Dan tsuki yaja tare da cewa a lokacin da yake karya kwana, shiga asibitin da zamu
Baba Wadda Salawatu ce, ta tafi Birnin Kebbi yau yanzu haka tana can suna tare da malam,
Baba Wadda yace may ta,tafiyi haka har can Birnin Kebbi,
Ina jin Yaya yai murmushin takaici yana cewa yar rashin mutunci ce nace sai ta roki malam gafarane,
Don ce mashi da tayi mugun tsoho shine don bata da hankali ashe ta tafi bashi hakkurin, da nace din,
Wanan matar taka mai sunan malam sai kai don daini gaskiya bamu shiri da ita ,
Cikin magagin ciwon dake damuna nace tunda har ta tafi don ALLAH Yaya kayi hakkuri please,,,
Bai tanka ba sai ci gaba da tukin motar da yayi tare da shafan fuskan shi da hannuwan shi yana mai sauke, ajiyan zuciya,

****** ********** ******
Muna zaune a gaban likita bayan yadan duba file dina yai rubutu akai ya dago idon shi yana kallo na yace,
Madam na fada maki sai kin bi jikin ki a sannu fa saboda ki samu lafiya shi wanan aman da kike yi ba komai bane don zai zo ya tsaya nan da dan wani lokaci saboda haka sai ki dan kara tsare bed rest din ki, please
Nace to doctor na gode yace ba matsala Allah ya sauwaka yanzu , ku sayi wanan maganin don wanan aman da ke yawan damun ki,,
Sai dai zakiyi ta barci sosai don maganin yana sa barci ne idan ansha,
Ina ganin fitan mu office din doctor na sauke ajiyan zuciya tare da Hamdala na godewa Allah na ,da doctor bai tona min asiri ba,
Mun sayi maganin muka juyo zuwa gida inda Yaya ke tambayana cewa,
Ko akwai abinda na ke son a saya min sai da na tofar da yawu a tissue nace kaza mai zafi da Ice cream
Bayan mun dawo na kara watsa ma jikina ruwa ko zanji sanyi don zafi nake ji sosai, a lokacin,
Ina zaune a bakin mirror na ina dan kokarin shafa ma jikina dan mai sama sama,
Yaya Abubakar ya shigo dakin yana kallona wani irin canzawa ya ga nai mashi ko ina nawa ya wani cicikowa na kara zama wata fresh,
Har ya iso inda nake zaune yana tambayana cewa kin ci naman kin sha magani, kuwa ?
Najawo Hijab dina ina sakawa nace yanzu zan sha Yaya, kazar kuma duk ta fita rai na wallahi,
Yace sai mai kuma to zaki ci ga abinci can baki taba ba ,na bare, magani nasha na kora da ruwa,
Ina kokarin hawa gado ne saboda duk na rasa may ke min dadi shiko yaya yana tsaye yana min kallon tuhuma, ganin yadda na canza a lokaci guda,
Da ga inda nake kwance Na gyara juyawa tare da lumshe


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login