Showing 48001 words to 51000 words out of 388021 words

Chapter 17 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8312

yan uwa kaduba iri mai kyau kaza ba
Don dai a gaskiya ba zan yarda tun ina da rayuwa ba, ace wai jikana ne ya auro irin wanan zurian agidan mu,,,

Abubakar wanda tun fara maganar kakan nashi yake sauraren shi ya ce malam
A gaskiya na fada maka akwai kalar matar da nake bukatar in aura tun farko,
Don haka yanzu kuma naga wacce nake so don Allah kubar ni inyi abin da rayuwana ke muradi,
Malam ya ce badai ita wanan din ba sai dai ka dawo nan gida kebbi ka duba kalar ta,,,
Daga haka tsohon ya kashe wayar shi batare da yajira yaji mai jikan nashi zaice ba,

Innalillahi kawai Abubakar ya iya nanatawa a lokacin don tun daga kafan shi har kai wani irin abu yake ji tankar ya fadi,
May zai sa suyi mashi hakane bayan tun yana yaro baida zabin kanshi komai akan umurni yake tafiyar da shi,
Rai bace ya lalabo noban Baba Samaila duk da dai ai har da shi a cikin masu zuwa su fadawa malam mumunar labari akan salawatu,
Bayan sun gaisa ne sai zancen da yasa ya bugo mai waya yafara da cewa,
Baba a gaskiya ban ji dadin abinda aka fadawa malam ba a kan wanan yarinyar da na tura ku nemar min,
Baba Samaila wanda a lokacin shima ya na zaune ya fara cin abinci a take yaji abinci ya fita ran shi,
Baba Samaila ya ce haba mai sunan malam ka kwantar da hankalin ka mana ka fahinci komai, yadda yake,
Koda zamu bata zancen ka ne ai kasan bakamar yadda kake nufi ba ko ?
Kaifa ba jahili bane ya kamata ace kasan yadda zancen yake,
To baba in banda abin malam auren zumunci auren sunna ne ?
Manzon Allah S A W babu yar uwar sa acikin matan shi ko da akwai ma bai tilasta yin hakan ba ko da acikin sunna
Kuma ai matan sa bawai duk yan kabilar sa bane,
Don haka ita dai wanan din itace zabina ita nake so in aura koma yaya take,
Kana ko cikin hankalinka mai sunan malam ?
Kada zancen mace ya sa ka koma mara biyayya ga iyayyen ka ?
To bara kaji wanan karon babazan goyi bayanvka muddin kace zaka bijerwa mahaifan ka,
Kabari abi abin asannu don a samu a rabu lafiya ai naga ko anan gida birnin kebbi akwai yan mata kyawawa da zaka so,
Baba har yanzu baku fahince ni sosai ba, ni fa ba wai al,adace a gaba na ba
Addini nake son koyi akai nasan cewa yaran mu suna da kyau da asali da tarbiya irin wanda yan birni basu da shi,
To amma ko wani namiji da akwai abinda ya ke so ga mace ,,,
To ka bari abi abin a sannu ko ina ga zaifi sauki sosai,,,,,



ZEEE MAKAWA YELWA,,,
[7/14, 10:48 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
2? 1?


ZAINAB IDRIS MAKAWA


ALLAH-AL-MUTAKABBIR

Sheshekan kukan da Meenatu ke yi yatayar wa amarya da hankali sosai cikin fada take cewa kiyi shiru Meenatu an,
In uncle din ki ya dawo zan fada mai yai masa iya ka dake,
Don su ba kunya bane garesu, ya dauka cewa ke irin dabi,un yaran gidan su ke gare ki,
Dabiar da za aita rugumar juna da dan uwa wai dabiun wayewa wanan ai lalacewa ne da watse,
Wanan maganar ya sa Meenatu dan dakata wa don ta saurari zancen amarya,
Anan ta shiga bata labarin rayuwar turawan da sukeyi a gidan su,,
Sai a lokacin meena cikin murya mai kuka tace to ni iyayye na ba yan aron al,adun wasu bane su yarda koyarwan iyayye da kakan,ni,
Mu gidan mu muna koyi da sunanan maikin Allah ne mazon rahama,
To kin ga ai hakan da kikai masa gobe bazai kara ba don ya san tarbiya ba daya,,,
A haka ta samu har meenat din tai shiru daga kuka da bacin ran da take ciki,

Sosai rayuwan uncle Nafi,u ya baci don jin abinda ya faru tsakanin Meenatu da kanin matar shi,
Duk irin mutuncin da ke a tsakanin Nafi,u da Ali,Abbas sai da wanan zancen yaso ya hada su fada sosai,
Amma da yake mazane sai suka kai rayukan su nisa suka sasanta da junan su,
Inda shi Ali, Abbas ya kwantar da kai gurin Nafi,u yana cewa shi wallahi auren Meena yake son yi ba wai yai mata haka da wani manufa bane,,,,,
Daga karshe dai uncle Nafi,u ya ce ya bari abi abin a sannu don har yanzu Meenat yarinya ce,,,,,,,,,

****** ******** ******
Abubakar yayi shiru yaji duk jikin shi yai sanyi lankwas,
Wanan sabon al,amarin da ya bolle mai maigirma ne sosai,
Don haka maganar Baba Samaila kuma gaskiya ne,
A hankali dole zai bi da malam tsoho ya samu ya lalaba shi akan zancen,
Shi in fa badon mahaifan shi ba bai ga dalilin da zai sa malam tsoho ya dinga taka mai burki ga al,amarin shi ba,

Duk yan kwanakin nan duk wanda yasan Abubakar yasan da cewa ya canza sosai,,
Ga kuma aiyuka da suka taso mai daga gurin aikin su,
A bangare Salawatu kuma duk da ba wani abinda tagani na canji daga Abubakar amma jikin ta ya bata cewa tun zuwan iyayyen shi Abuja akwai matsala sosai,
Don a irin yadda da farko yake nuna mata cewa bada dadewa ba zasu yi aure sam yanzu ya daina hakan,
Kwatakwata ma bai zancen auren su a yanzu din sai dai yana yawan nuna mata kulawa da kuma kashe mata kudi,,,
Abubakar yana sane da cewa hankalin salawatu a zuwa yanzu ya tashi matuka don dai bata ga fuska yadda zatai mai korafi bane,
Tun bayan wani rana da ta faraxmai magana suna acikin mota a hanyar su ta dawowa daga gurin aiki,
Tsawa ya daka mata tare da mata kashedin yi mai katsalandar ga harkan shi,
Yace bani nace maki naji zanyi ba koke ce kika sani ,
Salawa sai hakkuri kawai take ba shi a lokacin don ganin irin yadda idon shi ya rine a lokaci guda yai wani ja kamar garwashin wuta,
Mtsss ya ja wani dogon tsaki tare da rike kanshi da yake ji a lokacin tankar zai tsage,
Hannayen shi guda biyu da suje a cure guri guda yake dan dukka kadan kadan,
A wanan yanayin, shi kadai yasan,irin abinda yake ji a zuciyar shi
Zaune yake a office din shi saman kujerar shi duk da tolin aikin dake gaban shi ya kasa aiwatar da komai akai,
Mtsew ya sake jan wani sabon tsaki, tare da furzar da iska daga cikin bakin shi a lokacin,,,,,
Yasan duk inda wanan sherin yafito daga bakin kannen mahaifin shi ne,,,
Baba yahaya ko baba hamza don koda rantsuwa yayi bazaiyi kaffara ba ,
Baba samaila bazai taba yi mai wanan gamin ba a surin tsoho,,,
Ajiyan zuciya ya sauke a lokaci guda don tunawa da shawaran da Baba Samaila ya bashi yasan cewa shima Baba samailan zai yi wani abu akai ke nan,,,,

****** ******** ******
Tun faruwan wanan zance Meena bata wani sake jiki a gidan ba,
Kwatakwata ma hankalinta ya koma gida birnin kebbi ba abinda take so kamar taje taga kakan ta malam tsoho, mai bata sudin kwanon fura da waina,,da, baban ta da maman su da yan uwanta,,
Kasan cewar zasu kwana biyu ba su da lacca,
Musalin karfe goma na safe sai kawai ta yanke shawaran ta wuce birnin kebbi kawai ta gano gida,
Gurin anty amarya ta wuce ta sheda mata cewa zata je birnin kebbi yau,
Da mamaki uwar dakin nata ke kallon ta, tana tunanen kodai Meenatu nason zuwa gida tafadi abinda ya faru da ita ne,
Ido ta dan tsurawa meenatu din sannan ta kira sunan ta ,
"Meeena,
Meeenat wacce ta dan dago kai ta kalle ta a hankali,
Anty, tace kardai ince abinda yafaru tsakanin ki da Ali Abbas zai saki tafiyagida ?
Kai meenat ta kada a hankali alamar a,a badon shi ba zata tafi,,,
Murmushi anty ta, sake a lokaci guda tace, don Allah meenatu kada ki fadawa iyayyen ki don rayuwan su zai baci suga kamar ba,a ai maki rikon kwarai a nan,,,
Meena ta dubi anty amarya tace insha Allah anty ba zan taba fada masu wanan zancen ba,

Karfe daya saura Meenatu ta na cikin garin birnin kebbi, a cikin shiga ta mutunci,
Kallo guda zakai mata ka ga canji sosai daga gare ta saboda yanauin canjin gurin zama,
Mai mashin na sauketa a kofan gida da yar jakar ta da tasa kayan ta aciki sai kuma wani jakar vaco da ta saka tsaraban da su Anty amarya da mummy suka bayar ta kawo wa mahaifiyar ta da kannen ta,,
Tun daga nesa malam tsoho ya hango ta yaga irin yadda yarinyar ta canza a lokaci guda,
Su baba Buhari da ta sama a kofan gida su ta fara gayar wa dacewa
Baba ina wunin ku ?
Meeenatu ke, ta tahe yanzu,
"Ni ta Baba'
Ina wajen su kawun naki duk suna lahiya ko ?
Walleh duk lahiya muke Baba,,
To, a gaishe ki, ke ji

Da murmushi a fuskan ta, ta karasa gurin malam din ta na cewa malam ina fatan akwai sudin fura mai sanyi,
Ho yar nema kina son sudin fura kika tafi kika bar ni da fura na,
Meeena tai murmushi tace to ai gani naji kewar ka na dawo don in gan ka insha kuma fura,,,
Ke ta att ta he yau, ?
Ya ya gurin kawon naki da sauran jama,an ku,,
Lahiya lau muke malam tsoho,
Wani kamshi ne mai ma,ana yaji yana tashi a jikin jikar tashi,
Wanda hakan ya nuna mai cewa yanzu akwai canji mai yawa daga jikan tashi, sosai,
Mikewa tayi cikin fara,an ta zuwa cikin gida rataye da yar jakar ta a kafadar ta,
Da murnan ta tashiga ciki tana cewa Salamu,Alaikum,
A,a a maraba da mutan sakoto kece a tafe yau Meenatu, ?
Mutanen da ta ke cin karo da su a hanyar ta ta shiga cikin sashen su ke nan,
Murna sosai na jin dadi meena keyi don wani irin yanayi sa ta tsunci kanta aciki,
Matar baba yahaya, tace a a maraba da Meenatu, wallahibdazun nagama zancen ki,
Murmushi Meenatayi don tasan gaskiya ce saboda suna dasawa da ita sosai,
Daga haka Meenat ta wuce zuwa cikin shiyar su,
A bakin murhu ta samu mama,Saratu tana kokarin raba abincin rana,
A,a ke ta tahe yanzu ?
Darabon yau muci abincin rana da ke ?
Murmushi tayi kawai tana kokarin aje jakar hannun ta a cikin rumfar dake tsakar gidan ku,,
Ya wajen su kawun na ku da iyalin shi ?
Wani irin Meenat taji a lokacin da mama take mata wanan tambayar,
Duk yadda taso ta boye bacin ranta abin ya kiya don a daidai lokacin mama ta dago kai don ta kara tambayar ta,
Amma sai ta fahinci a kwai matsala ga zuciyar yar nata
Saboa irin yadda fuskanta ya sauya a lokaci guda,
A may kuma ya faru don naga kamar daga tambayar su kin canza fuska,
Murmushi Meenat ta kakaro na karfin hali don kawar da zargi daga mama,
Tace a haba dai mama gajiyane kawai nayi saboda motar da na shigo yar karamace duk a matse muka iso garin nan,,
To ki dan watsa ruwa mana ko zaki walware ko ?
To mama amma barin shiga in gaida su mama kafin in huta ko ?
Hakan yayi inji mama wace ke kokarin rufe tukunyar da ta gama raba tuwon shinkafa da miya yakuwa, da ya ji kulikuli,,,
Sashen su mama Ladi dake can ta karshen gida ta ziyarta karshe,
Mama Ladi wace tun sallamar Meena ta kalleta tun daga kasar ta har saman ta sanan ta bata fuska gami da karba sallamar ta,
Samira ce tafito a daidai lokacin da Meenat ta kai kasa tana gaida mama ladin,
A,a mutanen sokoto kune yau a garin namu, haka ?
Anty Samira kina ciki ashe,?
Ai na zata ko kin koma Abuja ne ai ,
Samira tayi dariya tace kai Meenatu akwai ki da zolaya
Ai nida Abuja ko ziyar balle leke indai da zamane, ?
Dariya suka sa gaba sayan su a lokaci guda meenat tace haka dai ki kace
Mama ladi dake daga gefe guda cikin kushewa ta ce,
Aiduk diya, ta gari a gidan uban ta an kasan ta ba yawo kalar dagi ba don kwadayi gashi kuma wasu har yanzu banda canza halitta basu zama komai ba,
Duk da Meena tasan da ita mama keyi amma sai tai dariya kawai tankar bata fahinci mama ladin ba,
Samira ce wace da jin abinda mahaifiyar ta tace ta bata fuska tadan joyo gurin Meenat tace dama ko ina son ganin ki kaina ta,
Akwai labari mai, dadi amna sai kin huta zan shigo har lungun ku in gan ki,
Wai ko Meenatu ke ga wadda kin ka koma kuwa ?
Walleh ke yi wani irin fresh da keyyah kamar ba keta ba,
Shin mi aa,r sirrin na muma mu shige ciki ?
Haba anty samira
Hadda keyya wurin yi min sheri?
Walleh ba sheri ba na Meena ke san ankusa bukin mu ,
Cikin budan ido da mamaki Meenat tace da gaske, shin ?
Mama Ladi wace ke tsaye ta na wa meena wani kallon kaskanci sanan tace,
To mayye na fadawa meenatu me zatayi maki?
Me ar gare ta ?
Sosai wanan maganar ya so ki zuciyar meena
Meenat tadan dago kai cikin murmushi tankar maganar bai zafe ta ba tace,
Mama na gaishe ku zanna in huta gajiya anty Samira sai ke taho,
Meenat na fita tun bata kai kofa ba taji muryan mama tana cewa ,
Samira so kike kizubar min da mutunci me zaki bida ga wagga diyan matsiyatan ?
Haba mama nida yar uwata zakice min haka na kedai san tsakan mu sai Allah ko ?

Rai a bace meenatabar sashen maladi da mamaki azuciyar ta yaushe mama zata canza halinta ne ?
Ba abin mamaki bane ganin yadda meena ta dawo cikin bacin rai ko ba,a fada ba tasan sun kwaso da mamaladi ke nan ?
Baba yaji dadin ganin meenatu gida da ya dawo,
Don haka sun kai wani lokaci zaune tare suna hira har ibrahim shima yayan ta ya dawo ya samay ta sukaci gaba da hiran su,
Sai dare lokacin da meenat ta san cewa malam ya shigo gida daga majalissan shi na kofan gida,
Lokacin ne taje gurin shi don su gais? da shi din kamar yadda ta saba yi idan tadawo,,,
Malam na murmushi da ya gan,ta yana cewa mutanen sokoto baki barci bane,?
A,a malam ina jiran ka shigo mu gaisa ne kafin in kwanta, ne,
Murmushi malam yayi yace ke yar nema kedai taho ki shanye min fura kawai
Dariya tayi don tuna baya irin yadda takan zauna don tasha furan malam tai,ya mai hira,
Ke da Abubakar dai kamin wanan halin duk cikin jikokina,
Sai a lokacin ta tuna da ta na da dan uwa Abubakar agidan su
Tambayar malam tayi ina yayan nasu da iyalin shi,
Malam yadan gyada kai yace yanan nan,
Kwanan nan yadauko rigima wai aure zai kara,
Allah sarki in,ji meena gaskiya yana da bukatar hakan,


****** ******** ******
Jin shiru da malam yayai Abubakar bai tuntube shi da zancen komai aasa shi tunanen ko ya canza shawara ne
Amma sai yace bari ya tun,tube shi yaji komay yake ciki a kan shawaran da yabashi na yazo gida ya nema anan,
Baba Samaila wanda yazo gaida malam din da safe kafin ya fita zuwa gurin neman kudin shi,
Baba Samaila yana shirin wucewa malam tsoho yace
Samaila dauki waya ka kira min danka Abubakar muyi magana,
A take yadauki wayan malam dake gefe yakira mashi Abubakar din,
Wanda alokacin yana zaune office din shi yana kokarin fara aiki,
Ganin nobar malam tsoho ke kiran shi tun da safe haka
Yasa gaban shi faduwa don yana tunanen ba lafiya ba kila, kira haka da safe,
Gaisawa suka fara sai kuma yar shiru da ya biyo baya
Can ya ke cewa dama na bugo makane don inji yazancen mu ya kwana ne,
Jiki a sanyaye ya cewa kakan nashi malam ina nan akan zance na,
Amma zan tafi England wurin karo ilimi na wata shidda sai na dawo zamu kai karshen maganar,
To shike nan Allah ya kai mu, Allah kuma ya kaika lafiya yabada sa,a,
To ameen malam nagode,,,
Daga haka suka kashe


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login