Showing 372001 words to 375000 words out of 388021 words

Chapter 125 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8192

a lokacin,
Duk yadda Salawatu tasan cewa zata dauke mai hankali ba tare da ya tuna da zancen matan shi na gida ba shi take yi,
Don tafe take da jakar kayan sihirin ta, don ance tsafi gaskiyan mai shi,
Tana jin irin yadda sukan ta masifa da Fatima ko Sadiya a waya idan sun kirashi, sai dai tace mai wai kishine ba komai ba ya fita batun su kawai,
Baida yadda zaiyi tunda magani yana aiki a kan shi a lokacin don haka sai kawai ya share su,
Ganin cewa na kirashi har sau biyu amma ya shareni tun a lokacin nafita batun shi bankara kiran shi a waya ba,
Gashi zuwa lokacin na mayar da jikina nai kyau duk da ina da damuwa a tare dani, amna bai hanani nuna cewa nayi lafiya,
Bakin cikin Salawatu shine bata taba jin na kira layin shi ba in yi korafi akai, kwatakwata ma batajin na kirashi,,
Yau suna zaune a falo yana aiki a vikin system din shi ita kuma tana kwance tayi filo da cinyan shi,
Tace mai wai Oga ita Meenatu bata Abujane naga bata kiran ka sam,
Duk da odan yaji zance na alokacin wani irin yanayi faduwan gaba yake ji,
Amma sai ya daure yana cewa ina zata tafi kawai dai bata da ra,ayin kirane kawai,
Wani haushi taji a ranta don ba haka taso ya fada ba a kaina taso taja zancen ta samu ta zuga shi,
Hakan yasa ta anyanawa a ranta cewa lalai sai takara tashi tsaye a kan wanan yar iskan yarinyar jikan malamai,
Nan ta soma tunane irin matakin da zata dauka akaina tunda ga dama ta samu yanzu,
To amma wai may ye matsalane tunda duk umurnin da aka bata ta aiwatar kamar yadda malam yace tayi,
Amma sam bataga wani canzawa ba daga Meenatun har ma shi Abubakar din don bataga yana ma Meenatu cin mutunci da yake da sauran matan nashi ba,
Shiru tayi tana ci gaba da tunanen irin matakin da zata dauka akai,
Yana magana da ita amma sam bataji may yake fada ba har sai da yadan tabota yana cewa ta hado mai ruwan zafi yasha magani,
Ta mike zuciyan ta fam da tunanen sheri tana nasa cewa, du yadda zatayi ko ta wace haline sai ta raba shi da kowace a duniya don ita kadai take son ta mallake shi a duniyan nan,

****** ********** ******
Hakuri kawai nake da daure a zuciyata amma wanan sharinyan da Yaya yai muna yai muni da yawa gaskiya don yanzu kusan wata biyu kenan rabon shi da ya ziyarci iyalin shi yana can tare da Salawatu wace ke ta cusa mai mugun agumo yana shanyewa,
A zuwa wanan lokacin hakurina ya kai bango don haka nake shirin zuwa gida birnin kebbi nida yarana da sister dina sai Anty raino,
Amma sai Ramatu ta tafi tafadawa mijin Fattu inda yai min nasiha kancewa nayi hakkuri don Allah kada na yarda na bari a gane halin da muke aciki,
Saboda shi kan shi Lawal din yana dan yawan yi mashi nasiha amma sai yace shi kawai bai ra,ayin zuwa ne a lokacin amma ba komai bane hakan,
Fitan shi daga part dina ina jin muryan shi a falo suna magana da Sadiya,
A daidai lokacin da na mike don zuba ruwa a cup in sha tea saboda yarana su samu ruwan nono wadattace su sha,
A lokacin ne wayana ya fara ruri alamar kira ya shigo min,
Ina dubawa naga malam tsoho ne ke kirana a lokacin wani irin dadine ya ziyarci zuciya na ya baibaye min duk jikina,
Na dauki wayan da sallama a bakina sai naji shi yana cewa ai nazaci kema bazaki dauki wayan ba irin na mijin ki,
Nace acikin dariya haba malam banda kazafi fa Yayana ba zai taba kin daga wayan kowaba balle kai Aminin shi,
Sai naji yana cewa cikin dariya ho "yan nema bata bari mijin ta yai laifi, ai,
Zaune na kai a bakin gadona ina cewa malam ina kwana ya amsa cikin murya mai dadi da cewa lafiya Aminatu yaya yaran yaya kuma karfin jikin ki,
Na amsa dacewa malam duk muna nan kalau wallahi,
Murmushi naji yayi yana cewa masha Allahu Aminatu na kira layin mijiki jiya da dare amna bai daga wayan ba shine nace barin kiraki in fada maki cewa ina son yin magana dashi,
Nace a sanyaye da tau malam zan bugawaya in fada mashi sakon ka insha Allahu,
Nan naji yana cewa Wadda ya fada min cewa ya kwana biyu bai samu shigowa gurin nakuba,
Nace aikine yai mashi yawa acan din shi yasa bai zo ba,
Naji yace tau Aminatu na sanki da hakkuri ki kara hakkuri akan wanda kike dashi don zaman duniya sai da hakkuri,
Balle irin rayuwan ku na birni da kuke mu,a mullada mutane da yawa,
Ga mijin ku mai son tara iyali, ne shi a rayuwan shi, don haka ki kara hakkuri ki rubonya hakkurin ki akan wanda kike da shi,,
Na amsa a cikin sanyin murya da cewa tau malam nagode insha Allahu zan tsare, amar yadda kace,
Ya amsa da cewa madallah Meenatu Allah ya albarkaci auren ku yai wa zurian ku albarka ya tsone idon makiya akan ku kiyi ta addua kinji meenatu,
Na amsa murya a raunane dacewa insha Allahu malam nagode zanyi duk abinda kace,
Yace yauwa Meenat kada ki manta sako na dan Allah ki fada wa mijiki yakirani akwai maganar da nak3 son muyi dashi,
Nakara amsawa dacewa insha Allahu malam zan fada mashi, a haka mukayi sallama dashi acikin dadin rai,
Kalaman malam tsoho sun tsaya min a rai matuka inda azuciya nake cewa da malam yasan irin halin rayuwan da nake ciki a yanzu da yasan cewa ina hakkuri sosai,
Inda ga rashin lafiya ga yara har hudu amma mahaifin su sam bai damu da yaji lafiyan mu ba ,
Yana can ya samu tsohuwar mace ya lake mata suna ta masha,an su,,
Ban san lokacin da idanuwana suka kawo hawaye ba a hankali tausayina dana yarana yafara ziyaran zuciyata ,
Gamu a garin mutane wanda ya kawo mu garin yai banza damu ya tafi ya barmu,
Cikin rashin kulawa da sanin irin halin da muke ciki a nan din,
Amma yanzu mutanen gida suna can suna zaton muna nan mna jindadin rayuwa mn fita batun su,
Sakon malam tsoho ne ya tsaya min a rai na rasa yadda zanyi na fadawa yaya Abubakar gashi nasan cewa tunda malam din ya bugo min wayan yana da bukatan magana da shine din kamar yadda yace,
Don haka na daure na daga waya da niyar nakirashi na fada mashi sakon tsohon dake bukatan magana dashi,
Kafin nakirashi sai da nadan dauki lokaci ina rike da waya a hannuwana sai faman tunane nake a raina yadda zai karbi wayan nawa,
Don kada ya tuhumi ko nayi karanshine a gurin dan tsohon mai albarka,
Cikin daurewa na dauki wayan na latsa kiran nomban shi inda naji tafara ringing,
Kalman sha hadda na sauke sau uku kafin ya dauki wayan yadaga daga bangaren shi don dama nasan bawai lalai ya daga wayan ba,,,,


ZEEE MAKAWA YELWA YAURI SEENABU,,,,,,
[12/21, 10:27 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
1? 0? 7?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH AL HAADI

JUMMA,AT MUBARAK TO OUR BROTHER'S AND SISTERS IN ISLAM ALL OVER THE WORLD,,,,
WISH YOU BEST OF LUCK FOR THESE SPECIAL DAY ALLAHUMA AMEEN YA ALLAH=?O?=?O?=?O?

Sometimes yakan yi tunanen iyalinshi amma da zaran ya ji muryan su sai yaji gaba daya hankalin shi a tashe yake da su bai bukatan jin muryoyin su a kunuwan shi ,,,
Sai yayi niyar kiran watan Meenatu amma sai yaji wata zuciya ta hane shi da kiranta a lokacin ,
Shi yanzu baida abin so da sha,awa daya wuce mai matar shi Salawatu don a ganin shi a gareta ne kawai yake samun piece din rayuwan shi,
Haka itama bangaren Salawatu duniya ta dawo mata sabuwa yanzu sai wanda kanta yake tana cin karen ta ba babbaka,,
Sai kokarin mantar da shi kowa take a rayuwa tana kara blackmailing din sauran a gurin shi musan man Meenatu,
Amir yai zazzabi kwana biyu, ban fada mai ba nice da Lawal mijin Fattu mukai ta kaishi asibiti har Allah yaba yaron lafiya,
Inda na godewa Allah shine yarana ba masu fitina bane don haka nake kara kula dasu una kuma basu abinci yadda ya kamata,
Abinda ban sani ba ashe mijin Fattu ya fada mashi zancen ciwon Amir din sai ya kama fada wai don may ni ba zan kirashi in fada mashi ba, sai dai yaji a gurin mijin Fattu din har yake cewa shi gaskiya yagaji da irin halaiyan da nake nuna mashi hakana,
Salawatu tashiga aikin zuga shi ya cika fan yana jiran na kirashi yai min cin mutunci,,,
Daga karshe yaga har anyi kwanaki bankira ba ga kuma zancen ya tsaya mai arai shi ne ya yanke shawaran yau ya kirani yai min tas,
Sai gashi yaga ina kiran shi a waya don na fada mai sakon malam tsoho din wanda ke bukatan yin magana dashi,
Ban sa cewa zai daga watan ba amma dai duk da hakan ina ta yin kalman shahada da Ya Fattahu a bakina,
Gaba da wayan zata katse naji ya daga wayan yana cewa he'llo
Sai ni kuma na dauka da cewa Assalamu Alaikum,
Azaton shi zancen Amir ne zanyi mai don haka babu ko gaisuwa saicewa yayi knga yaron ya kai ga galabaita yasa kika bugo wayan ko,
Sai kije kiyi yadda kike so tunda bukatar ki ta biya yanzu,
A hankali na maimai da cewa yaro wani yaro kuma ganin zai hauni da fada nace dakata malam ,
Ni ba wani abu yasa na kirakaba sai don na fada ma cewa malam yana son magana da kai don ya kiraka baka daga waya ba,
Daga haka na kashe wayan a cikin bacin rai ba tare da na tsaya jiran jin amsan da zai bani ba,
Raina a bace duk da jin muryan nashi ta haifar min da wani irin yanayi a zuciya ta amma sai na dake da irin abinda nake ji na basar dashi, kawai,

****** ********** ******
Mamaki ne ya cika mai zuciyar shi fam irin yadda na bashi amsa a zafafe abinda ban taba yi mai ba a rayuwa ke nan,
Sai kuma tunanen abinda nace malam tsoho yana son ganin shi ke nan ana nufin cewa na kai karan shi a gurin malam din ke nan ko may,
Yasan dan tsoho da dadin lafazi zai iya tilasta shi akan mu don haka ya yanke a ranshi cewa ba zai kira tsohon ba ma kwatakwata,
Bayan ya koma gida yake fadawa Salawatu wace a yanzu sai yadda tace don komai sai ya fada mata saboda irin maganin da taje ta dinkira mashi yana ci da sha da wanka ,
Gashi a koda yaushe rana manne dashi bata bari yayi wani isassashen ibada kamar yadda ya kamata ya dinga yi,
Don tasan idan ya fara yin ibada to duk wani plans din ta zai rushe ne kuma,
Gashi tasha alwashin duk sai ta rabashi da kowa nashi tabarshi daga shi sai ita tayi yadda ranta ke so,
K???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?wana biyu kenan da wanan zancen namu amma bai kira tsohon ba don bai son fitina,
Gashi kuma zuciyar shi taki sakat a lokacin don haka ya kasa sukuni da walwala a tare da shi,
A cikin yanayi mara dadi yake zaune duk abin dunita ya damay shi ya hana shi sakat a lokacin
Kiran tsohon yashigo mai Allah ya taimaka a lokacin Salawatu bata a tare da shi tana gida,
Ya dauki wayan a cikin sanyi jiki duk da gaban shi sai mugun faduwa yake ji
Muryan dan tsohon a cikin sallama irin ta addinin musulunci ya dauki wayan yana cewa , haba takwarana yau kusan kwana uku ke nan ina son ka dauki waya muyi magana,
Azaton Abubakar akan zancen iyalinshine za,a yi magana sai cewa yayi,
Malam nasan cewa ba kowa zai kai karana gurin ka ba sai Meenatu don bata da kunya yatake son na raba rainane wai ?
Aiki yai min yawa anan shi yasa na zauna amma su duk basu fahince ni ba sun mayar da zancen fitina.
Maisuna ka saurareni ni babu wanda ya kawo min karanka gurina,
Matsalace ta rashin lafiya nadan samu shine nake kiranka in fada maka ko Allah yasa kun san magani acan gurin ku a taimaka min,
Subbahanallahi Abubakar yace tare, da cewa malam may ke damun ka,
Cikin dan canza murya yake cewa, wallahi matsalace dai ta gurma nake gani don fitsarine ke min wuyan yi inda naje yin sa,
Subbahanallahi malam ai ba karamin matsala bane wanan kaje asibiti yace natafi sun bani kwayoyi kwanakin baya ,
Sai gashi kuma yanzu naga lalurar ta kara dawo wa kuma,
Shiru Abubakar din yayi yana nazari can yace yanzu abinda za,a yi idan na bin cika zan kira ka nai maka bayani,
Malam din yace madallah idan har an samu akirani don Allah don matsalan ba dadi wallahi,
Shine da nakira layin ka baka dauka ba na bugawa ita Aminatu ina fada mata cewa ina son magana da kai ka kirani din,
Naji shiru nake ce ko bata fadama bane yasa na kara bugo maka inji
Duk ya daburce yarasa na cewa sai sabari yake yana dan kamay kamay kawai,
A haka su kai sallama da junan su batare da sun tsaya wani dogon hira ba, kamar yadda su ka saba yi kullun,,,,
Sai dai bayan sun gama wayan ne kowan su ya shiga nazarin sabanin ra,ayin da suka samu da dan uwa,
Malam ya ce a ranshi may Abubakar ke nufi, da cewa Meenatu ta kawo mai karanshi wurin ta,
Hakan Yana nufin cewa ba lafiya a tsakanin su, ke nan, komay hakan ke nufi ne wai,
Amma zai kira Meenatu yaji daga bakin ta ko may ke gudana a tsakanin su,
Shi kuma Abubakar din tunane yake cewa watau Meenatu bata, kai karan shi ba ke nan shine dai yake tuhuman hakan,
Gashi bai ko samu tambayan lafiyan Amir ba yaji wani hali yake ciki ?
Amma zai kira Lawal mijin Fatttu ya fada mashi cewa yaje ya duba mai lafiyan yaron, don hankalin shi gaba daya ya koma ga yaton,
Amma kuma dai Meenatu takai yar zurfin ciki, ace wai har da malam da yake zaton takai karan shine gurin shi ashe bata kai shiba wani zancen ne can na daban ya ke neman shi da shi,
Sai kuma zancen rashin lafiyan tsohon yafado mashi a rai inda yake cewa ba karamin case bane, wanan ciwon da ke son kama malam din,

****** ********** ******
Ina zaune a kasan ties din falon gida inabawa Alhasan nono tare da dan shafa mai mai a jikin shi don naga kamar jikin shi yadan bushe wayana tai ringing Asmau ta dauko tana miko min,
Tana cewa, ga tsoho mai ran karfe yana kiran ki fa Anty,
Abinda yazo min a rai shine, Yaya Abubakar bai kira shiba yake ganin cewa, ban fada mai bane,
Ina dauka muka gaisa sai nake cewa malam don Allah kayi hakkuri nafada mashi amma bai tsaya ya fahince ni ba zan kara kiran shi in fada mai,
Malam yace Aminatu yanayin yadda ya kira sunana yasani fahintar cewa serious magana zai min, a lokacin,
Na amsa da cewa naam malam yace tambayan ki nake son yi amma ina son ki bani ansa tsakani da Allah,
Na amsa mai da cewa insha Allahu malam zan fada ma koma may nene idan na sani,
Ya ce Meenatu may ke tsakanin ki da mai gidan ki ne wai,?
Tambayan tazo min a bazata don haka sai nai shiru batare da na iya cewa komai ba,
Naji ya kara kiran sunana a karo na biyu don haka maimakon nayi magana sai kawai na saka mashi kuka,
Bayi magana ba sai ji nayi ya kashe wayan nashi hakan yasani barin falon zuwa uwar dakin nawa, inda na kwanta saman gado ina mai zubar da hawaye,
Kiran layin malam din na kara yi inda ya dauki wayan da murmushi yana ce min Meenatu kwantar da hankalinki kiyi min bayani yadda zan fahinta,
Nan na fara zayyana mai irin halin da muke ciki gaba dayan mu a gidan har yaran mu,
Sai cewa ummm, ummm malam ke yi da fadin assha assha,
Nakwashe komai kaf na fada mai inda naji ya sauke ajiyan zuciya yana cewa akwai sakacin addini ga maisuna na, sosai,
Kuma bayan haka shi asiri wani babban al,amari ga maiyin shi idan yasaka gaba a yin shi sai yaga yakai ga samun nasara, akai musanman sanan yake sake wani sabon shiri,
Don haka tun farko Meenatu ita wanan shumar abokiyar zaman taku bawai ta bar halinta bane akoda yaushe a cikin kawo maku hari take,
Amma Allah yana tsare ku daga sherinta yanzu haka wani sabon shiri ne ta sake wanda yafi wanda take a kan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login