Showing 162001 words to 165000 words out of 388021 words

Chapter 55 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8277

duk sun fitar mata da suran jikin ta, fili, kirjin ta ba komai ya shafe plat,
Wani mugun kallo ya watso mata tare da saurin kauda kan shi gare ta,
Sallawatu ta ganshi ta kuma fa irin kallon da yai mata,
Take tasha jinin jikin ta don tasan cewa tun jiya a hake yake da ita ga kuma wani babban zance da ya ahigo ciki,
Yaya Abubakar yana shiga daki ya fada bathroom din shi don ya watsa ruwa,
Ya dauki lokaci sosai yana wanke jikin shi yana tuna irin jinin da yaga yana zuba min ajiki,,
Sosai hankalin shi yakara tashi take yaji wani irin tausayi na ya kama shi,
Don yasan kamar yadda na fadi cewa ban san ina da ciki ba gaskiyan zancen ke na,
Shima da ya girmay ni bai sani ba tayaya ni zan san cewa ina dashi,
Bakowa yaja mashi wanan hasaran ba sai Sallawatu, wace yanzu aure ta ya zama mashi da ya sani,
Sai yanzu zancen malam tsoho kakan shi yake fado mashi a rai,
Yadda malam yadage yana fada mashi cewa bai hanashi aure ba amma ya auri yar asali,
Lalai malam yayi gaskiya auren yar asali shine aure don tarbiya da addini ,
Shi yanzu ba ma zai ce Sallawatu tana cika ibadan ta ba, don baya ganin tanayi,
Amma abaki tana cewa ita musulmace, sai dai bata cika ibadun ta,
Yana, fitowa daure da alwala, ya sa wata rigan ya fara sallah,,
Ya dade zaune a gurin ya na kai kukan shi ga Allah,,
Yunwa yake ji zuwa lokacin ya fito don ya samu abinda yaci,
Nice da girkin a ranan don haka ban gida sai ba wanda yai breakfast daga cikin su,
Har kitchen ya leka ko zai samu wani simple din abinci ya dan ci ba ko mai da zai iya ci gurin,
Zai fito ne suka hade da Sadiya, itama kitchen din zata shiga alokacin,
Au ka dawo a she ?
Ya bata ansa a takaice da cewa Eh,
Ya mai jikin da sauki ko ?
Alhamdullahi ta samu sauki sosai,
Bakuyi abinci ba, ke nan a gidan nan ?
Gaskiya bamu yi ba don banzaci cewa zaku dade haka ba ?
Mamaki kwarai tambayan ya bashi, don baima san ansan da zai bata ba a lokacin,
Har ya kai tsakiya sai ya juto yana cewa kina nufin cewa baku dafa komai da za,a kai masu asibitin ba, ?
Bata bashi amsa ba sai tai shiru don tasan cewa bata kyauta ba sam,
Keys din shi ya kwasa ya bar gidan cikin bacin rai rayuwan shi na mai daci,
Restaurant ya tsaya yasai abinci ya ci sai kuma yai muna takes ways din su,

Ba laifi da ya dawo yasamu idona biyu sai dai ina cikin damuwa a lokacin don haka,
Ya umarce ni da in tashi in ci abinci ba musu nadan mike tsaye duk da ina jinnjiri a lokacin,
Dai taimakon Fattu na, shiga banda ki na gyara jikina,,saidai jinin zuwa yanzu ya tsane min bai zuwa sosai kuma
Jikina dai ne ban jin kwarin shi sosai saboda jiri nake gani da na mike tsayen,
Nadan fara cin abincin amma sai naji ban iyawa saboda yadda nake jin badadi a bakina ga zuciya na yai min baki badadi saboda bacin rai,
Hawaye ne ya,silalo min daga idona duk yadda naso su tsaya min abin baiyi ba,
Fattu ce ta matso kusa dani tana fadi a hankali Meenat kibar wanan hawayen haka please,
Nace cikin dan daurewa Fattu abin da ke sani kuka,shine, idan na tuna da duk yawan hakkurin danayi amma wai saida Salawatu ta kaini ga kasa hakkuri ga al,amarin ta,
Maman Bi,u tace babu komai haka Allah ya nufa wanan ba rabo bane,
Duk yadda suka so inci abinci nakasa ci don haka nakai kwance ina mai rintse idona,
A haka barci ya kara kwasa na yai gaba dani ban san inda nake ba,
Sai zuwa yamma lis Allah ya bano ikon farkawa saidai wanan karon da wani itin matsakaicin yunwa na farka daga barcin,,
Anyi daidai mijin Fattu ya kawo muna pepper soup din kasan rago yaji kayan yaji sosai a cikin sa,
Sosai Maman Bi,u tazuba min kuma nasha da yawa,,
Saura kadan in karasa Yaya Abubakar ya shigo dakin hannu shi daukw da ledoji,
Fuskan shi na gare ni yaje cewa, kin tashi nace masa eh a hankali,
Sai kuma yakai kallon shi ga plate din dake hannu na ina sha,
Gab da gadona ya karaso yana tambayana may ke damuna yanzu nace masa babu komai,
Nan yake cewa yaso a sallamay yau amma yace wa likita yabar ni har zuwa gobe idan na kara jin karfin jiki na, a lokacin,
Maman Bi u tace gaskiyane hakan yana da kyau sosai,

Tare suka fita da, mijin Fattu wanda yau ne haduwan su na farko
Mijin Fattu bayan sun dan fita can kasan wani bishiyan mangoro da ke cikin asibitin,
Yake cewa Yaya Abubakar gaskiya abin ma yazo da sauki don ba karamin tashin hankali bane zuban ciki,
Saboda halin damuwa da Yaya Abubakar ke ciki yau shi da kan shi ke cewa mijin Fattu a cikin yar damuwa,
Kunsan ance idan magana taima yawa kasamu wani yardadde ka fada mashi don samun shawara, ko dan warware damu saboda kunci,
Abinda ya faru tsakanin mu da Sallawatu ya fada wa mijin Fattu din, inda ya kare da cewa shi yanzu ya rasa hukuncin da zai dauka akan mu,
Mijin Fattu cikin kwantar da murya yace mashi,
Hakkuri zakayi maigida don ka ga ita wanan dai itace aka zalunta,
Saboda kaida bakin kace tasamay ta tana aiyukan gida ita kuma bata gidan ma tun safe,
Kadai a takaice ita aka zalunta sosai don wanan barin ?ikin da tayi ba karamin rashi bane ai,
Amma ita wacen matar, ya kama ka dan hukun tata don tasan batayi daidai ba,
Yaya Abubakar ya kada kai, alaman ya gamsu da zancen mijin Fattu,
Don haka ya mike yana cewa, yagode kwarai da wanan shawaran don shi da farko, so yayi ya sake ta gaba daya, ya huta da tashin hankali,
Mijin Fattu yace a,a ba,a hakana ya dinga hakkuri da mata don su haka su ke, kamar tunkiyoyi,
Daga haka ya ci gaba da bashi shawara akan abinda ya dace da kowacen, mu,
A take Yaya Abubakar yaji dadin zama da mijin Fattu wanda a kullun sukan hadu massalaci amma ba wani, alaka a tsakanin su,
Sai yau da dalili ya hada su har suka danfahinci junan su,
Har zuwa dare suna tare don a tare su ka tafi gida ranan,
Daga gurin da nake a kwance wayana ya fado min a rai sai na tunacewa Fattu ta bani, wayan da safe da ta zo,
Don haka sai na lalaba wayan na a karkashin filon da nake kwance ,
Wayan baida wani enough caji sosai, amma dai zan iya kira dashi hakanan,
Anty Amarya ce nakira ta dauki wayan tana magana acikin fada tana cewa ,
Meenatu wai yau ina kin ka shiga haka tun safe na ke kiran wayan ki amma bai zuwa,,?
Nace cikin murya irin ta yanayin mara lafiya,
Anty Walleh banda lafiya na yau,
Cikin nuna damuwa tace missamay ki halan ?
Sai da na dan cije bakina na dan hade wani abin bakin ciki na furta a hankali na ce, miscarriage na nassamu Anty,
What ?
Tafada cikin wani irin daga murya mai, kara tare da kara maimaita tambayan ta,
Sai kuma tashiga cewa Innalillahi ,waina alaihim raj,un,
Yan wagga bakar diya sai da tajawo muna wagga, irin hasara,
Walle sai ta gani ga rabon ta,
Sai kuma tace shin yanzu kina ina na ?
Nace a hankali walleh ina asibiti anty tun daren jiya,
Subbahanallahi takara fada sai kuma tace,
To su asibiti shi mi sunka ce ?
Saida na dan gyara kwanciya na sanan na ce ban san ko min sunka fada mai ba,
Sai naji tana nanata ,a,a a miscarriage shi wagga diya anyi mugguyan shegiya,
Dama du wadda ankayi tasan cewa kina da ciki kila shina tattaho maki da jidali don dai kuyi fada ta goga maki tsiya,
To in Allah yayi duniya don Annabi kan ya za ya karewa,
Don ke kin godema Allah ke gwada itako wassa sherin da taka kunsawa,
Sannu Anty Amarya takara yi min tare da jamin kunne in samu mu rabu lafiya da ita,
Nacewa Anty amarya to tace hutun mu ai ya kare in shirya in naji sauki indawo sokoto kawai abina nace mata insha Allahu danaji sauki zandawo sokoto da zamane,
Ina jin kafin in kashe waya anty amarya tana ta surfawa Salawatu zagi na fitan arziki,

****** ********** ******
Ba laifi don zuwa yanzu Alhamdullahi na ji karfin jikina sosai,
Don waye wangari sai na tashi jikin nawa Alhamdullahi,
Wanan dalilin yasa likita da yazo dubani yabani Sallama
Tare da yan magungunan da zan sha don su kara min karfin jiki na,
Malam Abdullahi ne suka zo da driver suka maidani gida don Yaya Abubakar yana da Meeting a ranan,
Nasamu Fattu a dakina ta gyara min shi fes sai kamshi ya keyi, tankar ina dakin a lokacin,
Sai da na dawo gida Anty Sadiya tashigo har dakina na ta gashe ni,
Abin bai wani bani mamaki ba don la,akari da irin yanayin, mutanen mu gurin kishi,
Na mayi arziki da har tazo ta gaida ni ina matsayin kishiyar ta nayi barin ciki tazo gaisheni,
Don inda agida mu ke bazan samu wanan daman ba,
Sallawatu wace ban ma sa rai cewa zata zo gaida ni din ba don haka rashin ganin ta bai damay ni ba,,
Itama dai din a daidai wanan lokacin suna ta kwasan rikicine da maigidan ,
Don yace sai tabar masa gidan shi don bazai iya zama da fitinanan mace ba shi,
Sallawatu kan ta shiga tashin hankali sosai, don gaba daya ta rasa yadda zata shawo kan al,amarin,
Duk yadda taso ya tsaya su fahinci junan su dashi yaya Abubakar yaki bat lokacin sa,
Ta buga waya yafi a kirga yaki koda kallon wayan nata balle ya daga,
Ta yi tunane barkatai ta yadda zata bullowa al,amarin amma ta rasa mafita akan zancen,
Ta rasa tsaye ta kasa zaune a gidan don bata san abin yi ba,
Gashi bata son fita ta koma gidan yan uwanta da take zaune,
Don ko gida Lubbuna bata kaunar ta tafi don hakam tonon asirine agare ta,
Sai faman sintiri kawai takeyi, don hankalin ta baya tare da ita,,
Can daga inda take a zaune gefen mirror ta, taji karan shigowan motar shi gidan,
Zubur ta mike, ta leka ta tagar dakinta, ta hangoshi yana kokarin zuwa parking space din gidan,
Sosai tayi kokarin gurin tataro hankalinta, don samu ta fuskance shi,
Daga labulen dakin ta take hango shi lokacin da ya shigo gidan dauke yar case din shi kamar kullun,
Direct part dina ya nufa daga shigowan shi gidan abinda yasa Salawatu sake dan guntun tsuki ke nan a lokacin,
A take numfashinta ya shiga kai da komo wani azabbaben kishi ya ziyarci zuciyar ta, sai ji take tankar numfashinta zai dauke,,
Sai kuma ta tuna cewa yanzu fq ba lokacin kishi bane tukun dole ta aje komai a gefen,
Ta fuskanci yadda zasu sasanta da maigidan nata wanda izuwa yanzu duk ya jagula mata lissafi,

****** ********** ******
Kwance nake cikin dakin nawa saman gado na sai kuma Maman Biu wace ke zaune daga kofa tana dan lazimi irin ta manya idan an fara girma,
Da sallama a bakin shi ya shigo dakin inda yake kokarin gaida Maman Biu tare da mata ya gajiya,
Ta ansa da fadin lafiya kalau ya kokari da aiki ?
Dan murmushi Yaya yai mata yana cewa Alhamdullah,
Ya maijikin ta ji sauki ko ?
Ta bashi amsa da cewa ai jiki yai kyau, don yau kan Alhamdullahi gaskiya don babu matsalar komai,
Kokarin tashi Maman Biu ke yi don ta fita, daga dakin, saboda ta bamu guri,
Daga gurin da na ke kwance nace wa Yaya sanni da dawowa ,
Ya dan ya mutsa fuska yana kara matsowa gurina yace ya jikin naki ne ?
Nai murmushi nace naji sauli sosai yaya, Alhamdullah, ban jin komai yanzu ai,
Ya dan ya mutsa fuskan shi yana cewa naso nazo nadauke ku da kaina amma sai kuma ga meeting yazo muna,
Nace yaya aiba komai tunda ga driver da malam Abdullahi sun zo ai,
Yaya ya saki murmushi, ya ce ok barin tafi indan watsa ruwa in fito,
Zandan fita in samo maki fruit don likita ya ce a dinga baki fruits da vegetables kina ci,,
Nace cikin dan murmusawa ai nasamu lafiya Yaya ba sai naci ba,
Har yakai kofa sai ya juyo ya kalleni tare da cewa hmmm kawai,
Yasa kai ya fita daga dakin yayin da na sauke yar ajiyan zuciya
Saboda nasan cewa yanzu yaya ya daina fushin da yakeyi dani,

Yana shiga daki kamar yadda yace din bathroom ya shiga ya watso ruwa ajikin shi don yaji dadin kara fita,.
Jin fitowan shi yasa Salkawatu da ke zaune tana jiran fitowar shi yin,
Firgigit ta mike tsaye daga zaunen da take tana nufar sa,
Duban ta yakeyi a cikin mamaki da ganin karfin halinta na zuwa dakin shi,
Duk da irin kashedin da yayi mata na cewa kada ta yarda ya dawo ya samay ta a gidan shi
Cikin daure fuska ya ke kokarin zuwa gurin wardrobe din shi don daukan kaya,
Kasa takai da gwiwowin ta har biyu tana ce masa don Allah yayi hakkuri ya yafe mata,
Haushi da takaicin ta ne suka rufe masa zuciyar shi,,
Tayaya take nufin zai iya manta wanan abinda Salawa tai mashi a ratuwan shi,
Takara cewa dullah dun Annabi Mohammed (S,A,W) kayi hakuri Oga sherin shedan ne
Ta hada hannayen ta biyu guri guda tana cewa iam so sorry Oga
Banyi haka da wani manufa wallahi just dai akasi aka samu kawai,
Ya girgiza kan shi lokacin da tace hakan tare da mata wani irin mugun kallo,
Yace look Salwa zan iya maki sauki saboda Allah da Annabi Mohammed,
Don haka sai kinbar gidan nan na two days I am telling you,,
Wani irin mugun shock taji don jin abind yace mata,na zancen barin gida,
Yace cikin bacin rai I don't know who you are before , ,
Wani irin kallon mamaki tai mashi don jin abinda yace mata, tasan cewa rayuwan shi ya kai karshe ga baci,
Ya ci gaba da cew kin bani mamaki Salwa do min banzaci haka ba daga gari don nazaci samun peace of mind daga gurin ki saboda you are mutual enough,
Kokarin riko mashi hannu tayi yai sauri ya ja baya daga gurin ta, ke yana mai ture ta,
Wasu irin hawayen takaici ne suka zubo mata alokacin don takaici,
A take ta soma rera masa kuka adakin cikin wani irin murya mai ban tausayi,
Yace ke ce kika boye min true colour dinki don ban san cewa haka kike ba,
Yarinya karama acikin ku ma tafiku kwantar min da hankali a gida idan anyi magana sai kuce wai nafi son ta ne
Abinda Meenat ke mun na kulawa duk cikin ku babu mai mun shi,
For god sake Salwa live me alone please ?
I want to be alone for now
Yama kasa karasa zancen shi ya yasa kai yana mai barin dakin har ya kai kofa ya juyo yana ce mata kada ki bari indawo in samay ki a nan,
Ganin zata nufo shi yai saurin fita yabar mata daki inda yabar gidan gaba daya,
Wani sabon kuka Salawatu tasa a gurin inda ta durkusa ita kadai tana ta rusa kuka har sai da tagaji ta sauko daga sama zuwa part din ta,

****** ********** ******
Ina daga kwance naji motsin mutum anshigo dakina,
A zato na ko Maman Biu ce tashigo batare da na juyo ba nake cewa Mama don Allah ki dan kashe min Ac din nan sayi nake ji,
Naji an kashe AC din amma ba,ai magana ba don haka na juyo don ganin kowaye,
Salawa ce tsaye da rinanun ifon ta da tasha kuka su kayi ja,
Ganane ya fadi lokacin da na gan ta amma sai Allah ya bani ikon fadar kalman nan da akace yana tarwatsa muguwar kishiya,
Watau La,illah,ha,illah Mohammed rasululah,,,
A hankali naga ta tako zuwa inda nake kwance ta zauna
Idon ta na mai zubar da hawayen nadama cikin wani irin ban tausayin yanayi,
Kaina nakawar gefe saboda nasan cewa bata kaunana har cikin ran ta kawai dai muna funci ne ya kawo ta,
Amma yadda naga babba da ita tana kuka agabana sai ta bani matukar tausayi,
Takira sunana cikin muryan kuka tace Meenat nazo ne in baki hakkuri bisa ga abinda ya faru,
Wallahi banayi shi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login