Showing 66001 words to 69000 words out of 388021 words

Chapter 23 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8209

ya fito dauke da ledan a hannun shi yasa yaya Abubakar da sauri yanufi gurin shi don ya karbi ledar,
A cikin ladabi yaduka yana gaida baban nashi kuma surukin shi,
Da mamaki Baba,Samaila ke kallon shi don baisan yazo gatin ba,
Sai yanzu idon shi yagano mai dirkekiyar Jeep din da ya ke parke a kofar gidan su,
Sannu da zuwa cikin yar rudani da jin kunya yake mashi,
Shima dai yau wani nauyin Baba, Samaila wanda yake abokin hiran da kuma shawaran shi,
Shine yau yake jin kunyar shi da nauyin shi wanda bai san dalili ba,
Ledar hannun Baba Samaila ya karba zuwa cikin gida,
Inda ya shiga sashen na su mama tana tsaye a tsakar gida tana kokkarin harhada kaya saboda dare yayi,
Idan dare yayi Mama Saratu bata barin komai a tsakar gidan ta waje,
Saboda koyi da barin kaya awaje manya sunce baida kyau ko kadan,
Don haka daga kayan aikin ta randan ruwan ta tarufe su da manyan bahohi,
Har murhun da Mama ke girki a kai, sai ta sa wani karfen kwano ta aza sama,
Takalmomin su a kwashe asa acikin wani katon kwali ko buhu,
Idan da dare ne ka shigo sashen nata sai kace ai ba mace acikkn gidan saboda gurin yadda yake komawa,
(Mata don girman Allah mukula dayin wanan halin yanzu duniya baci sosai, barin kaya awaje cikin dare shedanu suna samun damar cutar da mu)
Acikin mutuntawa kamar kullun yake cewa Mama Saratu mun samay ku lafiya, ?
Ya gida ya jama,a ?
Alhamdiulahi
"Ka dawo lafiya?
Cikin dan murmusawa ya lafiya kalau,
A hanyar shi ta zuwa gurin Malam tsoho ne ya samu Baba Samaila tare da mahaifinshi,,
Wanan abin bawai wani abin mamaki bane don ganin su a tare,
Saboda kowa yasan cewa sun fi kusa so,sai don shawaran gudan su bai wuce guda,
Baba Buhari ne yace ma Abubakar kai mai sunan malam ji mana,
A cikin ladabi ya nufi gurin da suke yana kokarin kai,wa kasa Baba Samaila ya ce, a,a haba tsaya mana kaji,
Don haka yadan tsaya daga gefen su a cikkin ladabi,
Baba Buhari ne yafara magana da cewa,nasan gurin malam , zaka nufa yanzu ,
To ka tsaya kaji may zan fada maka da kyau, kafin ka isa,
Kabi a hankali akan duk abinda malam din zai fada maka, idan kun zauna,
Muna fatan muga mun gama da mahaifin mu lafiya akan duk wani doka ko umurni da zai bamu a gidan nan,
Kai madin muna maka wanan fatan akan mu don ka gama da kowan mu lafiya,
Kai yadan kada alamar ya gamsu da zancen mahaifin shi,
Baba Samaila ya dora da cewa,ka sanyawa zuciyar ka hakkuri da dangana tankar kowani dan adam da kaddara ta haushi,
Allah yai maku albarka abaki dayan ku yaba ku, kuma diya masu albarka kamar ku ,
Daga haka suka umurce shi da ya karasa gurin mahaifin su din,
A zaune malam din yake yana wuridi kafin ya shiga gida,
Yau ma dai don yana son zantawa da jikan shi ne a asirce shi yasa bai shiga gida ba har zuwa war haka,
Dan kara gaisawa, su ka yi sama,sama inda Abubakar ke sauraron tsohon cikin ladabi,
Tau kamar dai yadda mukayi da kai a cikin waya tun kana can kasar waje,
Maganar ta na nan kamar yadda kaji din da farko,
Don haka yanzu ina son inji wani shawara ka yanke akan zancen, da mukayi da kai, awaya,
Wani irin gumi ne ya dan feso mai a saman goshin shi,,
Bakin shi nada maganganu fadi amma bazai iya fadin su kai tsaye a gaban malam din ba
Saboda gwarjin da tsohon yai mashi a yau, don fuskan sam yau babu zancen jika da kaka, uba ya koma masa yau sak,
Daurewa yayi cikin dakewar zicuya yace ban da abinda zance akan zancen don ni agareni wanan ya wuce, ko
In har akwai matsala akan zancen bai wuce tsakani na da mahaifiya ta ba,
Yanzu zancen dake a gabana shine, akan maganar wanan yariyar da na fara gabatar maka da zancen ta ne,
Don na riga nai alkawari da ita da yan uwanta cewa zan aure ta,,,
Shiru Malam tsoho yayi don bai san may zaicewa wana jikan nashi mara godiyan Allah ba,
Wanda aka aurawa mace kamar Aminatu shine kuma wai har yake hangen wata mace ,can daban,
Fuska malam tsoho ya canza mai daga yar fara,ar da ke a fuskan nashi, zuwa daurewa,
Su Baba malam yace a kira mashi don ya fada masu sabon zancen da Abubakar yazo mashi da shi, kuma,
Duk kan su shiru sukayi suna sauraren maganar da mahaifin su ke fadar masu,
Gaba dayan su suna daga zaune, duk sunyi shiru daga gurin da suke ,
Kowa da irin abinda yake sakawa, zuciyar shi wasu daga cikin su ,sunji dadin hakan don yanzu babu, wani jin dadi daga diyar dan uwan su wanda ke gani kamar su da yar su sun take ke nan ai,
Baba Buhari yafara dafa ta inda yake shiga ba nan yake fita ba,alokacin,
Yakare da cewa don haka kai maz ka janye wanan zancen don ba zaka maishe mu mutanen banza ba,,
Baba Samailane ya ce a,a haba yaya idan fa har zamuyi wa yaron ga adalci to mubar shi ya aure wace yake so,
Don dai kowan mu nan yasan da wanan zancen da yake, magana akai ,,
A cikin bacin rai malam ya kara tsura mashi ido yara sa may zai cewa jikan nashi kuma,
Wanan yaron naso ya jefar yar uwar haihuwar shi a matsalar rayuwa,
Shiko Abubakar ko a jikin shi don dai, yasan cewa bazai daina wanan abin da yake da niyar yi ba,
Saboda ai wancan kudirin sune suka ai,watar mai don haka shima yanzu ga nashi nan ya gabatar
Ganin yadda kowa a gurin yai shiru bawani wanda ke iya cewa komai a kai,
Baba Samaila, yadan yi dim don yasan abinda zai yi shi ka dai ne, zai iya yin hakan kai tsaye,
Numfasa kadan sai yace cikin gyaran murya, tunda wanan shine ra,ayin shi malam ina mai neman wa Abubakar alfarma, abarshi ya yi abinda zuciyar shi ke so,,,
Gaba dayan su suka dago kai suna ma dan uwar nasu kallon cikin mamaki,
Malam tsoho wanda bai ce komai ba a lokacin sai kokarin mikewa tsaye da ya keyi don shiga gida saboda lokacin shigan shi har ya wuce,
A,daidai zai mike tsaye na yake cewa na biya sadakin ka da jikata dubu, hamsin,
Idan kaga dama ka hada mata lefe, don naso hadawa na ce barin bari har kadawo sai ka hada mata da kan ka,
Daga haka ya shige abin shi batare da yakara cewa komai ba,
Shima dai Baba Buhari mikewa yayi yabi bayan mahaifin shi zuwa, cikin gida,
Ya rage yanzu daga shi sai Baba Samaila azaune can Baba Samailan ya ce ka bari mu bi malam a sannu har ya sauko,
Don komai da albarka acikin sa yafi dadi agani na
******* ******** *******
Labarin dawowan yaya Abubakar Nigeria yazo mu na harda zancen da yazo wa iyayyen mu da shi na kara aure, wata,
Sai,dai Anty Amarya wace ke fada min ta boye wanan labarin, don ita kanta hankalin ta a,tashe yake,
Gabana ne ya fadi don sai a lokacin ne tunanen wai ni a yanzu matar aure ce ya fado min a rai,
Ido ?nty Amarya takafe ni da shi don ganin canzawar da ya,nayi na yayi a lokaci guda,
Tunanen may kike yi Meenat ki saki ranki ban son ki sawa zuciyar ki takura, akan wanan zancen,
Dawowar shi kasar ba yana nufi za,a kaiki gidan shi bane direct ko yau ko gobe ,a,a sai lokacin da da duk malam tsoho ya bukaci tafiyan ki can din
Don haka karki fara kisawa zuviyar ki damuwa ko kadan,
A hankali nace to Anty nagode na mike a hankali har don in koma dakin mu,
Am, Meenatu ki shirya zuwa gobe ina son muje gurin hajiyar mu da karfe goma na safe,
To kawai na iya cewa don har zuwa lokacin ban san may ke damuna ba,
A daki zaine nake a bakin gado babu abindanake iya tuna wa sai irin yadda yayan namu fuskan shi ko da yaushe take a murtuke,
Don bai dariyar a gida sai in ya,na tare da malam tsoho kawai zaka iya ganin hakoran shi,
Matar shi Sadiya ban san yaya zan fasalta nata zancen ba ,
Mutum wanda zaka zauna da shi bai umm, bai ummh,umm,umm da kowa sai can kaji maganar ta
Shigowan yaran Anty da suka dawo daga islamiya suka dan sani warwarewa,
Har nadan manta da zancen da mukayi da Anty Amaryan
Washe gari muna agidan mahaifan Anty dakin muke zaune tare da mahaifiyar nasu,
Aminatu naji duk irin abinda ya faru akanki irin yadda aka nuna maki ke da iyayyen ki fin karfi,
To amma idan kin kwantar da hankalinki hakan nada kyau sosai don gaba zaku ji dadin shi insha Allah,
Yanzu na fadawa uwar dakin ki cewa tafara shirya ki kamar yadda ko wace uwake shirya yar ta,
Idan zata tafi gidan mijin ta, Alhamdullah ga irin yadda tai min bayani da cewa duk wani tarbiyan da ya dace taba a yanzu tabaki shi ko,
Don haka ki daure ki nuna masu cewa ke din "yar albarka ce
Amma fa hakan bazai yi ba sai kin hada da hakkuri acikin al,amarin naki, kin ji Amina,
A hankali ta daga kai alansawa ansawa dattijuwan taci gaba da cewa,
Na fadawa Sumayya cewa daga yau ta fara shayar da ke gumba, masu kyau da asali,
Sam ban fahinci may take nufi ba illa gyada kai da nayi alamar, toh,
Jin haka sai naji anty Amarya ta ce ba matsala mama zan kokarta muyi duk yadda kikace,
Amina Allah yai maki albarka kinji Allah yasa muce gumma da akayi,,
Wanan karon ban ansa mata a fili ba saidai acikin zuciya,
Ido na ne naji ya ciko da hawaye masu zafi, duk yadda naso in controlling din kar su zuba hakan bai yi ba don sai da suka zubo daga ido na,
A hankali na sa gefen hijab dina ina dan goge idon ,
Sosai Anty amarya take ta kokarin gyara ni wani abin ma idan tai min sai inga kamar bata so na,
Don in ta kawo min abu komai bauri ko zaki saina shanye san,nan inbata cup,
Ni,kaina nasan cewa na canza fiye da duk yadda zan baku labari,

Mun gama aikin da duk za mu kasan cewar yau ba ke da girki ba don haka hirane da kallo kawai zamu a daki, yayin da yaran ke kokarin yin home work din su a,gefe guda
Uncle ne ya shigo dakin namu yana saye cikin wani kaya kamar na yan kwallo, wando da riga saidai wandon iya gwaiwa kawai yake mashi,
Da sauri na mike ina cewa Uncle ina wuni Meena yaki ya karatu, ?
Na ansa mai cikin murmushi da cewa Alhamdullah,
Kokarin fita nake yi daga dakin don komawa dakin mu,
Amma sai naji muryan uncle yana cewa zoki zauna Meena maganar ai taki ce,
Daga ni har Anty Amarya sai da gaban mu ya fadi don ba musan ko da may yazo ba,
Guri ya sa mu agefen gadon da Anty take kwance tana kallon TV,
Juyawa ya inda take suna fuskantar junar su, yin da nasamu guri na dan tsugun na maimakon in zauna saboda girmamawa,
Yau ina office munyi waya da malam tsoho dam, dam ga???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ba yabada a lokacin,
Ya bugo waya yana tambayana yaushe zaki samu hutu ?
Nadai fada mai cewa nan da karshen wani sati insha Allah,
Da sauri na dago kai na dube gurin da kawun nawa yake zaune,
Inda yaci gaba da cewa sai yake ce min don Allah yana son in turo ki kafin lokacin koda da ba zaki samu kwana ba,
Shiru duk su kayi don jin may yake fadi akan sakon malam tsoho da da ban da kamar shi a rayuwa na,
Amma yanzu da an ambaci sunan shi sai inji wani bacin rai,
Uncle yaci gaba da cewa, don haka ke Sumayya sai ki shirya ku tafi tare zuwa gobe ko jibi,,
Kokarin mikewa take zaune don tasan may zata ce alokacin
Saida takai zaune take cewa, amma dai bawai suna nufi da munje zasu rike ta ba,
Uncle wanda ke kokarin mikewa tsaye yace haba ai kinji may, nace maki sun ce ko ?
Bamu samu tafiba washe gari saida gari ya kara wayewa mu ka kama hanyar birnin kebbi
Alokacin saye nake cikin zani da riga na atamfa, dinkin rigar yar karama ce,
Ban yi amfani da gyale ba hijab nasa tare da sa takalma mai dan tudu,
Motar Uncle ce aka kai mu dashi a lokacin mun samu mutane sun dan watse sun tafi harkokin su na neman kudi, daga ciki har da mahaifina wanda ke sakkon barin gida tunda safe yake fita,
Malam ne tare da yan dattijan kon ince tsofi yan uwan shi awajen,
Yana ganin mu yaji dadi sosai har cikin ran shi inda ya kara yaba da hali irin na Uncle din mu,
Daga ni har Anty muka nufi gurin shi don mu gaisa dashi,
Kokarin yi min wasa yakeyi amma sai yau naji sam bazan iya ansa mashi ba kamar yadda muka saba, ba,
Acikin gida ma sai nake ji kamar ba gidan muba yau don sam ban iya shiga ciki yadda na saba zuwa gaida mutane,
Sai dai masu son yin gulma ne ke dan lekowa suna cewa ance Meenatu tazo,
Inda sun koma gefe sai asa gulman cewa nacanza a lokaci guda na zama wata yar boko,
Mama sai godiya take zabgawa Anty Amarya irin yadda ta taimakawa yar ta,
Cewa Anty tayi ai wanan kan ta taiwa tace yaya Meenatu halin ta ke sa ai mata komai,
Don yarinya ce wace tasan ya kamata, sosai don ta iya zama da mutane,
Murmushin jin dadi mama Saratu tayi don jin dadin an yabi diyar ta,
Sai cewa tayi, ai kin san cewa a babban gida ta tashi dole ta san yadda ake zama da mutane,
Duk da baba bai gari amma mama tayi kokarin wurin taron bakin su,
Don lafiyayyen girki ta hada masu tare da abin sha na gargajiya dana kwalba,
Malam ne ya aiko da cewa su samay shi a can gurin da yake zama waje,
Zaune suke ita da anty din suna sauraren shi cikin natsuwa,
Kudi ne ya zaro daga cikkn jikin shi suna dunkule acikin wata bakar leda da yake kokarin wawarewa ahankali, yana kuma kallon ledar,
Kudin da ke cikin ledan yake kokarin mikawa Meenat din yana cewa karbi nan Aminatu,
Hannu na dago a hankali na karbi kudin daga hannun kakan nawa,
Ya ce madallah,
Wana kudin da kika gani Sadakin ki ne,
A take na ji wani iri nauyi da kunya duk sun rufe ni a lokaci guda,
Inda Anty Amarya take zauna na kalla ina mai mika mata kudin da aka kira da,sunan wai sadaki na,
Tace min a hankali barshi kawai meena har muji ya ake cikki,
Malam yaci gaba da cewa,
Na,baki su ne a hannun ki kamar yadda shari,a ya tana da,
Wasu kudin ne masu yawa yakara daukowa daga jikin shi
Amma wanan karon Anty amarya ce yake kokarin mikamawa yana cewa,
Wanan kuma Hajiya don Allah idan kun koma can sokoto ina son ki saya mata abinda yadace wanda zata tafi dashi can garin da Abubakar din maigidan ta yake,
Don ku naga kunfi mu sani abinda duniya ke aciki yanzu,,
Anty takarbi kudin tana cewa malam din an gode a lokacin yana kokarin neman wani abu acikin leda daga cikkn tarin kayan shi dake gurin,
Karbi nan yace min yayin da yake miko min wani abu daga cikin leda abin baki tankar bakin tukunya,
Lashe shi yanzun nan duka,
A yadda na ga abin baki sai nake zaton dole yai daci gashi ban son abu mai daci sam,
Hakana fara lasan abin sabanin yadda nazata naji don baida wani dandano sam, tankar gawayi nake lasa,
Bayan na lashe yake cewa da kyau Meenatu, kusan sai dayaban abu sun kai kala uku a take gurin da yake,
Inda yake cewa Allah yai maki albarka Aminatu ke daice duk fadin gidan nan nasan cewa zan ma haka batare da na yi dana sani ba,
Kuma gashi kin gwada min cewa ke din diya ce don haka Allah yai maki Albarka acikon duk al,amuranki,
Allah yabaku zuria masu albarka, babu abinda zai samay ki insha Allah
Kedai ki zauna dakowa da zuciya daya kamar yadda kika saba,
Allah ya sa mu dace
Wani irin hawaye ne daban san lokacin da suka zoba ai atake nasa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login