Showing 156001 words to 159000 words out of 388021 words

Chapter 53 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8300

na farin cikin rayuwa da tarihi irin wanda mutum bazai taba mantawa ba,
Cikin dan hasala yace Meenat may kike son in mashi, ?
Kaina na dukar kasa bance komai ba sai dai na hade fuskana abinda ban taba mashi ba,
Sai ka dawo na fadi a hankali tare da kokarin juyawa ina lalaban filo na, da niyar kara kwantawa,,,
Bai juyo ba yasa kai yafita abinshi
Sam ban ji dadi yadda Yaya ya yi ba akan zancen haihuwan matar dan uwan mu,
Yin ranan a haka nayi a cikin bacin rai don gaskiya idan Yaya Abubakar zaici gaba da yi wa yan uwan mu irin wanan halin gaskiya ba,za,a samu cigaba da zumunci maidaurewa ba,
Don dai Babba shike hasa kan gida sanan na baya suji dadin biyo shi,

Kamar yadda na saba taya Anty Sadiya aiki yau ma banki yi ba don a tare mukayi abinda duk ya dace, sai dai jikina ba walwala a,tare dani,
Muna gama duk wanin abinda zamuyi sai da na tabbatar da cewa nayi,
Don haka na,shige daki abina na dan yi abubuwan da ya dace in yi,
Fattu na kira, muka gaisai mu kayi yaya kwana biyu, ?
Mun kai wani lokaci muna dan tataunawa akan zance Humaira,
Bayan kashe waya, ne ban kai ga ajewa ba sai na tuna cewa nace zan kira Yaya Awalu yau din,
Kira daya nabiyu na uku yadauka ya na cewa Meenatu yaya kuke ya Abuja,,
Nai dan murmushi na ce Yaya Awalu ya ruwan zafi ?
Kai haba Meenatu masu ruwan zafi suna gidan su inda suke,
Na ce a cikin mamaki, yaya gida ta haihune yace ,
Wallahi Meenatu daga asibiti suka wuce, da ita gidan su kinga yaya za,a yi, ba dole mu bar su ba,
Nace to Allah shi kyauta ya ce Ameen yanzu kinga ga suna sai kara matsuwa yake yi,
Gashi gwaunati batai albashi ba don banzaci haihuwan a yanzu ba,
Sai kawai kwatsan gashi yazo muna a bazata,
Nace akwai Allah yaya Allah zai rufa asiri insha Allah,,
Ya Awal ya amsa da cewa ameen Meenatu nace zakaji mu insha Allah kafin sunan yaya abin ne bai yi ready ba,
Mukayi sallama da Yayan nawa na kashe waya zancen shi suna damuna a rai na,
Daga daki ina jin karan TV da alaman yaya na kallon network News,,
Ban fita ba don tun gama girki mu naci shi a kitchen tsaye,
Duk zaman falon sai yaji ya ishe shi don rashin ganin na fito waje,
Sai dai yai kokarin danne damuwar tashi don gudun zargi daga sauran matan shi,
Sai dai bai san cewa Sallawatu duk ta fahinci halin da yake ciki ba,
Cikin dakewa yake cewa Sadiya Meenatu lafiya take bata fito ba,
Ina ga gajiyane kawai don tun da muka gama girki,tashige bata kara fitowa ba,
Ok kawai yace tare da ci gaba da abinda yakeyi a system din,
Barci, ne ya dauke ni sosai, don daga kallon sunna tv barci ya daukeni ban sani ba,
Kamar a mafarki naji maganan shi yana cewa barci baki kashe electronic, ba?
Nadan mike firgigit nace cikin idon barci zan kashe yanzu ai,
Tashi ki kashe ki rufe kofa, kafin barcin ya dauke ki,
Ban kara furta komai ba sai sai dan tashin da nayi don inyi abinda ya umurce ni dayi,
Maya hanaki fitowa falo yau,?
Dan marairai cewa nayi nace kawai dai banjin dadi ne sai na dan kwanta,
Batare da ya waiwayeni ba yace zancen Awalu kikewa fushi ko ?
Cikin wata irin murya kasa kasa nace ni ba fushi nakeyi ba ,
Akan may zanyi fushi tunda kaima ai dan uwanka ne,
Aini zan tura masu da abindake gate ni gobe insha Allah,
Kallon mamaki yai min yace ashe kudi gare ki haka?
Nace a,a kudin da kaba ni, in tafi,sallon ne mai sallon din ta raga nna ne zan hada da wanda ke gurina in aika mashi,
Hmm kawai ya iya ce min daga haka ya juya fita yana ce min sai da safe,
Yau ma kamar jiya na tashi fuskana a daure nafito daga wanka ina shafa mai ya shigo dakin cikin shirin tafiya office yau ya kasance juma,at,
Don hakani shaddane mai kalan milki sai shining yakeyi, da kyalli,
Ina kwana na,ce fuska ba yabo ba fallasa a cikin sa,
Ina kwana nai masa adan sake batare da na kalle shi ba ina shafa mai a cinyoyi na,
Ya saki ajiyan zuciya yana dubana cikin wani irin yanayi maradadi,
Yace ni zan fita babane za,a ba kudin ko Awalun ?
Nace cikin da murya karami da cewa karaba masu dai Yaya tunda kowa nada abin dai yi daga cikin su,
Ok zan turo maki Hamza ko Abdullahi sai ki mashi bayani yaje ya tura masu,
Ya dan duba agogon hannun sa yace ina ga bari a turawa shi Awalu da hamsin shi kuma baba talatin ko?
Nadan juyo ina duban shi nace dadai kabasu kowa hamsim din don lalura da yawa,
Ya amsa da cewa to shike nan zan ba shi ya tura masu sai kicewa Awalu ya turo da account
Nace cikin nuna farin ciki da Allah ya saka da alheri angode,
Yajuya yayin da nace Allah ya tsare cikin sakin fuska,



ZEEE MAKAWA YELWA
[8/18, 8:39 AM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
5? 7?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH- AL- WASIYU,,,,


Fatan Alheri gare ka da Zurian ka, Fatan gamawa da duniya Lafiya, Baba Alhaji Aliyu Harizami, Dan Amar Kano,,,, Gaba dai Gaba dai Baba Aliyu Dan Amar Kano,,,,,,,,


Zaune, Baba Musa yake Yaya Awal ya shigo gidan cikin farin ciki da jin dadi yana cewa,
Baba kaga ikon Allah ko ?
Wallahi, Mai sunan malam na ya aiko muna da alheri,
Masha Allahu, kai madallah aiko mun godema Allah,
Allah abin godiya inji mama matar Baba Musa mahaifiyar su yaya Awal,
Allahu Akbar inji Baba Musa lokacin da ya gama kidaya, kudin
Ya ce ance gari da yawa maye baicin kan shi, Allah ya rufa,muna,wagga asiri,
Wasu kudin yaya, Awal ya mikowa Baba yana cewa ga wanga,
Baba ya ce kuma ? Wai an mari kumama,
Yace Meenatu ta ce asai ma mai jego turmin zani wanga kuma naka na Baba,,,
Masha Allah inji baba ya karbi kudin ya nata sa muna albarka dubu goma ya ce cif,,
Allah kai ma wa yan ga diya albarka, Allah ka azurta, su zuri,a masu albarka,
Yaya Awal da Mama su ka karba da fadin Ameen ya Allah,
Kudin Baba Musa ya kaiwa malam tsoho ya nuna mashi tare da yi mashi bayanin komai,
Murmushi malam tsoho yayi tare da dan kad kanshi yana mai lumshe ido ya ce
Madallah madallah Allah mun gode maka da ka ba mu wannan yaro mai albarka acikin zuri,an mu,
Allah nagode ma da ka bu ikon hada auren wanan yaron da wanan yarinyar, mai albarka da sanin ya kamata,
Wana addu,an na karshe shi yasa Baba Musa saurin dago kai ya dubi malam,
Malam tsoho ya gane nufin shi, don haka ya dagawa Baba Musa kai tare da,sauran iyayyen mu da ke gurin,
Ya ce zaman Meenatu tare da mai suna,na wani babban TARKO ne na haka muna wanda gaba dayan ku baza ku gane hakan ba yanzu,,
Gaskiyane inji Baba Buhari wanda ke sauraren zancen su,
Yadan murmusa tare da fuskantar mahaifin su ya ce,
Ai malam iyanzu na fara fahintar, gaskiyan zancen ka sosai,
Don sanin halin yaran nan da,nayi gaba dayan su
Don ka ga shi mai sunan malam zuciya da saurin fushi,
Ita ko Meenatu uwayen hakkuri da sanin ya kamata,
Malam yace to kun ji dalilin hada tarko nan da nayi ke nan badon komai sai hankalin wanan yaron ya dawo gida gare mu,
Wanda idan kun kula ku kan ku za kusan cewa da, da, da yanzu nan ban daya ba ne,,
Don da farko sam maisuna badamu da damuwar mu ba ko kadan,
Yanzu kuma idan har kunyi la,akari sai kuga cewa, ai ba, duk wani harka yana dubuwa,
Gaba dayan su sukace haka ne malam maganan ka gaskiya ne ,
Baba musa ya ce, ai watau, malam wanan mahaukaciyar uwar tashi ita ce duk ta kawo wanan matsalan wallahi,,
Malam ya ce kusa ido kuyi kallo in akwai rayuwa ko bani da rai zaku ce na fada maku,
Don Ladi na kallon bai boyewa zai dinga yiwa yan uwa da abokan arziki alheri babu yadda zata yi,
Kuma shi kan shi duk wanan miskilancin nasa zai daina ya rabu da su a hankali, kudai sa ido a hankali zaku gane amfanin wanan hadin nawa,
Malam Bashir makwabcin mu yace lalai malam kayi babban hikima guri wanan hadin ba karamin TARKO ka haka ba,
Malam tsoho yace ai duk zage zagen da ake yi lokacin da nai wanan hadin auren ina ji ba wai ban ji bane,
Su wa yan nan yaran da kuke ganin cewa ai sun girmi ita Aminatu,
Su ya kama ta a hada da mai sunana, na ba gaskiya bane,
Don da sune aka hada dashi da zuwa yanzu anfara kai ruwa rana ko
Saboda ba zasu iya ratuwan mai sunana ba san nan ita Ladi irin wanan mugun fitinan da take yiwa Saratu da,shi kan shi samaila yana iya kawo karewan auren,
Gaba daya sukace wanan gaskiya ne malam don dai duk matan mu in ba Saratu ba babu mai iya hade fitinar Ladi,
Don,ko shi Samaila idan ya yunkura nasan cewa matar sa ke taushe shi yayi hakkuri,
Kowa yace gaskiyane malam gaskiya abin yayi kyau sosai,
Yace kun ga yanzu muna sani halinda suke ciki kamar yadda su ma suke sanin labarin gida a kai akai har yake taimaka mu na irin hakan,
Ko wa ya karba da cewa, gaskiyane malam abin yayi kyau kwarai da gaske,
Malam ya kare da cewa Allah ya kyauta Allah kuma ya raya muna su yasa albarka

Daga, haka a ka fara zancen abinda ya kamata su yi tunda kudi sun samu yanzu,
Baba Musa bai boye ba ya dinga fadin alherin da, Yaya Abubakar da Meenatu, suka turo masu,
Mutane sai albarka akesawa yaya Abubakar din tare da fatan alheri ga rayuwa,
Zance na yawo ya kewayawa har caraf a kunen Mama Ladi,
Mariya ce ta jiyo zancen ta zo tana shedawa mama cewa ashe , Abubakar ya aiko masu da kudin hidima,?
Mama Ladi tace bari zancen nan Mariya, akwaodai inda suka ranto (aro su) su ,
Walleh Mama shina ya aiko ma su da shiya kuma ance kudi na masu yawa ya aiko masu ,
Wai harda Meenatu sai da taturo da nata taimakon ita ma,
A take rayuwan Mama Ladi ya baci may mutanen gidan nan ke nufi da har zasu rufe min alherin da dan cikina ya aiko da shiya,
Mikewa tayi Anty Mariya tana dakar da ita amma ina wucewa tayi zuwa cikin gida,
Bata tsaya ba sai, sashen Baba Musa tashiga surfa jidalin cewa an maishe ta batasan komai ba kenan
Baba musa na jin ta yai wuf ya fito daga dakin shi, shi ya na cewa ke Ladi walle in kina cin kasa ki kiyayi na shurem,,,
Don tafi karfin taunar ki saboda dankon ta, kedai san ni bani dauka shedanar ki,
Don haka duk abinda kin ka jiya ba karyana ba gaskiya ta,
Sai ki tai ki hana gobe shi basuwa, ki gani inzai hannu maki,,,

****** ********** ******
Tsafi gaskiyan mai shi don Hajja tun daga Birni Kebbi ta tashi har bargu tai tafitan yini don kwana bai yi gare ta,
Ta samu bokan ta tai mashi bayanin irin rayuwan da take ciki yanzu inda take she da mashi duk irin abinda yanzu dodo ke ciki,
Shiru boka yayi kamar mai nazari can ya nisa yace ,
Abinda kike mashi da farko shine, yanzi baya samu daga gare ki,
Anyi alkawari dake kin amince yanzu kuma sai baya samun hakan,
Tace to amma ai naga dai ta nawa bangaren babu matsala,,
Don duk abinda, ya ke bukata na tsare mashi ina kokarin yi,
Boka yace dole a kwai matsala, don haka kawai ba zai daina abinda yai ke yi ba,
Muddin yana,samun biyan bukatun shi to shi kuma ba fashi ga abinda zai gudanar gare ki,,
Hajja cikin magiya take cewa bokan ta don Allah dai ya taimaka mata akan dodo ya dawo kamar farko,
Yan abubuwan surkulle boka, yai ma Hajja tare da mata albashir din komai zai dawo, daidai,
Ta bashi abinda ya kamata,ta bashi tare da mashi godiya sosai,
Ranan ta, juyo, daga can ta biyo ta garin illo don yafi mata saukin tafiya,
Sai zuwa yamma sosai ta iso gida da kunshin abubuwan da bokan ta ya ba ta tayi,,

Bata tsaya wani hutawa ba ta shiga aiwatar da abinda, boka ya bata tayin,
Wani hayaki da ta turara har makwabta sai da suka shiga damuwa saboda mugun karfin shi,
Amma sanin halin Hajja yasa kowa ya kama bakin shi da ita, don ba zasu iya jidali ba,
Sai da ta tabbatar da cewa ta gama hada komai san nan hankalin ta ya kwanta,
Ta ne mi abincin da zataci ta dan samu guri ta kwanta jiran tsan,mani,,,,

****** ********** ******
Kitchen na ke ina,aiki yau ni ce, ke da girki sai dai Anty Sadiya tace min bata jin dadin jikin ta, a yadda take fada min wai jikin tane ya mutu mata kai yai mata sanyi,
Bayan na idar da sallah la,asar, na fito falo ina kara gyara yan wguraren da ya dace in kara gyarawa,
Karan tafiyan takalmin naji shigowa gidan har mai shi ya kawo tsakiyan falo babu sallama,
Sau guda na daga kaina na dan kalli, gurin da naji motsin mutun shigowa,
Sallawatu ce wace tun safe tafita gidan sai yanzu tashigo,
Ko da zata fita ma batai muna magana zata fita ba don haka ni ma, na maida kai na ga abinda na keyi, batare da nai mata magana ba,
Don banga dalilin da zan mata sannu da zuwa ba bayan ba tai min sallama ba, da zata fita,
Daga gurin da take tsaye ta ke cewa abincin rana fa Meena,
Aikina naci gaba dayi batare da na nuna mata cewa najita ba,
Sai ji nayi tace, ke Meenat dake fa nake magana, zaki wani share ni,
Batare da na juya inda take tsaye da tana jiran abinci bayan yunwan da ta kwaso daga gurin gantalin ta,
Ji min rainin hankali ga wanan yarinyar abincin ma kuma shi bakin cikin bani kikeyi,
Nace sai kin dawo gurin koyon Sallama zan baki ansa ai,
Wani irin takaici da mamaki ne suka rufe ta a lokaci guda,
Karamar yarinya kamar Meenat, in badon rayuwan aure ba ina ita, ina yarinya kamar meenat,
A fusace Salawatu ta juya zuwa, part din ta tana kokarin aje kayan da ke a hannun ta,
Ta dan jima don lokacin har na karasa abinda na keyi ina kokarin shigewa,
Ta dawo cikin wani irin yanayi wanan karon fuskan ta babu dafin kallo,
Tace sai naga raini ya shiga tsakani na dake sosai don kina ganin cewa wai abu gudane ya aje mu agidan dake,
Nadago fuska na nace au da make baki sani bane sai yan zun nan,?
Cikin wani irin mamaki take kallon ta ce laila ma yarinyar na kin samu guri wallahi,
To bari kiji yau babu kowa a gidan nan idan ki kai min tsiya wallahi kafin wani ya shigo sai na nada maki dukan tsiya tukun,
Cikin wani irin rashin tsoro da karfin zuciya na ce Bissimillah uwata ,,,
Aiko ban yi aune ba naji tayo kaina gadan gadan, da nufin duka,
Ai take na Fulani ya ziyarce ni wani irin zuciya ya rufe min ido a lokaci guda,
Wani irin zazzafan mari takawo min na kauce nikuma Allah yaban sa,an ta nadago ta tun daga kasa na makata a tsakiyan falo,,
Zan kara yowa kanta naji an rike ni ta baya ban tasya ba nai cikin su ita da wanda ya rike ni ta baya,
Gam naji an kara rikeni sai wani irin tsimi jikina keyi a lokaci guda ,
Najuyo cikin masifa sai naga Yaya Abubakar ne a tsaye bayana rike dani sai kuma Anty, Sadiya, wace ke daga gefe acikin tashin hankali, ita ma,
A zuciye nake cewa a sakeni, dan Allah kafin wanan, mara mutuncin ta taso,
Cikin wani irin tsawa yaya Abubakar ya ke ce,wa, Meenatu kina da hankali kuwa,
Haushine da kishi ya kama Salawatu, dake kokarin mikewa ga kasan da nakai ta,
Ita a ganin ta irin yadda yaya Abubakar yayi yana magana kamar bai son yi yaudarane yana son ya goyi bayana ne,
Don haka take cewa Meenatu nice ki,kaiwa wanan abin haka?
Abubakar kana ganin yadda tai min ko


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login