Showing 360001 words to 363000 words out of 388021 words

Chapter 121 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8218

yaya Abubakar bada daewa ba itama take cewa zata tafi nai mata godiya ta tafi,
Suna fita na mika yarinyar gurin gwagona, na dan mike tsaye a hankali, na koma saman gado na kwanta,,
A hankali na lumshe idanuwa na inda abubuwa da dama suke min yawo a cikin raina,
A hankali na nisa ina cewa, Gwago zaman asibitin nan ya isheni wallahi, ace mutum baida ikon yadan motsa ko kadan sai bisa dokan likita,
Ni da an sallamay ni gida nake son zuwa can gurin yan uwana wallahi,
Muryan gwagona naji tana ceqa kada kifara shi don kn san yanzu idan kince gida zaki tafi hankalin mijin ki, zai kasu kashi uku ke nan bai can kasan , IBO bai nan guri iyali ga kuma ke kin koma gida,
Kafin nabada amsa Anty Amaryace ta shigo daki Sallama dauke abakin ta,
Dadi da murnane suka rufe ni wanda ban san lokacin da na fara kukaba,
Mahaifiya tace da sisters dina su biyu sai mummy kishiyar Anty.
Kuka kawai na saka masu don sai na rasa may zanyi a lokacin,,
Su ma din kukan sukeyi acikin tausaya mani irin yadda sukaga na ramay na kode na zama wata yar feyau dani,
Yaran suke bi da kallon mamaki suna daukan su a cikin sha,awa,
Anty Amarya wace itama ma ciki ne da ita mai alolayi shine ma ya hanasu zuwa da wuri don an mata karin ruwa a lokacin dana haihu,
Uncle dina sai addua yake min tare da kara kwantar min da hankali, na yana cewa Meenat kiyi kokari wallahi irin yadda muke ta samun labarin jikin na ki ba dadi wallahi,
Gashi ita kuma wanan bata da lafiya takuma ce wai sai ta zo,
Daga gurin da mummy take zaune tadan watsa wa uncle harara wai don may zai yi maganan Anty,
Tankar bai ganta ba yaci gaba da zancen shi daya keyi yana kara kwantar min da hankali,.
Duk zancen da ake tayi adakin ana maida bayanin irin abubuwan da suka faru abaya,
Mahaifiyata da yan uwa na sun kura min ido duk tausayina ya kama su,
Ba ai wani dadewa ba Yaya Abubakar ya iso yanacewa acikin muryan nan nashi ,
Kuna tafe shine baku fada muna ba musan da zuwan ku, Uncle yace haba wanda basu da kwanciyan hankali
Ankai wani lokaci muna tare dasu a asibiti inda mamana taba Baba na a waya muka gaisa dashi yana ta saka min albarka,
Zuwa wani lokaci akai masu jagora zuwa gida, wanan ne karo na farko, da yan uwana har da mahaifiyana su kazo inda nake aure,,
Sam basu so su tafi ba anan suka so su kwana dani amma sai ake fada masu cewa ai ba,a barin mutane da yawa asibitin ko su Gwago don likitan yana abokin Yaya ne aka bar su har su biyu,

****** ********** ******
Suna a part dina batare da damuwa da rashin zuwa taron su da mutanen gidan basuyi ba,
Alhamdullahi don Baba Ramatu mace ce mai mutunci ga kuma Fattu wace kusan tana gidan suna ta fama da dawainiyar bakin da suka shigo,
Tun bayan dawowan shi gidan yake hango wani gani, gani da suke mai a gidan amma sai ya kau da kai don akwai baki a gidan lokacin,
Kwanan su Mama Biyu suka juya suka koma gida saidai anbar min sisters dina anan zasu dan kwana biyu damu,
Don su taimaka min da abubuwa, saboda ita Hawwa tagama secondary ita, kuma Rabi,at suna hutu ne tukum
Kamar matan Yaya Abubakar suna jiran bakin mu su tafine aiko sai suka saka fitina,
Yana falo da daren ranan yana kallon news a tashan NTN
Sadiya tazo ta samay shi tana cewa dama muna son magana dakaine
Da farko ban so na saka baki na ba amma yanzu na,gane cewa abun yayi yawa wallahi
Kirikiri baka iya boye komai da ya shafi Meenatu a gidan nan sam na kasa fahintar may kake nufi da hakan,
Yanzu har Meenatu ce zata kafa maka dokan cewa wai ka koma gurin aikin ka ka bar mu
Takaici da haushin zancen tane ya rufe shi lokaci guda,
Sai ma ya rasa may zaice, cike da kulewa ya dago fuskan shi daurare yace mata wai Sadiya kina da hankali,
Yace da girman ki da shekarun ki har kike wanan zancen haka, kamar wata mara wayo,
Nine mace har zata bani doka ko oda akan abinda zanyi wa rayuwana,
Wani dogon tsuki ya kara ja tare da mayar da kan shi a TV falon yana mai dan kada kafan shi a hankali saman table din dake gaban shi,
A take cikin nazarin ta sai taga bataiwa kanta dashima maigidan ba adalci,
A tsawon dan zaman da sukayi dashi, yakamata tasan abinda zai iya dakuma wanda bazai iya yi ba,
Don shi mutum ne wanda wanda bai daukan raini ga mace ko kadan sanan kuma irin mazan da koda an masu asiri baya kama su,,
A take jikin ta yai sa???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?nyi don batai mashi adalci ba ko kadan,
Kamata yayi da aka fada mata abinda Meenatace wai ya wuce yabarsu don ba,a gida take ba tana asibiti ita ahine take masu bakin ciki su dake tare dashi suna ta cacaka,
Don itama Salawatu ce ta samay ta dazance inda ta juya maganan kan karya da gaskiya,
Ita kuma bata tsaya nazari ko bincke ba kishi ya rufe ta ya turnuke ta kawai ta samay shi da zancen,
A take nadama ya kamata tadan dago kai tana cewa, don Allah kayi hakkuri wallahi rainane ya baci ban tsaya na bincika ba,
Sai kuma tayi shiru batare da ta iya kara furta komai ba,
Shiru sukayi sai zuwa can taji muryan shi yana cewa bari ki ji inda aka kara wanan irin gulmace gulmacen bazan kyale kuba gaba dayan ku sai ranku ya baci,
Shiru tayi tana sauraren shi duk hankalin ta a tashe don ya dade, rabon da taga bacin ranshi akanta irin haka,
Jikin ta a sanyaye tamike tabar falon zuwa ciki fuuu, inda ya rakata da hararan takaici,

Washegari yazo da safe don dubamu a ranan ya samu Amira tana kuka saboda mura ya kamata sosai,
Ganin itace ke kuka yake cewa yau may ya samu mama ta tun a kofa nake jin kukan ta,
Gwago,ce ta bashi amsa da cewa, yau mura ke damun ta shine take kuka,
Yakarbeta yana dan mata wasa acikin ikon Allah sai yarinyar tai shiru har da dan barcin ta a hannun shi,
Kamar tasancewa shine mahaifin ta anan su gwago suka dinga ma ta sheri, wasan jika sa kaka,
Yaya Abubakar yace zai tambayi Fatima maganin muran da tabawa yar ta kwanaki da mura ya damki yarinyar sosai,
Nace idan ma dai ya rage ai sai ta bamu musha kawai,
Wani iri yaji aran shi don gani cewa ni Free nake koda yaushe don idan Fatima ce ko sunan maganin bazata yarda a tambayeni ba balle har tace akawo muna wanda sukayi amfani dashi,
A hankali ya shimfede yarinyar daga gefena sanan ya jawo kuheran shi zuwa bakin gadon danake zaune,
Yace ranan da nazo nan kike cewa nakoma gurin aiki daw,daw waye a dakin ranan,
Na lissafa mai su har da Lami ni azatona zaice ko hankalina baya tare dani,
Ban san ko suwaye a dakin ba saboda ciwo amma sai na ji yace, ok, ok Lami ce ta kai zancen kenan ko,
Aiko zamu hadu da ita udan tace gulma ta iya takai karshe,
Nan yake bamu labarin abinda tai mai inda maman biu take cewa wanan lami din dama akwai gulma sosai,
Hakkuri nabawa yaya don kada ya hanata gurin samun abincin ta,

ZEEE MAKAWA YELWA




****** ********** ******
Ina
[12/12, 9:59 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
1? 0? 4?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH AD,DAAR

Assalamu Alaikum yan uwa musulmai da farko ina mai baku hakkurin rashin jina dabakuyi ba saboda rashin lafiyan danayi kwana biyu,
Ina kuma mai baku hakkuri akan irin maganganun da kuke fada min dakuma sakon da kuke turomin,
Nasan cewa tsakani writers da readers din su babu adalci ko kadan don idan da adalci bazaku dinga yiwa writer bakar magana ba tunda ba wace ta saka ka aikin banza,
Insha Allah zuwa next page zan hada duk labarin guri guda na rufe a dunkule a kai karshen labarin,
Daga tarko in Allah yaso bazan rubuta wani online novel ba again duk da akwai tarin labarai da yakamata na rubuta maku don karuwan mu baki daya,
Amma gaskiya rashin adalci yai yawa ga al amarin.
Da fatan zaku fahinci abinda nake nufi ga sakona
Dama shi wanan TARKO din irin rayuwan da wasun mu suke tsuntuwar kan su acikin kishiyoyine da irin yan dabarun da zamu dinfa yi idan abubuwa suka daure muna kai,
Sai gashi uzuri ya hana nayi maku shi irin yadda na saba duk da dama nakan kwatan ta duk da ina cikin nawa uzurin,,,,



Alhamdullahi iyanzu na samu sauki sosai na kuma godewa Allah da ya sa yarana suka samu kulawa na musan man daga yan uwa da abokan arziki,
Don suyi bull,bull dasu gwanin ban sha,awa saboda sun samu kyakyawan kula ga su gwago da Maman Biu, da sauran mutanen arziki,
Duk da Yaya Abubakar yana can gurin aikin shi amma akoda yaushe yana bugo waya don jin lafiyan mu,
Mu kan dauki lokaci dashi a waya muna hira kamar ba kudi ake ci a wayan ba,
Bani kadai ba kusan duk wace ya kira acikin iyalin shi sai yau dauki lokaci yana fira da mai shi,
Satina uku da haihuwa inda dagani har yaran yanzu, Alhamdulkahi,
Wata safiya na tashi na gyara jikina ina zaune a bakin gadona ina shan tea,
Doctor ya shigo dakin yana saye a cikin kayan su na likitoci, fuskan shi dauke da murmushi kamar kullun,
Yaja kujera ya zaune acikin sakin fuska yana cewa Mrs Abubakar ya karfin jikin naki nai dan karamin murmushi ina cewa Alhamdullahi yace good masha Allah ,
Ya miko min wata farar takarda yana cewa yau dai asibiti sun tabbatar da lafiyan ki da na yaranki kamar yadda ya dace suyi,
Don haka yau din nan zamu sallamay ku, ku koma zuwa gida,
Ban san lokacin da na sake wani dan malalacin murmushi don a,zatona zolaya na kawai yake yi,
Sai naga ya miko min takardan yana cewa, ga takardan salaman ku,
A hankalin na furta hasbunallahu wani imal, wakeel,
Nace cikin wata murya mai sauni likita da gaskiya yau an sallamay mu asibitin nan ,
Ya gyada kan shi a hankali yace insha Allahu Mrs Abubakar mun kuma gode da handin kan da kika bamu gurin ceto rayuwan wayan nan yaran,
Yace kin kokari sosai gurin bamu hadin kai har zuwa lokacin da mu ka cin ma abubuwan da muke so,
Don haka mun yiwa wa yanan yaran naki gidauniya da ga gudun mawan da suka samu ga gurare da,dama as a gifts,
Wani irin murmushi nayi nadago kai ina cewa, doctor bara ku kai masu,ko yaya ,
Ya dan gurgiza kai yace haba Madam sam ba abinda kike nufi bane mukayi,
Yace kin san twins da shiga idon mutane wanan ne yasa muka nuna acikin nasarorin da muka samu a,asibitin mu cewa an haifa muna yan uku,
Shine jama suka dinga zuwa ganin su na kuma ba su alheri, don farin ciki,
Banji dadin hakan ba amma banda yadda zanyi dole nayi hakkuri,
Ina zaune ina tunanen yadda zan koma gidan mu yi rayuwa da abokan zaman mu, na gida,
Dakuma yadda zanyi rayuwa da yara uku a matsayin diyana in shayar da su a lokaci guda kuma,
Motoci hudune suke a haraban asibiti zasu tafi damu da tarkacen mu gida,
Inda mu kai ta sallama da mutanen asibiti irin su nurses din da mu kayi sabo dasu,a zaman mu, na asibitin,

****** ********** ******
A hankali motocin da muke tafe dasu suke tafiya zuwa gida ,
Ina bin ko ina da kallo sai naga kamar nai shekaru ban a cikin garin saboda canjin yanayi da garin ya,samu,
Gaba daya naga gidan na mu, ya canza min saboda yan sauya don yan gyare,gyaren da akaiwa gidan,
Abin alfahari nasamu Baba Ramatu da su Fattu tare da sauran makwabta suna tsaye a kofa suna jiran isowan mu tare da decoration din guri da flowers an rubuta welcome home, Three's, gwanin ban sha,awa,
Anty Saloon tare da mutanen ta da Anty Barrister, sun cika guri,abin gwanin ban sha,awa,
A hankali aka bude min motan na fito tare da taimakon Anty Barrister wace ta riko min hannu don na samu saukin fitowa, daga mota,
Duk da wai naji sauki amma jikin nawa sai a hankali, don jikin ba karfi maneji kawai nake yi,
Ina, tafe a hankali ina masu godiyan wanan karamcin da sukai min,
Hayaniyar mutane ya saka mutanen gidan mu fitowa don ganin may ke faruwa hakane a gidan suke jin hayaniyar mata,
Ashe basu san cewa, da wanan taron na taron mu ba don ba, a nan aka shirya taron ba anyi hakane kawai don a bata masu rai suji haushi,
Saboda mai kishiya bata kaunar ci gaban kishiya kona kwaran zara,
Alhamdullahi don manya mata masu mutunci da karanci sun cika min. Part, da gida sai yan ciye ciye da lashe tande tande da tsutse, tsutse, ga wakan yan matan larabawan kasan Sudan yana tashi wasun su suna dan rausayawa don farin ciki,
A take guri ya hade da murna da farin cikin dawowan na daga asibiti inda matan gidan babu wace ta leko daga part din ta,
Acewan su wai ba,a fada masu ba basu da masaniya akan hakan don haka bazasuyi attending ba,
Sai dai kuma suna tsaye suna dan lekawa ta bayan labulaiyan dakin su,
Anyi addu,oi da fatan alheri yadda ya kamata, an raba kyautuka,
Waliman yai matukar kyau fiye da tsan manin mutun don a gwada wayewa sosai a gurin,
Anty Salima Barrister sai cewa take aini sister din ta ce, don haka mutane ke min kallon yar uwan ta na jini,
Anty Salima da kanta takaiwa su Anty Sadiya gift din da sukayi rabo a gurin walima tana cewa ga kyautan yan Uku nan yau Allah yayi sun dawo gida,
Gaskiya duk yadda zanyi bayanin an gwada min so da kauna abin ba zai misaltuba don dai sai ince ni Meenatu abin nawa daga Allah yake,
Don duk abinda ban zata ba ban kuma taba tsan manin shi ba sai inga ubangiji Allah ya hore min shi a cikin sauki,
Tundaga auren yaya Abubakar duk yan matan dake gidan mu amma nice Allah ya zaba mai,
Shekaran shi yakai biyar da aure bai haihuba sai gashi ni Allah ya bani haihuwa daga cikin matan shi,
Ban dauki lokaci ba sai ga kyautan diya uku ubangiji ya hore min a lokaci guda
Ga ni kuma nice yar karama daga cikin su mafi kankantan shekaru,
Hakan yasani kara godewa Allah ubangiji subbahanahu wata,ala wanda ya hore min wanan alherorin a lokaci guda ,
Yau kuma sai ga matan birni yan gayu yan kwalisa masu fada aji wai sun taru a sanadina don tayani murnan haihuwa, da dawowa asibiti lafiya,
Ban san lokacin da na fashe da kukan farin ciki ba ina kara godewa Allah wanan matsayin dana samu daga gare shi,
Muryan Anty Saloon naji tana cewa ki daina kuka yar uwar maharkuci mawadaci idan har kabarwa ubangiji al,amarika to insha Allahu Allah na maka mafita ta hanyar alheri hanyan da mutum bai taba zaton samu ta girin ba,
Tace ubangiji yana son bayin sa masu hadiye fushin su ko bacin ran su,
Kamar yadda yake son bayin sa masu kyautatawa wa yan uwansu yan Adam,
****** ********** ******
Kayan gifts din mu dana asibiti dana gida da muka samu suna jibge a falona,
Inda da ka shigo dasu zaka fara arba wanan abin ya saka duk wace tadhigo yi muna sannu da dawowa alokacin da taro ya watse arba da kayan ,
Sai wani irin kishi da bakin ciki ya tokare su dacan abinda akaiwa Fatima na haihuwa ya tsone masu idanuwan su
Sai gashi sun ga na yarana ya cuna masu sosai,
Gaba dayan su wani kunci ne da kishi ya rufe su a lokaci guda har basu iya controlling din emotions din su,
Salawatu rai a bace takira wayan Yaya Abubakar a hasale tana kuka take cewa,
Haba sweet Oga may yasa baka da adalcine a rayuwa ko yaushe sai kai kokarin nuna banbanci a tsakani,
Innalillahi Wa,inna Alaihi Raji,un,
Abinda ya iya furtawa ke nan da yaji may Salawatu ke fada mai a cikin kuka,
Cikin tsawa ya dakatar da ita da cewa da akai maki may wai har zaki furta min wanan kalami haka, ?
Yanzu don Allah Ogana don kawai bamu haihuba sai mu yi ta kallon kana kashe wa matanka kudi masu yawa irin haka?
Kashe kudi ma waye


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login