Showing 51001 words to 54000 words out of 388021 words

Chapter 18 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8216

wayan suna mai sallama da junar su,,,
A lokacin malam ne wanda ke daga kwance yake dan kada kai a hankali,,,

ZEEE MAKAWA YELWA,,
[7/15, 10:10 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
2? 2?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH-AL-KHAALIQ,,,,

Bayan dawowar ta daga birnin kebbi, washegari, Meenat ta,shirya musalin karfe goma tana,son zuwa makaranta,
Falo ta nufa don ta samu ta danyi breakfast a lokacin kafin ta tafi, school,
Zaune yake a falon da waya shi a hannun shi, yana magana da wani adayan bangaren,
Rigar dake a jikin ta dogo ne har kasa yadan fitar mata da,sharp din ta a fili,
Dinkin rigar yai matukar yi mata kyau sosai, sister din anty a marya ce ta dinko mata shi daga kaduna,
Tun daga kofan falon ta hango shi a zaune ya na wayan,
Sai dai duk da wayan da yake yi hankalin shi gaba daya yana akan ta,,
Ji tayi kamar ta juya sai dai ta jure kawai ta karasa, karasowa cikin falon,
Inda ya zuba mata idanuwan, shi gaba daya, kamar wani tsohon maye,
Ya so ace yai mata magana amma sai ya tuna da yadda su kayi da uncle Nafi,u,, a kanta last two weeks,,
A haka tazo har ta gaban shi ta wuce batare da yai mata maganar komai ba,
Bayan ta yabi da kallo a cikin sha,awan irin kira da siffan jikin ta,
Ita ko Meena ganin yana waya yasa ta wuce,wa, batare da ta gaishe shi ba ,
Milk, take zubawa a cup, a lokacin ne taji yayi shiru ga wayar da ya keyi,
Don haka ta waigo don ta gaishe shi saboda kawai mutuncin yayar shi watau, mummy,
Ifon shi kar akanta a lokacin tankar maye wanda hakan yadan bata, tsoro,
Amma cikin daurewa ta ce, masa ina kwana uncle kamar yadda taji yaran gidan na kiran shi,,
Cikin dan i,iniya ya ansa mata da cewa lafiya kalau Beauty ya kika dawo,?
Lafiya tace masa a takaice, ,
Sai dai a cikin zuciyar ta tana mamakin wai har yasan cewa tayi tafiya kwana biyu,,
Ci gaba tayi da abinda takeyi na kokarin hada shayin da take yi,,,
Daga gurin da take tajiyo ajiyar zuciyar shi kamar wanda yai dogon tunane,
Muryan mummy ne taji daga bayan ta tana cewa brother,
May yasa kake son zubarwa kanka da mutunci ne ga diyan talkawa haka
Meenat wace ke kokarin juya tea din da ta hada a cup taji abinda mummy tace a kan ta,
Idon ta tadan rintse a hankali yayin da zuciyar ta ke mata dan kuna,
A gaskiya badon wanan karatun na cikin dadadawa mahaifan ta rai ba kamar yadda su ke burin suga tayi ilimi don cigaban rayuwar ta watarana,
A gaskiya da akan mummy da dan, uwanta zata iya barin sokoto gaba daya ta koma gidan mahaifan ta da ake kira da talkawa,
Eh to tamaji din su talkawa,ne to amma wai ita mummy damay suka fi su ne wai ?
Iya kan dai tarbiya Alhamdullah tana dashi wanda su diyan masu kudin suka kasa samu a yanzu,
Zaka ga dan talka yafi dan mai kudi tarbiyar da kuma sanin ya kamata,
To wai ita ma mummy dake cewa masu kudi har ina kudin yake a gurin su,
Tsukin da taja daga cikin ranta wanda har ya baiyana a fili,
Da sauri gaba dayan su suka waigo ta don ganin may takewa tsukin
Cup din ta dauka da nufin barin falon don ta basu guri,
Cikin wani irin murya taji Mummy ta kira sunan dashi tana cewa,
Ke Meenatu waki wa wanan tsukin newai,?
Shin may kike nufi da nine agidan nan ?
Tun farkon zuwan ki naga duk take, taken ki ba yau ba ,
Ido kawai na sa maki don inga iya gudun ki daga ke har wace ta kama maki a,gidan nan,
Kuma bari ki ji duk iya, yinki da kisisinar ki bazai yi tasiri a kaina ba nida dan uwa na da aka turo ki ,gare shi don ki bata mashi suna,
Ke har ina mace da zaki wani ce wai Ali,Abba's ya rugumay ki da niyar iskan ci,
Haba sister a gaskiya bakiyi wa,wanan yarinyae adalci ba,
Wanan ai sheri ne kawai irin naku na mata kike kokarin yi,
Na fada maki cewa ni nace ina son ta, nafada maku son ta nakeyi son nake in aure ta,
Sai a lokacin Meenat ta dago kai da fuskanta wanda ya jike dahawaye a lokacin,
Cikin wani sanyi murya ta bude baki niyar maga don har ta soma cewa mummy,
Sai taji muryan anty amarya a gaban ta tana cewa Meenat wuce,war ki zuwa inda zakina "ke ji,
Simi,simi meenat tabi ta gaban su gaba daya ta wuce zuwa ciki da cup din tea a hannun ta,,,
Wani mugun kallon rainin hankali Anty amarya ta watsawa masu,
Bata ce komai ba ta bibayan meenat ranta a bace,

****** ******** ******
Ba wani issashen lokaci yake da shi ba so,sai saboda tafiyan da ya taso mai a gagauce zuwa England,
Don, haka ya zo gida, a bazata don yai masu sallama duk yadda yaso ya wuce batare da yazo ba saboda baida issashen time,
Amma sai ya ga haka bazai yuyuba ba agare shi dole ne yai squeezing din time din shi ko na kwana gudane,
Azaune yake cikin daren da ya iso agaban malam suna dan ganawa,
Bayan ya gama fadawa malam din dalilin wanan tafiyan da zaiyi zuwa kasashen ketare,
Malam din yai mashi addu,a tare da fatan alheri,
Malam ne ya jefo mai tambaya akan cewa ya zancen maidakin shi Sadiya,
Abubakar ya dan gyara zaman shi a hankali ya ce a canzata zauna har zuwa lokacin da zan dawo,
Ita da wa ke nan zata zauna acan din ?
Batare da wani damuwa ba yace wata,ce yar uwar ta zasu zauna tare,
"Tau,
Inji malam wanda yaji zafin wanan zance na jikan nashi,
A ce mutum bai shawara da kowa acikin yan uwan shi,
Yanzu duk yawan yan uwan shi amma ace wai sai an fita waje an samo, mai zama da matar shi,,
Duk yadda malam yaso a lokacin yai magana irin wacce, za, a fahita abin ya kakara,
Sanoda yasan cewa bazasu fahinta ba a yanzu don haka ma ya ja bakin shi yai shiru, kawai,
Abubakar zaune a dakin mahaifiyar shi mama Ladi suna bankwana,
Sai addu,a da fatan alheri take kwarara ma dan nata,
Can kuma ta dan kashe murya tankar akwai wani wanda zai jin may zata ce a wanan lokacin,
May ake ciki akan zancen auren da naji ance zaka kara wai ?
Shiru Abubakar yai mata a wanan lokacin tare da dan dukar da kanshi a kasa,
Tau, saurara kaji koda kai wani aure ka kokarta ka kula, da matar ka sosai,
Don ban son ace kayi aure ka wulkanta diyar aminiyata,
Saboda ban son mu samu matsala da uwarta akan wanan auren ?
A cikin ladabi ya ansa mata da cewa, insha Allah babu abinda zai faru a kan haka,
Sosai mama Ladi taji dadin ansan da dan nata ya ba akan diyar aminiyar ta,
Zancen auren yar, uwar shi Samira wanda za,ayi baya kasan mama ta kawo a lokacin,
Abubakar yace ba kudi kukace na aiko maku dashi wanda zaku sai mata kayan daki dashi ba,
Ma kin san fa yanzu babu kudi sosai na riga da na yi duk wani planing akan tafiya na, ko,
Cikin dan marairaice murya mama tace amna aikasan dole ne sai mun kai kayan gara irin wanda mutane zasu sheda ko ?
Shiru yay tare da sa hannun shi a cikin aljihun shi,
Inda ya ciro kudi hannu suna rawa mama ta mika ta karbi kudin daga hannun shi,,
Tafiya yake yi alokacin zuwa sashen amaryan mahaifiyar shi wanda kusan a manne su ke da junan, su, said ai yar katangar da akayi a tsakanin su,
Tunane yake yi wai may yasa mama tafidamuwa da Safiya fiye dashi,
Yadda mama take nuna mai tankar Sadiya ce ta haifa a tsakanin su ba shi ba,
Duk irin mugun rayuwan zaman auren da suke yi a tsakanin shi da Sadiya mama bata taba ganin laifin hakan ba sam,
Saidai ita gurin ta kawai a gyarawa Sadiya rayuwanta sai kuma zancen ya ba da kudi aiwa gidan su Sadiya abu,
A haka yai sallama da duk kusan wanda ya kamata yai sallama da shi a wanan lokacin ya yi saboda safe zai wuce,

Da Baba samaila suka gana akarshe inda yake fadawa Baba samaila kudirin auren shi da yadawo daga England insha Allahu,
Inda baba Samaila yai mai alkawarin cewa zai tsaya mai akan zancen auren har komai ya tabbata,
Mama Saratu tana jin duk zancen da sukeyi a lokacin,
Don haka take mamaki da cewa wanan karon akan mace Abubakar ke niyar saba, wa mahaifan shi,
A nan taji muryan maigidan ta inda yake kara nanata wa Abubakar da ya kwanatar da hankalin shi yabawa Yarinya hakkuri, har zuwa dawowan shi
Sai a lokacin ne Abubakar ya tuna da cewa ai Baba samaila yana da yara masu dan girma akwai Ibrahim da kuma mace ai,
Wanda gaba dayan su baya jin duriyan su acikin zurian gidan nasu,

****** ******** ******
Wata uku ke nan yanzu da suka wuce rabon Meenat da zuwa gida birnin kebbi,
Sai,dai a ko da yau,she suna waya da yan uwan ta sosai,
Musan man Samira wace ke aiko mata da kudi ta na siyo mata abubuwan bukatu a garin sokoto,
Zaune ke da yar wayar ta a hannugama wayar ta ke nan da Abdullhameed,
Wanda zuwa yanzu sun rage irin hurda da su keyi a da dashi,
Wanda ita sam hakan bawai ya damay ta bane don tasan cewa yanzu take don abune mawuyaci tafi batare da ta dawo da sabon yyi ba,
Duk da TV dake a dakin su yana aiki kamar y tsage mutanen ciki su fito,
Hakan bai sa Meeenatu daga kai ta kalli TV ba ita hankalin ta, na ga wayan ta ,
Text take karantawa wanda duk kusan yan kwanakin nan mai text din na yawqn damunta da turowa,
A hankali har ta iso inda meenat din take zaune daidai inda take a zaunen,
Takai hannun ta, a hankali ta dafa ma ta kafadar ta,
Hakan yai sanadiyar dawo da ita acikin hankalin ta
Tadago kai suka hada ido da uwar dakin nata watau Anty amarya,
Ajiyan zuciya Meenat ta sauke tare da dan yin yake a fuskanta,
Da ganin dariyan bai kai ciki ba tadai yi shi ne kawai,
Gefen ta amarya ta samu ta zauna tana cewa
Meenat auren yan uwanki ya matso banga kina wani shiri ba akai,
Ido meenat ta lumshe kadan sanan tace anty ina ga fa sai kila ne ma in samu zuwa don ina da test awanan lokacin,
A ,a ke ko meena za ai buki a gidan ku kuce bazaki samu zuwa ba nan da birnin kebbi,
Anty Amarya ta dubi meena da kyau tace sai dai in akwai abinda zai hana ki zuwa
Fuska meena ta bata tace Anty kin san fa yar wajen mama Ladi ce fa da diyar baba shaibu,
Ni wallahi Anty ban son tozartawa sam wallahi saboda hakane kawai ban sa zan tafi ba,
Murmushi Anty tayi tace zaki tafi mana don in baki tafi ba basu ji dadiba musam man samira din,
Ai badon ita mama ladi zaki tafi ba ko ?
Ido ta tsurawa wa meenat din inda yarinyar ta ba ta tausayi sosai,
Yarinya kamar meena ace bata da kwanciyan hankali saboda kawai hassada
Hannu ta sa ta dauko ledar dake gefen ta kayane tafara ciro daga ciki
Kayane har kala uku Anty ta a mata wai tasha buki da su,
Baki bude Meena ke kallon uwar dakin nata wace a ko da yaushe tana ko karin ganin farin cikin ta,
Sabanin mummy wace ji takeyi tankar ta shake meena din yanzu
Wai ta yiwa dan uwan ta sheri, don ta bata mashi suna,



ZEEE MAKAWA YELWA
[7/16, 10:21 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
2? 4?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAHA-AL-MUSAWWIR


Bayan an sauko daga sallah jumma,a ne, din,bin al umman Annabi suka taru a kofar gidan malam manya don sheda daurin auren jiko kin shi,,,
Mutane da kauyu kan garin birnin kebbi, dama cikin garin sun shigo saboda sanayyan dake tsakanin su da wanan tsoho
An taru inda tsohon malami, ya bukaci manya diyan shi da su wakilce shi, ga daura auren,
Abin mamaki sai ga Malam din ya,bukaci Baba hamza da Baba shaibu da su matso gaba yace su yake son su fara karban auren,
A take gurin yai tsit, ana sauraron tsohon dattijon irin yadda ga Baba Buhari a zaune amma ya gabatar da yan kan,nin shi a gaba,
Anan ya umurci Baba Shaibu da ya amshi waliyancin dan shi Abubakar shi kuma Baba Hamza ya karbi na diyar shi Aminatu,
A take jama,an gurin suka fara kalon kalo suna mamaki kowa da irin abin da ya ke fada agurin,
A bokan Abubakar da suka zo daurin auren kan,nen abokin nasu, ta sanadin shi, sai mamaki suke yi a lokacin,
Ba baki ba har yan gida sun shiga cikin rudani, saboda sam basu zaci cewa,,
Ameenatu malam tsoho zai ce zai aurawa Abubakar ba,
Saboda ai ba daki guda mahaifan su suke ba ,ga su , su da suke daki daya da mahaifin shi, ai, "ya,"yan su ne ya kamata a hada dashi, din, ba sai anyi wani dogon shako ba, har zuwa sashen Baba Samaila,
Dole badon sun so ba aka daura wanan auren mutane na ta mamaki,
Baba Samaila wanda yai mutuwan zaune saboda duk ilahirin jikin shi zufa ke fita, don tashin hankali,
Shiko Baba Buhari sai cewa yayi Alhamdulillahi,
Allah mungode maka da kabar muna,wanan tsohon namu maitarin alheri,
Daga haka kuma akasa baba Samaila ya bada auren Samira, inda Baba Buhari tabada auren Murja,
Wanan abin yai wa din,bin jama,a sha,awa irin yadda tsohon yai hikimar hadin kai a cikin zuri,ar shi,
Sadakin kowace diya mace dubu sittin ne don haka kowace a ka mikawa waliyin ta,
Daga haka masu sanarwa suka fara shedawa al,umman dake daga nesa,
Maroka mata sukayo cikin gida suna guda da shewa yau Allah yayi an,daura auren Magajin malam Abubakar da Aminatu Samira da Aliyu, Murja da Dauda, jama,a sun sheda yau kun zama amaren angwayen ku,,,,,,,,

****** ******** ******
Meenatu da gwago Habiba wace suke cewa gwago Habi, ita kadai ce kauna ga mahaifin meenat din,
Hira sukeyi akan yadda mamata hana aba gwago Habi abinci tun zuwan ta gurin bukin,
Mama Saratu mahaifiyar Meenat tace gare ku wanan abin yake bako ko?
Naga hakan ai kadan ke nan daga cikin halin mama Ladi,
Baku ganin ko mariya diyar ta da yake bata da komai kuma a kauye take zaune ai kun ga bata hurdan komai da ita,
Gwago Habi tace ai tayi abin ta wata rana sai labari don Allah bai manta da kowa ba,
Muryan maroka matan da sukaji ya kaule gida shine ya dakata da su daga hiran da sukeyi,
Kamar amafarki wata mai murya rarara, ta sake cewa yau Aminatu ta zama matar Abubakar inji Allah Samira matar Aliyu Murja matar Dauda,
Gwago Habi tace ji mashiririciyar can abin da take cewa bata ko san sunayen amaren ba,,,
Again wata mai babban murya daga cikin marokan ta,kara maimaita abinda ta farkon tafadi,
Wanan marokiyar bata kara fadin zancen su samira ba sai ganin Meena Gwago Habi tayi ta mike zubur,
Itama din mikewa tayi don mamakin abinda sukeji a na fadi daga wajen marokan,
Guda mai karfi wata daga cikin dangin malam, tsoho da ta zo daga kauye ta rangada, zuwa sashen Baba Samaila din,
Abin da ya kara tayar masu da hankali kenan gaba daya,
Isowar matar tana wanan guda tare da,wasu daga cikin dangi yasa,Meenat cewa
Ya Abubakar shin ?
Sai ganin ta kawai gwago Habiba tayi tai kasa, a somay,
Kururuwa jama,a suka sa wanda ya jawo hankalin sauran al,umman gidan,
Ruwa aka zubawa,meenat din masu sanyi wanda yasa ta farfado cikin dan bude idon ta ahankali,
Sai ganin jama,a tayi still, a kanta dafifi, abinda marokiyar nan da gudar matan nan ya fado mata a rai,
Hakan ya kara,sata sumay wa again, a take duk gidan ya rude,
Wanan karon duk jikin meenat a jike yake, da ruwa
Amma shiru bata farko ba don haka aka fadawa maza a waje,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login