Showing 237001 words to 240000 words out of 388021 words

Chapter 80 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8282

ta sa har saida tabani tausayi tana cewa a cikkn kuka anhade mata kai agida don a cuta mata
Anyi sanadin kwace min yaro a gidan don arabani da shi yau har takai ace mai sunan malam yazo yaci abincin shiyan Samaila yabar nawa,
Baba musa yace indai mutum ya girma asan ya girma don dai kowa agidan nan yasan cewa mai sunan malam a nan sashen Samaila yake cin abincin sa idan yana gari,
Sai yanzune zaki kawo wani sabon zance kice an masa asiri anmallake shi
Anty Safiyae suka shigo part din mu ransu a bace tana cewa mahaifiyar su cikin kuka,
Mama sai da nace maki kada kizo don hakan ba daidai bane don kowa yasan cewa,
Yaya Abubakar komai nasa a wanan sashen yakeyin sa
Sai yanzu ne don ya aure Meenatu za ace wai saboda ita ne yazo nan wanan abin ai,bai,kawo gani ba wallahi,
Ni banson abin rashin gaskiya don sai da ce maki kada ki zo da Anty Mariya ta fada maki cewa yana can yana cin abin a sashen Baba Sama,,
Aiko kuma tai cikin Anty Safiya da masifa zagi ta ko ina kaman zata cinye ta danya,
Saida mutane su kace wa Anty Safiya ta dauki mayafin ta, ta wuce gida,kawai hakan zai fi sauki,
A kofan gida suka hadu da Yaya Abubakar wanda ya hango yar uwar shi fitowa daga cikin gida ita da yar ta da tazo da ita,
Ta na tafe tana sharan hawaye da gefen hijabin ta cikin bacin rai,,
Hakan yasashi kiran sunan ta yace Safiya lafiya kuwa,
Ta juyo gurin da taji muryan dan uwan ta, tana kokarin sakin fuska don ganin shi
Lafiya kuwa Safiya kike kuka daidai bayan motan shi ya jata suka tafi, su ka dan kebe wa mutane,
Yaya wallahi abinda maman mu keyi a gidan nan ba kyau sam
Tana zubar muna da mutunci sosai ga mutanen gidan nan,
Ace abu tun ana yara akeyinsa amma wai har yanzu, ba,a daina ba,
Dubi fa yadda jama,a suka taru mata a sashen Baba Samaila wai taje fada don kawai Anty Mariya munafuka ta tafi tafada masu cewa, ga ka can kana cin abinci, tare da Meenatu,,,,
Mama bata tsaya taji may muke fada mata ba sai kawai ta wuce da masifa zuwa sashen gurin ku,,
Murmushi Yaya Abubakar yadan yi har fararen hakoran shi suka baiyyana, fili,
Yace Safiya kuyi ta hakkuri da halin maman mu haka halittanta yake don inda ba haka ba ne da babu yadda za,ayi takara kallon Sadiya,
Don irin wullakancin da Sadiya tai masu da suka tafi wurin mu Abuja ai ba kadan bane,
Cikin ma nai mata kaca, kaca don bazan dauki wullakancin mace ba ni sam,
Ta ce ai sha,anin mama sai addu,a kawai don haka ki daina barin kuna fada tana zagin ki,
Tau yaya nagode tace cikin nuna kulawan ta tana cewa yaushe zaku koma yace da naso inyi sati amma yanzu gaskiya bazan kai hakan ba,
Zuwa next tomorrow zamu tafi insha Allah don ban tsayawa ana irin wanan tashin hankali akaina da iyalina,
Anty Safiya ta dan waiga bayan ta ko akwai maijin su,
Tace zancen cikin Meenatu gara da baka fadawa kowaba,
Don mama tace wai bazata taba yarda Meenatu ta haihu da kaiba,
Kuma wai sai ta raba auren, ku da ita don bazata yarda ta hada zuria da su ba,
Jifa yaya wai ko may sukai mata haka bata kaunan su sam,
Murmudhi yaya Abubakar yayi uace saboda wai ba kakan muce ta haifi Baba Samaila ba,
Salati ne Anty ta saka ce wanan ma kawai to ita wa take tayawa tunda matan badu da rai yanzu dukkan su,
Kedai kawi kuyi hakkuri don al,amarin ba dadi wallahi sam,
Kuyi fatan mu samu mu rabu lafiya da ita kawi neman albarka da samun gamawa lafiya da junan mu,,
Ta ansa dacewa hakane ma sosai gaskiya yaya,,,,


ZEEE MAKAWA YELWA
[9/15, 9:58 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
7? 4?


ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH- AL-HAIY


Fatan Alheri gare ku masoyana Alherin Allah yasamay ku a duk inda kuke,
Godiya maitarin yawa Gareki marubuciyar, HAWA,U ABDULLAHI SARKI nagode kwarai da kaunar ki gareni,


Anty Sadiya zaune a dakin yar uwar ta Habiba an cika mata gaban ta da kayan lashe, lashe da tandetande,
Yar uwan nata ne ta shigo dakin bakinta dauke da sallama ta samu guri a bakin gadon ta ta zauna suna fuskan tar juna,
Tambayan da tafa jefo mata shine
Innan mu tasan cewa zaki zo gurina ne yanzu haka ko daga gidan mijinki ka zo nan ?
Anty Sadiya wace ke daukan goran kunan Aya mai sanyi da zaki tace ba ta sani ba gaskiya,
Sao Habiba tai ajiyan zuciya tai shiru tana mai kurawa yar uwanta ido wace ke kwankwadan kunun Ayayan ta hankali kwance,
Sunan Sadiya ta kira cikin nunawa a fuskan ta tana son suyi maganan serious da ita,
Habiba tace Sadiya ina son ki kwantar da hankalin ki ki saurare ni da kyau da kunnen basira,
Ke dai ba yarinya,bace, yanzu ya kamata ki san ciwon kan ki,
Ganin serious matter ne zasu yi magana akai yasa Anty Sadiya ta mai da hankalinta ga yar uwar ta,
Habiba tace kada kiji gawani ko wata wanga zance da zan fada maki ki ji shi ga bakina maman mu MANYA ta (Witch)
Da sauri Sadiya ta dago kai ta dubi yar uwar ta cikin bacin rai
Tace a fussace Habiba ke ma kin tafi gurin malam zamani sun hada ki da uwar ki ko,
Habiba wace idon ta ya kawo hawaye a lokaci guda ta dan share hawayen ta hade wasu yawun bakin ciki, tace,,
Kada ki manta cewa nima mahaifiyata ce ba ke kadai ta haifa ba,
Don haka idan kinga zaki iya saurare na ki kwantar da hankalinki in maki bayani,
Sadiya taga babu wasa fa ko wani wargi, a harkan dole ta kurawa yar uwar ta ido,
Habiba tace, mutane sun dade suna zargin Innan mu,
Amma abinka da Da da mahaifi sai sam ban yarda ba, cewa gaskiya ne,
Ina gida akace min ga Innan mu can ta tafigidan surukan ki wai matan gidan iskan su ya yatashi daga ciki harda Mariya,
A fusace na taho daga gidan mu naga taton mutane, dafifi a kofan gidan,
Sai gata tafito a wullakance daga cikin gidan na tare ina fada ina cewa
Ni sai nayi karan su duk da akwai mutunci a tsakanin mu dasu amma sukai muna wanan cin fuskan haka,
Zan sa abata ruwan maita ihar tana dashi kowa yasani in bata dashi kuma a fitar da ita daga zargin bakin duniya,
Ta yi shiru tare da hade fuska ta hade wani irin takaici tukun tace hmmm,
Sadiya sai Inna mu tace min idan na kara zancen zuwa shan ruwan maita, sai ta yanke min kauna,
Dole ina ji ina gani na kyale duk inda tabi ana gudun ta cikin shiya mata dayara har ma da maza,
Sai watarana na zo gaishe ta kafin in shiva gidan sai naji na taka wani abu, ina cikin dubawa sai nake jin muryan. innan mu tana cewa,
Wai yanzu mugun tsohon ga duk yasa Dodon ta cikin wani yanayi gashi abinda yake samowa da yanzu ko kwatan shi bai samowa,
Don haka ita wallahi duk yadda zatayi ta rama abinda akai mata sai tarama,
Hakadai ta iya hakuri akan yaranta tabada mahaifan su balle wani katon bazan ya kawo mata chikas a vikin al amarin ta don ana bakin ciki da ita,
Halan in ta mutu suwana zata barwa arzikin ba diyan taba suci tare da mazajen su,
Tace walle Sadiya faduwa daina banyi ba agurin da nake tsaye sai dai naji kukan wani abu nadan leka don in ga ko minana,?
Ke wasu irin halittana kaman maciji gashinan dai ban san yadda zan kwatanta maki su ba,
Suna ta warki a tsakar gidan, har hawan jikin ta sukai bata damu ba,
Amma da na dan taka don in koma bayan sai kawai wa yan nan halittun sun ka bace kamar walkiya ban gan su ba,
Kafin Habiba taci gaba da zancen ta sai Sadiya tasa kuka kuka irin mai tsuma rai,
Gaba dayan su su ka taru suna kuka cikin tashin hankali, babu mai rarashin wani daga cikin su,
Sai Sadiya ce tai karfin halin cewa lalai na yarda da zancen ki,
Nan ta kwashe labarin irin abinda ya tashi shige mata a a gaban ta har tai ciwo kamar zata mutu da yadda ya hannayen ta yanzu suka koma kaman sun lankwashe basu mikewa,
Kuka sosai Habiba tayi tashi shine basu samu labari ba
Sadiya tace, sai daga baya nake jin cewa wai Innar muce tace ina ruwan ta a lokacin da aka bugo mata waya,
Nan dai ta kwashe labari tafadawa yar uwar ta kaf,
Cikin kuka Habiba tace to wa yai jinyar ki haka Sadiya ?
Tace wallahi Meenatu ce tai jinya ta sai daga baya tasamo min wata mata yar aiki ta dinga taimaka min,,
Habib tace amma ko wagga diya tayi maki mutun ci gaskiya don wace kishiya zaki samu yanzu tai maki hakan,
Sadiya tace amma dai kin san kishiya batai ma abu don Allah don haka ta dai yi ne don wani manufan ta kawai,
Habiba tace haba dai Sadiya irin wana kokarin haka har mutum zai yi don sheri,
Sadiya tace aiko sai tayi don sherin don mji yace ita ta Allah ce ,
Haba Sadiya aiko ma may ye tadai yi ita dayan matar tayi maki ne halan ,?
Sadiya takara tabe bakin ta ce, wanan yar iskan wake zamcen ta ko sannu ban samu ba daga gare ta tunda tasan sherin da tayi min,
Wani sheri kuma Sadiya tace wai turo min mugun abu inba ita ba kowa wani,
Ai ba yau muke nake da mijina ba wani Abu bai taba samuna ba sai yanzu,
Habi tace ke Sadiya kada ki daukan wa kanki wahalan zato wakike zaton cewa tai maki hakan a cikin su tace kada ki jawa kanki zunubi ga banza Allah,,
Nan dai su kayi ta hiran a tsakanin su suna tatauna yadda, al,amuran suke masu,
Dakuma mafita ita habiba take wa yar uwarta nasihan akan zaman duniya,,,

****** ********** ******
Har waye wan gari bamu hadu da Yaya Abubakar ba wanda tun, jiya da mama tai muna cin mutunci ya fita, bai shigo part din mu ba, sai wayan daya bugo min sama sama yana cewa nasha magani na kuwa,,,,,
Ina bashi ansa naji ya kashe wayan batare da cewa komai ba,
Sai yanzu nakira layin shi na sheda mai cewa ina son in tafi garin KALGO gurin gwagona don in dubota saboda ta samu kariya a hannuwan ta,
Muryan shi ya tabbatar min da cewa, yana barci ne a lokacin, saidai na daure na fada mai, ina son zuwa,
A takaice yabani amsa da cewa inbari zai zo mu tafi tare, ban so hakan ba don yini naso nayi a kalgon don sai yamma zamu dawo,
Yaya Abubakar sai zuwa sha biyun rana ya shigo gidan mu cikin shiga na mutunci da kamal ,,
Part din mahaifiyar shi ya wuce direct, don su gaisai,
Mama Ladi tana daga zaune a kofan dakin ta fuskan da gani tana a cikin damuwa a lokacin don haka ,
Ya zauna saman tabarman kaban da yagani shimfide,
Sai lokacin take cewa wai ya tashi a shimfida mai tabar man rubo saman wanan na kaba din,
Ya ce No abarshi kawai don ba zama zanyi indade ba zamu tafi Kalgo ne gaida gwago Habib,
Wayyo yau ina wuta Mama ta saka Yaya Abubakar wanda take ganin ya zama sallamamay a gareta,
Yanzu mai sunan malam baka tafi kagaida yan uwa na ba amma shine wai har zaka tafi gaida yar uwar matan ka,?
Ya dago kai cikin mamaki yace yanzu kuma gwago Habib ta zama yar uwar matata ke nan, ?
Yar uwan mahaifina ce fa ita bawai dagin matana ba idan da yar uwar mama Saratu ce shine zakice dangin matata ce ita,
Ko wacecen ka inda Habib ce baka zuwa ko ina
Ya mike tsaye yana cewa, zan fita dama akwai abinda nake son zuwa yi Zauro don haka bari kawai na tafi,
Sai kuma yai murmushi yana cewa saidai kuma,su Baba gaba dayan su suna kofan gida da malam tsoho
Nasan cewa da nafita tambayana zasuyi ina nabaro ita Meenatun kuma,
Kace masu kana zuwa ka dowa mana, ba shike nan ba,sai dai ka tahiyyan ka inda zaka, na,
Ya,Ce haba Mama mi zaisa in masu karya cewa dai zanyi ke ce ta tai ita kadai, don zan tafi nawa tsabgan ,
Yau Allah ya gwada min Da yanzu ashe halin nan naka na rashin boye gaskiya na nan,
To yaya kaka zama da matan ka don dai duk mai mata biyu bashi shuka gaskiya,
Dariya maganar ta yaba Yaya Abubakar don dai yasan yadda tun yana yaro su ke kwasa da ita kan karya ,,
Yace na tafi sai nadawo nika son mu zauna kafin in tafi,
Nikan tunda Yaya Abubakar ya tura cewa ace in fito mutai ban tsaya jiran komai don dama da yan kanne na ne zamu sai kuma yaran Baba musa , du biyu fon haka su biyar sunka matse a bayan mota,
Nafito saye da wata dogon riga baka tasha kwaliya mai kyau daga cikin kayan lefen da yaya ya sayo min yake,
Mun dauki tsaraban da nazo wa gwago na dashi da sauran sayayan da nai mata anan,
Kafin motan mu ya daga har yan gulma sun tafi fadawa Mama ko, ,
Ba wasu bane CID din Mama sai diyan Anty mariya da take riko har su biyu, mace da namiji,,
Ni da Yaya Abubakar muke gaban mota sai su sisters dina, zaune a baya motan kowan cen su ta,fito da na kasan akwatin ta ta saka,
Mai makon mu mike hanyan mu sai naga ya juya akalar motar shi zuwa cikin gari,
Alairu quarter's mu ka nufa hankan yasani gane cewa gidan Anty Safiya zamu,
Ba karamin dadi naji ba saboda na gane cewa Yaya Abubakar zai cika min alkawarin kai ni gidan dangi da kan shi,
Don haka wani murmushin dadi na sake tare da lumshe idona, a hankali,,,,,
Sai lokacin da muka bar unguwar mune na dan juyo ina cewa Yaya na Ina kwana,
Sai da ya karya kwana tare da gyara tukin shi yake ce min
Yaya kuka kwana, ya baby na ?
Na, ansa a hankali da cewa lafiya kalau ya bakunta da hakkuri,
Hmm kawai yace batare da ya kara cewa komai sai kwatance hanyan gidan Anty da muke mai, shi dai baice muna kala,ba har muka kai kofan gidan Anty Safiya,
Mijin ta muka fara gani a kofan gidan su inda ya fara yin wasa kamar yadda yake min da can baya,
Amma sai nai murmushi kawai ban bashi ansa ba, nace mai ina wuni ya aiki, yace da godiya,
Ya juya gurin yaya Abubakar yana mai gashe shi cikin girmamawa,
Yace matan manya kinga addu,ana ya zama gaskiya ko,
Inna ce maki matar manya ce ke sai kice ina
maki adduan auren tsoho,
Nace kai Baban Dule baka mantawa ko nai murmushi na shige cikin gidan, su , anan muka barsu shi da Yaya Abubakar,,,
Sosai Anty Safiya take murnan ganin mu gidan ta duk ta rasa abinda zatayi don murna,
Yaya Abubakar suka,shigo gidan dashi da Babab Dule suna dan hira sama sama,
Babu kujeran kirki a falon ta ga gidan irin na quarter's amma ba kyau gani sam don ba tsari,
Mun dan taba hira da ita inda mukai mata sallama kudi masu yawa ya ba maigidan ta wanda muke cewa Baban Dule,,
Tun fitan mu gidan naga duk yanagin shi ya canza sosai murmushi nayi a raina don nasan TARKO na ya soma aiki kenan,
Mun dauki hanyan da zai kaimu garin Kalgo Yaya Abubakar ke tambayana cewa babban sister din shi wace ita a kauye take aure nake cewa kauyen su yana nan Masama,
Sam Yaya bai san gidan Gwago Habi ba sai da muka gwada mai abinda yasani gane cewa baisan gidan kowa ce mace yar Family din mu ba,
Allah Sarki Gwago Habbi gidan tsoho gida ne sosai duk ruwan sama ya darje ginan gidan,
Muka fifita daga motan tana zaune acikin wani dan rumfar kara a gefen dakin ta,
Kanta da wani kitso soro shidda yai makal,makal dashi tankar anyi shekara ba ai kitso ba,
Kofan dakin duk ya kwakware sosai don daga dan inda ya zurma zaka iya hango cikin dakin,
Sai murna takeyi da lalai mar habbi? din ganin mu don har Yaya Abubakar saida muka shigidan dashi,
Nida kaina na shiga dakin Gwago fon dauko shimfida,
Daga inda take zaune take cewa in duba bayan kofa tabarma sabuwa yanan in dauko,
Kayan tsaraban ta muka zube mata su a kofan dakin ta tun


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login