Showing 105001 words to 108000 words out of 388021 words

Chapter 36 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8288

ke kokarin kai wa amma na hana ta sacewa haba dai Mama ba komai ai,
A cikin daurewa na karasa,duk aiyukan dake gabana,
Inda har zuwa lokacin abin da naji, daren jiya yana a cikin rai na,
Saidai wazan fadawa wanan zancen ne ?
Don haka na daure na rike abin a zuciya na ni kadai,
Da dare na karbi girki inda nai ta faman dawainiya da Yayana Mijina,
Daya daga cikin rigunan barcin da Anty Amarya tasayo min guda biyar ban taba amfani da shiba sai yau na jawo shi,daga kasan kaya na,
Turaren da Maman Bi,u tabani na kara shafawa yau ma again,

A hankali na tura keep fan shiga dakin yayana Abubakar
Dakin yana ta faman kamshin room fresh din da na feshe shi dashi,
Can na hango shi tsaye a bakin window dakin iska na dan kada fararen labulen sama,
Ya na dan tsaye yajingina jikin shi da bangon dakin,
Kafan shi guda ya na tokare ga bango ya dan dafe bayan shi ga gina,
Tun kafin in karasa isowa gurin da yake na fahinci da wanda yake wayan,
Mama Ladi ce don irin yadda naji yana ta bata hakkuri yana cewa mama kiyi hakkuri za,a yi yadda kikace din,
Ai ba wani abu mai yawa na basu ba kawai na shan ruwa hanyane na basu,
Tun lokacin da ya hangoni shigowa dakin na ji harshen shi ya fara sarkewa yana dan ce, mata,,
Mama zan kiraki da safe in kara maki bayani insha Allah,
Direct gurin da yake tsaye na nufa cikin irin tafiyan da ban san da cewa na iya shi ba sai yanzu,
Hannu ya mika min alamar inzo gare shi gurin da yake tsayen,
Ba musu nanufeshi a hankali, yayin da ya ware hannaye shi dukka biyu na shige ciki,
Duk da waya ya,ke yi da mama bai hana shi sauke wani irin ajiyan zuciya ba,
Tare da lumshe idon shi, yana shakan kamshi turaren da na shafawa jikina, a hankali sai faman sauke ajiyan zuciya yake yi,
Ita ko Mama sai faman fada takeyi acikin waya tana cewa duk abinda kake shiryawa akan wanan yariyar kada ka wuce wanan satin da zamu shiga,,
Abinda kunne na yajiwo min yasa nagane cewa dani mama take,
Kai na na matsa a cikin fadaden kirjin yayan nawa,
Yayinbda ya rugumoni da hannu guda yana dan shafa min kai a hankali kamar wata karamar baby,
Mama zan turo ta zuwa jibi ma basai andauki lokaci ba,
Albarka naji tana sa mashi yana cewa Ameen Mama nagode kwarai,
Da haka tana sababi ya kashe wayan tare da sauke ajiyan zuciya mai karfin sauti,
Abinda ya fado min arai shine zancen Mama lokacin da muka tafi da Anty Amarya sallamar su,
Inda take ce min babu abinda da yawa mutanen gidan mu yanzu suke son ji da gani kamar ace,
Aure na da yaya Abubakar ya samu matsala, nadawo gida na zauna batare da auren shi ba akaina,
Cikin wani irin murya Mamana Saratu da takawo nan tadan sasauta muryan ta tana cewa yar Baba don Allah ki daure kiba marada kunya ga wanan al,amari,
Don kinfi kowa sanin irin halin rayuwan da muke ciki agidan nan,
Don gaba daya sun dauki tsanar duniya sun sa muna mu da ku,
Kaina na tura a kirjin yayana tare da dora hannuwana abayan shi nai mai round dasu,
Kara sauke ajiyan zuciya yayi tare da matse ni gam ajikin shi kamar wani na son kwace a jikin nashi,
Meenatu ya furta acikin wani irin yana yi mai nuna kasala gamutum,
Yace nasan cewa kinji abinda mama take fadi a wayan nan
A hankali nadaga mashi kaina dake saman kirjin shi tare da dago kyawawan sexy eyes dina muka hada ido dashi,
Murmushi mai kwantar da hankalin mutum na sake mai,,
Don in samu damar shigar da kaina agare shi har ya manta da zancen Mama ladi,
Don bawai ba a yanzu shirye nake da in rike mijina kamar yadda kowace mace mai sanin ilimin rike,miji ke kokarin yi,
A daidai saitin kunne na yakara rada min Meenat duk ritse duk fitinar mama ban son ki barni, please,
Nasan cewa idan fitinar mama ya ishi, Baba Samaila zai iya yunkurin raba wanan auren da malam ya daura,
Kai na girgiza mai a hankali nace Baba bazaiyi hakaba don da zaiyi da bai bari ankawo ni gare ka ba,
Murmushi naji yayi sanan yace Baba samaila babanane bazai so abinda zai tabani ba nasani Meenat,
Yaya kada ka manta cewa nima fa Mama mamatace,
Duk abinda kaji Mama tana fadi a kaina anmata wani abinda ba daidai bane,
Saboda amatsayinta na mahaifiyar ka malam bai nemi shawan hada aurena da kai ba
Bayan yasan cewa ba kaka guda muke da kai ba a,gurin uba, kamar yadda mutanen gidan mu ke fadi,
Shiiii naji yace alamar inyi shiru da wanan zancen da nake kokarin fadi,
Cikin rausaya kai na dago ina dan kokarin wasa da igiyar bathrobe din dake jikin shi,
Nace yaya ai wan shine kawai kiyayyan mu da mutanen gidan mu,
A take naga jikin shi ya hau,rawa yana tsumi, yace wanan ba hujja bane bai kamata su dauki wanan akidar har yazama masu abin dogaro akai,
Ni gaba daya kowa na gidan mu guda na dauke shi, agareni,
Nasha fadawa mama tun ina karami irin yadda take gwada wa Baba Samaila da ta daina don ba kyau,
Gudun kar diyan shi su taso har ku gane hakan gashi ko ashe har kun gane ko may ke nan,
Nace yaya ai koda muka san hakan bai yi tasiri akan mu ba don mu duk kowa nagidan mu guda muka dauke shi,
Maganan ta shige shi sosai yace naji dadin jin,haka agare ku,
Jikin shi ya kara manna ni, a take ya shiga sarafani irin yadda yake so,
Lokaci mai,tsawo muka dauka ahakan ni da shi cikin wani irin ya,nayi da ba zance ga kamar shi ba, gare ku,,
A hankali yake mai da numfashi guda guda sama gado, yana kwance rairai fuskan shi na kallon saman rufin dakin,
Sunana ya kara kira akaro na biyu shigowa na dakin nashi, yace,
Meenatu Uncle din ki ya kirani dazun da rana yana sheda min cewa kun koma school a wanan satin, da zamu shiga, insha Allah,
Kara gyara murya naji yayi tankar maganan da zai fada ya makale mashi,
Don haka acikin sati maizuwa,zan sallamay ki ki koma sokoto,
Amma dai gaskiya ban so ance kin yi tafi a yanzu ba,,
Saboda nasan cewa kafin ki dawo nan abubuwa zasu iya faruwa,masu muhinmanci,
Sai dai babu yadda zanyi don karatun ki nada amfani agare mu gaba daya nan gaba,
Wani irin dadi naji jin azuciya ta, cewa zan koma sokoto cikin yan uwa na,
Za huta da zaman kadaicin da nake fama dashi nan inda ba abokan magana,
Sai dai ina son injadda maki cewa ki kula da kanki,
Don ni mutum ne mai kishin iyali na sosai,
Kada ki ga kamar cewa bazan, san wani irin rayuwa kike ciki a can din ba,
Duk da nasan cewa baki da wani halin assaha a tare da ke,,
Shiru naji yayi nima dai shirun nayi ina sauraren shi,
Meena kin san cewa ina son ki ba sai na tsaya fada maki da baki ba kamar karamin yaro,
Burina bai wuce in nuna maki hankan ba da kuma iyayyen mu,
Don haka kizama mai rikon amana ki kula da rayuwan ki acan,
Sabosa hakkina yana akan ki, a koda yaushe, inda zaki fita inason sani daga nan,
Don bazan so ace kin zama akuyar sake ba, a garin mutane,
Sanan duk lokacin da na dana bukaci, zuwan ki nan zaki zo ne,
A hankali na ji bakina nace mashi insha Allahu yaya zan ki,yayye,
Murmushin nuna alamar jin,dadi ga zance na naji ya yi ,,,
Ya jawo ni zuwa jikin shi yana cewa, sai ki fara shiri zuwa gobe,
Don zuwa alhamis idan ran mu ya kai, zan sallamay ki,
Don haka sai ki fara shiyaryawa yacigaba da sunsunan wuyana zuwa girji na,
Sosai naji ya matse ni a jikin shi yana mai rada mun wasu zantuka, a kunne na,

****** ********** ******
A washegatin da yaya ya umurceni da in fara shirin tafiya na fara yi,
Ranan ya kasance safiyan Monday ce, don haka akwai fita aiki a ranan ga yaya,na,
Don haka da safe kafin nabar part din shi ya ke ce min
Zanbaki kudi Meena kiyi duk wani shirin da ya kamata kafin ki wuce,,
Kudi masu yawa yaya Abubakar ya bani sai da nai mamakin haka sosai,
Yana daukan wani takardan shi dake saman table yace,
Wanda na baki last Friday, nasan cewa dashi kikayi amfani gurin taron su Baba da su kazo,
Cikin yar murya siririya nace baduka nai masu amfani dashi ba,
Na aikawa Babana da sauran kudin ne yayi lalura dashi,
Daidai lokacin da yake dagowa yakecewa nasani ai,
Mamakin abinda ya ce na yi sai cewa yayi batare da ya kallo gurin da nake, zaune ba,
Baba Samaila ya bugo min waya jiya da dare ya ke sheda min cewa kin aiko mai da kudin dana baku ke da Sadiya,,
Nace mai ba komai ni agareni dama nakune na,baku, na amfanin ku,
Kunyane ya kamani don ban tsanmanin cewa Babana zai min haka ba,
Bakin gado ya koma ya zauna yake cewa kin san shi Baba Samaila rayuwan shi daban ne,
Jeki yi aikin ki kada ki makara don rana ya soma yi,
Godiya nai mashi tare da fatan alheri ga rayuwan shi,
Murmushin jin dadi kawai yai min yana cewa haba ai ba komai bane wanan,
Na juya don in tafi har, na fara tafiya sai na tsaya ina cewa
Yaya don Allah inason inwa wanan makwabciyar tamu magana don ta rakani gurin gyaran jiki,
Daku yin tsaraba wasu anty Amarya da yaran su,a kasuwa,
Ok yace a yayin da yafara bude takardan hannun shi yana cewa
Amma ba,a motar haya zaku tafi ba ko ?
Kafin ince wani Abu yace ki dauki ga ke din mota can ku tafi da ita,
Wanan yaton dake shigowa ya kai ku,
Nagode yaya na kara furtawa a cikin ladabi
Ina fita , da ga dakin yabi baya na yana kallo na cikin, tausayawa da jin wani iri azuciyar shi,

****** ********* ******
Wani Sallon ne na gyaran jiki da kai muka tafi ni da Fattu da dan ta nagoye,
Matar mai gyara tana min gyara tana ta yabon irin kyau, halittan gashina da jikina,
Nan taje tambayana cewa ni yar ina ce acikin arewa,?
Nace mata ni yar Kebbi ce amma a gwandu nake ,
Tace kai zanso inga mutanen wanan yanki na ku na gwandu,
Nai murmushi nace mata mu Fulani ne na asali bawai haye ba don samun irin mu sai a jahar mu ta Kebbi,
Don mazan mu da matan mu duk kyawawane ga addini da tarbiya, akan addinin mu,
Dariya su kayi min da cewa kai amma dai kin iya zuzuta garin ku ?,
Nai mata yar murmushi mai kawatarwa nace, gaskiya nake fada maki anty,
Don mu din na daban ne a, ko ina,,,,,
Dariya sosai sukai min don jin dadin hiran mu, dasu,
Har kafa,na sai da aka wanke min duk wani staining, dake a jikina na koma ina jin,kaina wata irin kamar bani ba ce,,,,,



ZEEE MAKAWA YELWA,,
[8/2, 9:08 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
4? 2?

ZAINAB IDRIS MAKAWA


ALLAH-AL-LATEEF,,,,,

Assalamu Alaikun yan uwa musulmai, muji tsoron Allah ga al,amuran mu,
Mu daina yi wa Allah Ubangiji Izgili ga rayuwa kusani cewa,
Rahaman Annabin Rahama, Annabi Mohammed S,A,W itace muke samu a gurin Allah Ubangiji Subbahanahu,ta,ala,
Amma wai har shine mutum a zamanin nan zai san cewa ya aikata zunubi maigirma irin zunubin da, har wasu zamani saboda irin shi a juya wanan kasan tare da al,umman lokacin,
Yau sai gashi saboda samun guri har muna fitowa a fili mu ikirarin yin sa,
Wa,iyazubillah kuma a cijin diyan musulmai hausawa,
Ya Allah ka yafe muna kurakuran mu kasa mu mu,fi karfi zukatan mu
Ya Allah ka shiryar da duk kan Al,umman musulmi,
Ya Allah ka kare mu daga rudin shedan
Ya Allah kasa mugama da duniyar nan lafiya, =?O?=?O?=?O?=?O?=?O?=?O?=?O?=?O?


Sayayya sosai nayi wa su, Anty Amarya da yaran ta harda ma Mummy da yaran ta,
Uncle dina tare da yaya Abubakar na sayo masu unders irin na maza masu kyau,
Tsab na shirya tare da hada kayan dakina wanda nasan cewa zasu yi min amfani gaba,
I zuwa yan,zu komai na hada don tafiya da safe kawai,,
Abinda nasan cewa idan na barshi a gidan yaya zai lalace na kwashe nakai wasu Fattu da Maman, Bi,u,
Sai murna su keyi da sa min albarka da fatan samun cigaba da nasara arayuwa,

A yadda na ke gani, kamar babu zancen yafiya na acikin wanan satin,
Allah, Allah naje yi kada yaya Abubakar ya ce min an fasa tafiya don,
Naga cewa bai kaunar zancen tafiyan nawa sam,
Sai zuwa dare na ya shigo dakin nawa ko ina yabi dakin da kallon mamaki irin yadda na parking din komai,
Murmushi naji yayi duk da fuskan shi yana a daure babu fara,a acikin ta,
Na kalle shi a cikin natsuwa ina mashi sannu da zuwa, a cikin murya mai sanyi, ba tare da ya ansa min ba,
Idanuwar shi ya zuba min zuwa wani lokaci sai yadan nisa,
Gefen gado na ya samu yadan zauna, tare da sauke ajiyar zuciya,
Meenatu naso ace na kaiki har Sokoto da kaina, sai dai gaskiya hakan bazai samu ba,
A hankali na dago kaina nadan kalli inda yake zaune cikin dan dafe kai da hannun shi,
Alamar ya na tare da gajiya a jikin shi,
Murmushi mai kama da yake na dan sake mai, ina cewa ai ba komai yaya,
Amma driver tare da malam Mudi zasu da matar shi zasu kaiki goben, insha Allah,
Ina fatan idan kin je zaki bawa Uncle da Anty Amarya hakkuri rashin zuwa na,
Kamar yadda nakara fada maki yau ma zan kara sheda maki,
Ki kula min da kan ki kirike amana na dake kan ki,,,,
A hankali na furta insha Allah,
Daga karshe yaya yace nai maki yan sayayya don kije dasu gidan uncle, saidai, basu da wani yawa sosai,
Har an riga ansa a motar da zaku tafi dashi gobe,
Godiya na kara yi mai tare da fatan alheri, kudi ya kara cirowa daga cikin aljihun shi ya turo min a gabana yana, ce min kirike don yin amfanin ki,
Da sauri na kalle shi ina cewa yaya da akwai kudi fa a hannu na har yanzu,
Kai yagyada yanacewa nasa, ai amma kuma kin san yanzu ba da bane ko?
Do ajwai bambanci garayun ki nada dana yanzu,
So ki aje agurin ki don tare lalura ba sai uncle yayi maki ba,
Ya mike tsaye yana cewa idan kinje ina gaida uncle da matar shi,
Murya nane kawai zai isar da sakon da zuciya na ke ciki a lokacin,
Don wani iri naji saboda rabuwan da zamuyi da yayana bayan dan sabon da mu kayi na dan lokaci,,
Yana fita bayan tafiyan shi na adana kudin da ya bani, don tafiya, na,
Mikewa nayi zuwa sashen Anty Sadiya don in sheda mata cewa zan koma, gobe,,,
Na samay ta a zaune tana gyaran yatsun kafan ta a dakin ta,
Sallamana da ta ji ya sata dago kai fuska a daure, ba fara,a ko ka dan,,
Wani irin kallon kurulla naga tana min badon komai ba sai irin yadda gyaran jikin da nayi ya maidani, a lokaci guda,,,
Gaishe ta nayi a daure ta amsa min a cikin da matse fuska, kadan,
Anty nazo in sheda maki cewa, gobe zan koma insha Allah,
Dan sasauta fuskan ta tayi tana cewa, gobe goben nan, za,a tafi, ?
Sai da na,dan yi kamar zan wuce saina ce anty don Allah ki yafe, min,
Acikin muryan nan nata maikama da agajiye take tace min,
Allah ya yafe muna baki daya na ansa da Ameen nabar dakin,
Bina tayi da kallon mamaki yadda cikin da lokaci taga na wani canza mata ,
Take wani irin kishi ya turnuke mata zuciya don sam bata san har yaushe na zama haka ba,,

****** ********* ******

Sanmako mu kayi kamar yadda yaya Abubakar ya umurce ni da yi,
Motar hilux, ce ni da Maman Hanifa zaune abaya,
Maigidan ta malam mudi wanda a yanzu yake na hannun daman yaya Abubakar, zaune tare da driver a gaban motar
Driver wani yare ne don inaganin baya jin hausa sai turancin yan Lagos su,keyi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login