Showing 33001 words to 36000 words out of 388021 words

Chapter 12 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8195

a fili,
Tacewa Samira ga wanan ku kara a tsaraba ko ?
Murja ne ta ansa da cewa mun gode ,
Cikin wani kashe murya daidai lokacin da suke mikewa tsaye
Salawatu ta ce, Sir zamu koma ke nan Allah ya sauwaka,
Abubakar ya gyara tsayuwan shi da cewa barin sauke ku mana,
Koda mota ku,kazo abinda yasa har su sisters din nashi suka dago kai don su kara kallon matan,
No Sir motar tana wurin service wallahi kuma munga idan mun tsaya dare zai yi ,
Amma ka barshi kawai zamu dauki drop ai ba wani matsala,
No mu je kawai na sauke ku sai in dawo in kai, wa yan nan gida su ma,
Ba wani musu suka mike suna mai cewa Allah kara sauki,
Su kuma wasu daga cikin yan matan suna cewa mun gode Allah kai lafiya,
Da haka suka bar dakin cikin karairaiyan kwankwaso da kafadan su,

***** ******* *****
Leda ne rike a hannun shi babu komai a ciki sai kayan cefane irin su alaifo, tumatir, albasa, da tatasai,
Daidai lokacin da zai shiga cikin kofan shiga babban gidan nasu
A,daidai wanan lokacin mama Ladi ta ke kokarin fitowa cikin wani katon hijab, baki,
Kamar kada ta gaida shi da dawo wa amma sai ta dake tace,
"Illah ho,,
Ingwaiyyah,inji baba samaila, ya ansa mata gaisuwan da ta ansa mai,
Fuskan shi a daure kamarkullun idan sun hadu don haduwar su bai faye dadi ba,,
Yadan zarta ta kadan da niyyan shiga ciki sai yaji muryan mama Ladi tana cewa,
Shin yaushe yaran nan da kuka tura can gurin yaron nan zasu dawo ne wai,
Kaga gaskiya an takurawa wanan yaron da yawa don dai ace rai har biyar a lokaci guda,
Ai sai su ja mashi matsala, ga matar shi ko ga inda yake samu,
Inba hali irin na son kai ba da ganin iyaka wanan ai son ganin karshen mutum ne kawai ,
Cikin wani tsawa Baba Samaila yace mata ke dakata Ladi,
Wawiyar banza mala hankali da tunane, ke in har kina da kunya har zaki iya tarona ki ce wai bamu da hankali mun tura wa Dan ko yara,
Baki ta rike cikin shirin bada ansa sai muryan mijin ta baba buhari ta ji daga bayan ta,
Yana cewa ke kan Ladi tir da halinki mara hankali da wayo ,
Shin wai Ladi yau in tambaye ki Dan ga ke kadai adda shi ko kuwa,?,,,
Muryan ta na rawa tace don dai, na tambaya shine zakuyi min taron dangi,
Hakan ya jawo hankalin wasu daga cikin mutanen gidan,
Ganin an fara taruwa masu yasa ta wucewa inda ta nufa simi simi, da
Da wanan bacin ran Baba Samaila ya karasa shiga ashen shi cikin fada da mamakinnirin wanan karfin hali na mama Ladi,
Mama Saratu ce tai kokarin kwanatar mai da hankali da cewa
Malam ai wanan zancen bada kai ta ke yi ba don ba kai ka tura su zuwa inda yake ba,
Da malam take son tai jayayya kawai shi da ya tura su zuwa can,
Huci yayi tare da yin kwaffa mai karfi yace ai kyale ta kawai
Bari kawai yace ladi zata gane kuren ta,
Don duniya ka shirin bashe ta,

***** ****** *****
Zaune suke adakin su sunyi dadaya sai iran mamaki sukeyi irin yadda suka gani a gurin yayan nasu yau a asibiti,
Gulma yakai gulma don har gwada yadda kowa daga cikin su yayi sukeyi suna ta kwasan dariya,
Inda kuma suka juya suna sifanta irin yadda Salawatu take yi da taga Abubakar,
Muryan shine su,kaji a falo yana kiran samira acikin natsuwa, yake magana,
Abinci yake da bukatan ta hado mai don bai iya cin abinci a asibiti, shi,,,,


ZEEE MAKAWA YELWA
[7/7, 6:51 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
1? 5?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH AL-QUDDUS,,,,


KAUNA TA A GAREKU DAGA ALLAH NE,,,,,,,,,
BABY ISAH
SAFIYA HUGUMA
FIDDAUSI SODANG
BABY, DEEN
MAMAN FARIDA
NAFISA HARZAMI



Ya kai wani lokaci zaune a falon batare da sanin su ba,
Duk zancen da sukeyi a lokacin yayan nasu Abubakar yana sauraron ,su,
Bawani zance bane sai zancen wa yan nan bakin matan da suka kawo wa sadiya ziyaran dubiya a asibiti dazun da yamma,
A daidai lokacin da yake shirin magana ne yaji muryan da tun fara zancen bata ce komai ba tana cewa,
To ke anty Samira may ye abin kushewa a wanan zancen ?
Ina dai wa yan nan matan da kike zance akai da sanin yayan mu sukazo, gurin ko
Kuma ai yayan mu idan kin kula yai farin cikin zuwan nasu,
Don haka kama yayi mu ma muyi farin ciki ga duk wani abinda da dan uwan mu ke son don taya shi, jin dadin abin,
Amma ni sai banga wani abin kushewa ba sam ga re su, tunda don dan uwan mu suka zo gurin,
Bafa ke ce zaki zauna mai da su ba shike ra,ayin abin shi don haka namu addu,a kawai idan da alheri a ciki, Allah ya,,,,,,
Da sauri Aisha ta dakawa Meena tsawa tace Alheri a cikin may fa ?
Amma ko dai ke Meena ke bani mamaki kwarai da gaske,
Wa yan,ga yan barikin zakiwa yaya Abubakar kwadayin su,
Kallon mamaki Meena taiwa yar uwar nata kamar za tai magana sai kuma
Mike don kokarin barin dakin don zuwa bayi, ta watsa ruwa har takai kofa sai ta dan juyo tace
Ai da ku san cewa ba,kwa son su sai ku,ki karban kudin su da su ka baku,
Daga haka tabar dakin zuwa abinda take kokarin yi kai tsaye,
Daga gurin da Abubakar yake zaune yana jiyo hiran yan uwan nashi cikin fahintar ko wacen su,,,
Huci yayi tare da furzar da iskan dake a bakin shi zuciyar shi na mai suya, tankar ya fada dakin da yaran suke a ciki,

***** ****** *****
Bayan kwana biyu an sallamo matar yayan nasu daga asibiti bayan dan jiyan da tayi saboda ciwon maran dake yawan damun ta akai, akai, idan tana period,
Sai dai wanan karon ya fi na kullun matsala shine dalilin kwanciyar ta asibitin,
Sosai yaiwa malam tsoho tsaraba don jin dadin wanan tsohon,
Wanda ya sha wahala dashi alokacin da yake yaro da kuma lokacin da yake bukatan taimako,
Motar ma,aikatar su ce ya dauko don ta mayar mai da yaran da suka zo mai hutu daga gida,
Inda yaiwa kowacen su tsaraba daidai gwargwado,
Ranan Jumma, da safe sukai shirin tafiya komawa birnin kebbi, da lodin kayan su,
Yaso samira ta tsaya da su har zuwa wani lokaci amma fafir tace ita bazata kara zama ba inda tasa mai kuka da tashin hankali,
Yana tsaye yana kallon su har suka shiga mota inda Meena ce can baya zaune,
Driver ya ja mota suna dagawa yayan nasu hannu cikin bankwana,
Bacewar motar su yasa shi sauke ajiyan zuciya cikin sanyi,
Ya juya zuwa cikin gidan shi don shirin fita gurin aiki,,,

***** ******* *****
A sai musalin magriba suka isa saboda lalacewan da motar su ta dan yi a hanya,
Duk wanda ke gida ko haraban wajen gidan yasan da isowan yan matan gidan,
Don hayaniyar yan kannen su tare da sauran yan uwa da ya kaure shiyan,
Malam tsoho daga cikin massalacin shi inda ya ke zaune yana jiran lokacin sallah yai murmushi kawai,
Don jin dadin Allah ya kawo mai yan jikokin shi gida lafiya, daga sada zumuncin da suka tafi yi gurin dan uwan shi,
Duk wani tsaraban da suka iso da shi tun daga kayan su har na sako duk a sashen mama Ladi a ka jibge su,
Hand bags din sune kawai kowa ta samu karasawa dashi sashen su,
Meena dai sallah ta ga,batar a lokacin, don gudun kada lokaci ya kure mata,
Sai da ta tabbatar da cewa??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????, i,zuwa yanzu mutane sun dan rarage a gurin,
Sannan ta nufi sashen mama Ladi don ta gaida ita ta dauko kayan ta,,,
Hannu Meena rike da yar uwan ta tare da kanin su guda wanda ke binta a bayan ta,
Tun dan kwanar da zai sadaka da sashen na mama Ladi zaka iya jiyo muryan ta kamar fada,
Sannu a hankali Meena ta karasa gurin inda ta samu anyi dai, dai da kayan cikin da trolley din ta,
Ga kuma mahaifiyar murja ita ma a tsaye cikin tujara da nuna masifa a idon ta,
A hankali, Meena tace mama sannu da gida mun samay ku, lafiya ?
Mama Ladi wace bataji Meena ba alokacin saboda masifan da maman murja ke yi da ita cewa don may zata budewa yara kayan su ta kamar wa yanda sukayo sata, a can, ?
Idon Meena ne ya ciciko da hawaye don takaici da bakin ciki a hankali ta duka gurin tana dan tattara kayan ta cikin kunan rai,
Duk wani abinda ya danganci abinda aka saya masu a Abuja gefe guda Meena ta ahe wanan abin
Inda ta tattara yan kayan ta dama ba wasu shirgi ta tafidasu masu yawa ba don haka tamike tabar gurin
Meena na shiga sashen mahaifin ta wanda aka kewaye da dan guntun katangar jan laka,
Sai yar rufa ta kara wanda akayi tankar barandan kwano inda suke shan iska,
Dakin da take zama da yan uwanta can ta nufa a cikin bacin rai,
Kan,nen ta da sukaje tare sune ke fadawa mahaifiyar su cewa mama ladi ta budewa Meena kaya tana bincike ga maman Murja can ta na fada akai,
Duk da rayuwan mama Saratu ya baci amma sai ta kan,ne a cikin zuciyar ta kawai,
Daga gurin da take tsaye ne take wa yar nata fada akan to may zai bata mata rai har ta,shiga damuwa kamar wace bata san may ake a ciki ba,,
Mama ni ba fushi nake akan kayan ba yadda dai mama ta watsar muna da kaya a tsakar gida tana tone tone tankar munyi sata acan,
Baba Samaila ne ya shigo gida da murnan shi don ganin yarsa da yake ji da ita ta dawo, gida lafiya,
Bakin Baba Samaila har kunne don murna sai,dai kuma a irin halin da ya samu yar nashi a ciki sai murnan ya koma mai ciki,
Ladi ladi ladi Allah dai ya shirye ki abinda Baba ya iya furtawa ke nan a lokacin,
Ina kike Amina, ?
Gani Baba ko Ladi takawo maki kayan nan kada ki fara ki karbe su kin ji ko,
To Baba inji Meena cikin sanyin murya ta ansa wa mahaifin nata,,,

***** ****** *****
Mama Ladi bayan ta gama fada da mahaifiyar murja wace tai ma mama Ladi tas, kuma ta dauki kayan yaran ta tafi da shi cikin gori,
Sai a lokacin ne idon ta ya bude inda take neman jakar kayan Meena don ta mai da kayan nata ciki,
Samira ce ke fada mata cewa ai Meena tazo ta dauki kayan ta ta tafi tun dazun,
Idon ya kai gurin kayan da ta,zube kasa wanda dan ta Abubakar ya,sayawa su Meena din, a matsayin tsaraba,
Cikin tsawa tace wa Samira ta kwashi English wear takaiwa Meena ta bar mata turamen zannun ,
Center carpet da sautan kayan da ya aiko wa malam tsoho tana so , asa mata su a cikin daki,
Samira tace amma mama yaya fa cewa yayi akawo wa malam tsoho su yasa guda dakin shi guda kuma ya aje a waje gurin da yake bada karatu,
Shin wai Samira ke ta kin ka haihwa min mai sunan malam ko niya,?
Kayan Meena Samira ta kwasa don ta kaiwa yar uwan nata,
Sai dai tana shiga Baba Samaila yace Samira ta koma da kayan tace wa mama a bar su kawai, Meena ta gode don bata cikin ragga,,
Samira tana fada,wa mama sakon Baba samaila sai cewa mama tayi mahaukaci kawai,
Alluran sojan na ya motsa mai hita batune don rigima shika so,
Kaya dai na amshe su bashi kuma da wadda zai yi da ni don dana yai gaba ko ,
Shehu ya roka muna Allah ya amsa muna,
Abinda dawiwa shikai ya kwasa tunda ba shi iya sai mata irin su,

Washe gari tun da safe aka tashi da gyaran dakin mama Ladi inda aka shimfida mata carpet din da ta mamaye,,,
Sauran sakon mutane kuma sai wanda ta ba don son ran ta,
Meenat ko tun daren jiya tasawa kan ta hakkuri akan kayan nata badon komai sai don irin wanan cin fuskan, da mama Ladi tai masu ita da mahaifanta,
Don haka ranan shirin komawa sokoto ta yi ni dashi don duk wani abin da za,a bukata na tafiyan ta baba ya shirya mata su tsab,
Washegari tun da Safe tabat garin birnin kebbi zuwa Sokoto,
A cikin shirin ta ta tafi sallaman malam tsoho wanda a lokacin har yafito majalisar shi ko yana dan kishi gide yana lazimi a hankali
Inda yaji sallamar jikan nashi da sauri yadago kai yana kallon ta cikin mamaki, ya ce,
Amina badai tahiya zaki yi yau ba da dawowan ki baki ko huta ba, ?
Dauri ki bari wani sati ke ga sai ki shi makarantan ko ?
Meena wace take kokarin gyara jakar hannun ta don ta durkusa ta gaida tsohon tace,
Malam walleh ban tsayi kaga an, wuce ni ga karatu kusan sati biyu ke nan,
Me nika tsayawa yi gida in tai in isko notes da yawa,
Malam tsoho yadan kada kai cikin jimamyn zancen jikan nashi ya na kokarin tura hannu shi cikin aljihun wando shi
Yace to baku kun,katai birnin taraiyya kun kai ,zaman ku ba, ?
Hmm inji Meena wace ke duke a gaban tsohon kakan nasu mai farin gemu,
Ta,ce malam ko ni an bazama munkayi ba mata tai ta a bata da lahiya shina mun ka tsaya har taji sauki,
Subbahanallah halan missa may ta inji malam tsoho ya na tambayan jikan nashi cikin son jin karin bayani,
Walleh malam ban sani ba yadda dai niji suna hwadi shi na wai duk wata haka takai,
Mika mata kudin da ya ciro daga aljihun shi yakeyi ya fadin i maza ki boye tun yan sa idon ga ba su tai ciki hwada ma uwayen su ba,,,
Meena takarba tana cewa ta gode inda tabi umurnin malam tai sauri ta tura kudin cikin jakar hannun ta,
Tambayan ta yayi da cewa to Amina an, nan da sokoto shina ki kai wanga sakko haka?
Kafin taba da ansa daya daga cikin yan rakiyan ta yaba da ansa da cewa,
Don tana son kafin ta shiga makaranta ta dan tsaya gidan uncle din ta, ta, huta,,,,,
Tsohuwar motar akori,kura na Baban ta shine za,a kaita tasha daahi suna tafe hayaki na tashi motar na wani kara, booooooooooo,,,,,

***** ****** *****
Lokacin da duk ake wanan zancen Baba Buhari baya gari sai da ya dawo ne ya samu labari gurin kishiyar mama Ladi din,
A cikin bacin rai ya nufi gurin da mama Ladi take a bakin murhu tana tankaden garin dawa na tuwo ga karkashi a gefe guda wanda ta gama gyarawa zatai miya dashi,,,,,
Ladi, ke wace irin mahaukaciyan mata ce wai,
Shin ko kauyan cina har yanzu ka cin ki na ladi ko rashin mutunci irin naku Ginbanawa ka da mun ki,
Sai a lokacin mama Ladi ta dago kai ita ma a cikin masifa take don ta riga ta shirya akan wanan zancen ,
Don bazata dauki wanan rainin ba a dinga zuwa cin arzikin Dan ta kai tsaye,
Ita kan sam ba zata yarda da hakan ba sai dai duk wani sako ko aike yazo ta gurin ta direct ki kuma taba wanda ranta ke so,,,
Malam shin sau nawa kake son in fada maka cewa Dan ga dai dana ne ba wani na ya haifa min shi ba,,
Sakona ina so don haka sai a jira wani ko ?
Takare she zancen cikin muguda baki irin na mata kauye,
Tare da dukawa gurin murhun ta don ci gaba da aikin girkin da takeyi,
Tsaye Baba Buhari ya yi cike da mamakin irin wanan karfin halin na mama Ladi da kuma rashin kunya,
Ya san cewa idan ya tanka a lokacin za, ayi batatta don haka ya juya direct zuwa gurin mahaifin shi,
Don ya sanar dashi saboda malam tsoho yai ma duk diyan shi shamaki akan saurin daukan mataki ga iyalin su,,,,

****** ******* ******
Anty Meena


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login