Showing 99001 words to 102000 words out of 388021 words

Chapter 34 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8272

kurullah,
Mai dauke da tsana da kuma kishi mai zafi a idanuwan su,,,,
Kujera nake nuna masu still a cikin sakin fuska ina cewa bisimillah kuzauna,
Duk da falon a tsabtace yake amma sai nuna kamar suna jin kazan tan mu,
Ruwan gora nadauko masu acikin fridge masu sanyi nadora a saman turen, silver golding,
Ke ce Amaryan gidan ko ?
Ban basu amsa ba sai dai yar murmushin da nayi kawai,
Ina wuni nace masu alokacin da na koma saman daya daga cikkn kujerun falon,
A lokacin ne dayan su ke ce min maigidan ko yana ciki,
Acikin sakin fuska nace masu eh yana ciki,
Ok yi muna sallama dashi please ?
Nace tau acikin rashin nuna ko in kula, don dai banga abinda yayana zai yi da irin wa yan nan ba,

Ina tashi gaba dayan su sukabi bayana da kallon ban ko yi nisa da su ba,
Suka fara zance akaina, very young,
Bari ke dai wanan na kusa haihuwar ta ma ai lalai ashe akwai aiki,
Hadi wace bata ce masu komai bane sai yanzu tace amma da alaman yarinyar simply ce,

A hankali na tura kofan dakin tun daga kofa na hango shi a kwance rigingine saman gadon shi,
Hannun shi dafe da goshin shi, zuwa fuskan shi,
Idon shi suna a lumshe tankar mai barci, a lokacin ,
Ganin yanayin kwancin shi yasani juyawa don in sanar masu cewa yana barci,
Juyawa nayi don in koma falon ,
MEENA naji ya fadi a cikin wani irin murya mai ya nayin kasala,,
Saurin juyowa nayi ina kallon shi, still yana kwance kamar yadda na samay shi da farko,
Cikin dan daurewa tare da nuna dan rudewa nace bakine falon suke jiran ka,
Sai alokacin ya sauke hannun a saman goshin shi,
Ya sako min idon shi da sukai mai jawur alokaci guda,
Fuskan shi dauke da mamaki yake tambayana waye yazo ?
Kaina aduke nake cewa wasu matane su uku, su kazo,
Mata kuma ya tambaya cikin mamaki,
Na daga kai a hankali alaman eh,
Tashi ya yi daga kwancen da yake, ya yar tsuki da alamar antakura mashi dai,
Juyawa nayi zuwa falon yana bayana cikin tako irin na gajiya,
Aninin rigarshi ta sama a dan balle, fuskan shi adan ya mutse,
Ganin irin yanayi da yaya Abubakar yafito ni kuma ina ta gaban shi muna saukowa daga steps din,
A take Salawatu ta anyana zuciyar ta cewa shiga dakin gurin yayana har munyi wani abu dashi,
A cikin mamaki, yake kallon su tun yana saman steps din,
Da yar fara,a dauke ga fuskokin su daga shi har su, yake ce masu surprise visiting ?
Dariya suka kama yi atare suna cewa muna zancen zamu zo har gida muyi ma murna, bamu samu time,ba
Shine yau dai mu kace bari mu rako madam tazo har gida muyi ma murna biyu ke nan ko ?
Ga Amarya ga kuma karin girma,,
Murmushi naga yaya ya yi don jin dadin abin da suka ce mai,
Inda nake tsaye dan nisa kadan, dasu ina kokarin, kauda, remote din de a saman wani kujera,
Yaya Abubakar yake ce min Meena kizo ku gaisa da next Amaryana,
Azaton su zan yi wani sad re,action, ko shock amma sai sukaga ina dariya da murna na,
Nace a ashe Anty na ce tazo gidan ?
Yaya Abubakar yace min zo ki zauna ku gaisa yana kokarin nuna min gefen saman kujeran da yake a sama,,
Ba musu nazo na zauna yar fara,a na ina cewa, ashe amaryan yayana ne ban sani ba,?
Mamaki na ba su sosai karama dani wai na iya barkadon manyan mata,
Kira Sadiya su gaisa yaya Abubakar ke bani umurni da hakan,,
Mikewa nayi zuwa kiranta ida suka kara bin bayana da kallo gaba dayan su har maigidan,
Sauke idon shi da ajiyan zuciyar shi yai daidai a cikin na Salawatu wace duk kishi ya turnuke ta alokacin,
Murmushi irin mai kashe jiki ya sake mata, oole bata san lokacin da ta mayar maida irin murmushin ba,,,
Bayan na fada mata cewa yaya yace tazo su gaisa da baki a falo,
Inajin lokacin da tai tsuki alaman an damay ta fa,,
Nadawo falon ina cewa barin dauko maku abinci ko ?
No, No ,No ki barshi kawai we are ok ?
Anty Sadiya tafito fuska adaure babu walwala kamar kullun,
Ganin su yasa ta kara daure fuska tana cewa au, ku ne ma, ?
Shine tace wai baki,
Sun gaisa sama sama da ita suna mata wani kallon raini,,
Basu wani dade ba su kace za su tafi,
Na ce tun yanzu ku kuwa aida kubari dan anjima mana,
Kudi Lubuna ta debo daga cikin jakar ta tanacewa to amarya gashi kiyi hakkuri da su ba yawa mun sayi baki dai ko?
Gaskiya bazan karba na ce ai,kozuwan da kukayi ya wadatar, don mun gode gaskiya,
Haba dai ki karba mana kada ki raina please, ko bakiyi farin ciki da zuwan mu bane,?
A,uzubillahi mina,shedanin, rajin nafadi azuciya na na karba da Bissimillah,
To wacece Anty nawa ne wai na tambaya alokacin da suka mike tsaye don tafiya,
Dariya sukayi ba tare da sun nuna min ita ba,
Harkofan fita falo mukai masu rakiya dukkan mu har may gidan
Wanda a tare suka fita waje dashi yana masu rakiya,

****** ********** ******
A gurin da na sallamay sallah magrib nake zaune ina addu,a,
Tunane na keyi na matan dazu da yaya Abubakar yakira da wai wace zai aura,
Wanan ai duk manyan matane,
Babu tamtama sungirmay mu har shi, don babu warin shi aciki,
Mamakin may yagani agurin da har ya jashi haka ?
Naja yar tsuki nace kai namiji, ina cewa Anty Sadiya ta tsofe min ashe ga mamawo nan shigowa,
Gaskiya ni kan tawa ta samay ni zama cikin manyan mata,
May zan gane anan ?
Dawani zanjine wai,?
Allah ka kawo min dauki, ya Allah,
Banniya koda motaswa ba daga inda nake zaune takure, saboda damuwan da na shiga,
Kudin da suka bani yana zube saman gadona ina jiran maigidan ya dawo in kai may,
Don nasan cewa idan an ma alheri ta hanyan mutum to yakamata kaba shi sai in shi yace bai so,
Da farko anty sadiya naso inba kudin, amma sai naga bayan rakiyan da mukai masu ta wuce cikin part din ta da karfi,
To shi yaya Abubakar bai ko jin nauyin fada muna cewa wai matar da zai, aura ce haka ???

Munazaune falo da daren kamar yadda ya umurce mu da yi duk dare,
Tv ke ta aiki inda dani da Anty idanuwan mu su na kan TV,
Yaya Abubakar ya na daga duke saman laptop din shi ya na duba sakon ni, ciki,,,
Yan dubu dubu ne guda ashirin sabbi fil da su sai kamshin banki su keyi da na turare,
A saman dan table din da system din yaya yake na aje kudin a gefe,,,
Da sauri yadago kai yana dan kallo na,
Na may ye kuma nace kudin da suka bamu ne dazun,
To aike su ka ba bamu ba ko ?
Gefen da Anty Sadiya take zaune nadan waiga ina kokarin mika mata kudin,
Ki barshi kawai tunda ke suka ko ?
Ban iya cewa komai ba don irin yadda naga tayi da fuskan ta,

Gefen kujeran da yake naga yafito da wasu kudi masu yawa, a hannun shi,
Duk lokacin a takure nake don dai ni wanan zaman falon yazama min zaman takura gaskiya,,
Kirga kudi naga yanayi, sai da suka kai yadda yake so sai naga ya mikawa Anty Sadiya,
Sauran kuma ya miko min yana cewa kowa tasai abin amfanin ta dashi ,
Kudine masu yawa koda ban kirgaba sai da naji tsoro,
Ya dan kara dago da fuskan shi yana cewa zan samu wani driver ya kai ku kuyi sayayyan ,,,,
Kudin nake kallo a hannu na kara juya su cikin mamaki waini Meenatu yar Baba keda wanan kudin da sunan nawa hallal malal,,,,


ZEEE MAKAWA YELWA
[7/31, 9:29 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
4? 0?

ZAINAB IDRIS MAKAWA


ALLAH-AL-HAKAM


Assalamu Alaikum yan uwa musulmai, ku taya mu adduan ga yar uwar mu masoyiyar mu,
SAFIYA ABDULLAHI HUGUMA , marubuciyar WAYASAN GOBE,,, DA DAN GAN,TAKARZUCIYA,,,
Ta haifi diya mace yau sai dai munyi missing din lovely BABY Din namu,
Allah yajikan ta yai mata Rahama,,,,
Ita kuma Uwar Allah ya bata lafiya,,,,,=?O?=?O?=?O?=?O?


Tafiyan babu maihafin yaya Abubakar babu nawa mahaifin a ciki,
Daga Baba Musa sai Baba Shaibu da Baba Hamza sai Baba Wadda, sai kuma malam Jibrin ladan, sai dai a hikima irin ta malam tsoho sai yace yayana Ibrahim ya zo a madadin Baba na,
Wanan abin yan gidan mu basu ji dadin shi ba sosai,
Saboda muna da uban nai da ba su zo muna dakuma manyan yayye da basu zo ba,
Amma shine za,ace wai Ibrahim yazo, bayan gasu su ma sunan son zuwa,
Mama Ladi a ranan kamar tayi ihu don dai kawai anfi karfin ta ne,
Don har aike taiwa diyan ta dake aure a cikin gari mata suzo tana neman su,
Cikin tashin hankali suka iso gidan don su azaton su wani abune yafaru,
Cikin muryan tashin hankali ta zaiyyana masu komai,
Anty Safiya ce ta katse ta da cewa to Mama don iyayyen maza sun tafi gurin yaya Abubakar shine kuma abin ya da hankali,
Mama irin wanan abin shine fa ke kara sa yaya bai damu da kowa ba a cikin dangi,
Ke rufe min baki Safiya wani lokaci saboda irin halin rayuwan ki ke da samira sai nake ganin kamar bani na shayar daku nono ba,
Ida asibiti na haife ku da sai ince ancanza min ku ne, don sam babu inda kuka biyo ni,
Anty Samira wace ke ta fama da laluran cikin ta ta ce, Mama,
Wanga zance ma in har wani taji ta aikunya zamuji
Duk mutumin da baida yan uwa aduniya ai ba kowa bane,
Shege ma yana da dangi balle mai iyayye haka kamar yaya Abubakar,
Walle da nasan kan wagga managa aka kirana da ban zo ba,
Inkin hana yaya ya turo wa iyayyen mu alheri ai ita Sadiya naga tana aikowa nata yan uwan,
Kuma suna zuwa suma su ci arzikin su dawo,
May yasa baki hana su ba,?
Sai,kadan daga cikin diyan nata ne suka dan mara mata baya da cewa wai harda Ibrahim shim ?
Lalai yanzu sun samu guri ke nan?
Indai Sadiya na ai Meenatu bataga gidan zama ba,
Don Walleh turo waje zatayi,
Wanan ka zama da kishiya, ?
Basu dai gane komai ba tunda bazasu iya hana abinda malam tsoho ya kulla ba don ba wuri,
Don shi bai wasan jika da kaka da yara sai in ya so hakan,

****** ********* ******
Washegari na tashi duk jikina yana min ciwo saboda yadda yayana ya tafiyar dani a gado daren jiya abin bai misaltuwa,
Don har tsoro yabani irin yadda naga ya koma kamar wani tsohon driver da ya samu sabuwar mota,
Sam yau banda kuzari a jikina hakan ne yasani dan kwantawa,
? gurin da nai sallah asuba anan barci mai nauyi ya dauke ni,

Bayan su baba sun kamo hanya ne, Baba Wadda ya bugo mai waya cewa gasu a hanya,
Bai so zuwan su ba acikin ran shi don mutum ne wanda baya son takura ko kadan,
Kuma bai saba da irin haka ba kayi baki suzo maka da yawa,
Yayi tunanen to zuwan su may zai karashi da shi inma murna ne ai sun mashi a waya ya isa ko,?
Kai malam tsoho badai rigima ba,yanzu haka shi ya daukan masu shatan mota yasan da kudin shi,
Malam malam yace acikin zuciyar shi wanan tsoho da yayi ilimin zamani da ai san yaya zaiyi ba don wayo da hikima,
Lumshe idon shi yayi tare da dan murmusawa don tuna wa da Meena a daren jiya,
Bai taba samun daren da ya rayashi cikin jindadi da walwala ba irin daren jiyan adakin shi da Meenatu,
Gaskiya malam tsoho ba karamin gudun mawan rayuwa yai mashi ba anan,
Dan zaman yarinyar nan a cikin su, a iya kwanakin da tayi atare da su,
Yasa shi gane cewa mace wani rahamane ga da namiji so sai,
Yarinyar nada wani bawai na bam mamaki a tare da ita sosai,,
Dan rufe idon shi yakarayi yana tuno abubuwa akan ta da dama,
Barcine yai awon gaba dashi a cikin irin tunanen,da yake ba tare da ya sani ba,
Don shi ma yana jin gabobin shi ba lakka a lokacin yana bukatan dan maimaita barcin,
Ya kai dan wani lokaci yana barcin shi hankali a kwance ya farka ,
Ganin irin harzuwa lokacin safiyane yasashi mikewa

Su biyar ne chur su ka, kamo hanya tare da tsaraba irin kayan amfanin mu na gargajiya, daga gurin mahaifana, da malam tsoho,
Sai dai duk gaba dayan su a motar sai tsan mani sukeyi idan sunzo gidan yaya Abubakar za su samay,ni a rakube gefe guda,
Ko kuma acikin rashin walwala da kuma rashin sakin jiki
Don a cikin su ba bu sa,a yi na dole in koma abin tausayi acikin su,,
Babu dai irin zancen da basu nasawa zukatan su ba akai na,,
Saboda, a ganin su ban kai matsayin da zan zauna a cikin jin dadi gidan dan uwan nawa ba,

Ina farkawa naga rana yayi sosai a lokacin abinda ya sa ban damu ba saboda yau ya kasance weekend ne,
Babu zancen zuwa aiki a gurin yaya Abubakar sai dai idan yana da wani uzuri a can din,
Wanka na shiga bayan na fito ne na zauna na gyara jiki na cikin wasu atamfa zani da riga,
Ina kokarin daurin dan kwali ne yaya shigo dakin yake ce min,
Wai su Baba Musa suna hanya tare da sauran yan uwa,
A yadda na fahinci fuskan shi duk da dama rashin walwala dabi,ar shi ce hakan,
Amma na hango rashin jin dadin haka a tare dashi sai kawai naji banji dadi ba
Don dai nasan cewa wanan tafiyan tunda nashi ne da wuya idan babu mahaifina aciki,
Kamar in tambaye shi may za ai masu sai kawai na share shi don inga iya gudun shi,
Kokarin fita ya keyi daga dakin nawa, nace mai a hankali don Allah yaya ina son in da shiga gidan Maman Bi,u in bada sako,
Juyowa yayi tare da dan tsura min ido kamar zai yi magana, sai kuma ya juya yana cewa kada ki dade please,

****** ********* ******
Maman Bi,u ne da Fattu a zaune tsakar gidan su, suna gani na suka shiga washe baki,
Nagaishe su inda nadan rike hannun yaron Fattu ina wasa dashi,
Gurin da Fattu take zaune nake kallo inda nace mata nazo ne don Allah idan Hamza yana gida ya sayo min sako a kasuwa,
Ban boye masu ba naje sheda masu cewa mahaifan mune zasu zo daga gida taya maigida murna,
Maman Bi,u ce ke tambaya mu yan uwa ne da mijina nan na sheda masu yadda muke da shi,
Itace da kan ta tabani shawarwn abinda zan sayo ai masu kafin su iso,
Naji dadin hakan sosai don dama Anty amarya ta fada min cewa uwar daki da?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? tasan ciwon kan ta ke karasa mace hanya nagari,
Ba uwar dakin da zatai maka wayo ba tadinga cuta maka,
A tare da fattu muka koma gidan mu, ida muka fara masu girkin na taron bakin mu,
Hamza wanda nake cewa Babana shi ne yai tazuwa sayo muna duk abinda muke bukata,
Sai musalin la,asar suka shigo gari inda duk na rasa yadda zanyi saboda murna,
Basu shigo ba sun tafi yin sallah a massalacin unguwar mu,
Kafin su zo mun gyara masu dining table yadda zasu wallah,
Sai a lokacin yaya Abubakar yadawo gidan cikin yar rudewa yana cewa wai ya tafi kai mota service ne sai kuma ya tafi gidan abokin shi,
Ganin irin yadda na aiwatar da komai yasa shi dan tsayawa da mamaki a fuskan shi,
Don da farko har ya fara cewa, to gasu sun iso yaya za,ayi da abinci don yaga agajiye suke,
Sai idon shi yai arba da kulolin roban da na bawa Hamza kudi ya sayo min da rana,
A hankali yadinga budewa, abinda yagani a ciki ne ya bashi mamaki,
Cikin mamaki yake kokarin magana amma sai mukaji sallaman su shigowa, ciki,
Da murna nake masu sannu da zuwa, inda, suke ta kokarin kallon yadda nake
Gwiwa bibiyu a kasa na kai ina masu sannu da zuwa,,
Amina ke ta kezam mutane Abuja da, da ko


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login