Showing 339001 words to 342000 words out of 388021 words

Chapter 114 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8224

Mama tana cewa yajikin ita Amina kuma,
Sai da yadago kai ya dubeta sanan yake cewa tasamu sauki sosai itama don tafara warwarewa yanzu,
Anty Mariya daga gefe tace Allah dai yaba ku lafiya gaba daya,
A hankali Mama da zata kai lemo abakin ta ta amsa da fadan amin,
Hira suke yi na mutanen gida inda suke tuna wasu abubuwan da ya faru a baya,
Baba Wadda wanda ke daga gefe guda yana dan fuskantar wayan shi yace amma idan Meenatu zata haihu wanan karon anan zamu tsaya ayi suna ko?
Cikin wani irin murya Mama take tambaya ita Amina shin ciki na gareta kuma,
A,a Mama ?
Inji Anty Mariya tace wane irin tambayana haka shin,,
Shiru tayi batare da tace uffan ba sai sai hira ake amma ita bata samu abinda ta furtaba again,
Iyanzu ya fahinci cewa akwai wani shiri na makirci a tsakanin, Salawatu da Fatima wanda yasan bawai wani shiri bane na alheri su ke yi,,
Tsakanin Sadiya da Meenatu kuma akwai dan alaka amma ba mai tsawoba don kowa a dakin ta take zama sabanin irin nasu Fatima da Salawatu,
Amma yasan cewa ajuri zuwa wanan tafiyan ba mai dorewa bane,
Ranan da suka tabbata da zancen cikina a ranan kamar zasu yi hauka,
Salawatu tace wai kina nufin cewa wanan yarinyar cikine ta samu ma wahal da ita haka dama,
A take idanun Salawa ya juye lokaci guda tankar mashayiya,
Wai da gaske kike Fatima wanan labarin kodai wasa, ne wai don ni abin yq fara bani tsoro wallahi,
Fatima wace ita,ma ranta a bace yake a lokacin, cikin hasala take cewa, ni ba yau ba nasan makircin yan uwan Bukar sam basu kaunan suga bare a tare da su,
Salawatu dai barin gurin hiran tayi don yau duk a jagule take bata jin ta daidai ta rasa may ke mata dadi, a ranta,
Gidan Lubuna ta nufa a cikin bacin rai can taje da tashin hankalin ta, duk ta dagawa kanta hankali,
Ita ko Lubuna sai cewa tayi amma wanan Meenatun yar yawace yanzu ita kamar ta big chika zata tsaya tana wani yin ciki har kurkusa ma haka,
Wani irin harara ta watsa ma kawar ta tana cewa wallahi ke wani lokaci banza ce ana zancen gaskiya sai ki tsaya ki na shirma,
Haba Salawat ki duba fa ki gani dubi irin, yadda yarinyar nan t hadu ta koni
Ganin yadda hankalin aminiyar ta ya daga yasata yin serious cewa, yanzu sai mun shirya mutafi can cikin Masaka akwai wani sabon shigowan malami,
Wanda zamu shiga gurin shi don mutabbatar da cewa cikin yafita ko kuma ya sanyadda zai yi da ita,
Salawatu taji dadin wanan shawaran na aminiyar ta sosai don haka suka aje ranan da zasu tafi Masaka gurin malami,
A guje ta jawo mota zuwa gida ranta a bace duk ta rasa may ke mata dadi a ranta,
Ita ko Lubna wani irin haushin Meenatu taji duk wani plan da tanadi da take a kan jan ra,ayin Meenatu sai taji kawai tayi watsi da shi yaushe wanan Yarinya karama zata zauna taita haihuwa time to time irin haka,
It means bata da lokacin kan ta again sai na family kuma, don haka taja dogon tsuki tana cewa banza kawai,
Yarinya may zaki gane a gurin maza banda haihuwa dama may suka sani suka iya da zaki tsaya bata kan ki agare su balle wanan busurun mijin naku wanda ya tara mata a gida kaman zai kaisu kurmi ya yasayar,
Haka tai ta fadan haukan ta ita kadai a gida kaman wani ya sata ko ance tayi, sai kuma daga karshe haushin Salawatu ya zo mata duk tabi kanta ta susuce gana miji guda haka,
Sai kudin ta take narkawa a kanshi wai kawai don ya so ta amma abu ya gagara da farko dai sunyi nasara samun kan shi har ya auri Salawa din amma yanzu duk ya birkice masu duk wani hari da suke kai mai kamar sun shuka dussa ne,
Ita kuma Salawa din taki yarda ta hakkura da zancen shi ta manta da sha,anin shi duk da tace wai, sugar man ne shi,

****** ********** ******
Zaune yake a back yard din gidan yana shan iska don su Mama suna a falon zaune da mariya sai Maman Biu da tashigo gurin su, Fattu kuma muna daki zaune da ita muna hira,
Waya Fatima ta gama da mahaifiyar ta duk da Mama ta yi bata hakkuri a cikin wayan bai sa ta bar zancen ba,
A hargitse ta samay shi yana zaune yana shan iska sai dai aiki yake a system din shi yana kuma jin dadin yanayin garin na yau,
Bai yi aune ba sai ganin ta yayi a gaban shi ta zauna saman kujeran dake fuskan tar shi,
A hankali ya dago kai yai mata kallo guda ya mai da kan shi yaci gaba da abinda yakeyi,
Yagane cewa da masifa tazo ma ahi yau ma don haka yasaka a ranshi cewa zai maganin ta,
Muddin tarin rikicin da ya hango a tare da ita ba mai ma,ana bane kamar kullun tau zai ma tufkan magani,
Babu alaman firgici ko wani sauyin yanayi a tare dashi yaci gaba da aikin shi kamar yadda ta samay shi, yana yi da farko,
Zaune take a cikin huci batace kala ba sai cicika da take yi daga zaune hannayen ta suna a harde da junan su,
Da karfi takira sunan shi cike da tari bala,i da masifa a cikin kiran,
Abinda yasaka ahi dan dago kai kenan daga abinda yakeyi ya watsa mata harara acikin idanuwan shi da suka rine sukayi jajir,
Ance Meenatu wai ciki gare ta again, ?
Wani irin mamaki da kuma tsanan Fatima yadira mai a rai lokaci guda,
Dan murmushin takaici ya sake tare da cewa baki tabbatar ba ma kenan don kwankwato kikeyi ke,
Yaja system din nashi gefe guda yana fuskantar ta yace idan har kinji ne baki tabbatar ba sai ki kkoma gurin wanda ya fada maki ki kara tambaya ko yaya zancen yake,
Fuskan ta ta tsuke tare da gyara zaman ta tana cewa watau ma da gaskene kenan, Cikin ne da ita,
Shima kallon ta yayi acikin daga mata gira yace yes of course cikine da ita fa,
Ashe labari ya iso gareki haka da sauri ban yi zaton har zakiji shi da wuri haka ba,
Tashin hankali sai duban Abubakar take a cikin mamaki, don a lokaci guda sai ya juye mata, tankar ba dan Bukar din taba da suke shan minti a tare,
Tashin hankali take shedan ya kara zuga ta inda idon ta ya rufe, tafara fada mai magana tana cewa,
Tun da Meena tafi zaki da gardi ai dole kai ta dura mata ciki ita kadai acikin mu, don itace kawai kakake gani da idon mata,
Wata fi iya haihuwa da za,ace mu na zaune itace matar haihuwa muko matan jindadine kawai,
Tsab taga ya mike tsaye ya tsaya a gaban ta yana kallon ta a cikin firgitattun idanuwan shi da suka juye a lokaci guda,,
Hannayen shi ya saka a aljihu yana cewa cikin girgiza kai ,
Idan ke jahilace kin mata Allah ne ke bayarwa a duk inda yaso yaga dama kuma toni ban mantaba,
Don haka tunda dadi kike bani daga yau na daina shan dadin a gare ki kije na sake ki saki daya,
Dif, taji wani wuta ya dauke mata tankar bata numfashi ido waje take kallon shi,
Cikin taba kirjin ta da dan yatsa, tana cewa Bukar ni kace wa wanan kalman,
Wani shu,umin murmushi ya sake, tare da dan ware hannayen shi biyu, yana ce yes of course, na fada maki bake bama duk wata mace da ke son kawo min fitina a cikin rayuwana haka zan mata ko wacece ita din,
Na shiga uku ta fada da karfin tare da sulalewa kasa takai durkushe sai kawai ta saka kuka a lokaci guda,
Yaya Abubakar yace wait Fatima kada ki tara min mutane da wanan kukan naki, don koma may ye kece kikajawa kanki,
Daga haka ya juya a sukwane yabar gurin cikin bacin rai da tashin hankali,
Gidan ya bari gaba daya a lokacin bai tsaya ciki ba don bai son sauraren irin kuka da, Fatima ke gumzawa ,
Ita ko Fatima ba kunya ta shiga gida da kukan ta tana share hawaye cikin tashin hankali,
Wayar mahaifiyar ta takira acikin kuka takasa cewa komai sai kuka take sharbawa cikin tashin hankali,
Wai may ke faruwane haka tunda safen nan kin kirani kin kasa magana sai kuka kikewa mutane,
Da kyat ta iya bude bakin ta tace acikin wani irin murya mama ya sakeni ne ,,,
Kalman Innalillahi uwar ta iya furtawa ciki, tashin hakali itama uwar kuka ta saka a lokaci guda,
Cikin kukan take cewa shike nan Fati kin kaiga yadda kike so yanzu ai sai ki dawo ki share dakin ki na gado ki zauna,
Kukan da uwar ke yi yakara tayar wa Fatima da hankalin ta sosai don tasan cewa da biyu take wanan kukan,
Mahaifiyar nata bata iya cewa komaiba sai kashe wayan tayi acikin tashin hankali,
Uwar na kashe wayan ta kira layin Aliyu acikin kuka take zayyana mai abinda ya faru, a cikin tashin hankali kuma,.
Ya tambayi ko may ya kawo sakin amma sai maman tace itama bata tambayi dalili ba,
Aliyu cikin bacin rai yace ai ta huta saita dawo ga gidan nan ai ta zauna,
Dama ai bata san kowa ba ita kanta kawai ta sani sai yayan ta,
Uwar tace yanzu duk wanan bashine abin yi ba kawai asan yadda za,a gyara kafin tadawo nan
Yace yaji zai kira Abubakar ya farajin abinda ke faruwa tukun kafin ayi wani abu akai,

****** ********** ******
Yana barin gidan Lawal ya dauka suka fita tare duk da bai iyacewa komai ba amna ahi Lawal ya fahinci cewa maigidan shi ba lafiya yau,
Wayan shi da aka kira batare da ya amsa ba ya kashe wayan gaba dayan ta,
Sai fama zaga gari su keyi batare da sunje wani wuri na takamaimai ba,
Azuciyan shi yace ashe abinda yasaka Meenatu boye min zancen cikin Amir ke nan a lokacin can,,
Yanzu ashe don jahilci da bakin kishi har mace zata iya rufe idon ta tace wai an wa yar uwar ta ciki ita anki yi mata cki,
Don kawai tsaban kishi da hassada, tare da sawa kai wahala kawai,
Yanzu ita fatima har tana ganin wai tana bashi Bashi dadi ke nan ashe,
Ita bata san zaman hakkuri yake dasu ba itafa tausaya mata ya keyi don ya na tausayin mutuwan mijin ta sosai wallahi,
Gashi kuma yayan ta shakikin aminin shine na kwara bana wasa ba, don har abin yazama masu zumunci,
Amma ita sam duk batq duban wanan reason din akan ta,
Tashigo mai gida da wasu akidodi marasa ma,ana marasa kyaun koyi,
Hannuwan shi yakai a kanshi tare da furzo iska don fitar da relief azuciyaer shi,
Yace a hankali a fili mace kamar jahila komai akan idon ta aikin jahilai,
Yanzu inba hauka ba wai Fatima tace yaiwa wata ciki ita kuma yaki, yi mata don kawai tsaban kishi da hauka irin na mata,
Shi may ya rage Fatima dashine wai irin yadda yake mata dawainiya aiko, Meenatu da ke yar uwar shi matan shi uwar dan shi batasamun hakana, agare shi,
Gaskiya idan ba wani ikon Allah ba bazai kara zama da Fatima ba wai a matsayin matan auren shi, kuma again,

Ramatu ce tashigo daki take ce min a cikin kashe murya uwar dakina yau gidan ina ga ba lafiya don naga maman Aina tana kuka a bayan gida ita da maigida,
Daga,ni har Fattu muka dago kai a cikin tashin hankali mu na hada baki gurin cewa harshi maigidan ke kuka,
Tace cikin gyara tsayuwan ta a,a ba hakana nake nufi ba uwardaki na,
Nakoma saman kujera ina maida numfashina tare da tambayan ta ko may tagani,
Ta, gyara tsayuwar ta nan ta kwashe duk abinda tagani a lokacin ta fada muna, kaf
Fattu tace kinji jahila ko kinji sherin kishiya ke nan yanzuma ashe shi cikin mutum ne mai ba?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? kashi ba Allah ba, ashe,?
Duk hankalina naji ya tashi sai nake kuma jin tsoron kada suce za suyi min wani mugun abu, nan gaba, a gidan
Amna sai na tuna da zancen Maman Biu da ?nty Saloon da suke ce min baiwane Allah yai min don za,a yi mugun hassada a duk lokacin da cikin nan ya bayyana a jikina,
Ashe ko da gaske,ne don gashi, ba,a kai ko ina ba Allah ya fara nunamin hassadan su, a fili,gareni,
Tambayan Fattu nayi dacewa yanzu Fattu matan nan ashe basu ko tausayi irin halin da nake ciki na ciki, daje jikina
Cikin dake kwararan wata biyu ke nan insha Allahu,,

****** ********** ******
Jinta shiru yau bata leko ba yasaka Salawatu bin bayanta don taga ko may ke faruwa a dakin ta
Zaune take akasa duk ta ya kuce tafita hayacin ta Idanuwanta suyi hulu,hulu don kukan da tasha,
Da mamaki Salawatu ke kare mata kallo tana kuma dan bin dakin da kallo,
May ke faruwa, ne haka wai,
Idanuwanta ta dago cikin qani irin yanayi na tashin hankali tana kallon salawatu dashi,
Nazone dama nagan ki shiru yau baki fito ba, dan Allah kifita babu abinda zakice min yanzu,
Don kin riga da kin hada min sheri ko badon kin ce mu tunkari Abubakar ba aida bazanyi wanan shawaran ba,
Itama Salawati ganin yadda Fatima zata wullakantata, tace don Allah dakata malama don kin samu har nazo, gurin ki shine zaki kama fada min magana,
Daga haka cacan baki yafara a tsakanin su biyu salawatu zata juya sai Fatima abiyu ta har zuwa kofan part din ta yadda kowa ke iya jin irin fallasan da sukeyi,
Gaba daya gidan akafito waje ana sauraren su, cikin tashin hankali,

Dawowan maigidan kena tun a bakin get yake jiyo muryan su acikin tashin hankali,
Ga mamakin shi baiyi zaton cewa zai dawo gida ya samu Fatima a gidan ba don sanin da yayi cewa tunda sanyi safiya yai mata saki,
Azaton shi zata wuce zuwa gida tunda akwai time da zai kaita gida, a ranan har ma su huta,
Sai gashi ya dawo ya samay ta a gidan suna ta tonon asirin a tsakanin su,
A cikin takon kasaita ya kara so cikin gidan yana cewa cikin daka tsawa may kike jira ne gidan nan ne wai,
Ke kuma Salawatu bazan so inganki anan tsaye ba inba hakaba yanzu zaki jonata ku tafi tare,
Sadaf, sadaf ta juya ta nufi hanyan zuwa part din ta, ta, zauna tana huci,
Ganin ta, tafi yasa shi kokarin juyawa zuwa hawa sama da dan gudu gudu, yana mai kyatawa,
Su Mama dake daga falo suka yi cirko cirko suna kallon ikon Allah don abin ya basu mamamki so sai,
Fatima takoma daki tana hade rai, da kuma kuftawa don bakowa yaja mata wanan sakin ba sai uwar anyi ance,
Salawatu datajiyo zancen taxo ta zungurata akan suyiwa mai gidan tujara,
Yanzu gashi ta wargaza mata farincikin ta da keep marta ga mji da mutanen gida



ZEEE. MAKAWA YELWA
[11/26, 9:59 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
9? 9?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH AL MUQSIT


A cikin dare su Aliyu suka shigo garin Abuja shi da Mama da kanin mahaifiyar su, malam Alphaga Musa,
Sun samu gidan kowa na part din shi ba wani abinda ya nuna masu sign din cewa akwai wani abu, daya faru,
Sai dai a irin yadda suka samu tarone a gurin matan gidan, bai masu dadi ba saboda ba wanda ya nuna masu murnan zuwan su,,
Daga Anty Sadiya har Salawatu da su ka samu a folo ba wani karbuwan kirki, da su ka samu a gurin su,,
Ganin bani falon ya saka mahaifiyar Fatima tambayan ina yar mulkin gidan naku suke, alokacin,
Ina can part dina tare da su Mama Ladi da Anty Mariya, duk da dai har yanzu ba wai akwai wani shirin kwarai bane a tsakani da Mama Ladi din, sama sama muke da ita sai dai ina kokarin jure duk wani abinda zata gwada min don kawai mu gama lafiya da ita,
Ramatu ta shigo muna da labarin zuwan su iyayyen Fatima acikin wanan daren,
Haka na daure jiki ba kwari na fita zuwa yi masu sannu da zuwa,
Aliyu yana falo da, dayan mutumin da suka zo, tare da Yaya Abubakar zaune nai masu sannu da zuwa, inda na wuce dakin Fatima wanda zan iya cewa tun dawowa na gidan wanan ne karo na biyu dana shiga part din nata,
A hargitse na samay su ita da mahaifiyar ta da alaman kuka su keyi a lokacin, don duk sallaman da na keyi a kofan falon su saida na kara matsowa gap da kofan shigowa sanan suka ganni a tsaye
Naiwa matar gaisuwan mutunci tare da tambayan ta mutanen gida suna lafiya,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login