Showing 270001 words to 273000 words out of 278032 words

Chapter 91 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1791

lafiyansu lau ,to sannan ne fa hankalinsa zai kwata.Hanan ma da taji ruky nada ciki nanfa murna a gunta kamar me suna Kuma ziyartar junansu Babu laifi.haka nan dai su ruky suke rainan cikin su gwanin ban sha'awa har yakai five months na Hanan Kuma yana 7 month.awannan lokacin Kuma AA Arab ya samu k'ira Abuja akan president nasan ganinsa .Baiyi musu ba ya ansa akan zaije d'in Amma kuma yace da Ruky zasu tafi Dan bazai iya tafiya ya barta taba.

Ita Kuma tace idan ma sun tafi taren ai dole ya tafi ya barta tunda ba tare zasuje wajen president d'inba yace yaji ya Gani shidai da ita zai tafi haka nan dai Babu yadda ta iya washe gari jirginsu ya sauka a birnin Tarayya Abuja da sukai Sa'a ma a viller ma suka sauka Saida suka huta sannan da Daddare AA Arab ya samu damar ganawa da president,suka gaisa cikin girmamawa president ya numfasa yace .

"Ahmad Aliyu Arab mun Jin jina da k'ok'arin da kai Hakan yasa muka ga ya dace da zamu baka muk'amin Daya dace da kai na Matsayin IG na k'asa tunda shi Wanda yake kai na yanzu Bai fi nan da 3 to 4 month ba yayi ritierd so shiyasa nida muk'arra baina muka zauna muka tattauna zartar da kai amatsayin Wanda zai gaje wannan kujerar ta AIG na k'asa".ya fad'a Yana kallan AA Arab.

Tunda president ya ambaci wannan maganar AA Arab yake kallansa Baya ko kiftawa .me suke nufi ne da bashi wannan babban matsayin haka .take yashiga duniyar tunani na Wani lokaci, maganar da president yay ne ya dawo dashi daga duniyar tunanin Daya tafi.president yace.

"Ahmad Aliyu Arab Bakai ce Komai ba?.ya fad'a Yana kallan sa.

AA Arab yay murmushi kafin yace .

"thank you very hugely sir! I really appreciate ".

President yay murmushi kafin yace .

"you deserve it more dear"sun dad'e suna tattaunawa president Yana ta Yaba Irin namijin k'ok'arin Dayay akan Abinda Babu Wanda ya tab'a Yi a k'asar bayan baban ruky sai shi ,kafin suyi sallama bayan ya kawo ruky itama tai masa godiya da sallama haka suka koma Kaduna.
Washe gari AA Arab yaje har gida ya fad'awa Abba da ummi sunyi farin ciki sosai tare da Taya AA Arab murna, washe gari AA Arab yaje har government house ya fad'awa governor shima ya Saka Masa albarka Sosai.haka nan suke rayuwar su cikin kwanciyar hankali kamar Babu gobe.......


A b'angaren ibrahim Khalil shima dai ya tafi k'aro karatu zuwa k'asar London inda itace k'asar Daya zab'a,Yana can Yana Karatunsa cikin kwanciyar hankali da nutsuwa.





07066508376________
'?Follow the Mrs Sarakies=؋? =?1? HAUSA Novel Channel channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VbBRj1D35fLuSHibdq1Y




*____JAMI'AR TSARO ____*



*____THE WOMEN POLICE ____*




*NA*



*____NAJA'ATU UMAR FAROOQ ____*



*____(MRS SARAKIES =؋?)=?1?____*



*Bismillahirrahmanirrahim*



______season two ep 1?? 0?? 6??


*Bayan wata biyu*


Alhamdulillah Allah ya sauki Hanan lafiya ta haifi d'anta namiji Mai kama da ubansa sak,Babu ta inda ya baro shi .ruky tana zaune a falor wajen k'arfe 9 na safe tana zaune akan kujera 2 seater ga cikin ta nan Wanda ya fito Sosai Dan idan kika gani zaki ce haihuwa ko yau ko gobe saboda girman cikin Dan girmansa ya yafi watanninsa Dan baza kice bama cikin watansa bakwai ba, Bata Dad'e da saukowa k'asa ba ,Dan ta baro AA Arab a D'aki ya koma bacci tunda baya samun bacci idan ba weekend d'inba ,yanzunma lallab'awa tai ta fito Batare Daya sani ba Dan ta gaji da kwanciyar shiyasa ta fito falon sama ta zauna tana duba wayarta.K'iran anty mufeeda ne ya shigo wayarta take ta saki murmushi Dan tasan K'iran me tai mata ba zai wuci na taji lafiyar taba da abinda ke cikin taba.tana picking taji Muryar Anty mufeeda na cewa.

"Auta ya kiki?".

Ruky tai murmushi tace .

"Lafiya lau Anty! Ina su mimie da dadynsu?..."ta fad'a tana murmushi.


Anty mufeeda tace .

"Alhamdulillah! kinji Hanan ta haihu da ASuba kuwa?". ta fad'a cikin farin ciki.

Ruky ta zaro ido waje ta saki murmushi har tana rufe Bakinta kafin tace .

"Ko kad'an banji ba Anty!,Da Gaske Hanan ta haihu".ta fad'a tana kasa b'oye farin cikinta

Anty mufeeda tai murmushi tace.

Wallahi yanzu Nima hanaf ya k'irani yake fad'a min wai Basu fad'awa kowa ba Saida ta haihu ko zuwansu asibitin ma babu Wanda ya k'ira wai yafison idan ta haihu saiya fad'a Dan kada ya ta-da hankulan mutane".ta fada tana farin ciki itama.


Ruky tace.

"Kai Alhamdulillah anty! Amma me ta haifa?".

Anty mufeeda tace .

"Namiji ne, ki duba WhatsApp D'inki na tura miki hoton Babyn".

Ruky tace .

"to anty bari na duba" daga haka sukai sallama anty mufeeda ta Kashe wayarta ta.cikin rawar jiki data hannu ruky ta Bud'e wayarta ta kunna data ta shiga WhatsApp d'inta inda zata ga messages d'in anty mufeeda kawai take dubawa Aiko sai gashi ana hud'u tuni ta shiga tana Bud'e pictures d'in jaririn hanan,Aiko gashi nan yaro tubara kallah Masha Allah dashi jajir kamar ubansa sak ,take ruky ta rufe bakin ta da hannunta D'aya, hawaye na taruwa a cikin idonta tana Jin Wani farin ciki na ratsa har cikin zuciyarta ,tuni ta mik'e ta nufi d'akinsu.


Ta Shiga da sauri tai kan gadon tana K'iran sunan AA Arab da Dee! Dee!!". Take fad'a tana yaye bargon data lullub'e jikinsa dashi.


Cikin bacci AA Arab yaji kamar ruky na K'iran sunan sa da k'arfi ,take ya Bud'e idansa Wanda ke cike da bacci tana Murmushi ta mik'a masa wayar tare da cewa .

"Kalli jaririn hanan,Hanan ta haihu Dee!..."ta fad'a cikin D'oki tareda tsananin murna.take AA Arab ya mik'e zaune daga kwancen da yake Yana karb'ar wayar da ruky ke mik'o masa ya zubawa screen d'in ido Kafin ya kallo ruky cikin farin ciki shima yace.

"Masha Allah yaushe ta haihu?.."

Cikin farin ciki ruky tace.

" yau da ASuba".

AA Arab ya jinjina mata kadinta yace.


"Baby girl ne ko Kuma boy?"ya fad'a Yana K'ara zooming d'in hoton Dan Allah ya Gani take yaji San yaron ya shiga ransa Dan babu laifi AA Arab Yana son Yara shima.

Ruky tai saurin cewa.

"Baby boy ne".ta fad'a tana kallan wayar

AA Arab ya jinjina kai kafin yace.

"Allah ya yara"

Ruky tace.

"Ameen Dee!".

AA Arab ya murmushin ganin Yadda farin ciki ya bayyana a saman fuskarta ya jawowa kusa dashi Ya kai Hannunsa saman Cikin ta kafin ya duk'ar da kansa saitin cikin yay kissing d'insa ya d'ago Yana kallan ruky yace.

"Muma Allah ya sauke ki lafiya ki haifo mana masu albarka".ya fad'a yana kallanta murmushin a fuskarsa ".

Ruky ta D'ora hannunta saman nasa Dake kan cikin nata kafin tace .

"Ameen thumma Ameen Dee! ".


Sai Kuma tai saurin cewa "yauwa Dee yaushe zanje naga yaron wallahi I'm eager to see him" ta fad'a tana Wani murmushi.

AA Arab ya Bud'e ido Yana kallan ta kafin
Ya rik'o fuskarta da tafukan hannuwansa ya kawo saitin tasa fuskarsa Yana kallan ta ido cikin ido Kafin yace .

"Irin haka wannan farin ciki da zumud'i kamar kece maman babyn".ya fad'a Yana k'ok'arin had'e bakinsu waje D'aya.

Ruky tai juyar da kanta zata k'wace fuskarta domin tasan me Hakan yake nufin Amma ya hana Hakan ta hanyar rik'o rike furkarta tata gam gam Yana mata Wani Irin kallo.cikin dubar burcewa ruky tace .

"Baka sani ba d'ana ne mana"ta fad'a tana masa fari da ido.yay Murmushi yace.

" ko? Ashe fa hakane to Masu d'a Allah ya raya Sai Kuma yace.
" bari zuwa zuhr prayer sai muje , Amma kafin nan ma zan k'ira ya hanaf nai Masa barka Hakan ai yayi koh?".ya fad'a Yana kallan ta.
Ta Jin jina masa kai cikin farin ciki tace.

" Allah ya kaimu".yay murmushi Yana had'e bakinsu waje D'aya ya fara kissing d'inta romantically Babu k'akk'autawa, ganin haka yasa itama ta biye masa nanfa suka fara aikawa da juna hot romance's ya kwantarta da ita kusa dashi Yana binta ahankali saboda cikin jikinta suna cigaba da farantawa juna. kamar Babu gobe .


Lokacin da suka isa gidan Hanan , gabad'aya Ruky tana zaune kan kujera ta k'ank'ame yaron ta zuba masa ido tana kallansa da murmushi a fuskarta,Dan Jin D'an take kamar nata,ta Kalli Hanan Dake kallanta tana Murmushi itama tace.

"Hanan da wahala Dan Allah?". ta fad'a Tana kallan Hanan.

Hanan tace .


"Hmmm idan ana sallah ai ba'a magana sis".

Ruky ta zaro ido waje cikin fad'uwar gaba kafin tace .


"Dan Allah wai da wahala da naji kince haka" ta fad'a fuskarta na bayyanar da tsoro sosai.

Ganin Yadda ruky ta tsorata yasa Hanan tai dariya tace.

"Ke uwar 'yan tsoro da Wasa nake miki fa, Babu wata wahala sosai , kawai nak'udan ce idan tazo miki da sauk'i shikenan, Amma ni gaskiya banji Irin wahalar nan da naji mutane suna yawan fad'a ba ,Dan Alhamdulillah gaskiya banyi doguwar Nak'uda ba".

Ruky ta sauke ajiyar zuciyar salama kafin tace .

"Alhamdulillah! harna ji Dad'i araina kinsan da harna fara Fargaba tun daga yanzu?".

Hanan tace.

"Wallahi Karkiji komai in Sha Allah babu komai zaki haihu cikin ruwan sanyi " .

Ruky ta rausayar da kai kafin tace.

"To! Allah yasa".ya hanaf ne ya shigo d'akin da sallama suka ansa masa Yana kallan ruky yace.

"Kinbar mutum shikad'ai kunzo nan Kuna ta surutu Baki kai masa yaron ya Gani ba?".ya fad'a cikin fad'a.

Ruky ta sunkuyar da kai k'asa tana murmushi azuciyarta tace ah su ya Hanaf masu d'a Hanan ta kalleshi kafin tace .

"ayi hak'uri babban Yaya tuba Muke".ta fad'a tana murmushi.

Shima murmushin yay mata kafin ya kashe mata ido D'aya Yana k'ok'arin zuwa gunta dan ya D'an rungumeta sai Kuma ya tuna Ashe ba su kad'ai bane a d'akin,Hakan yasa yay sauri ya matsa baya Yana shafa kansa kafin ya Kalli Ruky ta gefen ido yace.

" kawoshi a kaishi ya ganshi"ruky tai saurin Mik'a masa shi Dan duk wannan abun da suke tana kallan su ta gefen ido tana tunanin Ashe shima ya hanaf haka yake ya iya soyayya.

Ya fita daga d'akin,bayan ya Fita suka cigaba da hira Hanan tana ta kwantar wa da ruky Hankali haka ruky ta wuni agidan Hanan sai bayan magrib AA Arab yazo ya d'auketa suka tafi gida .tunda akai haihuwar nan sau biyu ruky tazo gidannan Hanan .har yau daya kasance Ranar suna,


tun wajen k'arfe goma na safe ruky ta tafi Anty mufeeda tazo jiya ita da matar ya Tahir da itama take d'auke da ciki na tsawan wata biyar itama abinta Dan tare Daya ya Tahir d'inma suka zo.,gida dai ya cika mak'il da 'yan uwa da abokan arzik'i.yaro yaci sunan Baban ruky UMAR FAROOQ MaiTama Wanda ZA'A dinga K'iran sa da suna Irfan,Mai jego ta gaji Dan kyau tayi shiga iya shiga na tsadaddun kaya Kamar me,haka Suma su anty mufeeda da Khadija matar ya Tahir Suma sunyi shiga ta kece raini,sai Kuma Ruky ya Allah itama haka tai shiga cikin Wani rantsatstsan less Wanda ya karb'e ta d'inkin doguwar riga bubu Dan ta samu ta sake cikin jikinta yayi mata kyau Dan Bai hanata hidima ba,AA Arab ya bawa Mai jego gifts da shi kansa yaron ma kayan sawa masu bala'in kyau da tsada,ya bawa ya hanaf gudunmar kud'i har naira dubu Dari biyar suke ta godiya kamar me itama ruky ba'a barta abaya ba ta bawa jefo gift har ma da jaririn,suma su anty mufeeda duk sun Basu gift haka akai bikin suna aka watse,muka bisu da addu'ar Allah ya raya irfan.


*ZARI'A*

Baba asabe ana nan ana fama da jinyar gangar jiki data zuciya idan kika ganta baza kice ita bace ba, Dan a kullum idan taga zaliha tana shayar da 'yarta wadda tasan Bata Hanyar aure aka sameta ba sai taji kamar ta had'iyi zuciya ta mutu Dan Bak'in ciki,wai zalihar Data ci buri akanta take fatan ta auri Mai kud'i tunda duk 'ya'yanta Babu Wanda yake auren Mai kud'i shiyasa take da buri akan zaliha Amma wai yau 'yar data gama cin buri akanta itace ta haifa mata D'an shege acikin gidan ta tana ji tana gani wannan Abu idan ta tuno dashi ba k'aramin ta-da mata da hankali yake ba,yau ga 'ya'yan mak'iyarta Maimuna Wanda ta k'are rayuwar ta wajen k'unta ta musu yau sune suka zama wasu tunda ga Ameenah tana auran lauya Mai kud'i ga Kuma Nana itama tana shirin gama makaranta nan da wasu watanni kad'an ta zamo cikakkiyar nurse,wai Allah! lallai ba k'aramin cutar da kanta tai ba Dan wannan kanta ta cuta ba maimuna ba,ga lawisa har yanzu mijin ta ko biko Bai tab'a zuwa ba tunda akwai sauran igiya a tsakaninsu,bare Mardiya ita da auranma ya Haram ta ,take ta fashe da Kuka tana K'ara tsanar kanta da Kuma mummunan halinta...


A b'angaren ummah kuwa barrister shamsu dayazo gaida su haka ya kawo musu abun arziki har ya Basu jari na mak'udun kud'ad'e,haka sukai ta godiya.


A b'angaren Ameenah da barrister shamsu itama dai ciki ya samu ,Dan jinya tai na kwana biyu, aikuwa ya kwashe ta ya kai ta asibiti,ana yin test akaga cikin sati uku a jikinta murna agun barrister shamsu ba'a magana suka dawo gida abinsu suka cigaba da rainon cikinsu.


*Bayan wata biyu*


Ruky ce kwance akan gado ita da AA Arab tana jikinsa suna bacci misalin karfe 2:30 na daren ranar Alhamis ,kawai tana cikin baccin taji kamar Abu ya harbeta acikin cikinta take ta runtse idonta kafin ta gama recovering taji marar ta tai Wani Irin harbawa,ai Bata San lokacin data mik'e zaune daga kwancen da take ba tana salati da k'arfi tana yarfe hannu,cikin bacci AA Arab yaji salatin nata take ya farka Dan dama tunda suka shiga watan haihuwar ta da k'arewar kwanaki EDD d'inta ya k'auracewa nauyayyan bacci.afirgice ya Rik'o ta zuwa jikinsa Yana tambayar ta da lafiya?cikin tashin hankali.

Ruky ta rik'e hannunsa gam kamar zata b'alla saboda azabar data ke ji tana jujjuya kanta cikin azaba da gumi ya gama wanke mata fuskarta da jikinta gaba D'aya tace da k'yar.

"Marara zata b'alle Deeee!!!".ta fad'a tana Jan Deee d'in da Wani Irin k'arfi yadda marar tata Ra k'ara k'ullewa kamar zata rabe biyu.
Take AA Arab ya sauka daga saman gadon cikin sauri ya zura jallabiyarsa kafin ya Bud'e press ya d'aukowa ruky wata sauk'akk'ar dogowar riga da hijab ya hawo saman gadon ya zura mata rigar Jinta tare da hijab d'in ya na kallan yadda take kuka hawaye ya gama wanke mata fuskarta cikin damuwa Yace.


"Sorry Noor!bari naje na fito da mota saina dawo na d'aukeki kinji?".ya fad'a Yana sauka daga saman gadon ya d'auki akwatun haihuwar da suka loda kayan haihuwar da suka siya aciki yay hanya fita daga d'akin ya Bud'e k'ofar ya fita da sauri bayan ya d'auki key d'in motar Dake gaban mirror.


Babu dad'ewa ya dawo d'akin a hargitse ya d'auke ta cak daga saman gadon yay hanyar k'ofar fita da ita suka fita compound inda ya fito da motar wacce take a Bud'e ya shagar ta bayan motar ya rufe ya zaga driver seat ya shiga da sauri Dama already gate man ya Bud'e masa gate d'in yaja motar suka fita daga gidan da mugun speed Bai ji Allah ya kiyaye da Mai gadin yake masa ba saboda gabad'aya a rud'e yake.


Bai zarce ko Ina ba sai Wani special private hospital wanda anan ruky take awo suka isa suna zuwa ya fita ya shiga har office d'in doc Wanda shine shugaban asibitin tare suka fito da doc bayan yaywa nurse's d'in magana suka taho cikin sauri ganin haihuwa ce saukai maternity da ita.

Gabad'aya AA Arab ya gama rud'ewa ya yunk'uri zai bisu doc ya kalleshi cikin girmamawa da kwantar masa da hankali yace.

"Basai ka shiga ba in Sha Allah zasu kula da ita yallab'ai,zakuma ta sauka lafiya in Sha Allah ka kwantar da hankalinka" ya fad'a cikin kwantar da murya.

AA Arab ya kalli doc cikin damuwa yace.

"Doc ka tabbatar zata haihu da kanta?".ya fad'a cikin damuwa.

Doc ya Jin Jina kai yace.

"In Sha Allah yallab'ai! mudai Yi addu'a bari naje"AA Arab ya jin jina masa kai daga haka doc ya bi bayan nurses din.

Ruky ta jima tana gumurzu a d'akin haihuwar nan Amma Abu shiru kake ji gashi dai tun wajen k'arfe 3:Saura na dare Amma itace take fama har k'arfe hud'u na asubahi,AA Arab Yana waje ya kasa zama sai struggling yake a bakin k'ofar dak'in kamar ya afko ya shigo haka yakeji.sai Kallan time yake ganin Irin dad'ewar da akai Amma babu Wani bayani acikinsu babu Wanda ya fito bare ya tambaya, Yana ta sak'awa aransa Daya k'ira ummi ko yaya Amma Kuma ya kasa Dan baiso ya ta-da musu da hankali addu'a kawai yay ta zabgawa akan Allah ya sauki ruky lafiya..


Haka ruky tai ta fama har k'arfe biyar Saura duk k'arfinta ya gama k'arewa kukanma ta kasa baiwar Allah addu'a babu kalar wacce batai ba, k'arfe biyar dai dai na ASuba ta haihu , D'aya daga cikin nurse d'in tai saurin d'a???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ukar jaririn tana dubawa Taga baby girl ce wata uwar k'atuwa da ita tai ta tsallara kuka sai alokacin ruky ta sauke wata wawuyar ajiyar zuciyar salama tana runtse idonta da hamdala azuciyarta.d'ayar nurse d'in itama ta graya ruky.

Bayan sun gama gyara 'yar suka Mik'awa ruky wacce ke kwance tana sauke numfashi suka D'ora mata ita kan k'irjinta Dan taji dumin 'yarta itama jaririyar taji d'umin uwarta .Aiko take yarinyar tai shiru ruky ta shafa kanta tana Jin Wani bacci na furgarta Dan sun mata allurar bacci yadda zata huta sosai,Ganin ta lumshe ido alamar baccin ya d'auketa yasa suka d'auke 'yar suka fito daga d'akin gabad'aya.

AA Arab Dake tsaye bakin k'ofar dak'in Jin kukun jariri yasa kamar ya shigo d'akin Yana ganin sun fito ya nufosu yace.

"ta haihu?".suka Mik'a masa babyn Dake cikin Wani rantsatstsan towel na jarirai mai fari da blue ya karb'eta Yana murmushi suka ce

" congratulations sir ansamu baby girl" suka fad'a suna Murmushi.

sai alokacin ya d'ago ya Kallesu kafin yace.

"Thank you"ya fad'a cikin farin ciki.sai Kuma yay saurin cewa .

"Ina maman babyn tana lafiya? zan iya shiga na ganta", duk ya jero musu tambayoyin .

Suka ce "Yanzu ta samu bacci sir saidai idan ta farka zuwa anjima bai jira sun K'arasawa ya shige cikin d'akin suka bishi da kallo suna mamakin wannan soyayya suka jin jina kai daga haka suka fara k'ok'arin bar wajen


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login