Showing 81001 words to 84000 words out of 278032 words

Chapter 28 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1068

xage xage,suna Kuma cewa Hajiya SA'A Bata kyauta musu ba,dama tasan da matsala shine ta Aiko su, shiko hanaf ya buga tsaki,ya fita daga falon yay compound Saida ya tabbatar da sun tafi sannan ya koma cikin falon Yana mamakin Alhaji sunusi,da Irin karfin halin sa,yau zaiga iya gudun ruwansa,yasan zaixo Kuma Yana nan Yana jiransa dan wlh dai dai yake dashi,......



__________?&


A bangaren Ruky kuwa alokacin da ake kawo lafenta, ita Kuma alokacin ne ta baro office ta nufi kotu domin xuwa tai qarar lateef,Hanan cema ta Rakata itada Khalil, suna xuwa kuwa haka suka shigar da qarar lateef akan yay wa shafa fyade suna so a biwa shafa hakkinta,babu Bata lokaci kotu ta karfi report dinsu, sunce Kuma xuwa yamma ZA'A kai musu sammaci,bayan sun baro office din, ahanya Hanan tacewa ruky, Ruky Nifa wlh Ina tunanin wannan abun da mukayi,....


Ruky wacce ke driving Hanan agefenta Khalil Kuma Yana baya,ta kalli Hanan wacce ta tsareta da ido tana Jin taji me ruky xata fada , ruky tace tunanin me, Hanan tace wlh ruky mundauko Dala ba gammo, ruky tai tsaki tace ke wlh dadina Dake tsoro me Suka isa su mana ,wlh tunda har aikinmu xamuyi wlh Babu Wanda ya isa ya shiga mana aiki,Kuma ku kwantar da hankalinki wlh Babu abinda suka isa suyi mana in Sha Allah,duk da nasan uncle sunusi da kafiya da nuna cewa Dansa shine gaba da kowa, zai iya aikata komai akan Dansa,nasan xai iya ja da kowa indai akan lateef ne, Amma wlh tunda harshi ya aikata wannan laifin wlh Hanan sai an gurfanar dashi agaban kotu,dole saiya ansa laifinsa Hanan tai shiru,ganin Ruky ta harxuko mata.. .



Khalil dake baya yana saurarar su yace ASP Hanan ki kwantar da hankalinki tunda har sister Rukayya ta dauki damarar yin wannan case din kawai muma muyi muba ya'a mu ,sa Allah Aranmu, shine me komai ,me iko akan komai,me sanin abinda xai faru ,yanxu ne,anjima ne,gobe ne, Allahu a'alam,svd haka nidai wlh tunda har sister Rukayya ta tsaya tsayin daka zata bi case din nan,Nima in Sha Allah sai inda karfina ya qare,,Kuma kinga munada shaidu,Hanan tai murmushi tace shikenan,malam Khalil , Amma ni gani nake Aduba alakar Dake tsakani, ruky ta buga tsaki tace Hanan Dan Allah kidaina xancen wannan alakar, idan kina xancen wai Alaka wlh kina bani mamaki, wai kamar bakisan girman aikinmuba,kamar bakiyi rantsuwar cewa zakiyi aiki bisa gsky da Amana ba, Hanan tace shikenan naji Allah ya bamu Sa'a, Khalil ya ansa da Ameen ita ruky ko dan haushi ko magana ma,batai ba, driving dinta kawai take,tana Jin Hanan da Khalil suka dauko hirar AA Arab itakan ko kallansu batai ba,wlh Hanan tana Bata mamaki, wannan mutumin sai kace Wani Dan uwanta wlh ko Dan uwanta iya kacin qaunar da xata nuna masa kenan,baxaka tava xama da Hanan ba batai Maka xancen AA Arab ba,,ta tabe Baki ta cigaba da tukinta,.....




__________?&


Alhaji sunusi ne tsaye a falonsa wajen karfe 5: 30pm baidade da dawowa daga inda ya tafi ba,Dan yawan kanfen suke tayi ,Dan yanxu baya samun xama,Dan xabe ya gabato nan da 2 months masu xuwa,ya goya hannunsa a bayansa Yana Dan zagaye falon,ya Kara kallan Hajiya SA'A a karo na biyu wacce ranta ke a bala'in bace,yace yanxu kina nufin kice wai hanaf shi yay musu wannan Rashin mutuncin, Hajiya SA'A ta dago tace cikin bacin Rai wlh Alhaji, wannan yaron hanaf bashida mutunci,bansan haka ya rika a Rashin mutunci ba sai yau,da yaywa su Hajiya mansura wulakanci,....



Hajiya mansura tace wlh tunda uwarta ta haifeta ba'a taba ci mata mutunci Irin yadda wannan yaron yay mataba,tace wlh Saura kadan ya zagesu,tace kai duka ma tace wlh ya kusan dukansu, Alhaji sunusi ya jinjina kai, yace wai tsaya duk a gaban Hajiya Halima yay musu wannan wulakancin, Hajiya SA'A ta tabe Baki tace,wai sunce yace batanan, nifa wlh dandai kawai Dane ka haifeshi baka haifi halinsaba,baka isa ka hanashi ya hanuba, Amma wlh inta nice da tuni ya hkr da auran wannan yarinyar, tunda ba yar gwal bace,.....


Ni wlh banma ga Abinda ya Gani ajikinta ba,Wanda Sauran mata Basu da Shiba, da zai dage sai ita,sbd haka Alhaji wlh yau lateef ko mutuwa zaiyi saidai ya mutu Amma wannan AURAN kan Bai isa ya AURE taba,saidai ya Nemo wata ya aura tunda ba autar mata bace ba, Alhaji sunusi da yay shiru yana tunanin Irin matakin da xai dauka akan lateef yace, SA'A ki kwantar da hankalinki wlh wannan yaron a wannan Karan baxan kyaleshi yaci bulusba,yayi masifar rainani,wlh saina dauki mummunan mataki akansa yadda gaba ko sashi akai yamin rashin kunya baxai yiba,....



Sbd haka ki kwantar da hankalinki ni nasan me xan masa, Hajiya SA'A tace Alhaji duk naji Amma wannan aure dai baza'a ayi Shiba,saidai ya nemi wata, idanma xabin nawane baya so, Alhaji sunusi yace bari wannan xancen bari lateef din yaxo ki fada masa duk yadda akayi, Hajiya SA'A cikin bacin Rai tace wannan marar xuciyar aiba hakura xaiyiba,tunda bashi akayiwa ba, naga sawa tai aka kamashi aka kulle, Amma baiji haushiba,ya dage saiya aureta,to Ina Kuma ga wannan daba shi akayiwa ba, Alhaji sunusi yace naji bari dai yaxo din, suna cikin wannan halin akai sallama abakin kofa, Hajiya SA'A tace waye,P A din Alhaji sunusi ne na gidan yace Hajiya sa'ad ne, Hajiya SA'A tai shiru Alhaji sunusi yace ya akayi sa'ad , sa'ad yace sako aka kawo Maka yallabai ,Alhaji sunusi yace ya shigo, sa'ad ya shigo ya Mikawa Alhaji sunusi envelope,ya karba sa'ad Kuma ya fita, bayan fitar sa'ad Alhaji sunusi ya Bude envelope din, ganin takardune yasa ya fito dasu gabadaya,ya dauki ta farko yafara karantawa yaga sammacine daga kotu ,....



Cikin mamaki ya Kara karanta dayar itama sammacine, Daya ta lateef daga Kuma duka su su biyun, Alhaji sunusi cikin rawar Baki data hannun yace sammaci Kuma ,kotu lateef,me mukayi, Hajiya SA'A Dake sauraran sa,ta matso kusa dashi cikin tashin hankalin abinda Alhaji sunusi ya fada,tace Alhaji sammaci Kuma,waye yay karar ku, kaida lateef Kuma, Kodai Wani Abu lateef yaje ya aikata ,kai wannan yaron wlh baya Jin magana,Alhaji sunusi ya dago ya kalli Hajiya SA'A,sai Kuma ya daga kansa sama ya samu wuri ya xauna Yama rasa wani tunani xaiyi,sai jujjuya takardun kawai yake ahannunsa Yana mamaki ,bamaya Jin me Hajiya SA'A take cewa dake ta magana tana masifa,....







07066508376________
'?Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD





*____JAMI'AR TSARO ____*



*____THE WOMEN POLICE ____*



*NA*



*____NAJA'ATU UMAR FAROOQ____*



*____(MRS SARAKIES)___*



*=?1?QUEEN OF WRITERS ASSOCIATION (QOWA) =?1?*



*Bismillahirrahmanirrahim*



______season one ep 3?? 5??


__________?&



Yau xa'a Yi xaman kuto,karfe 11:30am akasa lokacin, Ruky tun karfe 10:30am dai ta baro office bayan ta gama duk ayyukan ta,11: am dai dai tana asibitin, itada su Hanan da Khalil,xata dauki shafa da baba lami, shikuma Khalil amotar Hanan xasu taho,haka suka fito daga dakin da aka kwantar da shafa ,baba lami ta ruko shafa,suka fito tare ruky Kuma tana gefensu,sai Hanan da Khalil suna gabansu, Hanan suka nufi motar ta ita da Khalil, ruky Kuma ta wuce wajen motarta,bayan sunje kusa da motar ruky ta Bude musu gidan baya suka shiga,ita Kuma ta wuce driver seat ta shiga,.....



Hanan ma ta shiga motarta Khalil Yana gefenta haka suka baro asibitin Wanda direct daga nan kotu suka shige , yanxu Kuma 11 da mintuna ,Dan basaso su Saba lokaci, Dan karfe 11:30 ne xaman kotun,ruky tana tukine ne Amma tunani ne fal aranta,motar tayi shiru kamar Babu mutane acikinta,kowa da tunanin dayake sakawa aransa, ruky tana tunanin yadda Shari'ar tasu xata kasance ne duk da haka tana fatan Allah ubangiji ya Basu SA'A, Amma tasan Alhaji sunusi hatsabibin kansa,ita Kanta tasan ganganci xatai, Amma tunda harta qudiri aniyar Yi,in Sha Allah sai inda karfinta ya qare,. danma jiya itada Khalil da Hanan sunyi fafutukar Neman lauyan da zai tsaya wa shafa ,sun karanta masa komai, Kuma shima ya gamsu yace su kwantar da hankalinsu in Sha Allah xaiyi iya bakin kokarinsa Kuma xasuyi nasara da yardar Allah,haka suka baro gunsa da hopping din in Sha Allah xa'a dace ,.. ahaka dai tana cikin tunanin har suka isa kotun inda tai parking a inda aka tanada domin yi,Suma su Hanan tuni sunyi sunma taho inda suke,haka ruky ta fito daga maxauninta inda ta taho ta budewa su baba lami,....



Wacce ta fara saukowa,tukunna ta kamo shafa wacce ke tafiya ba daidai ba,bayan ta sauko ruky ta rufe motar, sannan ta gyara xaman abayar jikinta,ta Kalli baba lami wacce ke Dan kalle kalle,tai murmushi tace baba karkiji komai kiyi mana addu'a kawai in Sha Allah zamu dace,baba lami ta sauke numfashi tace Allah ya bamu Sa'a jami'a, Ruky tai murmushi ta ansa da Ameen,sai Kuma ta juya ga kallanta kan Hanan wacce ta karaso tai Kiran sunan ta, ruky ta ansa tace ya dai ,Hanan tadan ya Mutsa fuska ta kalli agogon hannunta tace Kinga fa saura 10 minutes Amma naga alamar mutanan nan Basu xoba, ruky ta tabe Baki tace ai kinsan dole su xo,tace muje , Hanan ta sauke numfashi tareda ta daga kafada tace shikenan,haka suka wuce cikin kotun Khalil Yana biye dasu,....



_________?&


A gidan Alhaji sunusi kuwa, baiyi baccin kirkiba Yana tunanin wannan sammacin da aka kawo masa,baisan waye yay Karar Saba,tunda babu suna kawai dai rubutowa akai cewar ana nemansa a kotu,shida lateef,ko kadan Bai taba kawowa,wai ruky xatai qararsaba,sai gashi daxu da lateef sassafe ya taho part din Alhaji sunusi Wai yaji mummy tace baxa a aura Masa ruky ba,gashi Kuma wai ana nemansa a kotu,.....


Alhaji sunusi Bai tsaya sauraran Saba iya kaci kawai yace masa yaje ya shirya karfe 11 ya fito suje kotun suji meyake faruwa waye yay karar ta su,haka lateef ya fita cikin bacin Rai, Alhaji sunusi yay tsaki ya koma daki,..karfe shadaya da Rabi Alhaji sunusi ne tsaye a falonsa sai Hajiya SA'A da itama ke tsayen, gabadaya ranta a bace yake, Alhaji sunusi dashima ransa ke a bala'in bace yace wai Ina lateef din ya tafine bayan yasan shi name jira ga lokaci sai kurewa yakeyi,kodai tafiyarsa yay SA'A, Hajiya SA'A ta tabe Baki tace Yana part dinsa shiryawa yake aiyasan da xuwa kotun Babu inda xashi,.....


Kafin Alhaji sunusi yay magana saiga lateef ya shigo cikin shigar qananan kaya fuskarsa a hade, Alhaji sunusi yace muje, lateef ya tsaya yace daddy daurin auranfa ko sai mundawo , Alhaji sunusi ya kalleshi cikin bacin Rai yace lateef wai meyasa baka da hankali ne, kana fa ganin sammaci aka kawo min,ka tsaya ma mana mu kashe wannan case din tukunna, Amma kai kwata kwata bakada da lissafi,bakasan dai dai ba,yanxu xuwa kotun xamu fasa a tsaya daurin aure,....


Lateef yace daddy kawai fa tambaya nai, Hajiya SA'A ta tsuke fuska tace kai lateef Saidai uwar daurin AURE Dallacan wuce ku tafi marar hankalin nan, Alhaji sunusi yay tsaki ya fice, lateef yaywa Hajiya SA'A Wani kallo yabi bayan Alhaji sunusi, haka suka fito xuwa compound driver Yana ganinsu ya mike ya Bude musu motar suka shiga, Shima ya xaga ya shiga mota,yay mata key direct suka wuce kuton Wanda har karfe shabiyu Saura,....



A hanya Alhaji sunusi yaga message ya shigo wayarsa ya dauka ya duba ya karanta ganin abinda aka rubuta yasashi tashi daga kishingidan dayake,ya cire glass din fuskar da,yace what Rukayya Kuma ,yanxu yarinyar nan qararmu tai akan wannan case din, dama sammacin da aka tura mana dama itace tai qarar, lateef ya juyo Jin abinda Alhaji sunusi ya fada, cikin mamaki yace Daddy Rukayya Kuma, Alhaji sunusi ya Mika masa wayarsa, lateef ya karba ya karanta sakon,bayan ya karanta ya rike Baki Yama rasa me xaice,..


Alhaji sunusi yace bani wayar nan ,lateef ya Mika masa , saikuma ya gyara xamansa yace Daddy tunda akan wannan case din ne,mu koma gida kawai Dan xuwannamu baida wani amfani,yanxu yarinyar nan Dan Bata da kunya Dady harmu xatai qara, daddy ka barni da ita shiyasa nace ka aura min ita ,kaga da anyi auran aida Bata isa tace xatai qarataba,wlh yarinyar nan Dady saina nuna mata cewa ni nafi karfinta,saina koya mata hankali, Dady kawai muwuce a daura auren naje na dauko matata,Alhaji sunusi ya Kalli lateef yay Wani murmushi sai Kuma ya dafa kafadarsa yace Babu inda xamu lateef tunda yarinyar nan ta nuna ja Dani ,Dan wannan abun bada kai takeba Dani take, wlh saina kaita kasa,...


Saina nuna mata cewa sawun rakumi ya zarce na kaza, lateef yace daddy kabarni da ita kawai idan ta Isa ta Aiko aka mamu idan munki xuwa, Alhaji sunusi yace lateef kabari ayau zan kawo karshen wannan shari'ar bari kaga na kira barrister na,Wanda yakemin aiki,Wanda duk wasu barristers,masuji da kansu abayansa suke, kowani barrister tsoron case ya hadosu dashi suke,me karawa ma dashi saiya shirya,kabarni da ita ni xan nuna mata isata takai isa,xan nuna mata cewa ba'a ja Dani daga haka ya nemo contact din lauyansa,bugu biyu ya daga, bayan sun gaisa Alhaji sunusi yace kana gari barrister, Salman yace Yana nan, nan alhaji sunusi ya labar ta masa duk abinda ke faruwa da Kuma abinda yakeson yayi masa,yace Kuma Dan Allah yanaso su hadu a coat yanzu ,nan barrister Salman yace in Sha Allah gashin xuwa,.....



Alhaji sunusi ya sauke wayar sa ya kalli lateef Wanda ke kallansa,yace daddy da ka bari munkoma gida Da baka wahalar da kankaba,Bai kamata mu ja da wannan yarinyar ba, Alhaji sunusi yace lateef so nake na nuna mata cewa nafi karfinta, lateef yace Dady Dan Allah idan mundawo adaura aurennan kawai, Alhaji sunusi yace ka kwantar da hankalinka bari mu gama da case din nan tukunna,daga haka lateef yaja bakinsa yay shiru, Amma Kuma xuciyar sa tafasa kawai takeyi,Alhaji sunusi Kuma Yana Saka Wani Abu a ransa,


__________?&


A can kotu kuwa Ruky harta fara tunanin kila fa lateef da Alhaji sunusi baxa su xoba,Dan gashi har shabiyu kwata tayi,ga alkali ya gaji da xaman jiransu , har ya kira wata karar Dake bayansu anfara da ita,Hanan sai jan tsaki take kasa kasa tana kallan agogo,baba lami itama kanta jikinta yayi sanyi, Khalil ko yadai xubawa mutanan cikin kotun idone kawai Yana sauraran karar Dake gudana,....



Hanan Dake ta faman buga tsaki a karo na babu adadi ta kalli ruky wacce ke kusa da ita tana kallan agogo tai qasa da murya tace ruky wai har yanxu mutanan nan Basu xoba kodai baxa su xoba, Ruky ta kalli Hanan ganin yadda ta tsuke fuska,kamar tai dariya sai Kuma ta fuske tace aikema kinsan dole suzo,Hanan tace Amma bakya ganin time kuwa ruky tace Ina Gani mana,Hanan tace Amma wlh da karfin hali suke,kodai Sunsan akan me akai karar tasu shiyasa kila sukai burus da maganar,ruky ta tabe Baki kafin ta bawa Hanan ansa saiga su Alhaji sunusi da lateef a bayansa,adai lokacin Kuma da aka gama Shari'ar da suke saurara,.....



Alhaji sunusi ya samu wuri ya xauna Batare da ya kula dasu ruky ba, shima lateef haka ya samu kusa da mahsufinsa,ya xauna har lokacin Yana Wani ciccije lebe,itadai ruky ta xuba musu ido kawai haka ma Wanda suke cikin kotun,bayan angama da Shari'ar nan, alkali ya kira Shari'ar su ruky, bayan an Karanto Alhaji sunusi yay mutukar Mamaki,bama shiba shi kansa lateef yayi mutukar Mamaki Vai taba tunanin ruky xatai musu hakaba,....



Alhaji sunusi ya juya ya kalli ruky wacce ta kau da kanta gefe hakama, lateef, Alhaji sunusi ya girgixa kai tareda cije lebe,wlh tsabar mamaki ,kasama cewa komai yay ,Yama kasa hada tunaninsa waje Daya, yanxu Rukayya ce tai masa wannan cin kashin,da cin mutuncin,yanxu itace xatai qararsa shida lateef, lallai yarinyar nan,wato Bata ma duba alakar Dake tsakani ba kenan, tunanin sa ya katsene lokacin da aka kira lateef gaban kotun, Wanda tuni itama shafa baba lami ta kaita cikin wannan box din ta tsaida ita,....



Haka lateef ya Kalli Alhaji sunusi Wanda ke kallansa da jajayen idanuwansa,ya daga masa kai alamar yaje,haka lateef ya mike jiki ba kwari ya fita, bayan ya tsaya ya xubawa shafa ido wacce kanta ke kasa tana wasa da yatsun hannun ta, shi har Yanxu ma,baxai tava cewa ga kamannintava Dan duk wannan abinda da ake ko kallan ta ma Bai taba tsayawa yayi ba, wai wannan yar mitsitsiyar yarinyar ce yaywa fyade shifa har yanxu ba xai iya cewa ga kamannintava,tunaninsa ya katsene lokacin da aka gama Karanto karar da aka shigar akansa,alkali ya kira sunan lateef akan hakane akan zargin da ake masa ko Yana da ja ,lateef koh yace shi gsky ba haka akaiba Dan shi ko saninta Vai taba yiba,lauyan shafa ya tashi yaywa lateef tambayi sosai, Amma lateef ya dage akan shi baisan ma shafa ba Bai taba ma ganin taba, lauyan shafa yadanyi murmushi ya karantowa kotu hujjojinsa, sannan ya koma ya zauna,.....



Haka ma lauyan lateef ya tashi ya karyata abinda ake zargin lateef dashi,ya kumace kotu ta duba ta Gani ai shidar Gani da ido itace shaidai bawai abinda Baki ya fada ba,haka dai aka cigaba da fafatawa,Wanda daga karshe dai alkali ya dage Shari'a yace sai Wani satin,haka aka tashi daga Shari'ar nan, batareda ansa samu matsaya ba, mutane aketa ta surutu da cece kuce kowa sai fadar albarkacin bakinsa yake akan Shari'r,bayan sun fito daga kotun kowa ya kama gabansa mutanan kotun suna ta fitowa, kowa ya kama gabansa,su Hanan har sun shiga mota, Alhaji sunusi ya taho da sauri Yana kada babbar rigarsa ya nufi ruky, lateef Yana masa magana Amma ya kyaleshi so yake ya nuna mata cewa ita karamar kwaruwa ce,ya samu ruky wacce ke kokarin shiga motarta Dan tuni su baba lami sun shiga,ya kira sunan ta, ruky ta juyo ta kalleshi saikuma ta sakar masa murmushi,tace uncle Ina wuni ,Wani Irin Banxan kallo Alhaji sunusi yay mata tareda da Maka mata harara sai Kuma yay murmushi yace, Rukayya umar MaiTama,wato Dani xaki ja,to shikenan muxuba nidake mugani Dan halak ka fasa, lateef Daya biyo bayan Alhaji sunusi ya karaso kusa da ruky ya nunata da yatsa yace wato ni husband dinki xakiyi qara ko,to shikenan muxuba nidake mugani, wannan karar tawa da kikayi wlh saina Baki mamaki Rukayya,Kuma ki shirya AURENAH Dake gove goven Nan wannan shari'ar da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login