Showing 207001 words to 210000 words out of 278032 words

Chapter 70 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1063

daga ita sai after dress din jikinta,kanta abud'e yake gashin kanta datai parking dinsa sai reto yake a tsakiyar bayan ta ,AA Arab ganin tak'i sauraran sa yasa yay qasa da murya Yana kallan ta ya ce "ki nutsu, ki fad'a min meya faru? ruky tana kuka ta nuna masa toilet d'in,AA Arab shima ya Kalli inda take nuna masa saiya juyo Yana kallan ta ya ce "miye aciki"ruky tana sauke numfashi ta ce "tsaka"AA Arab ya saketa ganin tana Neman rud'ar dashi ya k'arasa kofar toilet d'in Yana lek'awa,shidai baiga komai ba,ya juyo Yana kallon ruky datai saurin Saka hijab d'inta da take xuwa dashi sbd yin sallah ,ta sunkuyar da kai qasa sbd kunyar abinda ta aikata,AA Arab Yana kallan ta ya ce "ni Banga komai ba"ruky ta ce wlh yana ciki"AA Arab ya qara dubawa sai ya hango ta wata 'yar qarama,ya juyo Yana kallon Ruky ya ce "akan wannan D'an abun kike wannan ihun "ruky ta d'ago tana kallan sa a shagwab'e ta ce "sir wlh Ina tsoronsa ne "AA Arab ya kauda kai ya ce "kedai raguwa ce daga haka yay hanyar kofar fita ganin ankusa shiga sallah, ruky ta ce "ayina to Zanyi alwalar, kamar Bazai magana ba sai Kuma ya ce "shiga cikin toilet D'ina kiyi ,kuma karki b'atamin" daga haka ya fita ruky ta sauke numfashi tana Dana sanin wannan abun kunyar data aikata, tana wannan tunanin ta shige cikin office d'in nasa Dan yin alwala........



Rukayya gabadaya sai taji kunyar duniya duk ta rufeta, sbd yadda ta rungume shi Allah ya Gani Bata son tsaka ko kad'an Dan ko agida idan ta ganta kamar tai hauka haka takeji sbd firgici, shi dai AA Arab daya dawo daga masallaci baima kalleta ba sbd gabad'aya ta qara susu tashi,haka ya kulle kansa acikin office d'in ya kure AC ya kwanta kan sofan d'akin yay rufda ciki yana Jin abinda ya faru dashi Daren jiya na Neman dawo masa sabo, baisan tsawan lokacin Daya d'auka ahaka ba,ita dai ruky tana zaune kan kujerarta Ganin lokacin tashin ta Yayi yasa ta fara mamaki yau ganin yau AA Arab meyasa Bai fito ya Bata aikin Daya Saba Bata ba kullum,Dan tunda ta dawo office d'insa kullum saiya k'irk'iro aikin da zai Bata tai masa, Amma yau shiru,wata xuciyar ta ce to kodai baida lpy ne sbd gabad'aya yau Yana yin nasa sai a hankali ita Kanta ta lura da haka, kawai saita tsinci Kanta da tunin meya faru yau to kodai laifi tai masa,ko Kuma dai akan abinda ya faru ne d'azu ,kawai sai taji jikinta yayi sanyi ,da lokacin tashi yay AA Arab ya fito ya Mik'awa ruky key d'in motar ta ,ya kalleta da shak'akk'iyar murya ya ce "tana parking lot, Ruky ta karb'a tai masa godiya shidai baiyi magana ba ya koma cikin office d'in ya qara kwantawa kan sofan sbd Irin abinda yakeji....






07066508376________
'?Follow the Mrs Sarakies=؋? =?1? HAUSA Novel Channel channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VbBRj1D35fLuSHibdq1Y






*___JAMI'AR TSARO ___*



*____THE WOMEN POLICE ____*




*NA*



*____NAJA'ATU UMAR FAROOQ ____*



*___(MRS SARAKIES =؋?)=?1?___*



*('TAURARI WRITER'S ASSOCIATION ('*



*TEAM THE 4 GOLDEN STAR (' WRITER'S*



*Bismillahirrahmanirrahim*



_____season two ep 8?? 2??



____________?&

A tak'aice dai a wannan ranar kwata kwata AA Arab bai samu sukuni ba, saboda ya kasa yarda da abinda yakeji akan Ruky, kwata kwata yak'i ya amince da abinda Xuciyar sa take gasgata masa akan ruky Dan Bai tab'a zato ko tsammani ba.Koda Daya koma gida awannan ranar kasa Gane kansa yayi,hatta ummi sai da ta lura da haka Amma Batai magana ba tadai zuba masa ido kawai tana kallan sa,,har dai taga ya shige d'aki ya rofo k'ofa ,Koda ya shiga d'akin ya kasa fita Koda da falor ne ,Dan da wuri yau ya dawo daga heardquater tun wajen karfe 8 na dare ya dawo gida saboda Irin abinda yakeji,yanxu haka k'arfe Tara da Rabi ne na dare Yana kwance akan gadonsa bawai bacci yake ba ,kawai dai yayi rufda ciki ne akan gadon Ya Kuma rufe Idanuwansa,Dan Allah ya Gani shiya San me yake ji ahakan, knocking d'in da'kin da akayi tareda turo k'ofar dak'in aka shigo lokaci D'aya ne yasa ya juyo da kansa daga kwancen da yake Yana kallan Mai shigowar, ummi ce ta K'arasa shigowa cikin d'akin da sallama abakinta tana kallan AA Arab da Mamakin meya sameshi haka, sannan ta Maida dubanta kan table d'in Dake daykin Wanda ke d'auke da manyan warmers na abinci Wanda ta kawo masa su tun d'azu Daya dawo daga aiki,ta qasarasa har gaban table d'in ta bubbud'e warmers d'in ganin Babu abinda ya tab'a na D'aya daga cikin abinda ta kawo masa yasa ta k'araso har gaban gadon nasa....



Tana kallansa da Kyau ta ce "Ahmad anya ko lpyn ka k'alau kuwa ? Ta fad'a tana kallan sa,AA Arab ya qara gyara kwanciyar sa sannan ya d'ago da idanuwan sa da Sukai jaa Yana kallan ummi dasu kafin ya d'auke kansa Yana kallan direction daban ya ce "ummi kaina ne kawai kemin ciwo"ya fad'a Yana D'an ya Mutsa fuska, da mikewa Zaune Yana zuro da kafafuwansa kasan tiles d'in da'kin, ummi ta xauna a bakin gadon cikin damuwa tana kallan sa da kyau ta ce "yaushe ka fara ciwon kan Ahmad ?Amma shine baka fad'a min ba da wuri?AA Arab ya D'an dafe Kansa Dake Sara masa Dan wlh jin ciwon kan yake sosai kamar zai fad'o k'asa haka yake ji,ya kamo hannun ummi Yana kallan ta ganin yadda ta ta-da hankalinta lokaci D'aya ya ce "ummi bafa Dayawa bane ba nama Sha magani"ya fad'a da sigar lallashi Dan kada ta tada Hankalinta.....



Ummi itama rik'e hannun nasa tai tana kallan sa da ta ce "Amma meyasa bakaci abincin Dana kawo Maka ba tun tuni?AA Arab ya D'an shagwab'e fuska Yana shafa Cikin sa ya ce "I'm full ne ummi shiyasa "ummi ta harare shi kafin ta ce " haba Ahmad Wani Irin k'oshi Kuma? Yunwa ce kawai,kana zaune ka wuni bakaci abinci ba sannan kace zakai lpy ?ai dole kanka yay Maka ciwo abinda yafi ciwoma zai Maka Ahmad,ba ka cin abinci kwata kwata na tabbata ko a wurin aikin ma ba ci kake ba,to inama zaka samu,bare ka nema,tunda baka ci abinci ba, Ina ko xakaji ka dai _dai" sai Kuma ta ce da sigar lallashi "kayi hakuri na had'o Maka ko kad'anne saika ci kaji?ta fad'a tana kallan sa da tausayawa,AA Arab ya kalleta ya D'an yamutsa fuska ya ce "Amma ummi kad'an zaki zuba min" ummi ta mik'e Jin yace d'in sai zaici Batace komai ba har ta had'o masa abincin, sannan ta dawo ta zauna ta mik'a masa tana kallansa,AA Arab ya karb'a ganin farfe sun kayan cikine yasa ya fara ci ,ga Kuma coffee agefe da shima data had'o masa, kad'an ya ci kayan cikin ya ajiye agefe , sannan ya d'auki cup d'in coffee d'in ya fara sipping,Saida ya shanye du sannan ya ajiye cup d'in yace Alhamdulillah Asaman lab'b'ansa, ummi ta sauke numfashi sannan ta ce "wannan Kuma Mai kaci? Ta fad'a tana nuna masa bowel d'in farfesun da Bai cinye ba ,AA Arab ya mik'e ya ce ummi wlh na k'oshi,ba gashi na sha nye duka cup d'in coffee d'in da kika had'a min ba? idan Kuma nace zan qara zan iya yin amai"ummi ta sauke ajiyar xuciya sannan ta mik'e ta ce "ka tabbatar kasha magani kafin ka kwanta" AA Arab ya ce "yes ummi" ummi ta kad'a kai sannan ta d'auki bowel d'in kayan cikin Daya rage ta juye sauran a warmer d'in sai ta juyo tana kallan sa ta ce "Ahmad zanje na kwanta idan kaji wani ciwo just let me know " AA Arab ya jinjina mata kai kafin ya ce "in Sha Allah ummi, for now ma I'm feeling better ummi"ummi ta jinjina masa kai kafin ta ce"Allah ya sawak'e" AA Arab ya ce "Ameen thumma Ameen ummi"daga haka ummi tai Hanyar k'ofar fita daga d'akin,tana fita Kuma ta jawo masa k'ofar ta rufe.AA Arab ya sauke ajiyar zuciya ya shige cikin toilet d'in cikin da'kin nasa.......



AA Arab Yana kwance saman gadonsa ya d'auki wayarsa ya duba time yanxu k'arfe goma Saura na dare,haka kawai ya tsinci kansa da yay K'iran Ruky ko zaiji abinda yake ji d'innan akanta ya sakeshi, wannan tunanin da yay yasa ya lalumo contact d'in Ruky yasa agaba kawai Yana kallanta, kamar Wanda ita yake kallo haka yaji, tunani kawai yake shin ya K'irata ko Kuma ya k'yaleta,wata zuciyar Kuma ta ce "to idan ka K'irata me zaka ce mata ,idan ma ka K'iratan bazaka tab'a daina Jin Abinda kake jiba akan na taba sai dai ma ya qaru, sannan a qarshe ka K'ara jawo wa kanka Wani ciwon" wata xuciyar Kuma ta ce "ka K'iratan kawai k'ila ko iya Muryarta kaji ka iya samun nutsuwa" da wannan tunanin yay kyokarin darling number ta Amma Kuma sai kawai yaji ya kasa,afili ya ce "Ina ai saita Raina ni, dama ya aka k'are ta raina ni bare kuma ace na K'irata, ai sai abinda ya qaru Kuma.kawai saiya ajiye wayar, Amma Kuma Bai samu nutsuwa ba,Hakan yasa ya tashi ya d'auro alwala sannan ya shimfid'a darduma a tsakiyar d'akin ya fara gabatar da nafilfilu,ya Dad'e ahaka kafin ya samu nutsuwar zuciya sannan ya koma kan gadon ya kwanta Yana sauke numfashi nan da nan ko bacci ya d'auke shi.....


Da ASuba bayan AA Arab ya tashi yayi sallah, zazzabi me zafi ne ya rufe shi, nan da nan jikinsa ya d'auki wani Irin zafi Sosai da rawar jiki. take yaja bargo ya rufe dukkan jikinsa,yanajin kamar duka sanyin da akeyi akansa yake qarewa duk da ba lokacin sanyi bane Amma shi sai ya tsinci da Jin sanyin.sai Kuma lokaci D'aya jikinsa ya d'auki Wani Irin zafi kamar kamar wuta haka ya d'auki tsawon lokaci a wannan Yanayin.ummi tana d'akin ta Batasan meke faruwa ba AA Arab ya Dad'e a Haka kafin bacci ya d'auke shi.wajen k'arfe bakwai da mintuna ummi tai knocking k'ofar dakin nasa Jin shiru ,Dan ya Saba duk asubahin duniya idan yay sallan saiya je har part diyn ta gaida ta dana Abba, Amma yau shiru Bai zoba,shiyasa Yanzu ta taho da kanta ta don ta duba shi ko jikin nasa ne yay tsanani,tayi knocking d'in k'ofar d'akin nasa Jin shiru ba'a ansa ba yasa ta turo k'ofar dak'in shiga ciki bakinta d'auke da sallama, gabanta ne ya fadi ganin AA Arab kwance akan gadonsa har yanxu, gashi ya jibgawa kansa Irin katon bargon nan , ummi ta k'arasa har gaban gadon cikin tashin hankali tana K'iran sunan sa tareda yaye bargon duk a lokaci D'aya tana kallan sa , ganin yadda ya had'a uban gumi sosai ga sai Wani karkarwa yake,yasa ummi ta rikice lokaci D'aya tana K'iran sunan sa.....


AA Arab Yana Jin ummi Amma ya Kasa Bud'e idan nuwansa yay yay ya Bud'e Amma ya kasa Yana Kuma San Bud'e sun Amma ya kasa Dan yayiwa ma ummi magana akan karta damu babu komai Amma Abun ya gagara,ganin yak'i Bud'e ido yasa ummi ta fita daga d'akin cikin tashin hankali xuwa part d'in Abba Dan ta kirashi,babu dad'ewa ko suka shigo d'akin AA Arab tare,ummi agaba Abba Yana biye da ita shima cikin tashin hankali,ya qasaro gaban gadon Yana kai hannunsa kan goshin AA Arab tareda K'iran sunan sa,Bai Bud'e idonsa ba bare Kuma ya ansa masa Amma Kuma Yana jinsu , Abba ya Kalli ummi wacce harta fara hawaye ya ce "ya isa Fatima babu abinda zai samu Ahmad in Sha Allah,when ya fara jinyar? ummi ta ce"jiya da daddare Dana shigo d'akin zan kwashe warmers d'in Daya ci abinci, dama tun da ya dawo na ganshi Wani iri kamar Wanda akwai abinda ke damunsa" ta fad'a tana goge hawayen Dake zubo mata,Abba ya jinjina kai kafin ya ce "bari na k'ira doc, jeki d'auko min waya ta a falor na"ummi ta ansa masa sannan ta juya ta fita tabar d'akin,tana share hawayen dayak'i tsaya mata, Abba ya Maida dubansa kan AA Arab cikin tausayawa, alokacin da ummi take dawo d'akin rike da wayar Abba, alokacin Kuma AA Arab ya Bud'e idonsa Wanda ya koma ja ja zur ya sauke su akan Abba,Abba ya kamo hannun sa ya ce "Sannu Ahmad, ummi ta qaraso ta Mik'awa Abba wayar sa tana kallan AA Arab Wanda ya kalleta ta ce "sannu Ahmad Ina ne ke Maka ciwo" ta fad'a tana rik'e hannun sa,AA Arab ya lumshe idonsa sannan ya Bud'e lokaci D'aya ya sauke su akan fuskar ummi,ya motsa lips d'insa kad'an ya ce"kaina ne kawai amma ummi kidaina Damuwa" ummi ta ce cikin damuwa"dole na damu Ahmad,sannu kaji "AA Arab ya jinjina mata kai kawai Amma baice komai ba....



Abba ya Kalli ummi ya ce "doc Yana xuwa"ummi ta jinjina masa kai sannan ta juya tana kallan AA Arab Wanda ya D'an sakar mata murmushin k'arfin hali ya ce "ummi ki kwantar da hankalinki Babu Wani abun fa , shidai abba ya samu kan wata sofa Dake d'akin ya zauna Yana yiwa AA Arab sannu .haka suka Saka AA Arab agaba suna kallansa,cikin k'an k'anin lokaci doc ya iso Abb ya bashi iznin shigowa har cikin bedroom d'in AA Arab,bayan doc ya shigo ya gama duba AA Arab sannan ya juyo Yana kallan Abba kafin ya ce "Alhaji ba wani Abu Mai girma bane kawai damuwa ce kuma ita ta kawo masa ciwon kan,idan har ya cire Damuwar aransa in Sha Allah babu wani abun,yanzu dai nayi masa allurar bacci wacce zai d'auki tsawon lokaci in Sha Allah yanayi,idan Kuma ya farka bazai tashi da ciwan kan ba lda yardar Allah" ummi ta kalli AA Arab sannan ta ce cikin damuwar abinda doc ya fad'a "Damuwa Kuma? wacce Irin damuwa ce take damunsa da har bazai iya shirring d'inta da kowa ba ya zab'i ya rik'e ta axuciyarsa ,sai Kuma ta ce "Ahmad wacce Irin damuwa ce wannan take Neman tarwatsa rayuwar ka ,ta fad'a cikin damuwa, Abba ya kalii doc ya ce "shikenan doc mungode sosai Allah ya Saka da Alkhairi"doc ya ce "babu komai Alhaji ya Kalli , sannan ya Kalli AA Arab Dake lumshe ido alamar bacci na gab da fusgarsa ya ce "Allah ya sawake" ummi ta kalleshi ta ce "mungode sosai doc"doc ya ce "babu komai hajiya Allah ya bashi lpy"ummi ta ansa da ameen ,daga haka doc yay hanyar k'ofar fita daga d'akin, Abba yabi bayansa suka fita tare....



Ummi ta kalli AA Arab taga har yayi baccin sannan ta mik'e ta fito d'aga dakin ta rufo masa kofar,Dan barinsa yay baccin Amma Kuma ta k'udiri aniyar indai Allah ya bashi lpy saita tambayeshi wacce Irin damuwa ce wannan da har doc ya fada yanayi har take kokarin tab'a lpyarsa


____________?&


Ruky tana office axaune gabad'aya damuwa ce qarara ta bayyana a asaman fuskarta,Dan ita dai tunda ta koma gida jiya take cikin zullumi kodai taiwa AA Arab laifine ita duk damuwar ta idan laifi tai masa karya fad'awa mamah.yau ta shigo office da zummar indai Bai Bata Aiki ba kamar yadda yake mata Zata sameshi ta tambayeshi kodai laifi tai masa? Idan har laifin tai masa zata bashi hak'uri Kawai,sai dai tun tana xuba idon zai zo har ta fara tunanin kodai bazai zo bane ganin fa yanxu har k'arfe 2 saura na Rana ,ga ita ba abin ta k'irashi awaya ba yay mata fad'a,ko Kuma yay mata wata fassarar sau Kusan biyu tana attempting k'iransa Amma ta kasa ,Hakan dai ta daure ta cigaba da aikinta, tana wannan tunanin wayar ta tai ringing alamar k'ira ,ta jawo wayar ta duba Mai K'iran ganin Ameer ne yasa tai tsaki tak'i d'aga call d'in ,Bai hakura ba ya cigaba da k'ira ,sai da yay mata kusan miss call biyar batai picking ba,shima Kuma bai hak'ura da k'iran ba daga k'arshe ma ganin batai picking ba texts ya hau tura mata, ruky taja tsaki ta kashe wayar ma gabad'aya,Tana Jin duk Hanan ce ta jawo mata wannan abun....



Haka Ruky tai wannan wunin a office tana tunanin Rashin zuwan AA Arab.gefe D'aya Kuma gabadaya ta damu ganin AA Arab yau Bai zoba gashi har lokacin tashin ta yayi ,da ta duba Time taga K'arfe biyar da Rabi ,jiki a Sanyaye ta fara har had'a kayanta,Saida ta gama tas sannan ta fito daga office d'in ta nufi parking lot ta d'auki motarta.wajen k'arfe 9 na dare ruky tana kwance kan gadon ta gefe D'aya Kuma tunanin AA Arab ya mak'ale mata azuciyarta gabad'aya ta kasa samun sukuni tunda ta dawo gida,tunani kawai take Anya ko lpy AA Arab Bai shigo office ba yau ,kawai sai tai deciding data k'ira shi,take ta jawo wayar ta shiga call log tai darling number sa ,tana Jin tana ringing ta rintse idanta sbd yadda k'irjinta yake bugawa a kowanne ringing da wayar zaiyi ji take kamar da bugun xuciyarta ya ke bugawa,Sai da ta kusan tsinkewa sannan taji yay picking yay shiru baiyi magana ba,cikin dubur burcewa terada runtse ido ruky ta ce "good evening sir"AA Arab da farkawarsa kenen shima Yana kwance saman gadonsa ne Yana ta tunanin ya K'irata ne ko ya k'yaleta sai kuma gashi ta k'irashi , take ya sauke wata wawuyar ajiyar xuciya Yana Jin nutsuwa na saukar masa aduk kan xuciyar sa da ilahirin jikinsa,sannan ya ce cikin shak'akk'iyar murya"evening"saikuma yay shiru, ruky ta daure ta ce "dama na k'ira ka ne to check on u, sbd yau baka shigo office ba, lpy?ta fad'a cikin dauriya,AA Arab ya lumshe idonsa jin duk wani Abu Daya to Kare masa k'irji Yana narkewa ahankali ,ya ce cikin cool voice d'insa "thanks alot ASP"ruky ta ce "hope dai lpy?AA Arab yay qasa da murya ya ce "I'm not feeling fine"cikin damuwa ruky ta ce "ayya sorry sir Allah ya qara lpy"AA Arab ya ce "Ameen"ruky ta ce "shikenan na gaisheka good night "....


AA Arab ya ce cikin wata iriyar murya "noo karki kashe"


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login