Showing 231001 words to 234000 words out of 278032 words

Chapter 78 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1038

ka sa a kawo sun indai bakasan b'acin Raina", ta fad'a tana tura Baki gaba.


AA Arab ya Bud'e ido yace .


"Oh hakane abun?",kafin ya cigaba yace.


"oh ni Ahmad na gamu da Auta ,kuma Rigimammiya ai shikenan zan sa a kawo su", shikenan Ina .

Ruky ta gyada masa kai kamar Yana gaban ta. Kafin ta ce nidai ba Rigimammiya bace ba ",


AA Arab yace .

"Ba gashi kin min ba yanzu? ai gashima yanzu kinyi ya fad'a Yana murmushi",

Ruky ta tura Baki gaba tace "Allah nidai banyiba"

AA Arab ya gimtse dariyar sa yace. "alright it's okay",Sannan ya cigaba yace .


"Nifa sai naga ma Kamar kinfi d'okin zuwansu akan nawa ya fad'a da sigar tsokana",

Ruky tace.

"Yo idan ma nafi mene ne ai ya kamata ne",

Yace "ok to tunda hakane na ma fasa sawa a kawosun Dan karma su fini samun matsayi a wurinki,Dan naga tun daga yanzu ma har an fara yimin wariyar launin fata, ya fad'a Yana tura Baki gaba Kamar Wani k'aramin yaro.

Ruky tana dariya tareda da saurin cewa.

"Da wasa nake maka Dan Allah karka fasa "ta fad'a tana dariya

Yace "hmm ke koh, aishikenan,Daga haka kuma aka koma hirar soyayya sun jima suna hira kafin suyi sallama ganin dare yayi sosai....



Tun daga wannan ranar AA Arab ya daina yin Wani Abu Wanda ya danginci koya kusanta shi da ruky sai dai nesa nesa,babu abinda ya sauya na soyayyar su sai dai ma k'aruwa Amma Kuma fannin abinda zai sa ya kusan loosing control d'insa akanta Yana iya bakin k'ok'arin sa awajen ganin ya daina barin haka ta faru,zuwa yanzu kuwa acikin headquarter Babu Wanda Bai son AA Arab da ruky soyayya suke ba Kuma har an saka musu ranar AURE ba,Dan har shi kansa DCP ya sani ,haka dai ya k'araci jinyar zuciyar sa ya hak'ura ganin dai AA Arab yafi k'arfinsa Kuma ya fishi samun Sa'a kan Rukayya nesa ma ba kusa ba,Dan soyayya suke Mai k'arfi wadda har basa iya b'oye ta ko agaban waye ....


Feenah da taji labari jitai kamar ta had'iye zuciya ta mutu Dan Bak'in ciki, Amma Kuma tace Bazata tab'a hak'ura da AA Arab ba tace na tane ita kad'ai, Kuma dole a yau sai taje office d'in AA Arab ta fad'a masa abinda ke ranta akansa.sannan ta k'onawa Rukayya zuciyarta ta hanyar zuwa office d'in AA Arab.



Wajen k'arfe biyar dai dai na yamman Ranar ta shigo cikin heardquater directly ma office d'in AA Arab ta nufa,tana zuwa ta Bud'e k'ofar second falor inda ruky take zaune ta shiga Babu ko sallama,ruky tana zaune kan table d'in gabanta tana k'arasa aikin Daya rage mata ta d'ago da kanta Dan ganin Wanda ya shigo office d'in haka Babu ko sallama,taga feenah ce hakan yasa ta bita da kallo da mamaki harta gama shigowa tsakiyar falon falon taga ta nufi k'ofar office d'in AA Arab batai mata magana ba ta bita da kallo tana mamakin Rashin kunyar feenah,itako feenah kallo D'aya taiwa ruky ta d'auke kanta tana Jin kamar ta Shake'ta saida yadda take Jin tsanar Ruky azuciyarta,har zata Murd'a k'ofar office d'in sai Kuma ta dawo da baya zuwa gaban table d'in ruky tana mata wani wulak'an taccen kallo kafin ta duk'a dai dai fuskarta tai k'asa da murya tace .

"Hmm Rukayya kenan, Ashe muna fuka ce ke Mai fuska biyu bansani ba ,ashe shiyasa ranar nan Dana tambayeki me kike a office d'in saurayina Baki bani amsa ba, Ashe dawowa kikai office d'in sa da zama Dan yace Yana sanki ,hmm kuma Gashi burinki ya cika tunda gashi har an saka muku Ranar AURE, to bari Kiji na fad'a miki abinda Baki saniba ,wallahi AA Arab na feenah ne nini kad'ai ko kin d'auka sanki yake ,ai tun kafin yace Yana sonki ni ya fara cewa yanaso ,kuma yanzu ma shiya k'irani akan nazo Yana San ganina, ko ranar ma da kikaga nazo shiya k'irani yace nazo office d'insa Yana son ganina, to yauma shiya k'irani akan nazo ,idan Kuma kin Musa bari kiga naje zakiga abinda nake fad'a miki ta fad'a tana wullawa ruky wata muguwar Harara.


daga haka ta k'arasa bakin offer d'in ta fara knocking k'ofar office d'in , Saida tai sau uku sannan ya Bata iznin shiga ciki.

ruky da gabad'aya ta sume d'aga mamaki da feenah ta Bata,sai alokacin ta dawo hayyacin ta Ganin feenah ta juyo ta watsa mata Wani kallo tare da Yi mata gwalo tai k'asa da murya ta ce.

" Kinga tabbacin shiya kyirani koh?gashi ya bani iznin shiga", daga haka ta shige cikin office d'in, ruky ta bita da kallo tana mamakin k'arfin halin Irin na feenah da kuma fitsara,itadai tasan AA Arab bazai tab'a cewa feenah tazo office d'insa ba ,tasan sharrin feenah ne kawai Dasan taga ta K'ona mata Rai ta kuma fusata ta,ita ko tasan feenah tana shiga saita fito kamar yadda rannan ma yayi mata,ta zubawa k'ofar office d'in ido tana jira taga AA Arab ya Koro feenah, Amma Kuma sai taga feenah sama da mintuna uku Bata fito ba , a'a aka k'ara Wasu mintuna hakan yasa ta kasa jurewa ta mik'e ranta a b'ace tana hana zuciyarta yarda akan abinda feenah ta fad'a mata ta Murd'a k'ofar office d'in a fusace ta shiga Dan gasgata abinda feenah ta fad'a mata...





07066508376________
'?Follow the Mrs Sarakies=؋? =?1? HAUSA Novel Channel channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VbBRj1D35fLuSHibdq1Y

JAMI'AR TSARO

____THE WOMEN POLICE ____

NA

_____NAJA'ATU UMAR FAROOQ _____

(MRS SARAKIES =؋?)=?1?

Bismillahirrahmanirrahim

______season two ep 9?? 1??

_____________?&

A lokacin da Feenah ta shiga cikin office d'in AA Arab, ta tarar dashi a zaune kan kujerarsa yana aiki acikin laptop dake gaban sa,harga Allah shi d'aukar sa ko Wani acikin yaran sane yazo gunsa shiyasa har ya Bada iznin shigowa,saidai me,Jin muryar mace yasashi juyawa da mamaki Yana kallan wacece ta shigo masa office, feenah da ya gani a tsaye daga bakin k'ofar office d'in sa yasa mamakinsa kasa b'oyuwa, Amma saiya maze ya zuba mata ido ya Kawai yana kallan ta, sannan Kuma yaji meya kawo ta , bayan tai sallama ya ansa mata har lokacin Bai d'auke idonsa akanta ba,tai murmushi tare da sauke Kanta k'asa cikin girmamawa da wata lank'wa shash murya tace .

"Good evening sir ", ta fad'a tana rang wad'a Had'i da wata Iriyar murya.

AA Arab sai ya tsuke fuska a Mai makon ya ansa mata ,kafin yace cikin had'e Rai.

"what?.cikin husky voice d'insa

Cikin inda inda feenah tace .

"Am sir dama zuwa nai na gaida kai", ta fad'a tana d'agowa da kanta ta kalleshi.

AA Arab ya d'auke idansa daga kallan ta kafin yace.

"Alright Thanks u can go",ya fad'a a k'asan mak'oshi kafin ya cigaba Yace.

" is that All? Ganin tak'i tafiya Ya fad'a Yana watsa mata Wani kallo Dan yaga abinda nata rainin wayo ne.

Feenah kasa furta Komai tai kawai taji ya mata Wani Irin kwarjini da yawa, ga kafafuwanta da suka sage saboda abinda yay mata ,Hakan yasa ta wayence ta fara Sosa kai kafin tace.

"Ehm shikenan sir nagode bari naje "ta fad'a tana k'ok'arin juyawa.

AA Arab ya daka mata tsawa kafin ya nuna ta da yatsansa alamar warning yace .

"Keee", ta juyo tana kallon sa,ya cigaba yace

"daga yau karki sake zuwa office d'in nan bare Kuma ki K'ara zuwa gaida ni kinji na fad'a miki? Idan kuma kika K'ara zuwamin office I swear sai kinsha mamaki na" kinji ko balijiba?,ya fad'a Yana yiwa feenah Wani wulak'an taccen kallo.

Feenah ta sunkuyar da kanta k'asa kafin ta gyad'a masa kai jiki a Sanyaye gabanta na fad'uwa, jikinta har Wani irin rawar tsoro yake.

Yace "get out",ya fad'a a fusace.

A dai dai lokacin da ruky ta shigo cikin office d'in domin taji tsawar Daya dakawa feenah,take suka juya suna kallanta_ ta tsaya daga bakin k'ofar tana kallan su D'aya bayan D'aya taga suma kallanta suke, ta tsayar da idonta akan AA Arab Wanda fuskar sa take a had'e , Kuma ta sauya lokaci D'aya.take ta Gane meke furuwa,sai Kuma ta kalli feenah wacce jikinta yay sanyi k'alau itama tana kallon ruky cikin Jin kunyar k'ila fa ruky taji abinda AA Arab yay mata koh?, ruky batai mata magaba iya hararar feenah kawai da tai, ta juya a fusace ta bar office d'in ta rufu musu k'ofa tana Jin zuciyar ta na mata Wani Irin zafi.

Ganin yadda Ruky ta fita ranta a b'ace yasa AA Arab K'ara rud'ewa ya dakawa feenah wata tsawar da tasa ta tai saurin matsawa baya cikin rikicewa tana zare ido,kafin AA Arab yace a tsawa ce.

" I Said get out before a slap u", ya fad'a Yana iyowa kanta Kamar zai Dake ta, feenah ta ruga aguje ta Bud'e k'ofar ta fita tana jin kunyar duniya ta k'are a kanta ,ita dai ruky tana wajen zaman ta Amma Saida ta juyo wannan tsawar da AA Arab ya dakawa feenah ta tab'e Baki kawai Zuciyar ta na Wani Irin tafasa, feenah tana fita Bata tsaya ko a wajen ruky ba ta nufi k'ofar fita jikinta na rawa,Ruky ta bita da kallo tana mamakin Rashin kamun kai Irin na feenah,dama already tunda ta fito ta gama har had'a kayanta ta fara k'ok'arin barin office d'in tunda dama lokacin tashin ta yayi.har taje Bakin k'ofar ta kama handle d'in tana k'ok'arin fita daga office d'in ,AA Arab ya fito daga office d'insa cikin sauri a fusace ya k'ira full name d'inta,

Kamar ruky bazata juya ba sai Kuma ta juya ta Dake tana kallon sa dakyau,AA Arab ya Dan fara kame kame kafin yay k'asa da murya yace.

" Fiancee? please Ina zaki? please ki dawo magana zamuyi",ya fad'a cikin damuwa.

Ruky ta k'ura masa ido kafin ta dawo da baya babu musu ta tsaya a tsakiyar falon har sannan tana kallansa ya k'araso har gabanta Yana kallan ta da kyau Yay k'asa da murya yace.

"Fiancee! Ina fatan dai ba fushi kikai Dani ba ko?,ya fad'a Yana kallan ta.

Ruky ta k'alalo murmushi tana hana abinda ke ranta fitowa tace .

"Ni ba fushi nai ba ",

Yace .

"Amma shine naga zaki tafi bakiyimin sallama ba, bayan ba haka kika Saba min ba?", ya fad'a cikin Wani yanayi.

Ruky ta juyar da kanta gefe ,sai Kuma ta juyo tana kallon sa kafin tace.

"To me zan tsaya nayi bayan na gama aikina, Kuma ma ai lokacin tashi na yayi ko?", ta fad'a tana kallan sa.

AA Arab ya hard'e hannayen sa a k'irji Yana kallan ta kafin yace cikin deep voice d'insa.

"Nima ai bance ki zauna ba , Amma kuma naga Bakizo kinmun sallama ba , kamar yadda kika Saba shiyasa nai tunanin ko Abinda ya faru ne tunda ba haka kika Saba min ba ", ya fad'a cikin damuwa.

Ruky ta juya idanuwanta kafin ta sauke numfashi tana kallan tace.

"Ok ",sai Kuma Ta had'e hannayenta guri D'aya tana kallan sa tace"am so sorry,Kayi hak'uri na tafi", ta fad'a tana murmushi,AA Arab ya Sauke ajiyar zuciyar salama ganin Ruky ta fahimci shi yasa yace.

"Thanks for understanding me fiancee! ,but let me ask u a question? Bai jira cewar taba yace.

"Amma meyasa kika bari ta shigo har office d'ina,bayan kina zaune ta shigo Baki Hana taba"ya fad'a yana kallan ta.

Ruky ta D'an waro ido waje cikin mamaki kafin tace.

"Miye nawa aciki da zan hanata shiga office d'in ka ,nasani ko akan aikine yasa tazo gunka , infact dan me ma zan hanata shiga office d'in ka,naga ai ba yau ta fara zuwa ba, shiyasa Nima na K'yaleta, sannan nai tunanin k'ila ko kasan da zuwanta ta",fad'a tana juyar da kanta gefe had'i da tura Baki gaba Wanda yazame mata d'abi'arta.

AA Arab Yay k'asa da murya kafin yace .

"Billah!, bansan da zuwanta ba Amma fa idan har kin yarda Dani, ai kina ganin dai yadda mukai ta ita yanzu ko?na rasa Mai yake kawota office d'ina ma, Amma yau na mata warning idan har ta sake zuwa min office saina Bata mamaki",ya k'arasa fad'a on a serious note.

Ruky ta Dan tab'e Baki kafin tace.

"Alright,zan tafi lokaci na tafiya",ta fad'a da Yana yin gajiya.

AA Arab yace.

"Ok ,safe trip fiancee ,idan kin Isa gida let me know ",

Ruky ta gyad'a masa kafin juya ta Bud'e k'ofar ta fita.AA Arab ya bita da kallo Yana sauke numfashi kafin ya Koma cikin office d'in Yana Jin Wani haushin feenah na K'ara kama shi tare da aiyanawa aransa cewa dole ma saiya d'auke mummunan mataki akan feenah idan har ta K'ara zuwar masa office....

Ruky ce tsaye bakin window d'akinta wajen karfe 8 na dare,waya ce kare akunnanta sunayi ita da Hanan bayan ta gama sanar wa da Hanan abinda ya faru d'azu a office ta k'arasa fad'a cikin b'acin rai,inda daga D'aya bangaren naji Hanan tace cikin masifa.

"Kambun bala'i ,Yanzu Dan Allah ita feenah ce taje har office d'in AA Arab d'in,Kuma tai wannan abun ke Kuma kina kal??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????lan ta kome?Amma wallahi ruky kin bani mamaki da har zaki tsaya feenah ta gasa miki Irin wannan magun gunan sannan ki tsaya kina saura ranta baki fasawa shegiya Baki ba,kuma babban takaici nama dake da kika yarda da maganar feenah bayan kema kinsan halin ta sai dai kibawa Wani labari",ta fad'a cikin masifa

ruky ta sauke numfashi tace cikin k'asa da murya.

"Hanan niba haushinsa naji ba,ki Gane mana,abinda feenah ta fad'a min shine nake jin haushi wallahi".

Hanan ta jinjina kai kafin tace cikin masifa.

"Inama Ina nan ta fad'a miki wannan maganar, wallahi da saina wanka mata Mari,na buge bakiji shegiya,tunda Ita Rashin tarbiyar tata harta kai haka ,Kabi saurayi har Inda yake aiki,saurayin ma na wata daban da ban Daba naki ba,uwa uba ma ba cewa yay Yana sanki ba, bare Kuma har ki isheshi kallo "ta fad'a cikin b'acin ran abinda feenah tai.

Ruky ta sauke numfashi kafin tace.

"nidai ba wannan ba, Hanan me Zanyi Wanda zanji zuciyar ta ta daina Jin haushinsa Dan wallahi ni gabad'aya jinai Ina Jin haushin sa", ta fad'a cikin damuwa.

Hanan ta ce.

"Bansani ba, ke wallahi ruky kina da matsala kina nufin kice min wai laifin AA Arab kika gani koh yaya?,ta fad'a tana jiran ansar ruky.

Ruky ta ya Mutsa fuska kafin tace.

"Hanan! ni wallahi bansan meyasa ba banason naga wata mace ta rab'e shi ko yaya , kuma ko ba Wani abun bane ya had'a su sai naji zuciya tana Jin haushin sa", ta fad'a cikin damuwa.

Hanan ta sauke numfashi kafin tace.

"Wannan kuma duk kishine Irin namu na mata, ni yanzu abinda nakeso Dake shine kidinga rarrashin zuciyarki tare da k'arya ta_ta Aduk lokacin da Irin wannan abun ya taso miki kinji", ta fad'a cikin sigar lallashi.

Ruky ta sauke numfashi kafin tace.

"Shikenan in Sha Allah zanyi k'ok'arin ganin na daina",

Hana tace .

"Shikenan Allah yasa",

sannan tace "ita kuma feenah ki barni da ita wallahi saina mata tas, ke K'iran ta ma Zanyi a waya, wallahi saina mata rashin mutunci.ta fad'a tana huci..

Ruky ta Bud'e ido kafin tace.

"Dan Allah Hanan karki mata magana shima ya mata warning kuma idan Mai Jice ai zataji ",

Hanan tai tsaki tace.

"Ke dama ai matsora ciyace , Amma Kuma idan kishi ne kinbi kin iya,saboda haka malama Babu ruwanki ki zuba min ido kawai ",

Ruky tace .

"Dan Allah Hanan ki Rabu da ita,idan halin tane zata sake ai ",

Hanan taja tsaki tace.

"Saidai fa kiyi Amma wallahi saina yi bazan fasa ba",daga haka tace" dalla malama har kin ban haushi ma sai anjima",daga haka ta kashe wayar,ruky tabi wayar da kallo tana girgiza kai kafin ta sauke numfashi ta koma cikin d'akin..

___________?&

Wajen k'arfe 10 na daren ranar ruky ta gama shirin kwanciya kenan taji wayarta tana vibrate , Koda ta duba taga AA Arab ne tasan dama shid'in ne Mai K'ira a Irin wannan lokacin,Saida ta kusan tsinkewa sannan tai picking tai shiru takai kunne tana sauraran sa.

Daga D'aya b'angaren AA Arab ya lumshe ido kafin yace.

"fiancee!"

Ruky ta ansa masa a k'asan mak'oshi,

Yay k'asa da murya yace.

"Wai meyasa kwata kwata yau tunda abun nan ya faru bakya Wani farin ciki bayan ba haka kika Saba min ba", ya fad'a cikin damuwa.

Ruky ta Sauke numfashi tana tuno da magan ganun Hanan kafin ta sauke numfashi ta ce.

"Wallahi abinne ya Bat'a min Rai, bansan me yasa ba indai naga wata mace tazo ko kusa da kaine nake Jin zuciya ta Bata samun nutsuwa ko kad'an ,barin ma feenah wacce naga tazo ranar yauma Kuma gaji tazo ai dole na damu Koda ko Babu abinda ke tsakanin ku da ita"ta fad'a cikin damuwa.

AA Arab yay murmushi kafin yace .

"Billah idan har kin yarda Dani bani da Wani Had'i da yarinyar nan,duk abinda na fad'a miki d'azu shine gaskiyar magana, kuma kema kin Gani ai,Amma wallahi Rukayya Babu wata 'ya mace azuciyar Ahmad sai ke kad'ai,idan har kin yarda Dani Dan ni azuciya ta Daga ke ke kad'ai ce kuma daga ke Babu k'ari in Sha Allah",ya fad'a har cikin zuciyar sa .

Ruky ta lumshe ido tare da sauke numfashin salama kafin tace.

" shikenan ya wuce,but please mun Dan Allah ka hanata zuwa ",ta fad'a cikin shagwab'a.

AA Arab yace.

"Ai tun a Time d'in nai mata warning kuma nasan kema zaki iya juyowa ",

Ruky tace shikenan". thank u",

AA Arab yay murmushi kafin yace "shikenan ya wuce?",

Ruky ta gyad'a masa alamar, kamar Yana gabanta,

AA Arab yay k'asa da murya yace

"Ashe ni D'an gatane bansani ba? ,haka dama Rukayya take Sona da kishi na har haka",ya fad'a cikin sigar tsokana.

Ruky ta rufe fuskarta da tafukan Hannunta tana murmushi tare da cewa

"nidai ka bari banaso", ta fad'a cikin shagwab'a.

AA Arab yay Wani murmushi kafin yace .

"Alright na daina fiancee! shikenan ",

Ruky tace "eh " ya Jin Jina kai Kafin yay k'asa da murya yace .

"I love u fiancee!",

Ruky ta rufe fuskarta da tafukan Hannunta tana murmushi k'asa k'asa

Ya Dan had'e Rai yace.

"Bakicemin I love u Ahmad ba "ya fad'a da 'yar shagwab'a..

Ruky ta runtse ido tai k'asa da murya tace.

"I love u too ".

AA Arab ya k'ank'ame filon Dake kusa dashi Yana Jin Wani yanayi wanda ke Neman fin k'arfinsa yay sauran kawar da tunanin sa,Jin Ruky tana magana.

Daga haka suka koma hirar soyayya kamar


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login