Showing 123001 words to 126000 words out of 278032 words

Chapter 42 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1069

sunusi Bai fita ko Ina ba, sai office din jam iya dayaje, Dan har anfara campaign .gobema Yana Saka ran xasu shiga local government din Kaduna Dan yawan kanfen.Dan xaben Bai wuce sati biyu da kwana kiba, ....Washe gari AA Arab daya shigo office dinsa signing kawai yay. Dan a kan computer ya wuni , tracking din Alhaji sunusi kawai yake.yaga ko zai samu Wani information.Bayan Wanda yasa su bibiyeshi.....


Saidai duk xaman da yay kan computer,baiga Alhaji sunusi ya tafi Wani wurin ba ,ko Kuma yay Wani abun da xa'a Gane cewa Bashi da gsky ba.kuma still Yana waya da jami'an da suke bibiyar Alhaji sunusi,sun tabbatar masa suna kula da duk Wani motsinsa,haka yay sallama dasu ya ajiye wayar hannunsa,bayan ya tabbatar musu Dasu kula , sannan duk Wani bayani da suka samu su fada masa,suka ansa masa cikin girmamawa.daga nan ya fara aikin office din da xaiyi,....



?&A bangaren mamah kuwa, kawai dai rayuwa take Amma bawai tana Jin dadin duniyar ba.,Dan tun ranar data kwanta jinyar nan , bata qara samun lpy ba .har yau,da ruky take kwana aranta take tashi, kullum Saka Rai take ko xa'ace anganta, Amma shiru....yau Ruky take cika sati Daya da Bata . yanxu ita mamah harta sa aranta cewa Rukayya Bata raye.Kuma har lokacin anty mufeeda Bata koma ba , tana zaune tareda mamah Dan kada kadaicin yasa ta kamu da Wani ciwon. ya Tahir ne dai ya koma sbd yanayin aikinsa ,daga wurin aikin sai kiransa suke tayi, akan ya koma.shima kuma Dan mamah ce ta takura masa akan ya koma din, Amma yace "idan yay two days xai qara Dawo wa"... Hanan ma tana gidan har yau Bata koma gidansu ba, tana zaune tare da mamah da anty mufeeda . ita kan maman Shareef ta daina kwana agidan sbd itama tana da su shareef da jikokinta dole Wani abun sai ta na_gidan xai Yiwu, Amma duk da haka Kuma ,tana xuwa tana wuni sai dare ta tafi .....



Hanan ma gabadaya ta fita hayyacinta.ta rame ta zabge,sbd damuwa .,ta kasa tsaida tunanin ta waje Daya, kullum cikin xullumi take,tunda har yanxu babu Wani bayani ko shaida da xai nuna Alhaji sunusi shiya dauki Rukayya.,duk da haka Bata saki jikinta ba,itama tana kula da kanta , tana Kuma taka tsam_,tsam da kanta,kamar yadda AA Arab ya fada mata,. kullum cikin addu'a take Allah yasa asamu Rukayya, har yanxun dai Alhaji sunusi take xargi,..daga mamah har anty mufeeda Babu Wanda ta fadawa yadda sukai da AA Arab na xargin da suke yiwa Alhaji sunusi ,da bibiyar sa, AA yace "kar a fada musu sai bincike ya tabbatar da hakan, tukunna., itama Kuma ta gamsu da Hakan.




?&A bangaren Khalil kuwa,tunda Alhaji sunusi ya takura masa akan ya fadi inda evidence din suke ,ko Kuma idan ma wasu ya bawa, yace "ya fada masa yasa a karbo masa.". still Khalil yaki fada..dayaki fada, Alhaji sunusi yasa aka dinga gana masa azaba kala kala. Kuma har yau ba'a fasa ba . shima Kuma Bai fada ba.,Dan ya shirya fuskantar komai tunda har Alhaji sunusi ya tabbatar masa da cewa Rukayya ma ya sa andauko Mai ita.,to waye shi da baxai kashe Shiba.to anan ya qara jinjina ,Rashin imani Irin na Alhaji sunusi,. tunda ya iya sato yar Dan uwansa ya gana mata Irin wannan azabar .to waye Kuma shi da baxai masa ba,tunda yaji yace "Rukayya ma tayi taurin kai Taki fada shima Kuma Bai fada ba," sannan su yarda da sharru Dan ,Daya gindaya musu , jin haka yasa shima Khalil yaji aransa baxai taba ansa masa ba.,kamar yadda Rukayya ma tsaki fada,duk kuwa da wannan muguwar azabar da ake gana musu,. ya gwammace Hakan, Dadai ya fada din.Abu Daya ne ke sa yaji kamar xai Karaya, Shine, iyayansa. idan ya tuno dasu yakanji kamar Bai musu adalci ba,.sai dai idan ya tuno da sunan nan suna masa addu'a sai yaji wani juriya taxo masa,duk da haka shima Bai manta da ubangiji ba Yana kai masa kokensu na Allah ya kubutar dasu shiga Rukayya daga hannun Alhaji sunusi....




?&A bangaren Ruky kuwa tun ranar da Alhaji sunusi ya sumar da ita Bata tashi tsintar kanta ba,sai tsakar dare.Dan babu Wanda yaxo kanta,. akuma ranar ko pure water da Dan bread din da ake kawo mata Ba'a Bata ba,har wayewar gari .ga wata azababbiyar yunwa da takeji,duk da ba cin abincin da suke kawo mata take ci ba sosai.gashi duk ta rame tayi Baki fatar bakin ta ta gama bushewa, . kuma A Hakan Alhaji sunusi yasa adinga axabtar da ita ,har sai taji wuya ta fadi abinda yake so ,ta yarda ta_ Kuma amince da sharadin sa, Amma itama taki ansa, ta shirya karbar duk wata ukuba da zai mata. Idan ma kashe tanne saidai yayi,. Amma wlh baza ta taba bin umarnin Saba.har yanxu mamakin halin Alhaji sunusi take,ta kasa yarda Anya ko akwai xuciya akirjinsa,?Anya ko ,wannan Yana salloli biyar din da aka umarce mu da muyi?,ta kasa yarda ciki Daya suka fito da mahaifin ta,duk da tasan ciki dayan suka fito, Amma abun yayi yawa Rashin imanin yayi yawa, Bata tunanin haka, Bata tunanin Yana da imani, xuciyar sa kamar Dutse take,kai harma tafi dutsi kekashewa. Yanxu abu Daya take tunawa taji ta Karaya,wato mamah tana matukar tausayin halin da mamah take ciki,da duk Wani masoyanta.tasan tana can cikin damuwa.idan ta tono da haka ,tayi ta kuka kenan tana tsinewa Alhaji sunusi.



Yanxu ma haka tana xaune tayi nisa cikin tunanin da take., taji anbude kofar dakin, Bata tago da kan taba,sanin masu tsaron kofar da take ciki ne,ko Kuma masu gana mata azaba da Alhaji sunusi ya sasu cikin biyu baxa a rasa Daya ba..,bayan ya qaraso ya tsaya agabanta furkarsa arufe take har lokacin tunda dama kullum ahaka suke xuwa gunta ya kalleta,yace "y'allai ya kira yace kin shirya fadar abinda yake so din ki fada, Kuma kin Amince da abinda yakeson kiyi?,, ko Kuma aci gava da gana miki azavar.?ruky tai Banxa ta kyaleshi ta kurawa waje Daya ido kawai.ya qara Mai _mai ta mata tambayar.kamar baxatai magana ba,sai Kuma ta fasa ta kalleshi ido cikin ido tace "ka fada masa banshirya ba,ba Kuma xan taba shirya wa, ba ." mutumin baice mata komai ba ya juya ya fita..bayan fitarsa, saiga wasu sun shigo masu axabtar da ita din ,Daya ya shureta Daya Kuma ya Danko ta ya janyo dogon gashin ta,take ruky ta saki Kukan axaba, tana Mai kokarin kwace kanta, Amma Ina ta kasa,dayan ya kwarfeta ta xube a qasa kanta ya Dake kujera take bakinta ya fashe,suka dago ta .,suka daure ta da sarqa , sannan suka fara dukan tafin kafarta da wayar wuta, babu digon imani ko tausayi azuciyarsamu, ruky tun tana kukan harta kasa,tun tana sanin a inda take har hankalinta ya gushe ta ta sume musu a xaune Amma ko a jikinsu , su Ina ruwansu _su ai umarni aka Basu .Kuma dole su cika,idan ma basuyi ba idan Alhaji sunusi yazo sun San sauran,ata kaice ruky Batasan yaushe suka gaji suka kyaleta ba....





07066508376________
'?Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD?mode=ac_t





*____JAMI'AR TSARO____*



*____THE WOMEN POLICE ____*



*NA*



*____NAJA'ATU UMAR FAROOQ ____*



*____(MRS SARAKIES)____=?1?*




*Bismillahirrahmanirrahim*




_______season two ep 5?? 3??



___________?&


*Bayan kwana biyu.*



gabadaya ahalin gidan su AA Arab ne zaune suna yin breakfast a dining area .ko wanne cikin shirin fita yake. Amma Banda ummi, Abba shima zaije Wani company sa yau, Dake cikin garin Kaduna,AA Arab dama cikin shirin fita aiki yake already .su zuhrah ma sunyi shirin fita school.Yana zaune dining table Yana sipping coffee a cup din dish Dake hannunsa wanda ummi tai serving dinsa, plate din Dake gaban sa Kuma soyayyan Irish ne da Kwai da aka soya shima da ban,dining din yayi shiru bakajin qarar komai saina spoon.ummi ce ta dago ganin AA Arab ya mike alamar ya koshi,gashi ko Irish din ma Bai Wani ci sosai ba,tsarguwa yay da kallan da ummi take masa,yasa ya kalleta.sai Kuma yay Dan murmushi kadan tareda shagwabe fuska ya shafa cikin sa yace "I'm full wlh" ...



Abba shima kallan nasa yay,kafin yayi magana ummi ta rigashi tace "ni Ahmad bansan yaushe xaka dinga sakin jikinka kana cin abinci ba,ko sai kayi aure oho?," Abba ya dire cup din hannunsa ya zari tissue Yana goge bakinsa yace" AURE Kuma" mutumin da har yanxu ba AURENE agaban Saba sai kayi magana yace " zaiyi "AA Arab yay saurin dukar da kansa qasa Yana shafa kansa da Dan murmushi,sai Kuma ya dago ya dubi Abba Wanda yay maganar yace "in Sha Allah Abba xanyi .Ina nan Ina addu'ar Allah ya hadani da tagari.ummi ta dube shi tace ,"kullum haka kake fada tagari_,tagari,to tagarin ita xata kawo kanta tace Gani . ba dole sai annema ake samu ba.amma kai ka xauna baka nema dinba sannan kadinga fadin wai tagari, aiba kana zaune zaka samu ba,AA Arab ya langwabar da kai,ummi ta harareshi, Abba yace " hmmm kadaiji koh ,AA Arab ya jinjina kai, ummi ta kauda kai sai Kuma ta kalli Abba tace "wlh Abba abin nan na Ahmad Yana damuna, ya kamata ace yanxu ya aje iyali bawai kullum ka dinga zama godai godai da kai Ina serving dinka abinci .ba ,sai kace Kaine su zuhrah',atare Ameerah da zuhrah Dake kan dining din har sannan suka saki dariya kasa kasa , AA Arab ya wulla musu harara take suka Mike suka bar dining , suka haye sama Dan daukar school bag dinsu.,....



AA Arab ya kalli ummi yace "ummi Kinga gashi Kinsa yaran nan suna min dariya koh,?! ummi tai murmushi tace to ai abin dariyar kai,godai godai mana aiba karya nai ba idan kayi xuciya ka kawo matar auran ka Gani idan sun sake Maka dariyar.AA Arab ya kauda kai xai bar dining din, Abba ya ruko hannunsa Yana murmushi , sai Kuma ya kalli ummi da murmushi a fuskarsa yace "yau Kuma Hajiya Fatima kece kike kokarin batawa Ahmad Rai kuda ba'a jin kabku "ummi tace "nifa gsky na fada kaima aika sani ai ".Abba ya mike ya dafa kafadar AA Arab Wanda yay kicin kicin da fuska Dan wlh Allah Yana Gani shi har Yanxu Bai samu matar da tai masa ba.abba Yana murmushi yace"to Ahmad kadai ji, tunda Fatima ta magantu akan Hakan nasan gajiya tai da xuba Maka idon data takeyi ,ko yanxu tayi Maka Kara ai,Nima Kuma na gaji da ganin ka haka,saika daure kasamo matar AURE".AA Arab ya jinjina kai, ummi tace "idan ma Bai samu ba ni xan samo masa," Abba ya dawo da kallan sa Kan ummi yace"adai bashi lokacin xaifi.ummi tace "ka manta Wani lokacin ne bamu bashi ba,ko kafison ya tsufa agabanmu,"AA Arab ya saki murmushin da Bai shirya ba, Abba ma haka,AA Arab ya langwabar da kai yace "ummi tsufa Kuma? , ummi ta harareshi tace"yo ai koyanxu ma ka fara,"ya kalli agogon hannunsa yace "ummi zan tafi time na wucewa ," ummi ta qara hara rar shi tace"nidai na fada Maka tunda nema kake ka ShaShan tar da xancen ",AA ya jinjina mata kai , sai Kuma yay hugging din Abba, Abba yay patting bayansa yace "Allah ya kiyaye",AA Arab Yana dagowa yace"Amen Abba "sai Kuma ya matsa gaban ummi itama ya rungumeta" ummi ta saki ajiyar xuciya tai patting bayansa tace"Allah ya kiyaye, Allah ya kawo Maka mata ta gari,AA Arab ya lumshe idansa yace "Ameen Asaman labbansa,"sai Kuma ya saketa ya sumbaci hannun ta ya nufi kofar fita daga falon, ummi ta bishi da kallo tana binsa da fatan alkhairi....



Su zuhrah suka sauko daga sama rike da jakan Kunan school dinsu, suka qaraso har kusa da ummi Dake tsaye a dining har lokacin, Abba Kuma ya shige part dinsa Dan qarasa shirin fitar da zaiyi.zuhrah ta rungume ummi tai kissing Kuma tun ummi, tai murmushi tace "ummi zamu tafi,"ummi ta shafa fuskar zuhrah tace"Allah ya Bada sa'a Auta, Ameerah itama ta kamo hannun ummi ta sumbata sai Kuma ta rike hannun tace "ki wuni cikin amincin ya ummi.ummi tai murmushi ta shafa kanta tace "Ameen thumma Ameen tareda ku Ameerah tah", sai Kuma Ameerah tace"yauwa ummi dama Yaya ya auri ukty ikleema Kinga Yadda take mugun sanshi , ummi ta ce"Kinsan dai ba Santa yake ba,sai dai muyi patan Allah ya bashi wacce zatai masan , Ameerah ta langwabar da kai tace "Ameen,daga haka suka ce" sun tafi" ummi ta Rakasu da patan dawowa lpy,daga haka ta nufi part din Abba Dan xuwa suyi sallama......



Bayan fitar AA Arab direct office ya nufa Dan yau suna da lacture da meeting a heardquater daga kan ASP xuwa sama .Bai shiga headwater ba sai wajen karfe 10:30am Yana xuwa Kuma direct hole din ya nufa inda xa'ayi meeting din,.....



?&A bangaren mamah kuwa tana kwance akan gado tana yin bacci kamar yadda ta Saba sbd Saita Sha magani take iya bacci ,sbd kwata kwata Bata iyayin baccin ko barawo ne Bata daukar ta .daxu anty mufeeda tai mata wata allura sbd ta samu tai baccin tunda ba Yi take ba.tana cikin baccin tayi Wani mummunan mafarki .wai ga Rukayya zaune acikin Wani bakin daji daure da sarka,sai Kiran sunan mamah take da Kuma 'Yan uwanta taha kuka tana kuru ruwar su kawo mata dauki .take mamah ta farka afirgice tana addu'a tana Kiran sunan Rukayya .anty mufeeda Dake tsaye gaban wardrobe din mamah tana gyara mata kayanta ta juyo tai kan mamah da sauri tana riketa,ganin mamah ta zuro da kafarta zata sauka daga saman gadon.cikin raxana da yadda taga mamah tace "mamah Lpy?, meya faru?.mamah tana kokarin boye raunin ta tace"mufeeda Rukayya"anty mufeeda tace "me Rukayya tai Ina take, ?mamah ta rike hannun anty mufeeda tace"tana bukatar tai makonmu yanxu nayi Wani mummunan mafarki wai Rukayya tana cikin Wani Hali," mufeeda Rukayya tana raye Ina zamu sameta, innalillahi wainna ilaihi rajiun.haka mamah Kawai take fada.....



Anty mufeeda ta qara rikicewa tace "mamah please relax, mafarki ne kawai amma ba GSK bane,mamah ta rike anty mufeeda ta kura mata ido tace"mufeeda ni na tabbata wannan mafar kin danai GSK ne, Rukayya ce Rukayya na gani tana Kiran sunana akan na tai maketa.anty mufeeda ta rasa ya xatayi sai kawai tace"shikenan mamah ki kwantar da hankalinki in in Sha Allah Rukayya xata dawo cikin koshin lpy, mamah ta girgixa kai tace "Ta yaya mufeeda ta Yaya xan kwantar da hankalina bayan bansan halin da Rukayya take cikiba?"anty mufeeda ta rungume mamah, cikin dauriya da Hana kanta kuka tace "bansan me kike jiba mamah, Amma Nima Ina Jin kwatan kwacin abinda kike ji . Allah ya bayyana Rukayya, mamah ta qara rungume anty mufeeda tana Jin jina kai, Amma batace komai ba sun Dade ahaka kafin su saki juna,anty mufeeda tace da Mamah ta kwanta babu musu ta kwanta samon gadon,ta kurawa pop din dakin ido tana xubar da hawaye,sai yaushe, sai yaushe zata fita daga cikin damuwar nan,sai yaushe Rukayya xata dawo gareta,haka ta lumshe idanta tana sake sake cikin ranta anty mufeeda ganin mamah ta kwanta yasa anty mufeeda ta jingina jikin wardrobe din tana Mai share hawayen ta., tana tausayin mamah, lallai ta jinjinawa kokarin mamah ba qaramin dauriya mamah take ba 'yarka budurwa a nemeta Sama ko qasa arasa, bakasan awani Hali take cikiba,ta daga hannun ta Saka tace "ya Allah ka fimu sanin abinda yake aboye ya Allah ga baiwarka nan Anne meta sama ko qasa,ya Allah idan tana raye Allah ka bayyana ta cikin aminci, Allah karka bawa duk Wani azzalumi damar cutar da ita,Dan Alfarmar Annabi Muhammad (s a w )e&?.ya Allah ga baiwarka nan mamah tana cikin damuwa har Hakan na kokarin taba lpyarta .ya Allah kayi gaggauwar bayyana Rukayya aduk inda take,kasawa mamah hkr da juriya ya Allah ka san ya ya mata ranta,"daga haka ta share hawayen ta cigaba da gyaran wardrobe din...



__________?&


Abangaren lateef har yanxu ya kasa hkr da Rukayya,ya kasa yarda Rukayya ta Bata , Anne meta sama ko qasa anrasa duk yadda zaiyi yaga ya samu inda Rukayya take yayi Amma abin yaci tura tun Yana iya boye damuwarsa har abun ya fara fin karfinsa,yayi Neman yayi cigiyar Amma kwata kwata Bai samu inda Rukayya take ba, ko Kuma Jin labarinta kamar yadda abin yake.haka kawai zakiga yayi tagumi musamman idan Yana gida ko Kuma part din Hajiya SA'A,,tun Hajiya SA'A Bata lura ba harta Gane,ta dinga Masa masifa tana "Yana kokarin Dorawa kansa hawan jini,akan yarinyar da kila ma guduwarta tai,tabi samari. kila tana can hankalinta kwance",idan lateef yaji Hajiya SA'A ta fadi wannan maganar to sai yayi kokarin Yi mata rashin kunya,...



Da cewa ko me xata fada shi yaji ya Gani Rukayya yake so, Hajiya SA'A saidai ta saki Baki tana kallansa,tsabar mamaki,tayi tayi ta dawo da lateef kan hanya ya kyale batun Rukayya Amma ta kasa shawo kan lateef, Alhaji sunusi yasan ko meke furuwa, Amma sai yayi kamar baisan komai ba,Dan shi yanxu hankalin sa ma Yana kan zabe,Bai fiye xuwa wajen Rukayya ba, Saidai yasa ai mata yadda yake so.....



Khalil ya fita hayyacinsa ya rame ya kode jikinsa duk tabo ne,na wuta da dukan wayoyi,ga horon yunwa da aje musu A yanxu..yanxu haka Yana xaune Amma tunaninsa da hankalinsa Suna kan Rukayya.tausayin Rukayya kawai yake ji domin yasan itama anacan ana gana mata azabar, yasan Bata Saba ,ba kuma xata iya dauka bane .shi kansa tun Bai Saba da axabar da ake gana masa ba . gashi harya Saba,bauta kuwa babu kalar da bayayi, addu'a kawai ita ya rika akoda yaushe,sallah Wani lokacin idan Bai samu ruwa ba, tai mama kawai yakeyi .wanka kuwa haka bama a zancensa, Dan kuwa Saida nutsuwa ake yinsa to Babu nutsuwar,...



?&Rukayya tun wannan dukan da aka mata Saida Ta kwana ta wuni Batasan Ina kanta yake ba,xuwa Yanxu ta tabbatar da Alhaji sunusi kila ya fita daga cikin musulunci,Dan wannan azabar dayake sawa ake mata .Mai cikekken imani baxaiyi haka ba.kuma har Yanxu tana kan bakarta babu ranar da xata fito ta fadi ba'a gana mata azaba ba, Gashi ta kasa sabawa da Hakan har yanxu,. yanxu haka kwance


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login