Showing 15001 words to 18000 words out of 278032 words

Chapter 6 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1019

tace suna shigowa indai lokacin shigowar tasu yayi ruky ta jinjina kai,dai dai nan Kuma Khalil ya shigo bakinsa dauke da sallama , suka ansa masa ,ya gaida ruky cikin girmamawa,ta ansa masa da fara'a,tace ya gajiya malam Khalil,yayi murmushi yace Babu gajiya ranki dade,...

Ruky tace akwai mana tun fa safe kana nan yayi murmushi yace Babu komai ranki dade tace Allah yasaka da Alkhairi,ya dan Bude ido yace haba ranki dade Dan Allah karki qara godemin akan wannan domin yiwa Kaine tace gsky ne wannan malam Khalil,...

Tace Dr ko yaxo yace eh yaxo dama shigowar da nai kenan na fada miki, ruky ta mike tace muje to ta kalli baba lami tace baba bari muje likitan Yaxo baba lami tace to shikenan Jama'a saikun dawo , Allah yayi albarka daga haka suka nufi kofar fita,..


Suna xuwa dama komai anriga da ankai na ganin file din nasu(file din shafa )tun jiya yanxu jiran Kiran Dr kawai suke jira ,Dan mutane yake gani sosai domin babban likitane,ana xuwa kansu, ruky ta shiga ,inda ta samu kujerar Dake passing dinsa ta xauna,inda ta gaida shi cikin harshan turanci ta nuna masa I'd card inta,ganin police ce yasa shi nutsuwa sosai tare da Bata dukkan hankalinsa,inda ta koro masa abinda ke damun shafa,yace zaishigo har dakin da take yaxo ya ganta,..

Haka Ruky tai masa godiya ta mike ta fito, ibrahim Khalil ya tareta suka jera suna tafiya ta fada masa yadda sukai da Dr, Khalil yace ai babu komai, haka suka wuce dakin da aka kwantar da shafa, suna xuwa kamar da 45 minutes saiga Dr ya shigo, inda baba lami da Khalil suka fita aka bar ruky sai Dr, alokacin shafa ta tashi allurar baccin da akamata ta saketa, bayan ya qarewa shafa kallo Batare da da ya tabata ba ya Kalli Ruky yace tabiyo office haka ta bishi,bayan sunshiga cikin office din Inda yace cikin harshan turanci, yace yarinyar ganie Dr xata Gani( Gani Dr likitar mata) sbd wannan abun dole saidai ita,sbd itace xata dubata ciki da Vai sosai,ruky ta Sauke numfashi tace itama cikin harshan turancin yanxu ayina xamu ganta yace akwaita a asibitin nan but sai ranar Wednesday take xuwa,tace ya xamuyi da yarinyar nan,yace Babu matsala tunda ana treatment dinta yadda cutar baxata cigaba da cinye taba ruky ta sauke ajiyar xuciyar salama tace Nagode Dr,yayi murmushi yace ur welcome Mrs da sigar girmamawa,daga haka ta fito ta wuce dakin da akwai kwantar da shafa tasamu baba lami da Khalil ta fada musu duk yadda sukai da Dr, Khalil yace ai babu komai ma hakan indai har xa'a dace,baba lami ma tace wlh Babu komai jami'a ahakan ma ai munsamu Kuna kokari saidai Allah ya biyaku da mafificin alkhairi, Allah dai ya Saka muku da Alkhairi suka ansa da Ameen , suka qara duba shafa sannan suka fito sukaiwa baba lami sallama suka tafi,inda ta ansa da Ameen sukace sai sun dawo, suna fitowa ruky ta kalli gari ta Kuma Kalli time ganin time din magrib is approaching yasa ta sauke numfashi suka shiga mota inda suna tafiya suna hira da Khalil sama sama Wanda Rabin hirar tasu a kan shafane,hardai ta kawoshi unguwar su inda ta ajiyeshi,ya juyo ya duveta yace ranki dade,tace na'am,ganin yadda mood dinta ya canxa tundaga fitowarsu ya lura da Hakan,yace karki damu Kanki in Sha Allah everything will alright ,ta sauke numfashi tace in Sha Allah,yace gobe Monday nasan kina da aiki indai baxaki Samu time din xuwa gunsuba, karki damu ni sainaje svd aikinku ku Yana da tsari ,ta dube shi tace a'a Khalil ku mafa naku aikin ai Yana dashi ,,yayi murmushi yace ni Ina samun time sosai ranki dade kawai duk abinda kikeso aimusu indai kina ganin bakida lokaci,ko Kuma bawai yaxama lallai kixo bane karki damu ki Kirani, kanki tsaye kawai ,ruky ta Sauke ajiyar xuciya tana kallan Khalil kawai , saikuma tace masa da Wani Baki xan gode maka yace Babu godiya tsakanin mu rankidade ni na dauke kine amatsayin yar uwarta kawai, ruky tai murmushi tace Nima Haka malam ibrahim Khalil nagode sosai ,yayi murmushi yace Babu komai,daga haka ya sauka daga motar Yana mata Allah ya kiyaye,Inda itama ta ansa masa tana maiyin reverse ta wuce gida,

Tana xuwa gida ,tun kafin tai parking taga motar Shareef take gabanta ya fadi ,tana addu'ar Allah yasa mamah batace WA Shareef komai ba akan fitar tadai Dan indai ta fadawa Shareef cewa taje duba Hanan Bata da lpy ne kila a iya harbo jirginta, saikuma tai tuna nin tunda ba Kiran Hanan din xasuyi su tambaya ba aishikenan,haka dai tai gundun balar shiga gidan kanta tsaye,


*GIDAN AMEENAH*

Yau gabadaya da xaxxabi na tashi Mai mugun xafi na tashi ga cikina kamar anmin yasa svd yunwa gashi har qarfe bakwai da Rabi yanxu,Kuma Ina tunanin Kabiru be dawo va tunda banji motsin Saba,gashi banida ko kwayar gero agidan,haka na mike da bin bango na nufivDan kitchen Dina inda na kare masa kallo Dan Wani biyu biyu ma nake Gani,kwanikina ne kawai sai Kuma Wani vuhu inda na nufi buhun na jawo shi ko zan samu ko kanxo ne a Irin Wanda maman saude take Aiko min dashi ,dan mokociya tace duk da akwai tata tsakanin mu Amma dai ahakan itace a kusa dani danni gidana shikadai yake,ita kadai ce wacce tasan halin da nake ciki sbd Ina Jan yarta ajiki Kuma itama ina mata kitson,duk da ban fito fili na fada mata Damuwa taba amma tana gane halin da nake ciki,duk da ta fini dan a haife ma takusa hai fata kawai dai tana da kirkine ,kuma tana tausayina,haka na duba buhun na jawo wata bakar Leda na matsa Ina addu'ar Allah yasa abincine,Aiko Ina budawa naga kanxo ne take naji sanyi araina,haka na juyoshi a kwano na fito xuwa bakin randata naji 'Kashi, Saida ya jiku sannan na shiga daki na dauko maina Dana boye a Kasan gado sbd indai na barshi Kabiru ya Gani wlh shima saiya rabani dashi, haka na xuba bayan nasa yaji,inda na xauna na cusasi sbd yunwa bama na barin na bakina ya qare nake qara Wani akai, haka na cinye tas na kora da ruwa,inda sai alokacin na dawo dai dai , Amma sai me ba'a minti biyu ba na amayoshi ,Saida na amayar dashi tas,na kwanta awurin Ina sauke numfashi,na shiga tunanin yadda baba asabe ta dinga bangaroni daga jikin ummah akan wai dole saina dawo gidan kabiru,narasa Mai naiwa baba asabe datasa dole saidai baba ya AURAmin Kabiru, Wanda gashi babu abinda nake Sha sai bakar wahala a wajensa haka hawaye ya dinga xubomin banima da qarfin daxan sharesu sbd Wani mugun xaxxabi Daya rufeni,.....
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD


*____JAMI'AR TSARO____*


*____THE WOMEN POLICE____*


_____THIS STORY IS TOUCHING HEART, I WAS SPEECHLESS TO EXPLAIN IT, BUT WE SHOULD SEE ON WHAT HAPPENED TO OUR LIFE KNOW SO, BE WITH ME U LOVE IT MORE THAN U EXPECTED _______
'?


*NA*


*____NAJA'ATU UMAR FAROOQ____*


*____(MRS SARAKIES)____*


*=?1?QUEEN OF WRITERS ASSOCIATION (QUWA)=?1?*


*Bismillahirrahmanirrahim*


_____season one ep9??


________
'?
'?

Tana shiga folon ta tarar da Shareef kan Daya daga cikin kujerun falon inda ya Mike yace da mamah bari yaje masallaci ya dawo Jin ana kiraye Kirayen sallah haka ya mike dai dai lokacin da ruky ta shigo dakin bakinta dauke da sallama ,suka ansa mata mamah tace au gatanan ma ta dawo, Shareef yace AUTA Ashe dubiya kikaje yanxu nake tambayar mamah, ruky ta qaraso cikin falon tayi murmushin yake tace wlh yanxu nadawo, yace ya maijikin tace da sauki yace Allah ya qara lpy,in Sha Allah xankirata na mata yajiki ai bansaniba,...

Cikin fuduwar gaba ruky tace ai tamaji sauki basaika kira tava, Shareef yace,oh nikenan karna samu ladan kenan, gashi kinje harda bubiya , ni Kuma dabanje dubiyar ba ,aisaina kirata,mamah tace Aiko dai yaka mata Shareef , Dan naga Auta kwana biyun nan San xumunci take ta San lada,daga haka tace ni bari naje nai alwala daga haka mamah ta wuce, Shareef yace Aiko xankirata mamah daga haka yace bari naje nai sallah saina dawo,yasa kai ya wuce masallaci,ruky ta ansa masa ta haura sama itama, ruky tana shiga ta sauke ajiyar xuciya,ta cire hijab dinta,ta wuce bayi Jin ana kokarin shiga sallah,tai Maza Maza tai alwala ta fito,...

Ta tayar da sallah tana gamawa tai azkar,ta sauya kaya ta sauko kasa ,ta tarar wannan Karan harda ya Hanaf suna hira,ta karaso falon ,ta gaida ya hanaf ya ansa Yana kallonta, Shareef yace ni baxa a gaida Niva,ta harareshi tace wazai gaida kai,yace aikinsan dai na fiki koh ,tace Dan ka fini aiba harfata kai ba,uban San girma ta fada tana hararar sa, mamah tace aitunda ya fiki ai zance ya qare,uwar San girma, Ruky ta tura Baki gaba tace wlh mamah duk ke kikesa Shareef yake rainani ,mamah ta Bude Baki tace auta kinfi karfina , Shareef yace mamah Rabu da ita, dan taga munyi class dayane Kuma yanxu muna aiki wuri Daya duk shi yasa,mamah tace Shareef dai yafi ki ,ta qara hararar sa ,yayi dariya sanransa, sannan ya mata gwalo,ta dauki filon kujera xata wurga masa yace mamah kin ganta koh ,mamah tace ai Bata isa ta buga Maka filo agabana ba, Ruky ta cika tai fam tace Amma mamah ai kina ganin Yana tsokana ta,mamah tace bakonka annabinka Auta ta,ni bangani ba,ruky ta tashi tai hanyar stairs,ya hanaf yayi dariya yace mamah kintavo mana Auta ya ZA'Ayi baxaki rarrashetava, mamah tace sun Saba indai ita da Shareef ne,Jin ana Kiran sallahn isha'i yasa su mikwa gabadaya suka tafi ,da suka dawo haka aka gabatar musu da abinci sukaci gabadayansu harda ruky wacce alokacin har sun shirya ita da Shareef dama haka suke kodan abokan wasa ne,...

Inda suka Dan tava hira da Shareef bayan sungama cin abincin sundawo falon ,kafin yayi musu sallama, mamah tace ya gaida mata yayar ta da kyau da kyau,yace xataji in Sha Allah, haka Ruky ta rakoshi har compound din gidan kafin ta koma ciki,...

Washegari Monday haka ruky ta wuce wajen aiki,inda ta tarar da zasuje sabon gari xasu kamo wata mata data daki kishiyarta,shine Yan uwan matar suka kawo qara sbd ta ji mata rauni sosai ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????Kuma shi nijin Bai dauki mataki ba ,yanxu haka ma matar tana gadon asibiti,haka suka kamota,inda aka Saka matar a cell,bayan ruky ta tashi daga aiki Saida taje ta duba jikin shafa,ta samu tana barci domin yanxu tana samun hutu sosai,Bata xauna ba ganin lokaci yana kurewa, Dan haka taiwa baba lami sallama,Dan Bata samu Khalil ba,baba lami tace yanxu babu dadewa ya tafi Dan sun kusan wuni dashi a asibitin, ruky taji dadi sosai,baba lami ta kuma tabbatar mata da cewa Khalil Yana musu kokari shima,haka ruky tai wa baba lami sallama ta tafi bayan ta Bata kudi wai ko xasu nemi Wani abun,..

Baba lami taki karbar kudin tace ai su babu abinda xasuyi da kudi tunda babu abinda xasu siya komai Yi musu akeyi , ruky tace nidai baba Baki nai kawai bawai sai Kuna bakatar Wani abun ba,baba lami taki karbar tace ai wahalar ma take ta isa koma take kanyi,ganin taki karbar kudin yasa ruky aje mata tai mata sallama ta tafi,haka baba lami ta dinga Saka mata Albarka,tana mata addu'ar gamawa da duniya lpy, Allah Kuma kareta a duk Inda take, ruky tana fita tasaka Kiran Khalil awayarta,bayan sun gaisa tace masa yanxu naje asibitin ancemin daxu kaima ka tafi ,daga Daya bangaren Khalil yace wlh koh ranki dade ya aikin tace Alhamdulillah,ya naka Aikin shima yace lpy lau,suka Dan tava hira sannan sukai sallama,bayan ruky ta Isa gida ,harta huta ma ,bayan ta idar da sallah tana zaune kan sallaya,taji wayarta tana vibrate ta shafa addu'a ta mike ta Isa inda wayar take,tana ganin me kiran take ranta ya Baci,...

Ta Kyaleta ,ta cire hijab dinta da xanin data dora akan rigar da take jikinta Dan iya gwiwa ta tsaya mata Kuma Mai qaramin hannu ce,sai gashinta data daure da ribom Wanda ya sauko har tsakiyar gadan bayanta Wanda yake reto,ta matsa ma kusa da wardrobe dinta tana jera kayan ta da aka wanke aka goge tun juya, tana Jin wayar ana ta kira Amma Batai picking ba, Kuma ba'a fasa Kiranba,kawai sai taji anbude kofar dakinta an shigo babu ko sallama, Hakan yasa ta juyawa tana mamakin waye,Dan itadai babu Wanda yake shigo mata daki sai anyi knocking ta Bada ixni tukunna,...

Ganin Wanda ya yashigo da batai tsammani ba yasata cillar da rigar da xata Saka acikin wardrobe din ,ya qaraso cikin dakin ruky tai baya ganin ya nufota,saikuma ya tsaya yana kare mata kallo Yana taune lips, Ruky ganin inda yake kallo yasata duba jikinta saitaga Ashe wannan shigar ce ajikinta Dan haka tai Maza xata wawuro hijab dinta a inda ta ajiye ya rigata dauka,Hakan yasa ta tai baya ta nufi wardrobe dinta ta lalumo Wani hijab din, tasa saikuma ta juyo ganin Yana a yadda ta barshi still yasata hade Rai tace meyasa xaka shigomin daki haka kanka tsaye babu knocking babu komai ,kasan a Irin yanayin da xaka tarar Dani,ta fada tana kallansa ranta yana qara baci,har lokacin baiyi magana ba kallan ta kawai yake,taja tsaki qasa qasa tace Dan Allah ka fita , maimakon ya Bata ansa saiya jefo mata tambayar meyasa bakya picking call Dina idan na kiraki ,tai Banxa ta kyaleshi yace Ina tambayar ki ,ta dago ta qara hade Rai, still batai magana ba,ya fara matsowa kusa da ita Dan haka tai sauri ta haye saman gado ta tsaya sbd shine gab da ita,ta qara tsuke fuska tace ya lateef kafita min daga daki,ko Kuma wlh Allah nai maka ihu ,ta fada jikinta na rawa,yace wlh ko kiban ansa ko Kuma wlh nai miki abinda bakya tunani,tace to muje falor saina baka ansar yayi tsaki yace ni anan nakeso ki bani,ta turo Baki gaba tace ni Banga Kiran kava, lateef ya qara tsuke fuska yace Baki ganiba har yanxu Dana kiraki shima baki gani ba kenan ,ya fada Yana watsa mata Wani kallo, tai Banxa ta kyaleshi,ya nufota tai hanyar toilet da gudu tana ihun Kiran sunan mamah, Amma kafin ta isa toilet din ya dankoto ya hada ta da jikinsa Yana kallan yadda take kokarin kwace kanta jikinta na rawa,tana ihun Kiran sunan mamah,ganin haka yasa ya toshe mata Baki,yace ki nutsu kimin mgn ko Kuma wlh nai abinda naga Dama Dake ,taki tsayawa tana kokarin kwace bakinta da ya toshe mata Dan kartai ihu,tana kokarin yin amai sbd gabadaya warin giya yake,ganin taki tsayawa yasa shi kokarin cire mata hijab ,ganin haka yasa ta Bude ido tana kallansa hawaye na xubowa idanta tana girgixa masa kanta tana masa magiya da idonta,...

Yayi murmushi yace akace bakya ji ,kinsanni, ba sanin bari nai ba koki fadamin ko Kuma wlh nai abinda naga Dama ,yace xakiban ansa ko Kuma nai abinda nace din da sauri ta gyada masa kai ya saketa,tai sauri tai baya tana xare ido ga amai yaxo mata ,haka tai sauri tai hanyar toilet,ta dinga kwarara amai kamar xata amaryar da hanjin cikinta,bayan ta gama tasawa kofar key Dan ko ganin lateef batasanyi,haka lateef ya bita da kallo Yana qara Jin Santa na mamaye duka sassan jikinsa,..

Ganin tasawa kofar key yasashi sakin murmushi ya qarasa kusa da toilet din dan ya tabbata baxa ta Bude ba, yace ki Bude just ki fito ,tai Banxa ta kyaleshi yace magana fa nake miki ko saina balla kofar na shigone,ruky ta fashe da Kuka,ganin tana kuka yasashi sassauta murya yace please ki budemin Beb e&?,ta qarasa sautin kukan nata,sai Kuma yace ok nine I'm sorry dear wlh kece kika Bata min Rai shiyasa nai duk abinda nai din Amma wlh not intentionally, kina Ganin fa bana qasar sbd ke na dawo sbd bakya picking call Dina, haba dear, Amma na dawo babu well coming Dina babu komai kika Bata min Rai ,nanma ta kyaleshi kukanta kawai take,ya furxar da iska Mai xafi yace please ki fito muyi mgn,nan ma Bata tankashi ba, ganin baxata fito ba yasa shi cewa shikenan xan tafi but please idan na kiraki kiyi picking call Dina, idan Kuma bakiyiba wlh kinsan ni sarai ,bani da kyau,daga haka ya fice,ruky ta Sauke ajiyar xuciya Jin rufe kofar alamar ya tafi,ta kife kanta da jikin kofar tana kuka qasa qasa saida tai kukanta Mai irsarta Sannan ta hkr yaushe lateef xai kyaleta,yaushe xai gane ita ba sanshi take ba,Amma duk da haka Bata fitoba,Saida tai wanka domin gabadaya jitai tana warin giya kamar itace tasha,tai tsaki kusan 30 minutes tana wanke jikinta sosai sbd gabadaya jitai tana tsantsanin jikin ta,itako me xatai da lateef ko mazan duniya sunkare,ai wlh koshi kadai ya rage autan mazan duniya Wanda be AUREBA wlh gara ta mutu babu auran da dai ta AURI lateef,haka dai tai wankan sannan ta fito bayan ta dauro alwala sallan isha'i,taje Tai Maza ta sawa kofar key sannan ta wuce gaban mirror ta shafa lotion dinta ta feshe jikinta da turaruka masu bala'in kanshi,sbd gabadaya jinta take atakure tunda har laleef ya tabata,tai tsaki yafi cikin carvi tana yiwa lateef Allah ya isa sbd tabatan da yay,...

Haka ta shirya ta tada sallah bayan ta idar tai azkar, sannan ta mike ta haye gado,ta lumshe idanta tana fatan bacci ya dauketa Dan ko kasa jitai Batasan sauka Dan karma ta hadu da lateef duk da tasan bama xama xaiyi ba,tana tunanin mamah tana Ina lateef ya shigo mata daki kusan mintuna 20 aka mata knocking har bacci ya fara daukar tace waye, atsorace,Dan wlh tayi mugun tsorata da lateef, baba hasiya tace nice uwata, ruky ta mike taje ta Bude mata, baba hasiya tace uwata Hajiya tace ki fito kici abincin,ruky tace ya lateef ya tafi, Baba hasiya tace a'a lateef din xuwa gidan yay,ganin baba hasiya Batasan xancen ba tace kice ma mama nakoshi ,bacci nake ji, Baba hasiya tace uwata kindai San Hajiya baxata bari ki kwanta Bakici abinci ba,tace baba hasiya Dan Allah kice wlh a koshe nake


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login