Showing 126001 words to 129000 words out of 278032 words

Chapter 43 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1087

take cikin wannan halin taji anbude kofar dakin da take ciki ,tasan bazai wuce xuwa akai adora daga inda aka tsaya ba .idanta alumshe yake sbd axaba ,da kyar ta iya Bude idanta ta xubawa Wanda ya shigo din. bayan ya shigo ta xuba masa ido kamar yadda shima yake kallanta yana Yi mata murmushi kafin ya fara struggling a cikin dakin itadai kallansa yake bata ko kiftawa.....


Ya sauke numfashi Yana jinjina kai yace"Rukayya umar MaiTama",sai Kuma ya tsaya ya xuba mata ido,ya Wani mele Baki , yace", wannan ya xamto xuwa na qarshe da zan miki keda wancan qasqantaccen Dan jaridan,wlh daga yau idan Baki fadamin ba,wlh next time idan nazo,wlh kashe ki Zanyi, Kuma karki dauka sawa Zanyi, a'a ni da hannuna xan rabaki da ranki,idan Kuma kin Musa Allah ya kaimu lokacin, sannan daga wannan satin ba lallai ki qara Gani naba may be sai bayan naci xabe so gara ki fadi abinda na umarce ki dayi kafinnan kafin sati Daya, Rukayya ta xuba masa ido tana kallansa kamar yadda shima yake kallanta,...



Tace "meye ribarka idan ka zalinci Wani sbd duniya,da abinda ke cikin ta,bayan duniyar ma barin ta xamuyi,babu Wanda xa'a bari yayi gadinta, uncle sunusi kaji tsoron Allah, kaji tsoron ranar Saka mako. wlh duk wannan abin da kakemana Allah Yana ganin ka Kuma baxai barka haka ba,Kuma ni har yanxu Ina kan bakata wlh saidai idan kashe nin xakayi kayi Amma wlh baxan tava canxa ra'ayi ba., Alhaji sunusi yay murmushi yace "oh haka kikace ".Rukayya tana share hawayenta tace "eh kaka ba fada" Alhaji sunusi ya matso kusa da ita yace "naga alamar har yanxu wannan horon danasa ana miki baya shigar ki, lallai xan sauya Wani,Dan so nake ki tafi lahira da taban buna,sai Kuma ya nuna ta da yatsa yace "daga yau ki fara kirga kwana kin barin ki duniya, Rukayya tai murmushin takaici tace"bazan fara ba,idan kaga na bar duniyar nan to dama kwana nane ya kare ,sai dai kai kazama Sila amma baxaka taba kashe niba, Alhaji sunusi ya juya ya nufi kofar fita daga dakin, haryaje bakin kofa ya juyo Yanuna ta da yatsa yace "daga yanxu xaki San ba wasa nakeyi ba,wlh sai kin gwammaci mutuwarki da abinda na tana dar miki,Kuma ki jira xakiga sauyin axabar danace ZA'A Yi miki,Dan sai an linka wacce ake Yi miki akan ta da . daga haka ya fita daga dakin, Rukayya ta jingina da bangon dakin ta rintse idanta tana ambatan sunan Allah,ko xuciyar ta zatai sanyi,Dan kukanma yanxu saita nemeshi ta rasa.....






07066508376________
'?Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD?mode=ac_t





*____JAMI'AR TSARO ____*



*_____THE WOMEN POLICE _____*



*NA*



*____NAJA'ATU UMAR FAROOQ ____*



*____(MRS SARAKIES)=?1?____*




*Bismillahirrahmanirrahim*




______season two ep 5?? 4??



__________?&


AA Arab sunyi xuga sun nufi wannan daji na iyaka Kaduna da Abuja,kamar yadda zailani ya fada masa. Saida sukai kwana biyu suna shiri Dan xuwa wannan daji sbd Basu San me zasu tarar acan ba.wajen karfe shadaya na dare suka tafi, Amma Basu isa ba sai wajen karfe shabiyu da Rabi na dare,daga kan AA Arab, CP, DCP da sauran manyan police jajirtattu.AA Arab Bai kyale kowa ba,Dan CP Bai so xuwa bashi ,dan Alhaji sunusi ya "takura masa akan ya sawa zailani gubar Daya bashi yasa masa ko Kuma allurar, acikin biyu yayi Daya.saidai idan yaxo zai aiwatar da shirin nasa sai kawai kiga police din da AA Arab yasa su kula da zailani suki matsawa nan da nan .Kuma shi ba abun yace su fitaba idan Wani Abu ya samu zailani xasu iya cewa shine.dan ya kula suna Ankare da duk Wani motsinsa,Ya rasa Taya ma zaiyi ,Dan kada Azargeshi ......



AA Arab Saida ya bawa kowa position din da zaibi ya kasance,sunyi Lambo sunyi taku Dan kada Wani Abu da zai reaction agane cewa sun shigo dajin Dan motocin Suma acan farkon dajin suka barsu Basu shigo Dasu ba sunbar wasu police din awurin Dan suyi monitoring motocin nasu,Dan komai Saida dubara.sunyi tafiya daga bakin titi xuwa cikin dajin nan daya kai kusan kilo meters bakwai.kafin AA Arab ya iya gano Wani dogon tsohon Gini a Wajen take kowa ya nutsu suka fara gyara gun dinsu suna Kuma tun karar wajen, saida suna gab da Isa wurin sannan AA Arab ya dakatar da wasu daga cikin jami'an, ganin ya fara hango wasu daga cikin 'yan ta'addar, wasu suna zagaye inda inda suke sbd Suma kullum cikin shirin kota kwana sukeyi,AA Arab yayiwa jami'an alama da yatsunsa guda goma ,yay musu nuni da su zagaye ginin gaba Daya cikinsu kuwa harda CP babu musu sukai yadda ya umarcesu,sai Kuma ya qara alama da yatsunsa hudu,akan su biyo shi ,babu musu Suma suka biyo shi,haka ya rarra Basu, cikin wadanda suka bishi cikinsu akwai DCP sai wasu jami'an guda uku,sai shi AA Arab cikon na biyar din.....



Tafiya suke cikin sanda ,AA Arab yay musu ja gaba suka fara binsa abaya cikin iya taku na police idan xai kama criminal,suka fara tun karar inda mutanan suke ta wajen kofar shiga wurin.sai dai suna gaf da nufa suka hango wasu daga cikin "Yan ta addar wasu a tsai tsaye da bindigu ahannun su,wasu Kuma suna daga bakin kofar wasu Kuma suna kwance,CP dashi da tawagarsa suka fara bin ciyayi suna buya suna Lambo Dan kada 'yan ta'addar su ji motsin su ko Kuma su gansu .da haka da haka har sukai nasarar xuwa bayan dogon ginin suka zagaye shi ,kafin kice me tuni sunyiwa wajen qawanya.yanxu abinda kawai suke jira umarnin yin harbi kawai suke jira daga wajen AA Arab. danga air pode a kunnan CP . Wanda suke communicating da AA Arab .AA Arab ko _shima da tawagarsa tuni Suma suka tsugunna ganin 'yan ta'addar sun fara hankalta dasu Dan har wadanda suke tsaye sun fara Ankara da jin Wani sounds Wanda basu Saba dashi ba . kamar akwai Wani Abu Dake shirin tunkaro inda suke.Daya daga cikin Yan ta'addar ne Wanda ke tsaye ya juya ya kalli Daya daga cikin Wanda ke kusa dashi shima tsaye yace "tsaya kamar fa taku nake ji anan ?Wanda ake fadawa maganar ne ya Dan kashe kunne alamar saurarawa shima yaji, saidai me babu Wani motsi dayaji ,ya dubi dayan yace " nifa banji motsin komai ba"daga haka ya juya ya cigaba da smoking din sa,ya bishi da kallo kawai Dan shi gsky akwai Wani Abu da yake ji kodai shi kadai yakejin alamar motsin ne, kawai saiya matsa kusa da Wanda ke zaune Yana xuqar sigari yace baba wai bakaji Wani motsi ba,Wanda aka kira da baba yace "ayina?ganin shima da da alamar baijiba yasa ya matsa daga kusa dashi ya kunna sigari shima ya fara xuqa ......



Haka kawai yaji hankalinsa Bai kwanta da wannan bakon sounds din dayajiba, Kawai saiya jefar da sigarin hsnsunsa cuwa qasa yasa kafa ya murtsuke ta ya gyara ruqon bindigarsa ya nufi hanyar da zata sadashi da shiga building din,ya tafi dan sanar da ogansu wato goga abinda yaji tunda su sauran Basu jiba ..,goga Yana falon zaune. agefe guda kuma ga wasu Yara Irin wadanda suka satowa su kawosu nan su ajiye kafin ranar da xa'a daukesu a fitar su daga qasar Irin wadan aturance akeciwa human trafficking masu safarar mutane kenan.suna akwance a qasa wasu adaure suke wasu Kuma suna zaune.Kuma ba iya na falon bane kawai akwai wasu a cikin dakunan dake cikin wannan qaton building din.bayan goga akwai wasu Yan ta'addar sunkai su goma zagaye da yaran suna gadinsu,wasu Kuma suna gadin na dakin .Dan kadama suyi yunqurin guduwa .ya qaraso wajen goga Wanda ke kishingide Yana gyan gyadi ya taba shi .goga yaji an taba shi, take ya Bude idansa Wanda ke cike da bacci ga binduga ahannunsa. dan tun lokacin da aka kama zailani shikenan gabadaya kullum acikin xullumi suke dan sun tabbatar zailani idan yaji wuya dole ya fadi inda suke, Kuma Koda yaushe ZA'A iya kawo musu hari shiyasa kullum cikin shiri suke. da Kuma rarrabuwa sbd tsaro ,ya dubi Wanda ya tabashin goga yace "lpy"dayan yace cikin Yanayin muryar sa "oga nifa kamar fa motsi naji awaje Ina tsaye. Kuma na tabbatar da haka",goga ya mike xaune daga kishingidan dayake yace "motsi Kuma ?Wani Irin motsi?Kuma ba wasu daga cikin mu bane suke motsin?yace "eh oga na tabbatar da haka"goga yace "shikenan jeka Amma fa kasa ido sosai"yace "no yawa oga" goga ya Kuma cewa " idan ka fita ka tashi su bukar duk ku mike ku kasance cikin shiri Kuna Jin Wani Abu daba daidai ba kuyi harbi kawai," ya jinjina kai yace"angama oga" daga haka ya nufi kofar fita,AA Arab dayaga shigarsa ciki take ya qara matsawa gaba ya buya bayan wata motar 'Yan ta'addar Dake kusa da kofar building din inda Wannan Wanda ya Shiga cikin yabi ,AA Arab ya labe Yana jiran fitowarsa domin duk sauran wadanda suke tsaye sun samu waje sun kwanta dansu duka Basu ji Wani motsi ba Yana ganin fitowarsa take ya fito daga maboyarsa ya seta shi da bindigar hannunsa,Yana sa kafarsa Daya biyu take AA Arab ya harbeshi ,tuni ya banqare ya saki ihun azaba....



Wannan ihun dayay shiya Ankarar da Sauran Dake kwance suka mike arazane suna waige waige kowa da bindigarsa ahannu Dan har sun gaji da tsayuwar sun fara barci ,sun saita bindigarsu sun fara harbi Jin qarar harbi ta ko Ina gabansu da bayansu,goga afirgice ya fito daga cikin wurin dayake zaune shima da wata mahaukaciyar bindigarsa ya saita ta sai harbi yakeyi ta ko Ina.AA Arab tuni ya saki Bullets sai sakin harbi yake ga duk Wanda ya samu Dan 'yan ta'addar nan sai fitowa suke ta ko Ina Ashe yawa ne dasu kamar turu ruwa.take gurin nan ya hargitse da qarar bullets ta ko Ina sun Dade suna fafa tawa kafin su fara fin karfin 'yan ta'addar nan.goga ganin sun fara fin karfinsu take gogo ya gudu ,AA Arab dama dashi suke fafatawa tuni yabi bayansa sauran police din Suma suka takewa wadanda xasu gudun baya,AA Arab Bai samu goga ba Dan tuni ya bace masa ya nemeshi sama ko qasa ya rasa saidai ya samu nasarar kama wasu daga ciki, tareda wadanda suka mara masa baya,suka ruko kugunsu suka zaunar Dasu wasu police din suka xagayesu, sauran ma Wanda aka kama din tuni Suma sun kawo su an tarasu waje Daya....



AA Arab ya shiga cikin building din Dan ganin meye aciki DCP ya mara Masa baya,AA Arab Yana shiga ya tadda mutanen da aka kama sun takure afalon sun cure kamar wasu kuli kuli.ganin su AA Arab sun shigo tuni suka saki ihu daukar su Wani abun ne, DCP yace" ku Kwantar da hankalinku Kuna tareda da jami'an tsaro ne",sai alokacin suka saki juna suka fara rarrabuwa suna sauke ajiyar xuciya,AA Arab ya lalleka duka dakunan Dake cikin building din, gabadaya sun fito babu kowa sai wadanda aka sawa sasari kawai, take AA Arab ya fito ya qaraso falon ya Kalli DCP yace "muktar kira police guda hudu suxo,"cikin girmamawa DCP ya fita bani dadewa ya dawo da police guda hudu kamar yadda aka umarceshi, suna xuwa suka Sarawa AA Arab,ya Kallesu yace"biyu su shiga su kuncewa wadanda aka daure biyu Kuma su tsaya awurin DCP "babu musu wadanda aka umarta dasu shiga dakin suka shiga suka Kun tosu gabadaya.suka fito dasu suka zaunar su a falon cikin sauran .....



Saida AA Arab ya gama leka ko Ina dama da qatuwar fitilarsu suke tare Irin na police din nan me axabar haske .ya dawo falon ya tsaya yana qare yaran da aka sato din kallo,wasu Yara Dasu wasu basufi shekara goma Sha biyu ba ,Dan Rashin imani a dauko su daga gaban iyayensu akawo su nan .manyan Basu fi shekara 18 ba xuwa Ashirin daga mazan har matan.sannan daga nan ai safarar su xuwa wasu qasashe daban. lallai wannan qasar akwai gyara acikin ta,AA Arab ya kalli ASP Anas yace "ka fita dasu xuwa waje kafin akawo motocin su tafi dasu , ASP anas yace "ok sir "daga haka yace gabadaya su tashi su biyo shi babu musu suka shiga tashi Daya bayan Daya suna mikewa jikinsa na rawa ga datti ajikinsu kamar Wanda aka tono daga cikin Rami.kafin daga karshe suka nufi kofar falon suna maijin Wani farin ciki har ransu ganin yaudai ankawo musu dauki.....



Tuni AA Arab ya fita yasa aka dauko wadanda suka ji ciwo daga police din har 'yan ta'addar Aka ware Wanda suka ji rauni guda bakwai , wadanda Kuma suka mutu guda uku,acikin police din su AA Arab mutane biyar ne kawai suka ji ciwo wadanda 'yan ta'addar suka samu nasarar jiwa rauni, Amma babu Wanda ya mutu acikin police din.take AA Arab ya kira Wanda suka bari suyi gadin motocin su Dake Bakin titi umarni qara sowa Dasu ciki,dansu kwashe su,babu dadewa suka qaraso suka fara yiwa su AA Arab sannu ,sannan wasu suka fara kwasarsu suna sawa cikin motar,bayan sun gama kwashe 'yan ta'addar amota daban sannan suka dauki jami'an tsaron su suka sasu adaya motar, sai Daya motar suka Saka yaran aciki. AA Arab ya dubi DCP yace " muktar ka shiga motar da aka Saka criminal dinnan direct idan muka fita kuyi heardquater dasu atsare su sosai har gobe,ni daga nan hospital xamu kai jami'an mu da Kuma criminal din da suka ji rauni Dan basu treatment kafin suji sauki mu kawo su, wadanda Kuma suka mutu zamu san yadda xa'ayi dasu"DCP ya ansawa AA Arab cikin girmamawa,AA Arab ya Kalli CP yace "CP kai Kuma ku tsaya kaida tawagarka daga nan har gobe Dan kulawa da dajinnan,Dan kokadan banasan wannan ogan nasu ya kufce mana nasan Yana cikin dajinnan babu inda xashi, kafin gobe NASA akawo wasu police din wadanda zasu Yi gadin wurin suyi bincike har muyi nasarar kamashi."yasa Wani DPO ya shiga motar da aka saka Yaran da suka kubuto dasu dan kulawa dasu Suma.Suma yace asibiti ZA'A kai wadanda suka jigata masu lpyar kuma ayi heardquater dasu .daga haka ya shiga motar da tun tuni aka Bude masa,bayan ya shiga atare suka ta-da motocin suka nufi hanyar fita daga dajin, CP Kuma shida sauran jami'an kusan su Ashirin suka fara rarrabuwa kowa da inda xashi ya tsaya .Saida AA Arab suka shiga cikin garin Kaduna sannan suka rarrabu Dan alokacin har karfe hudu da Rabi ta ASuba tayi.....


Direct police clinic sukai dasu Dan Basu taimakon gaggawa,an warewa duka bangaren uku dakunan da xa'ayi musu treatment din,AA Arab Bai bar asibitin nan ba Saida ya tabbatar da kowa anmasa abinda ya kamata sannan ya wuce gida karfe takwas Saura ,Dan ummi tun ahanyarsu ta xuwa kaduna taita Kiran Kiran shi awaya taji lpyar sa .baya tunanin tayi bacci ma ita da Abba.yana xuwa gida ya tarar da 'yan uwansa a falor dukansu sunyi tagumi, ga ummi da hijabi da tasbaha ahannunta Abba ne kadai baya falon,Yana shiga ummi ta nufoshi tana dudduba jikinsa taga ko yaji rauni, shidai Kawai binta yake da kallo Yana murmushi harta gama dube dubenta sai Kuma ta dago ta rungumeshi tai hamdala afili.....



AA Arab shima rungumeta yay tsam ajikinsa yana maijin qara qaunar mahaifiyar tasa har cikin ransa, ummi ta sakeshi ta kamo hannunsa tai hanyar part dinsa da shi su zuhrah suka Yi masa sannu da xuwa ya ansa musu daga haka yabi bayan ummi Dake rike dashi har bedroom dinsa,bayan ya shiga ta dubeshi tace kai wanka bari na kawo Maka abinci yay murmushi ya kamo hannun ummi ya sumbata yace shukran ya ummi,ummi tai murmushi ta juya bayan ta jawo masa kofar.....



Kafin karfe 9 tuni gari ya dauka an kama 'yan ta'addar da suka takurawa al'umma,gidan TV Dana radio gabadaya zancen ake duk tashar da kika kunna indai ta labarai ce to wannan xancen kawai ake AA Arab ya shiga dajin nan da wasu daga cikin police ya kama 'yan ta'adda.,sai albarka ake ta da masa tunma kafin ski Gskyr zancen...to agidan su ruky ma hakane yau dai mama????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ?  h jikin nata da sauki Dan harta fito falor ta zauna,tana kallan labarai tana Jin yadda ake ta zancen ankama 'Yan ta'addar da suke yiwa kauyukan Kaduna dauki dai dai na 'ya'yan Jama'a.kuma ansamu nasarar ceto wasu yaran wadanda ba'a kai ga fita dasu Daga kasar ba,sai dai har yanxu ba'a samu yin magana da AA Arab ba ,balle aga ' Yan ta'addar da Kuma yaran da aka samu nasarar ceto war, Amma yanxu suke shirin fita heardquater idan AA Arab ya shiga Dan xuwa su dauko rahoto haka aka dinga muhawara a gidan TV na GADANGA TV & RADIO..da sauran gidajan TV...



mamah ta rintse ido hawayen da take dannewa suka samu damar xubo mata take Rukayya ta fado mata sai taji inama da Rukayya acikin wadanda aka ce an ceto dinnan ,sai taji inama hakane, anty mufeeda Dake hankalce da ita . itace ta matso kusa da mamah ta dinga rarrashinta itada Baba hasiya, Dakyar mamah ta tsagaita da kukun da take, mimie ta matso kusa da mamah tasa hannunta tana share mata hawaye,take mamah ta Dan saki murmushi tace "nadai na kuka takara?,mimie ta dagawa mamah kai .mamah tace da muryarta wacce Bata fita"to na daina takwara daga haka ta zaunar da mimie kusa da ita wacce ta fara mata surutu, Ganin haka shima moha ya taso daga kusa da baba hasiya yazo wajen mamah ya xauna agefen ta Yana kallan ta,ya kasance Sunsan ta atsakiya ,mamah ta ruko habar moha tace" me gida indai na kuka koh?moha ya dagawa mamah kai.take mamah ta Dan saki ranta ,anty mufeeda ta shige kitchen ita da baba hasiya ganin mamah ta Dan saki ranta, har ga Allah Batasan ganin mamah cikin damuwa, Amma ya ZA'Ayi tunda damuwar ta zama dole, addu'a kullum yinta suke Allah ya bayyana Rukayya,Dan Hanan tuni ta fita government house. Dan yau suna da tafiya da matar governor....



?&Baba lami da shafa suna cikin damuwa sosai na Batan da Rukayya tai,Dan tun lokacin da sukaji labarin batan da Rukayya tai baba lami Bata qara samun lpy ba, duk da police din da aka tura musu Dan kulawa dasu


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login