Showing 57001 words to 60000 words out of 278032 words

Chapter 20 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1065

fuska cikin ganin qarfin halin jami'an tsaron ya Kalli jabir cikin ido Yace kai harni xan rike kofa kaima ka rike kasan koni waye kuwa ko kasan ubana waye ko a jihar nan,dama qasa Baki daya,sajen jabir yace waye kai Dan gidan uban waye kuwa ,babu ruwanmu dakai ko Dan uban waye Aikine ya kawo mu Kuma shi muka xo Yi ,....


Mutumin ya Wani tura jabir har Saida ya kusan faduwa sannan yay banging kofar ,kafin yasawa kofar key ,Kofur Audu cikin xafin nama ya tura gate din da iya karfinsa,sajen jabir ya qaraso da sauri ya shiga gidan ,DCP ma ya Mara Masa baya yace oya arrest him Jabir,jabir ya rike shi Kofur audu zaisa masa handcuff Amma ya fara tirjewa ganin haka yasa ASP anas qarasowa ya rikeshi shima ,Yana zaginsu da kyar suka sa masa handcuff din,wannan hayaniyar ita ta fito da hany daga cikin falon taga meke furuwa,Aiko tana fitowa taga Yan sanda suna kokayin fitar da mutumin daga cikin gidan ga handcuff a hannunsa,Aiko tai maxa zata koma DCP daya ganta yace oya cofur come with her ,Aiko cofur ya shiga gidan ya cakumo hany dake kokayin rufo kofar falon Bayan ta shiga,ta dinga kuka tana ita Kuma me tai ,ko sauraranta baiyi ba ya shigarta bayan motar inda aka shigar da mutumin da kyar ,Yana kokarin fitowa,Amma Ina sajen jabir ya shiga gefansa, cofur Audu shima ya shiga daya side din da hany take ciki ASP anas Kuma Yana driver seat sai DCP agefensa,yaja motar da mugun speed suka bar wajen , direct headquarter akai dasu,.....



___________?&


Yauma dai Saida goga sukaje Wani qauye suka,afkawa mutanan suka kwashe musu yara daga mata har maza Kuma Yan mata da samarin qauyan,wasu Kuma suka harbesu da bullets Wanda kenan sukai taurin kai wasu Kuma sukai musu yankan rago kamar yadda suka Saba haka suka,kwaso su iyayansu suna Gani babu damar magana,idanko sukai gigin magana saidai suji bullets a jikinsu ,haka suka tisa yarannan agaba , suka durasu a motar da sukaxo da ita Sannan suka nausa cikin dajin da suke ajiyar yaran,....


Sai bayan sun baro gun sannan jami'an tsaro sukaje gun,Dan kai musu dauki,suka tadda ga wawwakin,shima CP yaje gun sbd kiran governor Daya samu,gabadaya abindai babu kyan Gani,sun rasa ta Ina xasu bollowa lamarin,gashi Suma kullum al'ummar gari xaginsu suke suna ci musu mutunci a social media,ga governor shima ya takura musu da adinga sa tsaro sosai Amma gabadaya,Yan ta addar nan sun San yadda zasuyi su shammacesu su kai hari gabadaya ankasa gano matsalar daga Ina take,haka suka kwashi Wanda aka jiwa rauni akai asibiti dasu acikin ambulance ,Wanda Kuma suka mutu suka tattarasu washe gari ayi musu jana'iza,.....


Alhaji sunusi ne, tsaye yake cikin Wani dakinsa na sirri,Yana shan jinin wata yarinya,Dake sama wacce aka salkayota daga sama a tsakiyar dakin wacce take daure da igiya,Saida yagama Shanye jinin nata tsaf sannan ya kuntota,yay hanyar kofar dakin da Ita fuskarsa tayi jaga jaga da jini da bakinsa ,bayan ya fito daga cikin Wannan daki Mai bala'in duhu babu komai ajikinsa daga shi sai Wani dan xani ja Daya daura daga cibiyarsa xuwa kan guiwarsa, fuskarsa daga janjini ta koma Wani Irin Baki ,babu kyan Gani,bakinsa sai fitar da Wani bakin jini yake Mai guda guda ,hannunsa dauke da wata yarinya wacce akalla xatai shekara goma Sha Daya,ya nufi wani daki Dake opposite din Wanda ya fito din ,bayan ya shiga ya daga carpet din Dake malale a tsakiyar dakin ya aje gefe, take tiles ya bayyana awajen ,ya dagaWani babban tiles Wanda shi kadai ne Wanda ba'a jikin Sauran yake ba ,take Wani Wani babban Rami ya bayyana,ya dauki yarinyar wacce babu alamar motsi a jikinta ya jefata acikin Ramin,...


Bayan ya jefata ya mike,ya fara xagaye wajen Yana surutai saida ya zagayashi sau bakwai sannan ya maida tiles din yadda yake kamar Wanda babu abinda yake kasansa sannan ya jawo carpet din ya Dora a wajen sannan ya fito daga dakin ya koma Wani dakin,ya cire wannan Jan zanin sannan ya shiga toilet yay wanka,bayan ya fito ya shirya kamar Wanda babu abinda ya aikata ,ya shirya tsaf cikin manyan kaya ya fito a Alhaji sunusin sa,bayan ya fito falor ya tadda wayarsa tana ringing ganin goga ne ke kiransa ya saki murmushi harsaida hakoransa suka bayyana a fili ya furta aikin ya kammala kenan .....


Sai Kuma yay picking daga Daya bangaren goga yace cikin takama da yanayin muryarsa yallabai komai normal Amma yau baxan samu xuwaba sbd babu hanya,xaka iya xuwa ka zabi Wanda kace ZA'Ayi aikin dasu, Alhaji sunusi cikin murmushi yace goga aikinka kullum qara kyau yake banyi nadama ba da muka kawar da shuba , sai Kuma yace kajirani nan da karfe biyun dare zan shigo daga haka goga ya kashe wayar, Alhaji sunusi yabi wayar da kallo sai Kuma ya wani kyakyace da dariya yace, Allah Dai ya kaimu ranar zabe,.....


Bayan ya sauke wayar babajo Ali ne ya kirashi akan Yana bakin gate haka yaje ya Bude masa gate din bayan yay Parking ya fito shima day fuskarsa dauke da murmushin , Alhaji sunusi ya qaraso kusa dashi haka suka rungumi juna kafin daga bisani su shige cikin babban falon gidan,....


Bayan sun xauna kan kujera, Alhaji sunusi da har sannan murmushi ne shimfide kan fuskarsa,ya dauko musu ruwa da lemuka da alcohols, sannan ya xauna yace babajo kaji aiki ya kammala koh,babajo Ali dashima harsannan murmushi ne kan mummunanar fuskarsa yace naji labarin a duniya, Alhaji sunusi ya tuntsire da dariya yace ai haba kace har an baxa a duniya, babajo Ali yace hmm tun yaushe kasan Yan Nigeria dama kiris suke jira suji Abu ya faru kaji an yada Abu a media, .....


Alhaji sunusi yay dariya yace wlh babajo sainasa governor nan Kuka da idansa kafin dai Wanda suke takamar wannan AA Arab din ya dawo wlh saimun jijjiga jihar Kaduna,saimun linka abinda muke samu kan wannan kasuwancin namu, tukunna,idan ya dawo Kuma saimu sauya taku,....



babajo Ali yace sosai kuwa Dan idan Sunsan wata ai Basu san wata ba,wlh sai sun Raina kansu ,Dan zagon qasa kawai zamu musu, Alhaji sunusi yay Wani murmushi yace hmm wai AA Arab ko wlh idanma BB Arab ne wlh saiya Raina kansa,sai sunyi danasanin ma dawowarsa kasar Dan saimun kunya tashi,babajo Ali yay dariya yace kai MaiTama wlh ni kaina Ina tsoron sharrinka, Alhaji sunusi yay murmushi yace, kasan ni bana yafiya ko akan waye kuwa,babajo Ali yace Niko nasan da wannan, kaida ka kau da jininkama,to waye Kuma baxa ka iya kaudawa ba, Alhaji yay murmushi ya dauki cup ya tsiyayi ruwan gabansa ya kai Baki , babajo Ali Kuma ya dauki kwalbar alcohol ya kai bakinsa,....



____________?&


Babar saude ce xaune a tsakar gidan Ameenah,wacce bayan ta gama mata kitson ta dubi Ameenah tace Niko Ameenah inane garinku, Ameenah tace ZARI'A,bavar saude tace dama nan kusa ma kike ZARI'A Amma shine naga kin Dade ba Kije gida ba, Ameenah tai shiru ta rasa abin fada babar saude duk tana lura da ita ganin Ameenah baxatai magana ba, yasa tace,awaccen unguwar kike, Ameenah tace tudun wada,...


Babar saude tace laa Kinga koh Nima inada wata yayata Dake aure a ZARI'A tudun wada, inda unguwar ku dayama,kila ma ko Kunsan juna bansaniba, AMEENAH ta Dan waro ido tace Allah babar saude Allah sarkie,awanne layin take babar saude ganin zata samu abinda takeso cikin sauki yasa ta qara gyara xama tace layin transformer, Ameenah tace laa ainima anan nake Amma mu muna daga tsakiya,idan kikaje xakiga wata solar ta ruwa a wajen to nan ne daidai kofar gidanmu,zajiga gidanmu Mai blue din kofa, babar saude tace Allah Aiko In Sha Allah indai naje ZARI'A xan biya har gidanku na gaida babarki,....


Ameenah tai murmushi har hakoranta na fita cikin Jin dadin Wanda yasan unguwarsu tace Aiko da zan Baki Sako kikaiwa babarmu,babar saude tace Aiko In Sha xanje, kwanan nanma domin zanje na duba Dan yayar tawa da akayiwa kaciya, Ameenah tace ya dubets tace ya sunanta,maman saude tace maman suhail ake ce mata , Ameenah tai jumm tana tunanin kota San matar Amma Kuma saita kasa tunowa,sai tace wlh bansantaba,maman saude tace eh ai dayake Basu Dade da komawa layin transformer ba, Ameenah tace shiyasa, nan dai suka cigaba da hira Ameenah tana Jin dadin maman saude ta san unguwar su ,harma tace xataje ,itako meman saude tai hakane Dan kawai taje gidansu Ameenah Amma Kuma da GSK tana da yayar da take aure a ZARI'A Kuma unguwar su Ameenah,,.....




*Masu so a tallata musu hajarsu xasu iya magana ta wannan number Dake qasa*







07066508376________
'?Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD


*_____JAMI'AR TSARO_____*



*____THE WOMEN POLICE ____*



*NA*


*_____NAJA'ATU UMAR FAROOQ _____*



*____(MRS SARAKIES)____*



*QUEEN OF WRITERS ASSOCIATION (QOWA)*



*Bismillahirrahmanirrahim*



______season one ep 2?? 6??


__________?&

Karfe 12:30am jirginsinsu ya sauke a airport din,Dake garin Abuja,yayinda mutanen cikin jirgin suke kokarin saukowa daga cikinsa,sannu a hankali Wani matashin saurayine Wanda a kalla bazai wuce shekaru 34 ba,yake saukowa daga cikin jirgin,bayan ya sauko ya shiga Dan karewa airport din kallo ,ya Dan tsaya ya kalli tsintsiyar hannunsa Wanda yake Sanye da wata tsadaddiyar agogo kamfanin, Armani ,sanye yake da kananan kaya riga da Wando ,rigar milk color wandan Kuma coffee color Wanda suka amshi fatarsa, gashin kansa Irin na larabawa Wanda ya kwanta luf akansa bakikkirin dayasha gyara ya fara kadawa Yana Dan mikewa tsaye, yadan fara tafiya cikin nutsuwa Yana maijin sanyi aransa , Wanda ya rasa na menene, Amma Kuma baya tunanin zai wuce na farin cikin ganin familyn sa musamman ma umminsa, wacce ya shafe shekaru Bai ganta ba,Yana cikin wannan tunanin,wata black Prado ce tai parking a gabansa tareda wasu x Prado duk abayan motar da Kuma motar police abayan sauran,....


Ya daga kansa ya Kalli arnayan motocin da sukai parking agabansa ,adai dai lokacin Kuma Sako ya shigo wayarsa Wanda ya Maida hankali kan wayar, Yana duba sakon,Yana kokarin dubawa drivern ya fito ya qaraso gabansa ya Dan risina sauran ma suka fito , suka qaraso,sai jami'an tsaron duk suka fito suka xo gabansa gabadaya suka qame masa, bayan ya gama karanta sakon ya dago ya Kallisu da sexy eyes dinsa Wanda suke farare fat kamar Madara ga dan ruwa ruwa Daya Dan kwanta a qasan idon ya qarawa idan nasa idonnasa Wani Irin sihirtaccan kyau,.....


Sukai saluting nasa ya ansa musu da ka,sannan suka risina sukace welcome sir, ya jinjina musu kansa alamar ansawa Daya daga cikin su da alama shine babba yay magana yace ga mota sir IG ne ya Aiko a dauke ka tun kafin ku sauka muke nan ya fada Yana karbar trolley sa da Kuma brave case dinsa Bai musaba ya Mika masa yay hanyar motar datai parking daidai inda yake tsaye domin da alama itace wacce xai shiga,domin tun kafin ya sauka akace xa'a xo daukar sa yanxun ma sakon da aka tura masa shine masu daukar tasa suna airport din ,Kuma sune sukaxo daukar tasa haka ya shiga Bayan anbude masa bayan motar,..


Sauran ma duk sukai sauri suka shiga motarsu bayan sun shiga Sukabi bayan driver sa,cikin nutsuwa suke tukin,har suka fita daga cikin airport, gwanin ban sha'awa,suka hau kan titi Wanda babu hayaniya sai qarar tayoyi motar kawai ke tashi,shiko Yana bayan motar yadan jingina da kujerar Yana latsa wayarsa lokaci lokaci Kuma ya dago ya kalli hanya Yana tuna when last rabonsa da Nigeria, ranar da ta Zame masa ranar da bazai tava mantawa ba arayuwarsa,ranar bakin ciki,Ranar da aka fitarsa daga qasarsa ta karfi da yaji yanaji Yana Gani,ranar da aka ci zarafin aikinsa,ranar da makiyansa sukai dariya suka xuba ruwa akasa suka Sha,....


Ranar da aka rabashi da iyayensa, da yan xuwansa gabadaya,har suka amince daya tafin,bashi da damar xuwa garesu saidai suyi waya koh video call,har gomnatin datai masa wannan Rashin imanin ta sauka ,wacce Kuma take kai Ayanxu data hau lokacin bayan wacen ta sauka suka bashi damar dawowa yaki ,ya gommaci Dai yay xamansa a inda aka sabar masa sabuwar rayuwar,maganar da driver yay ne ya dawo dashi daga tunanin daya tafi Inda ya xuba masa ido, driver risinar da kansa yace sir munxo ya lumshe idansa ya Bude at the same Ganin an Bude masa motar yasa ya fara zuro kyawawan kafafuwansa Daya 'kasa ya fito da dayar ma ya sauko Yana Mai daga kansa sama ganin inda aka kawoshi,ya furxar da iska daga bakinsa...


Wani tafkeken estate ne Dake ba bayan villa ,Wanda ya gaji da haduwa,domin xubin ginin ma abin kallo ne,ga motoci cikin parking lot din sama da goma,ga apartments kusan uku, police din daya karbi trolley sane ya qaraso cikin girmamawa yace sir bismillah,haka ya wuce gaba Yana binsa a Baya har suka qarasa babban apartment din inda ya danna Wani Abu kofar ta Bude yashiga shima police din ya shiga Tanga memen falon Daya gaji da qawatuwa Dan anyi bajakolin dukiya afalon ,komai ya xauna,ya ilihi komai na falon ba daga Nigeria ya fitoba gabadaya na qasar waje ne,sai asannan ya Bude Baki yace shukran , ganin police din ya kalleshi yasa Yace sorry thanks, police din yay murmushi Yana mamakin yadda larabci ya xauna Daram a bakinsa kamar wani balaraban saudia,sannan ya dubeshi yace xaka iya tafiya cikin girmamawa police din ya ansa masa tareda ajiye trolley da brave case din,ya fita shikuma ya qara karanta sakon Daya qara shigowa wayarsa sannan ya fara jefa qafarsa cikin lallausan carpet din nan Wanda Saida kafarsa ta lume aciki sbd laushi ya haura sama rike da brave case din, Bayan ya haura sama ,nanma wata Aljannar duniyar ne,ya qarasa wata kofa Dake opposite dinsa ya danna Wani Dan Abu take kofar ta wangale Wani luxury room ne Wanda komai nasa tamkar gold haka yake ya qarasa shiga ciki ya aje brave case dinsa kan site drawer ya qarasa gaban press ya
Buda ya dauko rigar wanka ya ajiye ya fara rage kayan jikinsa,sannan ya dauki rigar wanka ya bare wacce ke cikin ledarta domin komai na gidannan sabone dal,tunda babu abinda ba'a xuba aciki ba haka ya shiga toilet domin ya watsa ruwa koxaiji jikinsa ya ware,Kuma ya fito yay sallah,......


___________?&

Anan kuduna kuwa ruky tun tuni tabar office dinta Dan tun 5:30 ta tashi shiyasa Batasan wainar da ake toyawa ba,har DCP suka dawo aka shigar dasu mutuminnan cikin kanta,aka zaunar dashi ga handcuff a hannunsa sai hararar su DCP yake da sajen jabir,suko ko ajikinsu gabadaya idansa ya kada yayi jajur,itama budurwar sai kuka take , cofur Audu ne ya daka mata tsawar da dole tasa ta tai shiru ,sai asannan ta kama bakinta da hannu bibbiyu,tana sheshshekar kuka har lokacin, shiko mutumin sai kallansu yake Yana taune lips ba'a taba ci masa mutunci ba irin yau , harshi xa'a je har gidansa a daukoshi batareda yasan yayi laifiba,sunko San koshi waye kuwa,....


DCP ne yaywa su ASP anas alamar su tafi ,yace da sajen jabir ya shigar da hany cikin Wani Dan daki,babu musu ya kaita ya rufo dakin sannan shima ya fita akabar DCP da mutumin Wanda har sannan handcuff ce a Hannunsa, DCP ya Kalle shi ganin yadda yake harararsa yasa ya Dake Yana dan sassautawa ganin Bai gama tabbatar dashine Mai laifinba ko bashi bane ya fiso yay bincike tukunna, bayaso yay Masa komai shiyasa ,DCP yace, idan ka shirya ansa tambayar da xan Maka,inaso ka ansa min,idan har ka ansa min Kuma naga baka da laifi ayau zan sakeka ba washe gari ba,har lokacin kallansa yake , yace tambayar ka nake, mutumin yay tsaki yace ni Kuka sawa handcuff batareda nasan na aikata Wani laifi ba, sannan kuka kawoni office dinku kumin tambaya,maiya hanaku kumin tambayar tun a inda kuka dauko ni Saiyanxu,....


DCP yace aikaine baka bamu hadinkai ba a lokacin,sai alokacin mutumin yay dariyar rainin hankali yace oh hakama xakace officer, DCP ya hade Rai yace kai kashiga hankalinka kasan agaban WA kake kuwa, mutumin ya dage kafada yace so,ko agaban WA nake babu abinda ya dameni, DCP yay tsaki ya mike yace idan ka shirya na dawo nama tambayar,ya mike yay hanyar fita, mutumin ganin babu Wanda yasan ankawo shi nan ga Yabar wayarsa agida ballantana ya kira ko dadynsa ne,ko mummy yasa yace officer I'm All ears, DCP da harya kusa bakin kofa ya juyo yace what, mutumin yace I'm ready to answer ur questions,DCP yay Wani miskilin murmushi ya dawo ,Yaja kujerar Daya tashi ya xauna, akai Yana kallan mutumin....


Mutumin yace kafinnan ka ciremin wannan handcuff din, DCP ya girgixa kai yace wannan dokar aikinmuce,so listen to me, & answer my questions if u know it,mutumin ya Wani hade Rai yana taune lips, DCP Yace tambayar dazan Maka da farko itace, yace Kaine mamallakin gidan da muka daukoka daga can hayin rigasa, ma'ana Kaine me gidan DCP ya fada Yana qare masa kallo, mutumin ya kura masa ido, Shima DCP Kallan NASA yake, mutumin yace meyasa kamin wannan tambayar , DCP yace kawai tambaya nai eh ko a'a, cikin Rashin damuwa mutumin yace yes nawane , DCP yay murmushi Jin dadin abinda yake San ji cikin sauki ,sai Kuma ya dawo serious yace Amma meye sunan ka, mutumin yace meye Kuma xakai da sunana DCP yace ,eh mana ya kamata nasan sunanka,cikin kosawa mutumin yace sunana
*Abdul Lateef sunusi MaiTama, Wanda akafi sani da s MaiTama*,.....



DCP baisan lokacin Daya waro ido waje ba, yace kai Dan gidan Alhaji sunusi MaiTama ne, Wanda na sani na nan Kaduna ko kuwa ,lateef yace eh, DCP ya jinjina kai cikin mamaki yace,amma wanne daga cikin Alhaji sunusi MaiTama, Wanda ya daina siyasa ko Kuma Wanda yake kan mulki Ayanxu ,lateef yace basai na fada Maka ko wanne bane tunda har na fada Maka sunana saika nemi wanna sunusi MaiTaman,cikin mamaki da daurewar kai DCP ya dauko wayarsa ,ya lalubo hoton shafa yace kasan wannan ya fada Yana nunawa Lateef hoton , lateef ya tsurawa hoton shafa ido baya ko kiftawa, wacce take xaune kan gadon asibiti,Sanye da blue din hijab fuskarta ta fito sosai danta Dan ciko ba kamar Daba, da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login