Showing 135001 words to 138000 words out of 278032 words

Chapter 46 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1103

gefen ta tayi haske alamar shigowar kira ,ta jawo ta duba,ganin me kiran Kuma a wannan lokacin yasa take taji xuciyar ta tsinke, tareda bugawar xuciya,Saida ta kusa tsinkewa sannan tai karfin halin yin picking,tareda sallama da gaida shi, alokaci Daya, jikinta a Sanyaye. bayan ya ansa ya fada mata abinda yasa Hanan tai saurin mikewa ,take ta mike tsaye tace' what?are sure "tsabar kidimewa Batasan tai masa wannan tambayar ba ,sai Kuma ta saki wayar akasa Tasa ihun murna tareda karasawa wurin mamah Dan rungumeta take duk suka mike suna tambayar Hanan da lpy......





07066508376________
'?Follow the Mrs Sarakies =?1? HAUSA Novel Channel channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VbBRj1D35fLuSHibdq1Y






*____JAMI'AR TSARO ____*



*____THE WOMEN POLICE ____*



*NA*



*____NAJA'ATU UMAR FAROOQ ____*



*____(MRS SARAKIES)____=?1?*




*Bismillahirrahmanirrahim*



_______season one ep 5?? 7??



___________?&


A lokacin da CP suka rabu da AA Arab cewa zaije office dinsa yay aiki,babu Wani aiki dama da xaiyi kawai tunanin ta wacce hanyar zaifi Dan ya aiwatar da aikin da Alhaji sunusi ya umarceshi da yayi masa, sbd kullum saiya kirashi akan yayi abinda yasashi idan baiyi ba wlh saiya kashe shi, shikuma yanasan ransa , shiyasa babu yadda ya iya ,yaki Yi masa musu . duk da yasan Hakan da yay ba daidai bane ,yasan indai aka kamashi wlh saiya gane kuransa.bayan ya shigo office dinsa,tunani kawai yake Yi har na Wani lokaci ,Sakawa kawai yake yana warwara ya rasa mafita, yaso ace AA Arab gida zai tafi Dan so kawai yake yaga baya cikin heardquater nan, inyaso saiya shiga wurin zailani da kansa ya bashi gubar ko Kuma yay Masa allurar., matsalarsa Daya wadan nan police din Dake gading zailani yasan sune matsalarsa kawai, yadda zaiyi ya shawo kansu Subar wurin kawai yake tunani.....



Kasa xama yay ya dinga zirga zirga daga bangon office dinsa xuwa bango.yanayi Kuma Yana leken window Dan ganin AA Arab ko ya fito daga office dinsa ko yaya,Dan window office dinsa Yana pessing office din AA Arab ne,baya so Kuma ya shiga wurin AA Arab Yana nan, Dan Gani yake zai iya fitowa koda yaushe yaje bangaren bincike,idan ko ya kamashi yasan kashin sa ya bushe.saida ya kusan one hour Yana wannan tunanin Bai samu mafita ba ,can ya hango AA Arab ya fito daga office dinsa cikin sauri,ga motocinsu na police guda hudu duk anfito dasu ga police dayawa duk suna tsaitsaye jikin motocin da dukkan alamu shi suke jira, ganin AA Arab na xuwa aka bude masa mota suka ja aka Bude musu gate suka tafi baisan lokacin Daya sauke wata nan nauyar ajiyar xuciya ba,Dan wlh dama jira yake kawai AA Arab ya tafi ya samu ya lallaba da sauri yaje ya aiwatar da aikin da aka bashi koya samu salama Dan da dukan alamu AA Arab baxai dawo da wuriba......



Saida yay kusan mintuna biyar a office dinsa da fitar su AA Arab sannan ya fito daga office dinsa da poison din da Kuma allurar, acikin aljihun Wandansa.saidai me Yana xuwa department din daga nesa ya hango masu tsaran zailani agaban dan akurkin wurin dan ba'a hadashi da sauran ba har yanxu shikadai ne a inda aka kawo shin , police ne kusan su hudu a wajen take ya fara tunanin Tayaya zai ce su fita su bashi waje,Yana gefe Yana tsayen daga gefe Yana tunanin mafita, baisan lokacin Daya dauka ba saijin wayarsa Dake aljihun uniform dinsa tana vibrate take gabansa ya fadi bayan ya zaro wayarsa yaga Mai Kiran, kamar baxai picking ba kawai sai Kuma Yayi picking yakai kunne, abinda Alhaji sunusi ya fada masa da yayi _yasa shi sandarewa a inda yake tsaye , xufa ta shiga tsatstsafo masa, kamar yayi kuka me Alhaji sunusi yakeso ya maidashi,garin Yaya ma harya yarda da kudurinsa, take yahau nadamar sanin Alhaji sunusi.baitaba tunanin wannan Rashin imanin da yake kokarin aikatawa ba ko kadan. Allah ya Gani ba'a San ransa kwata kwata zai aikata ba Dan dai kawai Alhaji sunusi yayi masa barazana ne,bashida mafita .babu yadda ya iya haka ya ansawa Alhaji sunusi abinda yasa shi yayi din cikin rawar murya da kamar yayi kuka take ya dafe kansa Dake kokarin tabewa biyu.....



Cikin dauriya ya qarasa wurin da police din suke.take ya tsuke fuska, police din wurin suka hau kamewa suna Sarawa CP, CP ya dinga ansa musu batareda ya Kallesu ba,yay ta maxa yace"inaso ku fita ku bani waje Zanyi magana da wannan criminal din." take suka kalli juna kafin su sauke kansu qasa,Dan baisan cewa tun daxu AA Arab ya kirasu ya fada musu cewa karsu bar kowa yaxo gun ba harshi kansa CP.Daya yace " sir , Boss yace karmu sake Mubar gunnan kowaye ko yaxo , CP ya Kallesu da Mamaki yace" har Nima ya fada Yana nuna kansa," yace" yes sir " yace har kai,take CP ya qara tsuke fuska yace "oya kubar gunnan idan yaxo ni xan fada masa ni naxo" suka qara sunkuyar da kansu qasa cikin girmamawa sukace" kayi hkr sir," Amma yace " karmu sake mubar nan ".CP ya rasa ya xaiyi ya kasa barin wurin na tsawan lokaci.bai Ankara ba kawai yaji jiniya ta karade heardquater,ai tuni yay Maza ya bar gun domin yasan AA Arab ya dawo kenan tuni ya koma office dinsa,ya hau kan kujerar sa ya fara rubuce rubucen karya......


Bayan anyi parking AA Arab da kansa ya fito,baijira an Bude masa ba,a fusace ya qarasa inda motar da aka sako Alhaji sunusi take.yasa afito masa da Alhaji sunusi Wanda hannunsa ke sanye da handcuff , Alhaji sunusi ya Kalli AA Arab da idansa Daya rine xuwa ja sbd bacin Rai har lokacin Bai iya cewa komai ba , AA Arab ya Bada umarnin a wuce dashi.direct Wani daki na musamman na Irin masu aikata manyan laifukan nan yasa akai masa shi,Saida ya tabbatar da Alhaji sunusi an shigar shi gunnan sannan ya kwace wayoyinsa,yasa police guda biyar Wanda xasuyi monitoring dinsa, sannan Yabar wurin ya koma cikin mota Suka fita daga heardquater direct suka nufi wani private hospital domin kai su Rukayya, wacce har lokacin Bata cikin hayyacinta, Tariga da ta galabaita, suna isa asibitin emergency akayi dasu , nurses suka fito cikin sauri aka dauki Rukayya akan gado sukai ciki da ita, sannan aka dauki Khalil shima akai ciki dashi Amma bangaren kowa da ban.....



AA Arab Saida ya tabbatar da likitocin sun hau aikinsu sun fara bawa su Rukayya taimakon gaggawa sannan ya sauke ajiyar xuciya,Bai samu salama ba Saida yaga an fito da su daga emergency bayan Wani lokaci ZA'A kaisu Wani daki daban Dan cigaba da Basu treatment din,VIP room akai dasu ,kowa dakinsa daban ,saida ya tabbatar da komai in Sha Allah ya dai daita sannan yaja gefe ya dauki wayarsa yay darling number Hanan Dan yasan har yau hankalinsu baya jikinsu gara ya fara musu albishir da wuri,Saida ya duba Time yaga hudu Saura na ASuba sannan yay darling number ta......


Saidai me Yana fada mata ta rude ta hau masa tambaya. batama gamajin Abinda xai ce mata ba tasa ihu, yanaso yace karta fadawa kowa ta bari Saida safe gudun karsu ce zasu taho awannan lokacin, Amma Bata tsaya sauraran Saba,ta kashe wayar,. Yana Jin hayaniya kila ko suna tare da 'yan gidan ne ,ya sake Kiranta Amma Batai picking ba, kawai saiya hkr ya kyaleta,ya shiga dakin da aka kwantar da Khalil yaga Ankara masa ruwa,sai bacci yake cikin wahala, take xuciyar sa ta karye ganin halin da Khalil yake ciki,duk da baisan Shiba amma ya tabbatar ba halittar sa bace haka Sbd yadda ya rame ya xuke sai kace skeleton.take ya fito xuciyarsa na tafar fasa bayan ya fito yay dakin da aka kwantar da Rukayya,Yana shiga ya Tarar itama tana bacci ga drips Ankara mata ga Kuma jini,take ya tausaya mata,Dan duk da ba sanin ta yay ba , Amma tayi Wani Irin rama,ta fita hayyacinta, take yaji Alhaji sunusi lallai ba qaramin azzalumi bane,ya fito daga dakin Jin wayarsa na vibrate,ya xaro ta daga aljihun sa ganin ummi ce ke kiransa yasa ya saki murmushi yay picking yakai kunne.ummi cikin damuwa tace "Ahmad kana Ina,patan kana lpy,kun dawo ne"?,Dan duk inda xashi saiya fada mata.sbd ta tayashi da addu'a,AA Arab ya qara sakin murmushi Jin wannan tambayar da ummi ta jero masa yace " ummi I'm fine,Gani nan xuwa, mundawo" daga Daya bangaren ummi ta sauke numfashi tace" Alhamdulillah ya Allah, I'm really appreciate,so I'm waiting for u please, kadawo yanxu ka huta nasan ko abinci baka Samu kaci ba "yay murmushi yace in Sha Allah I'm on my way "daga haka sukai sallama ,ya samu doc sukai magana sannan ya nufi motar suka bar asibitin bayan ya bar police din da xasuyi monitoring din su Rukayya, Saida suka je heardquater suka aje motocin sannan,ya shiga motarsa driver yaja suka tafi gida......


Yana xuwa ya Tarar da ummi tana jiransa,ta nufi shi da sauri ta rungumeshi, tana murmushi ta kama hannunsa sukaje har dakinsa ta hada masa ruwan wanka sannan ta juyo gare shi ta shafa fuskar sa,tace "Allah ya Kara karemin kai Ahmad"Yana murmushi ya ansa mata tareda sumbatar hannunta , Daga haka ummi ta fita Dan xuwa ta kawo masa abinda zai taba, shikuma ya fara rage kayan jikinsa Dan ya samu ya watsa ruwa, Dan gabadaya a gajiye yake......



__________?&


Mamah ta rude ganin yadda Hanan ta rungumeta tana kuka tana murmushi,mamah ta dago da Hanan tace "lpy Hanan meya faru,?ta fada tana kura mata ido.anty mufeeda da baba hasiya ma haka suka hau tambayar ta arude da lpy,ya hanaf Yana gefe yana kallan Hanan.yana mamakin meya sameta take wannan abun wa Kuma ya kirata awaya .da kyar Hanan ta iya nutsuwa ta Bude Baki tace Alhamdulillah mamah ansamu Rukayya, oganmu Boss AA Arab ya dauko Rukayya daga inda aka dauketa, shiya kirani yanxunnan yake dafamin,sun sameta " ta qarasa fada tana rungume anty mufeeda,ba mamah ba harta ya anty mufeeda da baba hasiya da ya hanaf,kasa magana sukai they are totally compuse & speechless.sunma kasa hada tunaninsa waje Daya bare su fahimci me Hanan take nufi.....


Baba hasiya ta riko Hanan tace,"me kikace Hananu ", Hanan ta rike hannun baba hasiya tace,"baba hasiya anga Rukayya yanxun nan wayar da aka kirani xancen aka fadamin,"baba hasiya sai hawaye ta rungume Hanan tana "Alhamdulillah," anty mufeeda ta riko Hanan tace "da GSK kike "Hanan ta gyada mata kai tareda rungumeta cikin murna."anty mufeeda sai hawaye,ta saki Hanan ta koma wajen mamah wacce har lokacin tana sandare binsu kawai take da kallo,kila mafar kin data Saba ne kawai takeyi, Saida taji anty mufeeda tana fadin Alhamdulillah mamah ansamu Rukayya,mamah ta rike fuskar anty mufeeda,ta kura mata ido, kamar Bata gane abinda take fada ba.xuciyar ta na bugawa da sauri da sauri,axuciyarta tace" ya Allah idan mafarkin da sabayi ne ya Allah ka farkar Dani , Allah yasa ya kasance gsky ne .anty mufeeda tai murmushi Mai hade da hawaye tace "mamah ansamu Rukayya," ganin kamar mamah Batasan me take fada ba .mamah ta rungume anty mufeeda Jin dai a xahirine ba mafarkin da ta sabayi bane.sai hawaye shar shar,ta dago tace "da GSK kike mufeeda ".anty mufeeda tace " wlh da GSK ne mamah,Yanxu ogansu su Hanan ya kirata awaya yake fada mata,"mamah ta saki anty mufeeda ta fuskanci alkibla ta kai sujjadar Shakur take gabadayansu suka kai sujjadar suna godewa Allah,har ya hanaf Wanda shima Dakyar ya iya dawowa hayyacinsa ,Dan yayi matukar shiga shock.....



Mamah ta dago wacce fuskarta tai jagab da hawaye tareda murmushi ta mike tace "Hanan yanxu Ina Rukayya take?, Hanan na murmushi tace "yace ankaisu hospital ne,"mamah tace Wani asibitin Hanan ta fada mata,take mamah tace "ku tashi mutafi,babu musu dukansu suka mike kamar suna kan gwiwa,tunda kowa dama da hijabi ajikinsa,ya Hanaf ne ya daukesu a motarsa,iya ma aikatan gidan kawai akabari,saisu mimie da suke barci tsabar rudewa sunma manta dasu .direct hospital din suka nufa kowa fuskarsa ta cika da annurin,rabon da mamah tajita cikin farin ciki harta manta.dan tun kafin a sace Rukayya.sanda sukaje asibitin, alokacin ana ta Kiran sallahn ASuba,Saida sukaxo asibitin sannan suka tuna ai basuma San inda Rukayya take ba, take Hanan tace "bari ta kira AA Arab ya fada musu inda Rukayya take, ta kirashi baiyi picking ba,kusan 5 Miss call tai masa Amma baiyi picking ba, ta kalli anty mufeeda wacce ke kallan ta .anty mufeeda tace "kila baya kusa"Hanan tace " eh Ina tunanin haka,ya hanaf ne ya Kalli agogon hannunsa ganin lokacin sallahn ASuba haryayi yace " muje muyi sallah,kafin ya kira ,babu musu suka ansa masa,ya nufi masallacin Maza su Kuma Suka nufi na mata......


Har suka idar da sallah AA Arab Bai kira ba, alokacin da suka kira AA Arab, ga hankalinsu yaki kwanciya burinsu kawai suga Rukayya....AA Arab kuwa alokacin wayarsa tana silent ne, Kuma ummi ce tace saiya kwanta Kona mintuna 20 ne,bayan ta tilasta masa yasha coffee.Kuma har yay sallan ASuba,Bai duba wayarsaba,sai wajen karfe shida da Rabi sannan yaga miss call din Hanan,take yay Kiranta cikin rawar jiki Hanan ta gaidashi Tareda shaida masa cewa sunxo asibitin Amma Basu San dakin ba,AA Arab ya fada musu yace Kuma xaiyi magana da doc din, sannan xata hadu da police dinsu Wani ya kaisu har dakin,tunda dole sai police din sun amince tunda a qarqashin kulawar su suke, Babu musu Hanan tai masa godiya ta fadawa mamah,take suka nufi dakin, saidai Dr ya hanasu shiga sbd Rukayya Bata farfado ba har lokacin, yace "saidai su lekata ta window babu musu suka amince,mamah data hango Rukayya Saida ta kusan faduwa sbd shock yanxu Rukayya ce ta dawo haka,autarta ce ta dawo haka,ta rame tayi Baki,ta fita hayyacinta, lallai baxata taba yafewa wanda ya sace Rukayya ba .ga drip ga ledar jinji ana qara mata, innalillahi wainna ilaihi rajiun me sukayiwa Rukayya haka, su waye metai musu.take mamah ta hau kuka tana Mai tausayin halin da Rukayya take ciki, tana Kuma fatan Allah yasa Rukayya ta tashi .gabadayansu babu Wanda Bai xubar da hawaye awurin ba sbd tausayi, Basu San tsawan lokacin da suka dauka ahaka ba,Saida wata nurse taxo ta Basu hkr, tace su koma kan kujeru su xauna.suka koma kan bencin kofar dakin da Rukayya take suna jiran farkawarta.....





07066508376________
'?Follow the Mrs Sarakies =?1? HAUSA Novel Channel channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VbBRj1D35fLuSHibdq1Y







*____JAMI'AR TSARO ____*



*____THE WOMEN POLICE ____*



*NA*



*____NAJA'ATU UMAR FAROOQ ____*



*____(MRS SARAKIES)____=?1?*



*Bismillahirrahmanirrahim*



_______season two ep 5?? 8??



__________?&


AA Arab Saida yay wanka wajen karfe 9 na safe ya sauko downstairs cikin shirin fita aiki, sannu a hankali yake saukowa Yana daure disigner agogon Dake hannunsa,Yana saukowa yay Arba da ummi Dake dining area ,idon da suka hada da itane yasa shi qarasawa dining din,da da harga Allah sallama zai mata kawai ya fita .ya xauna Daya daga cikin kujerun dining din yana gaidata, ummi ta ansa masa da murmushi a fuskarta, ta kalleshi tace "me xan xuba Maka" ta fada tana bubbude warmers din, AA Arab ya kalleta yace" ummi komiye ma xanci" ummi ta rufe sauran warmers din ta bar 2 warmer din Wanda ke dauke da soyayyan Irish da Kuma kwai ga ferfesun kayan ciki ,ta xuba masa a plate daban daban, sannan ta hada masa coffee ta dire agaban sa tace na_ga iya plate dina, ta fada tana kallansa, shima kallan nata yake Yi ,da murmushi a fuskarsa ya shafa cikin sa ya marairaice yace " ummi ya xanyi da wannan tulin abincin haka? , Ina zan kaishi?, ummi tace " cikinka zaka Kaishi" yace " ummi Dan Allah kiyi hkr "ummi tace wai Dan Allah Ahmad meyasa bakasan cin abincine sai kace Wani karamin yaro,ka wuni ja kwana kana yawo Amma common lokacin cin abinci baka dashi"AA Arab ya shagwabe fuska yace" ummi awurin ki aini yarone Dan Allah ki bari naci dai dai cikina, ummi tace"hmmm Amma kaci ka koshi" yay murmushi yace "in Sha Allah,daga haka ummi ta shiga kitchen, AA Arab Kuma ya Maida hankali kan abincin Dan Bai san ma ta Ina xai fara kaiwa cikinsa ba.....



AA Arab ya fito falor bayan yaci abinda xai iya ci ,na daga cikin abinda ummi ta tula masa agaban sa,adai dai lokacin da ummi Kuma ta fito daga part din Abba,ummi ta tsare shi da ido tace "fatan kayi abinda nace?AA Arab Yana murmushi yace"eh ummi naci na koshi."ya qarasa fada yana shafa plat cikinsa ummi ta gyada kai tace "shikenan,"AA Arab yace "ummi bari na tafi lokaci na tafiya, ummi tace"Allah ya kiyaye " kaje wajen Abbanka? ya girgixa kai yace "yanxu xanje tace shikenan Allah ya tsare"daga haka ta haura sama Dan taso su Ameerah Dan sunce yau basu da lacture sai karfe 11am,shi Kuma AA Arab ya wuce part din Abba,ya shiga falon bakinsa dauke da sallama, Abba ya Tarar xaune kan Daya daga cikin kujerun falon sa Yana karanta jarida,ganin AA Arab ya shigo da sallama abakinsa yasa ya ajiye jaridan hannunsa gefensa Yana gyara xaman glass din fuskar sa yace"wa'alaikassalam" da murmushi a fuskarsa.AA Arab ya duka har qasa ya gaida Abba, Abba ya ansa masa da kulawa, sannan yace "Ahmad xa'a fita ?AA Arab ya "eh Abba "Abba ya jinjina kai yace"Allah ya kiyaye ya Bada sa'a adinga kula "AA Arab ya gyadawa Abba kai yace " in Sha Allah Abba",daga haka ya mike ya fito daga dakin Jin wayarsa na vibrate,ya xaro ta daga jikin suits dinsa, ganin DCP ne ke kiransa.......



Bayan yay picking,Daga Daya bangaren DCP ya gaida AA Arab,AA Arab ya ansa masa, DCP yace "ranka Yi Dade munji lvr Mai Dadi Allah ubangiji ya qara dauka, Allah ya qara kareka aduk inda kake.,AA Arab ya ansa masa Yana kokarin shiga motar da aka Bude masa tun fitowarsa,bayan ya xauna a motar,AA Arab yace"muktar kashiga office ne? DCP yace"yes sir "cikin girmamawa,AA Arab yace "ok inaso please ka tsaya kaida kafa ka kula da shiga da ficen kowa xuwa wajen masu laifin nan kafin nazo" , DCP yace"in Sha Allah sir ",AA Arab yace"thank u saina shigo" daga haka ya kashe wayar,"ya kalli driver yace hospital xamu "driver ya jinjina kai yace"ok sir ".....



A Asibiti kuwa har yanxu wajen karfe Tara da mintuna Rukayya Bata farka ba,mamah ta damu ta matsu taga tayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login