Showing 66001 words to 69000 words out of 278032 words

Chapter 23 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1093

kwatantamin gidansu Niko nace in Sha Allah xanxo mu gaisa,ga Sako ma tace abaki,ta fada tana Mika mata wasikar da Ameenah ta rubuta musu ita da Nana ta bawa ummah, ummah ta karba tana juya ta kardar tace saidai idan Nana ta dawo ta karanta mana,....


Ko rufe Baki batai ba,saiga nana ta dawo daga islamiya, Bakin ta dauke da sallama,suka ansa mata sallamarta,ta karaso har Inda suke ta gaida maman saude, maman saude ta ansa mata da fara'a tana kallan yadda Nana take mugun kama da Ameenah Hakan ya tabbatar mata da lallai kamannin ummah duk sukayo kenan,bayan sun gaisa Nana ta mike xata shige daki,ummah ta kalleta tace Nana wannan fa makociyar Ameenah ce daga hayin rigasa take, Nana ta dawo da baya cikin murmushi tace ko kece kike aika mata da abinci kullum,aidanaje take fadamin, maman saude ta sunkuyar da kai tana Dan murmushi, ummah ta waro ido waje tace wai dama itace wacce take taiwa Ameenah dawainiya kai wlh Masha Allah, gsky kin kyauta da kika xo kika karaso mana har nan,. ...



Har nake cewa wlh xanje takanas idan naje duba Ameenah na qarasa nai miki godiya yadda kike dawainiya da Ameenah Allah ya Saka da Alkhairi ya bar xumunci, babar saude tace wlh Babu komai ummah aini na dauki Ameenah tamkar qanwata, komai na mata ban fadiba,tunda nima tanayiwa tawa yar hidima,Kinga koh ai Danna mata ban fadiba, ummah tace wlh muke da godiya bisa dawainiyar da ake mata ko nace ake kanyi,Ina Ameenah take koh patan tana lpy,maman saude tace lpy lau,dama Nima akwai naganar danxo miki da itane, ummah ta gyara xama tace Inajinki baiwar Allah,ganin magana xasuyi ummah tace Nana ungo wannan sakone Ameenah ta Aiko akawomin xaki karanta min anjima, Nana ta karbi wasikar nan ta shige daki,.....


Ummah ta dubi maman saude tace Ina jinki Amma ya sunanki,manan saude tace sunana Harira, ummah tace to Harira Ina jinki ,maman saude tace bansan ya zaki dauki maganar danaxo miki da itaba ,Amma Nima garaje xanyi , Dan Allah koya xakiji idan har abinda xan fada miki kinsani Amma kuke ganin bakomai bane,to Dan Allah nidai a gafarceni ,banasan shiga hurumin daba nawaba, ummah cikin kaguwar taji me maman saude taxo dashi tace Inajinki babu komai ki fadi ko meye kanki tsaye, maman saude tacedama akan yanayin xaman da Ameenah takeyi ne agidan mijinta Kabiru,xaman agsky na fuskanci ba Dadi take jiba,inkinga yadda Kabiru ya Maida Ameenah saikiyi mamaki,nan ta kwashe komai na iya abinda ta sani na yadda Kabiru yake axabtar da Ameenah ta Kara da idan Kinga Irin dukan dayake mata, dukan yau daban na gove daban baya Bata abinci babu wata kulawa babu komai, wlh dukan Daya mata shekaran jiya har chemist na kaita sbd yadda ta kasa motsi,...


Kusan sau biyu Yana dukanta Ina kaita chemist Wannan dinma iya Wanda na sani kenan , domin ita ba fadamin Damuwarta take ba,bansaniba ko ku tana fada muku halin da take cikiba, ganin yadda ummah tai Suman xaune ya tabbatarwa da maman saude cewa lallai ummah Batasan meke furuwa ba, ummah tace innalillahi wainna ilaihi rajiun sai hawaye shar shar ,Dan tama kasa cewa komai ta rasa abin fada,sbd takaici ko bakin ciki,maman saude ganin yadda ummah take xubar da hawaye yasa jikinta yay sanyi ta fara bawa ummah hkr,sai ganin baba asabe sukai akansu,baba asabe ta fito buzur daga daki Dan tun lokacin da maman saude tai sallama tana daki tana lissafin kudi har xaman da babar saude tai a kofar falon ummah duk taji,da har xata fito Amma Jin ta ambaci Ameenah yasata kin fitowa , Kuma Hakan ya tabbatar mata da cewa bakuwar ummah ce,Dan haka ta matsa saitin window tana gyara daurin xaninta ta tsaya a Dai dai window ta Kasa kunne take Jin duk conversation dinsu,Dan inda sukai shimfida saitin window tane,Saida ta jira ta gama jin komai Sannan ta fito tana gyara daurin xanin ta dayake Neman kadata sbd sauri,....


Ta nuna babar saude ta yatsarta tace kedai ba'a kwai shaidaniyar mace ba annamimiya , yanxu inbanda muna furci kitaho tundaga Kaduna hayin rigasa har ZARI'A sbd kawai ki kashe AURE, yanxu yarinyar nan Ameenah tana xamanta lpy a gidan mijinta, Amma sbd San ki kashe mata AURE kice wai mijinta mutumin kirki Irin Kabiru wai Yana axabtar da ita,yanxu da ace,Irin wannan axabtarwar da kika lissafo yake mata aida wlh baxata xauna ba,da tuni ta dawo gida da kafarta, tunda ai Ameenah ba yarinya bace,ta karasa fada tana Mai wurgawa babar saude mugun kallo Dan wlh ji take kamar taje ta shaketa sbd bataso ta wargaxa mata plan dinta ,...



Ummah da tunda baba asabe ta fito take harararta , hade da mugun kallo,harta gama magana tace asave Ina ruwanki yarki ko tawa babu ruwanki,wai ke meyasa bakyason axo atafamin halinda Ameenah take cikine, indai akaxo aka fadamin cikin muwuyacin Halin da take ciki,saiki ruwa kiyi tsaki kice wai qarya ake yiwa Kabiru,waini Kabirun nan kinada Hadi dashi ne da bakyasan laifinsa, ummah tace to babu ruwanki,Kuma aure in Sha Allah Ameenah ta gama yinsa kenan agidan axxalumin mutumin nan, wai ko bakiji Irin axabtarwar dayake gana mata, bane, to tunda har kike karesa bari idan Allah ya kaimu gobe yanxu dare yayi wlh da yau zanje na dauko Ameenah,idan ya saketa saiki aurawa zaliha Kabiru, Kinga shikenan saiki cigaba da kareshi,daga haka ummah ta kalli mamah saude wacce jikinta yay sanyi Jin yadda baba asabe ta gama zakinta, ummah tace baiwar Allah nagode kinji,Kuma in Sha Allah xan dauki mataki gove govebennan,....


Maman saude ta mike tace Babu komai ummah bari na tafi ummah tace Amma ba yau xaki koma Kaduna ba koh, maman saude tace ayau zan koma Dan na bar Yara agida, ummah tace bari naxo ta shige daki babar saude koh hartakai kofar gidan, Baba asabe tace oh hakama zakice maimuna toh shikenan bari malam yadawo wlh saina fada masa cewa wata taxo takanas xuwa nan gidan Dan kawai ta kashewa Ameenah aure, ummah koh tai Banxa ta kyaleta ta shige daki Dan daukowa babar saude abin arziki,Dan bataso su Saida Hali agaban Babar saude shiyasa ta kyaleta Amma bari ta tafi wlh ayau saidai malam ya saketa Amma saita gurjewa baba asabe Baki,......



__________?&

A bangaren Ruky kuwa tana xuwa asibiti direct dakin da aka kwantar da shafa ta nufa inda ta tarar da baba lami kan sallaya, shafa Kuma tana xaune bakin gadon da alamar hutawa take, sallamar Ruky ce yace baba lami juyowa xuwa gareta tana ansawa itama shafa kallan nata take ta ansa sallamarta tana Kuma gaidata da mata sannu da xuwa ruky ta ansa cikin sakewa,baba lami tace sannu da xuwa Jama'a ruky tai murmushi ta gaida baba lami, baba lami ta ansa mata da kulawa,...



Ta mike ta kawo mata ruwan jarka Wanda yake katan katan acikin dakin da lemo ta aje gaban ruky wacce tuni ta kai xaune kan kujeran Dake bakin gadon,tace sannu baba da kinbarshi Dan Nasha ruwa a office,baba lami tace a'a jami'a Dan Allah Kisha cikin murmushi Ruky tace nagode,ta dauko wayarta ta shiga gallery ta binciko inda hotonan lateef yake,na da Dana yanxu,Wanda haka kawai shi yake tura matasu Batare da ta bukata ba,Ashe xasu mata Rana Dan Bata taba gogewa ba,ta tsaya kan Wanda xaiyi kusan 2 years da turo mata da yay,ta mikawa shafa wayar tace shafa kinsan wannan,......


Ta fada tana Mika mata wayar, shafa ta karba tana kallo,sai hawaye shar , ruky ta kura mata ido sai Kuma ta sauke numfashi tace kinsan shi shafa tace Anty wannan aishine Wanda yamin fyade, ruky tace kin tabbata , shafa tace wlh anty shine baxan tava mantawa ba, shine Wanda kullum yake xuwa har unguwar mu ya daukeni ya kaini wannan gidan nasa,wlh anty baxan tava mantawa da fuskar Saba,ko bacci nake fuskarsa ce kawai take min gixo, ruky ta sauke numfashi tace shikenan tunda har kin tabbatar dashi yay miki dama haka muke bukatar ji,ta karbi wayarta ta kashe recording din da tai, sannan tace ki kwantar da hankalinki shafa in Sha Allah shima saiya fito ya ansa laifinsa, Alhamdulillah tunda har mun gano Wanda yay,...

Baba lami da tunda ruky ta Mikawa shafa wayarta take sauraran su, tace jami'a ba Raina kokarin ku naiba,Amma idan shine kinsan fa daga Ganin shi wlh me kudine,ni dama hkr kawai kukayi muka barshi da Allah Dan shine xai saka mana, Ruky tai murmushi tace baba karkiji komai in Sha Allah komai xai tafi yadda Mukeso,mudai kawai ki tayamu da addu'a,tunda Kinga har ankama shi Yana Hannun hukuma kinsan ko ai in Sha Allah kamar anbiwa shafa hakkin tane,baba lami tace gsky ne to Allah ya Baku SA'A Ruky tai murmushi ta ansa da Ameen, sannan ta bubi wayarta ganin Khalil na Kiranta tace baba bari naje results ya kusa fitiwo koh , nanda kwana biyu, Allah yasa Muji alkhairi,baba lami ta ansa da Ameen,tace da Ruky Allah ya kiyaye ganin ta nufi kofar fi???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ta, ruky ta ansa da Ameen tana Mai barin dakin,...


Direct inda tai parking motar ta ta nufa anan ta tarar da Khalil Yana jiran ta ,Dan dama ta fada masa,bayan ta qarasa ta sakar masa murmushi har dimples dinta suna lobawa,tace sannu da xuwa Ibrahim Khalil, shima saiya sakar mata murmushin yace sannu da kokari jajirtacciyar JAMI'AR TSARANMU,sai Kuma yay saluting nata,ta qara sakar masa murmushi sai Kuma ta dan harareshi tace,ni banaso,ya dan Bude ido yace bakyasan me,ta turo Baki gaba tace ai ka sani sai Kuma ya shafa kansa Yana murmushi ya rusuna yace na tuba, itama murmushin ta qarayi tace shikenan ka fanshi kanka ....


Shidai murmushi kawai yake yana kallanta ,baisan Mai yasa ba Ruky tana burgeshi sosai komai nata simple ne batada hayaniya, tunanin sa ya katsene lokacin data ce masa yauwa kaga suspect dinmu, koma nace muntabbatar ta fada tana nuna masa wayarta da hoton lateef ya bayyana,ya kurawa hoton ido sai Kuma ya dago yace ranki dade shine wannan ruky ta jinjina masa kai har sannan murmushi ne a saman kyakkyawar fuskarta,ya jinjina kai yace meye sunansa tace *Abdul Lateef sunusi MaiTama*



Khalil ya xaro ido waje yace wai kina nufin Dan gidan Alhaji sunusi MaiTama ne Wanda ke Neman tsayawa takara senator Ayanxu, ruky tace kwarai kuwa, shine sai Kuma ya jinjina kai,sai Kuma yay sauri yace tsaya Amma ba kanin mahaifin kineba, kodai Dan gidan tsohon Dan siyasar nanne Alhaji sunusi MaiTama shine, Ruky tace no wannan din Mai Neman takarar senator din shine kanin abbannamu Kuma Dansa ne lateef din, Khalil ya xaro ido waje yace ranki dade shine,Kuma zaki tsaya adauki matakin,....


Ruky tai murmushi Mai ciwo tace ko ka manta Ranar Dana ce Maka ko ciki Daya muka fito da Wanda yay wannan xalincin sai inda karfina ya qare,to kazuba ido ka Gani in Sha Allah sai inda karfina ya qare,sai anbiwa shafa kadinta ,cikin mamaki Khalil yace Amma ranki dade, ta Dora hannunta kan bakinta tace shiiii idan Kuma kai ka janyene baxa ka iyaba ,xaka iya kyaleni nayi kayana,cikin sauri Khalil yace a'a ranki dade,tace to ka manta da wata Alaka Dake tsakani na dasu ,kamar yadda Nima na manta xanyi aikinane kamar yadda nai ALKawari ,Kuma nai rantsuwar cewa xanbi tsarin aikina yadda doka ta tsara, bayan ta fadi haka tace mushiga mota mutafi daga haka ta Bude motar ta shiga, shima Khalil ya zaga Daya side din ya shiga Yana mamakin karfin halin Ruky haryanxu,...



_________?&

Alhaji sunusi kuwa da isarsa gidan da babajo Ali ke jiransa ya sallami driver yace yaje da motar idan ya gama xai kirashi,Dan shima wannan gidan,Wani gidan sirrinsu ne dasuke tattauna mugun nufunsu da komai acikinsa,haka ya shiga gidan bayan maigadi ya Bude masa gate din, direct falon gidan ya wuce Dan babu inda Bai saniba agidan, ko sallama baiyiba haka ya shiga falon ya tarar da babajo Ali tsaye Yana xagaye falon hannuwansa goye a bayansa, idanuwan sa sunyi jajur sbd bacin Rai ga karar tabkekiyar TV saiyi take,sai ganin Alhaji sunusi da yay kamar anjehosa,.....


Ya juya yaga Alhaji sunusi da gabadaya kallo Daya xaka masa kasan cewa a firgice yake,babajo Ali da daukar sa shima yaga abinda ke faruwa ne a TV na xuwansu AA Arab yasa shi firgici yace kaima kaga abinda ke faruwa kenan ta tabbatar da tsinannan yaron nan saiya dawo kasar nan, kasar ma jihar Kaduna Kalli yadda dumbin mutane sukaje airport tarbarsa , Banda ma masu posting a social media na tayashi murna,sai kace Wani president ne yaxo,komu da muke Yan siyasa bantaba Ganin sun tarar mana a wajen siyasarmu kamar yadda mutane sukaje tarbar wannan tsinan nan yaron airport ba,kaji yadda ake kokawa da mutane wai sai sunje gunsa sai kace Wani waliyi,ya fada Yana nunawa Alhaji sunusi TV dakeyi afalon har lokacin,......


Alhaji sunusi xaiyi mgn kawai ya fasa ya kurawa TV ido , Yana kallan dumbin mutanen dake airport babu abinda yake tashi awurin sai muryar jama'ar wurin Dake Kiran sunan AA Arab,ga jami'an tsaro ta ko Ina ,sai korar mutane suke,haka ya rintse ido Wanda shima ya kada yay jajur,duk San karyaga AA Arab yasa ya rintse ido Amma Saida ya ganshi adai dai lokacin Kuma da yake sakin tattausan murmushi Mai tsayawa axuciyar makiyansa da suke ganin kamar hakane wato irinsu Alhaji sunusi,ai Alhaji sunusi baisan ya kai zaune jagwab ba,yace babajo kashe TV nan, kashe kaina xai tarwatse idan na cigaba da kallon wannan taron jama'ar indai ba mu akeyiwa ba,wai kana nufin yarannan power sa harta kai haka, a kasarnan bama jihar nan ba,kaduva kaga a masu masa rakiya harda minister tsaro ga Kuma IG na qasa, ga Kuma manyan mutanen qasar nan,babajo Ali da shima yakejin xuciyarsa na masa xafi bayan ya kashe TV yaxauna kujerar Dake passing ta Alhaji sunusi yace baga shi ka Gani ba ,wai kardai ace kai sai yanxu ka Gani , Alhaji sunusi ya cire hular kansa sankonsa ya fito sosai yace,ni sai Yanxu na gani, babajo Ali yace ai bakaga komai ba Ashe Dan tundaxu ake ta nunowa tun kafin daukarsu,bakaga yadda aketa Saka hotunansa a social media ba, status kuwa duk inda ka shiga hotunan sane kawai suke yawo,.....


Alhaji sunusi ya dafe kansa yace babajo , yanxu Bata shi nake ba,ankama lateef Yana headquarter,nayi ta Kiran CP banasamunsa,nasan Kuma baxai wuce Yana wajen tarbar wannan tsinan nan yaron ba,naje headquarter ma, Shima DCP baya nan, nasa adubo min inda yake sunce Basu San ankawo lateef wurin ba,harni da kaina na duba Amma narasa Inda suka kaishi,yanxu jira nake CP ya dawo a yau ba gobeba,wlh sai sun fitomin da lateef,Kuma wlh saina ci musu mutunci xasusan ni xasu kullewa da,wlh duk saina wulakanta rayuwar su, .



Babajo Ali yace wai lateef aka kama to meya aikata har haka dayasa aka kamashi,Alhaji sunusi yace mekuwa xai aikata kawai San atonamin asirine acikin al'umma , akuma cimin zarafin siyasa ta shiyasa akeso ayi anfani da lateef wajen wargaxamun siyasa ainasan baxai wuce magauta ba,Dan babu Wanda ya isa ya kama lateef ajihar nan sai Wanda ya isa, babajo Ali yace gsky Aiko bamuga ta xama ba bari su dawo sai muje, Alhaji sunusi yay tsaki saikuma , ya furta A fili, AA Arab saiya saki Wani murmushin yake yace zan dawo gareka ne bari na gama da wannan matsalar tukunna,babajo Ali yace ai dole gove su goga sukai hari a fita aiki dan yasan babu abinda xa'a fasa , saiga Alhaji sunusin ki ya ware ya manta da abinda ke damunsa Jin mugunta, Alhaji sunusi ya kyalkyale da dariya yace kai babajo dadina da kai akwai barisa, babajo shima murmushin yay yace wlh ya jira dai,daga haka suka cigava da tattaunawa akan yadda xasu takurawa jama'ar qauyuka,da dauke yayansu,




*Masu San a tallata musu hajarsu xasu iya Yin magana ta wannan number Dake qasa*






07066508376________
'?Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD





*____JAMI'AR TSARO ____*



*____THE WOMEN POLICE ____*



*NA*



*____NAJA'ATU UMAR FAROOQ____*


*___(MRS SARAKIES)___*



*QUEEN OF WRITERS ASSOCIATION (QOWA) =?1?*



*Bismillahirrahmanirrahim*



_______season one ep 3?? 0??



__________?&


Bayan su AA Arab sun sauka a government house inda aka saukesu a masauki Mai kyau na musamman, Dan wurinma abin kallo ne,bayan sun huta aka fito domin yin lunch,wurin lunch dinma duniya ne,an hada musu liyafa ta musamman,bayan sunci sun Sha,suka wuce office din governor Wanda a canne zasu tattauna komai,inda aka sake sabuwar gaisuwa,bayan sun gaisa minister yay bayanin sa ,bayan ya gama IG ma ya Dora da nasa tareda da Bada sakon president,awurin governor shima ,take awurin aka bawa AA Arab gida abayan government house,hade da motocin hawa acikinsa,a anguwar asokoro inda xai xauna, bayan an Mika masa takardun da keys ya karba ya Gani,...

Sai Kuma ya dago da kansa ya kalli governor Wanda ke kallansa da murmushi yace ur exerlency a gafarceni Amma ni bana bukatar gida, sbd Ina da gidana,Kuma ga gidan iyayena so Gani nake bana bukatar Wani gida, governor yay murmushi yace munsan baka bukatar gida,Amma wannan gidan da muka baka bawai Dan Wani Abu bane, kawai sbd xamanka a kuduna ya xama comfortable,yasa muka baka,Amma Kuma saidai idan Rainawa kayi,....


AA Arab yay murmushi yace Noo ur Excellency kawai Gani nake Banda bukatar Wani muhalli bayan Wanda nake dashi ,Kuma daga Nan ma in Sha Allah gida xansauka, IG ya
Dafa kafadarsa,yace Ahmad saidai haryanxu fushi kake baka huce ba,AA Arab ya Dan waro ido yace Noo sir ni bana ruko, abinda ya wuce ya riga da ya wuce,IG yace to indai hakane ka karbi gidan da Mai girma governor ya baka,yay murmushi ya shafa kansa, ya dago ya kalli governor cikin cool voice dinsa yace thank u very hugely ur Excellency, am very appropriate with ur gifts , governor ya ruko hannunsa yace never mind Dear, Allah ya dafa Maka,adukkanin alamuranka,AA Arab ya ansa da Ameen,daga haka aka mika masa keys din gidan,bayan Sundan qara tattaunawa kan yadda xa'a bullowa Yan ta'addar nan, sannan daga bisani Kuma Suka mike Dan tafiya,....



Haka suka fita xuwa wurin motocin da already aka tadasu,bayan sun shiga nan ma Wani comboi din akayi ,da ZA'A raka su IG airport Dan tafiya xuwa Abuja,Wanda jirgin karfe biyar da Rabi xasubi , bayan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login