Showing 183001 words to 186000 words out of 278032 words

Chapter 62 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1066

ambatan sunan Allah......


Ji tai anyi knocking din da'kin tana ji Amma Bata iya dago da Bude dakin ba, har kusan minti Daya sannan taji anturo kofar anshigo ,har lokacin kanta Yana cikin filo data cusa Bata dago ba , switch din dakin aka kunna take haske ya bayyana acikin d'akin,ya hanaf ne ya shigo har tsakiyar d'akin Yana kallon ruky, ya ce "Auta" ruky ba ta dago ba, Amma tana jinsa ya qara Kiran sunan ta akaro na biyu sai alokacin da juya Dak'yar tana tashi xaune tana kallonsa da rinan nun idanuwan ta ,ya ce "me aka miki Dana shigo banganki a falor ba, na tambayi mamah ta ce nazo na sameki na tambayeki? Me aka Miki? ni nasan tunda bangan ki a falor ba nasan ba lpy ba" ya fada yana kallan ta,ruky ta fashe da Kukan ta take ta son tayuwa wani ko zata ji Dad'i,ya hanaf ya Bud'e Baki Yana kallanta Yama kasa cewa komai sbd Mamaki,Saida tai Mai isarta sannan ta tsagaita tana kallan ya hanaf ta ce "mamah ce" yace me tayi miki? Cikin Kuka ta ce "wai baxan koma wajen aikina ba wai na ajiye aikin , ya Hanaf text message fa aka min akace lallai gobe na koma Kuma ya Hanaf kasan yanayin aikinmu wlh ahakanma sun min" ta Karasa fad'a tana qara sautin Kukan ta.....


Ya hanaf ya gyara tsayuwarsa Yana kallan ta ya ce" meyasa Baki Bata hakuri ba" ruky ta ce "wlh na Bata Amma ta ce ta gama magana" ya Hanaf ya ce "kinsan mamah ta na sonki yadda bakya tunani koh?Kuma kinsan baxa tak'i abinda kike so ba dole sai tana da nata dalilin ko? Yacigaba ya ce "da kin dage kin cigaba da Bata hakurin ni Nisan zata hakura" ruky ta ce "wlh na Bata ya hanaf" ya hanaf ya sauke numfashi ya ce "Ina xuwa" Amma kafinnan ki fito falor yanxu kici Abinci,ta kalleshi ta ce "ni na koshi" ya hade Rai ya ce "idan Baki fito ba wlh baxan mata magana" ganin da GSK yake yasa ruky ta ansa masa da ka sannan ya juya ya fita daga d'akin ,bayan fitar sa ruky ta sauko daga saman gadon da k'yar ta shiga toilet ta wanko fuskarta abun ka da farar fata har tayi jaa sbd kukan da tai ta balli paracetamol Dake kan mirror ta Tasha dama da ruwan gora a d'akin,bayan Tasha ta fito ta sauko kasa ta tarar da ya hanaf kusa da mamah suna magana bayan ta qaraso ta kalli mamah ta gaisheta mamah ta ansa mata da kulawa sai Kuma ta wuce dining ta zauna tana Jin yadda ya hanaf yake ta convincing mamah akan ta barta ta koma bakin aikin ta, Amma mamah ta dage taki ,har Baba hasiya ta juyo su itama ta fito da kanta tana Taya ya hanaf bawa mamah hkr,da k'yar mamah ta ce "idanma ruky xata koma aiki to Ina da sharadi"......



Ya hanaf ya Kalli mamah ya ce "Wani Irin sharadi mamah ?,muna ji ?mamah ta ce "dole saina samu Wanda xai dinga sa mata ido sosai awajen aikin Yana kulamin da ita danni auta ta ban tsoro tunda har ta iya sa kanta cikin wannan matsalar ai baxan bari Kuma ayi na biyu ba,ya hanaf ya ce "to wa zaki sa ya dinga kula mikin da ita ?mamah ta ce tana kallan ya hanaf "Ahmad zan kira na rokeshi ya dinga sa mata ido Yana kula min da ita sosai tunda nasan duk wajen aikinsu D'aya, Kuma Yana da hankali ni nasan xai kula min da ita" ai da Wani Irin mamaki ruky take kallan mamah Jin abinda ta ce "wai adinga kula da ita kamar wata qaramar yarinya,ya hanaf ya ce "shikenan mamah Hakan ma muke da godiya" ai sai ruky ta fashe da Kuka me sauti tana kallan mamah ta ce "wlh mamah nidai karki had'ani dashi ni ban isa na kula da kaina ba sai an kula Dani " ta qasara fada tana Mai rushewa da gunjin kuka,mamah ta kalli ya hanaf da baba hasiya ta ce "to na fasa baza ta koma ba ,tunda ita Bata yarda da abinda na fada ba" Baba hasiya tai sauri ta kalli ruky ta ce "uwata kiyi hkr ki bi abinda Hajiya ta fad'a miki kinji uwata ,kema sai kinfi samun nutsuwa,ruky sai ta qara sautin Kukan ta mamah ta tace "ku tashi ku bani wuri tunda tak'i yarda da sharad'in nawa, Kuma na fasa"ai ruky ganin da GSK mamah take yasa Cikin Kuka ta ce "na amince" daga mike daga xaunan da take ta haura sama da gudu tana fashewa da Kuka......



Washe gari kamar yadda mamah ta fad'a ta sa hanaf ya kira mata AA Arab awayarsa wajen karfe 11 na safe lokacin ma har Yaje office tun tuni,bayan sun gaisa da ya hanaf yake fad'a masa mamah ce xatai magana dashi Babu musu ya ansa masa,bayan mamah ta karb'i wayar ya gaida mamah cikin girmamawa,mamah ta ansa masa da kulawa sannan ta fad'a masa abinda take so yay mata da Kuma dalilin ta na Yin Hakan,baiyi mata musu ba ya ce "in Sha Allah xai kula da ruky" mamah tai tai masa godiya Ya ce "babu komai" daga haka sukai sallama, ruky tana gefe tana turo Baki gaba ga hawaye ya gama wanke mata fuskarta Jin yadda mamah ta disgata agaban wannan mutumin ,mamah ta kalli ya hanaf ta ce "hanaf kuje ka kaita Allah ya kiyaye" Babu musu ya hanaf ya Kalli Ruky wacce keta tura Baki gaba k'iris ya rage ta saki Kuka ya ce "muje Auta " ruky kasa tafiya tai ta fashe da Kuka ta rungume mamah, mamah itama rungume ta Rai tana murmushi tareda parting bayanta ta ce "miye Hakan Auta? Ruky dai tak'i yin magana sai kuka da take rerawa, mamah ta Riketa tana rarrashinta ta ce "Yi hkr Auta Amma wlh kinban tsoro ne shiyasa nai haka Dan baxan tab'a yadda ki Kara Mai maita abinda ki kai ba,bawai Dan banyarda Dake bane, a'a kawai so nake hankali na ya kwanta, ruky ta saki mamah ta ce "mamah na tafi" mamah ta qara rungume ta tana murmushi ta ce "Allah ya kiyaye Auta ki kula ki Kuma bi umarnin Ahmad kinji ai ,duk abinda ya hanaki ki hanu , ruky dai batace komai ba,sbd takaici , mamah ta koma ciki daga haka ruky tabi bayan ya hanaf Wanda yake jiran ta a waje.....



Ruky tana shiga headquarter bayan ya hanaf ya sauke ta ya juya shima ya tafi office dinsu,direct department din su ta nufa, glass ma tasa a fuskarta Dan kada ma akawo mata raini inji ta,tun ahanya abokan aikin ta suke tai mata jajen abunda ya faru da ita tana ansa musu cikin Kulawa,tana shiga office Bata tarar da kowa ba Dan haka ta samu waje ta zauna akan kujerar ta bayan ta ajiye handbag dinta, wayar tace ya fara ringing ta ciro tana ganin me kiran Kamar baza tai picking ba sai Kuma tai picking,Hanan ce ta ce "ya sis kin shigo office din kuwa? Dan jiya Ruky ta kitara ta fad'a mata abinda mamah tace, Ruky ta ce "eh Ina nan,Hanan ta ce
"shikenan xan shigo anjima Dan akwai labari wlh wannan Ameer din fa ya takura min da k'ira babu dare babu Rana tun ranar Bai barni na huta ba wai dole saina had'a ku dashi awaya kunyi magana dashi" ruky tai tsaki ta ce "wlh idan ma shine sai kawo ki wlh Allah karma kixo Dan bazan tab'a sauraran kiba"naga tun aranar nai miki warning shine Baki jiba koh?Hanan tai murmushi ta ce "haba ruky Dan Allah ki daina Irin wannan" ruky ta ce nidai na fada miki", Hanan ta ce "to Dan Allah ya kike so nai dashi"nace miki fa kullum wlh saiya k'irani qarya kawai nake masa na gaji dayi masa qarya gsky gara kawai ki fad'a masa da bakinki ko zai kyalieni" ruky ta ce " ke kika sani ko ki kyalenshi ko Kuma kici gaba dayi masa qaryar wannan dai kika sani "Hanan ta ce "Dan Allah karki man haka" ruky ta ce"wlh sai dai Kuma kiyi" daga haka ta kashe wayar ta, tana Jan tsaki qasa qasa ,.....



Ta jawo laptop din gabanta ta hau aikin da yake kanta Kamar hauka ta fara ta dinga ta fa keyboard din kamar xata sauke haushin da takeji akansa..bayan Azhar lokacin ruky har tayi sallah tana kan dardumar ma tana duba wayarta taga message dinsa ya shigo wayarta kamar haka Wanda ko layi Daya Bai kaiba sbd ta Gane number sa "meet me in My office" kawai taga an rubuta ,Wani kululun bakin ciki ne ya to Kare mata kirji kamar kar taje haka taji , wato tun daga yanxu xa'a fara kenan,Amma da ta tuno da kalaman mamah sai kawai tai shiru kamar tai kuka Sai da Tai kusan mintuna 20 sannan ta mik'e ta fita daga office din nasu ta wuce nashi office din......




____________?&


*ZARI'A*

Bayan su ummah sun Koma gida aranar suka tadda itama lawisa ta dawo gida da 'ya
'yanta, ummah batace komai ba ita sai kawai ta shige dakinta tareda da Ameenah, Nana da taji abinda ya faru awajen ummah taji dadi sosai barinma da taji Ameenah sun rabu da Kabiru, ba qaramin Dad'i taji ba , baba asabe dai ta kanta take yanxu Dan har lokacin Batasan me ya faru da Ameenah ba sai dai abinda ya Bata mamaki shine yadda taga Ameenah ta dawo gida gashi ummah sai farin ciki take ,ita dai Bata bi takan wai dole sai tajiba Dan ita yanzu abinda yake gabanta ma ya ishe ta,Saida ta bari dare yay sannan ta shiga dakin Malam Auwalu,bayan ta xauna tana kallan sa ta ce "malam lawisa fa itama ta dawo gida jiya wannan tsinan nan mijin nata lurwanu ya sakota ,ta fad'a cikin bacin Rai.....



Shidai malam Auwalu kallan ta kawai yake Amma Bai ce komai ba,sai can Kuma ya ce "ansaki lawisa Kuma? baba asabe ta ce "eh malam" malam Auwalu ya ce "Allah ya sawake to " daga haka yaja bakinsa yay shiru, Baba asabe tai masa Wani kallo ta ce Malam ko bakaji me na fad'a Maka bane haka fa na ce Maka ansaki lawisa? Malam Auwalu ya ce "to me kike so nace asabe?Wanda ya wuce nace Allah ya sawake, baba asabe ta ce "cikin fushi Amma malam ba haka ya kamata kace ba ,aikaima uban tane me zaisa baxaka nuna alhinin kaba akai sai dai kawai kace wani Allah ya sawake" malam Auwalu ya gyara xama ya ce "asabe Dan Allah tashi ki bani waje idan har wannan maganar ce ta kawo ki karki b'atamin Rai" daga tafiya fa na dawo ,Amma babu cewa sannu xuwa babu komai, kawai kixo ki hau kawomin korafi ,da Maza Jen nasu suka sako sun ya kike so nayi ko xance dole sai sun Koma ne? Baba asabe ta ce a fusace " kaima da Kuka tashi tafiyar ku kaida matar so din taka Kun min sallama ne? To Nima Danme xance sannu da xuwa ko kun fad'amin xukuyi tafiya kawai sai wayar gari nai naga ban ganku agidan ba sai dawo warku nagani tare, da kai Sa'a ma ban ta-da muku da hankali ba" malam Auwalu ya girgixa kai kawai Amma baice komai ba Dan idan ya ce zai Yi magana asabe baza taji Dad'i ba, Dan xaiyi mata abinda Bata taba zata ba,Dan haka shirun nasa shiya Fi sauki ,Dan batama San mugun haushin ta yake ji ba tun akan yadda ta nuna masa bai Isa da zaliha ba, shiyasa shima yanxu ya kawo Ido ya xuba mata da sannu duniya zata koya mata hankali Kuma yasan yanxu ma ta fara Gani.baba asabe ta mike afusace ta fice daga dakin tana cewa duk Wanda ya zalince ta itadai Allah ya isa......



Washe gari da safe ummah ta ce da Ameenah ta shirya zasuje asibiti, Ameenah Bata kawo komai aranta taba ta ce "to" Saida suka isa asibitin sukaje har lap, taga anbata wata roba a kace tai yo fitsari aciki ta kawo a ka nuna mata toilet ta shiga Babu dad'ewa taiyo ta kawo wa nurse din ,ta karba aka dauki jinin ta shima again sannan akace su jira a waje ,Saida sukai kusan 20 minutes suna zaune suna jira sannan wata nurse ta fito ta kira ummah ta fada mata results din,cewa Ameenah bata da ciki ai sai ummah tai murmushi ta ce "Alhamdulillah ya Allah " sai Kuma ta kalli nurse din ta ce "mungode sosai likita, ita dai nurse din nan kallan ummah kawai take da taji tana murna ,ta fara tunanin meyasa take wannan farin cikin haka, Amma tai shiru Bata ce komai ba har ummah ta biya kudin gwajin sannan ta karbi results din suka tafi ,ita dai har lokacin Ameenah batace komai ba har sukaje gida......



Ruky taje office din AA Arab kamar yadda yace mata,tai Knocking, Amma ba ai magana ba Saida ta qara sannan ya Bata ixnin Shiga,Sau daya ta kalleshi ta sunkuyar da kanta k'asa,ta tsaya a tsakiyar office din ta ce "sir gani" shidai AA Arab hannunsa Yana kan laptop din gabansa Yana abinda yake Bai yi magana ba,ruky ta kusan min tuna biyar awajen tun tana marmarin tsayuwar da tai har ta gaji, kuma har lokacin Bai d'ago kansa daga abinda yake ba, ganin Bat'a mata lokacin ta kawai yake baiyi mata magana ba,kamar ta juya ta tafi haka taji ,ganin abunda ke gabansa kawai yake baima Kula taba yasa ta ce da ladabi "sir Gani" sai alokacin ya dago Yana xuba mata idanuwan sa sannan ya ce "ni zanzo na sameki? daga haka ya cigaba da Abinda yake ,Wani takaici ne ya kama ruky Jin Wani rainin hankali wurin sa , Amma saita daure ta qarasa kusa dashi ta D'an tsaya tana kallansa ta ce "Gani" yana aikinsa ya ce "mamah ta bani amanar ki wato na kula Dake nasa miki ido kan abubuwan da duk zakiyi karna bari k'i kauce hanya right",ita dai ruky tai shiru ta sunkuyar da kanta k'asa , yacigaba ya ce "ko bakiji bane? Ya fada Yana tsaida idansa akanta ,da kyar ruky ta iya motsa lips dinta kad'an tana kokarin hana kukan Daya taho mata ta ce "naji" ya ce ok u can leave" Daga haka ya Maida dubansa kan screen din laptop dinshi ya cigaba da aikinsa, ruky ta fita daga office din tana Jin duk wata kunyar duniya ta lullube ta,Danme mamah zata had'a ta dashi, aikuma shikenan ta shiga uku ya dinga Raina mata hankali kenen da k'yar ta qarasa office dinta tana danne kukan Daya taho mata.....



Ruky bayan ta koma office d'inta Kuka tai kamar ranta zai fita sbd ba'a tava disgata a rayuwa irin yau ba,ta Dad'e tana Kuka kafin ta gaji ta hak'ura,kasa tab'uka komai tai har lokacin sallah ASR yay ta tashi tayo alwala tai sallahn, tana kan sallaya wajen k'arfe biyar saiga Hanan ta shigo office din nata ruky ta daga kai tana kallon ta harta qaraso cikin office din da sallama abakinta,ruky ta Ansa mata tana d'auke idon ta daga kan Hanan tana qara tsuke fuska.hanan ta qaraso da murmushi a fuskarta ta ce "ya haka wannan had'e mun ran fa da kau da kan da kike min Dan kin ganni, kamar kinga makiyin ki ,sai kuma ta samu kan kujera ta zauna tana kallon ruky, ruky ta juyo tana kallon Hanan tana Kuma hara rar ta , Hanan tana kallan Ruky har sannan ta ce " wai Dan Allah meye kike min wannan kallon kina Kuma Hararata? Ruky ta kauda kai ta ce "ba komai Hanan ta tab'e Baki ta ce "ai shikenan" idan tai tsami xamuji" kodai har yanxu fushi kike akan Mamah ta bawa ya Ahmad ragamar kulawa Dake"ta fada tana gintse dariyarta ganin yadda Ruky ta juyo a fusace, ruky ta ce "wa ya isa nasa damuwarsa araina ai wlh Babu"Hanan tai dariya kafin ta ce "uhmm nidai bari nai abinda ya kawo ni , na kirashi na had'aku koya kyaleni daga haka ta fara kokarin d'aukon wayarta ,ruky ta qara tsuke fuska tana kallan hanan ta ce "wlh Hanan karki kuskura ki fara" Hanan ta ce "Dan Allah ruky karki mun haka ni kawai so nake yaji da bakinsa ki fada masa ko zai yarda ya kyaleni ,Nima wlh basan wannan K'iran da yake min nake ba, ni Dana fad'a masa kin yarda ai yay , Amma idan yaji da bakinki ai tafi yarda"....



Ruky ta ce "da wayace ki bashi number naki , saiki solving matsalarki ka kanki" Hanan ta xuba mata ido tana kallon ta sai Kuma ta maze kawai tai darling number Ameer tasa a handsfree yadda ruky zata ji.ruky tana ji har ta katse Bai yi picking ba,sai Kuma take ya k'ira , tana Jin yadda muryar sa ta fito ranga d'ad'au ta cikin wayar Yana tambayar Hanan Ina Rukayya"Hanan ta fara kame kame ganin yadda Ruky take Hara rar,sai Kuma ta ce "ehm Ameer na fad'a Maka wlh ta ce baxa ta tab'a karb'a ba Amma yanxu gashi nasa a handsfree ka Fadi duk abinda zaka fada tana Jinka Dan bana son kullam kake ganin kamar nice bana son na had'a ku da ita" Ameer yay gyaran murya ya fara Kiran sunan ruky Yana mata magiyar datai magana Amma kamar s
Da Dutse yake haka Ruky tai gim da bakinta , Ganin taki magana yasa ya hau jero mata da kalamai da wlh shi Son ta yake da GSK , ruky dai tak'i ce masa komai Amma tana jinsa daga qarshe ma ganin lokacin tashi yayi yasa ta tattara kayanta ta barwa Hanan office din tana Jin yadda take Kiranta Amma tai Banxa ta kyaleta.......







07066508376________
'?Follow the Mrs Sarakies=؋? =?1? HAUSA Novel Channel channel on WhatsApp:


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login