Showing 102001 words to 105000 words out of 278032 words

Chapter 35 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1091

ruky da jakar kayanta da mamanta ta kawo mata,Dan tai wanka ta canxa kaya,bayan Hanan ta fito daga wanka shaf shaf ta shirya cikin uniform dinta ganin Tara da Rabi har tayi, bayan ta sauko kasa ta tarar da mamah tana Dan Shan Lipton din dasu maman Shareef da maman Hanan suka tilasta mata Sha da baba hasiya ta kawo mata,ta durkusa har qasa ta qara gaidasu sannan tace musu xataje heardquater Dan ta sanarwa da ogansu,duk suka ansa mata da adawo lpy,da Kuma fatan dacewa,mamah ta dubeta ta kamo hannun ta da murya ta wacce ta dashe tace Hanan Allah ya miki albarka kincika Kawa ta gari ,babu abinda xan cemiki saidai nace Allah ya qara hada kanku keda kawarki idan Allah yasa tana raye ki kula da kanki kinji, Allah ya kareki,ita Kuma Rukayya Allah ya bayyana ta idan har tana raye, ta qarasa fada tana xubar da hawaye,duk suka ansa da Ameen, sannan suka hau bawa mamah Baki, idon Hanan ya ciko da hawaye,mamah ta share nata hawayen tana jijjiga kai,da kyar Hanan ta Mike sbd yadda magan ganun mamah suka qara tsinkar mata da jiki tai hanyar kofar falon tana share hawayen dayaki tsaya mata,.....




___________?&


Kwance take cikin Wani daki Mai bala'in duhu,Wanda ko tafin hannunka baka isa gani ba,sbd duhun dakin, ahankali ta shiga motsawa sai dai Jin jikinta kamar andaure ta da sarka yasata Dan Bude idanta kadan, saidai babu shiri ta mayarsu ta rufe ,sbd yadda sukai mata nauyi,jitaima Gabadaya jikinta yayi mata mugun nauyi ya xamto ko Hannanta ta kasa dagawa bare Kuma tai kwakkwaran motsi,jin dai ta tabbata adauran take yasata qara rintse idanta Tareda, matsawa kanta da tunanin nan Ina ne meya faru da ita da har xataxo nan ,meya kawota nan,.....



Tunowa da abinda ya faru da itane na xataje government house dauko Hanan da anan abin ya faru da ita yasata, sakin salati, tana ambatan sunan Allah,adai dai lokacin da taji motsin Bude kofar ,take kuka aka Bude kofar dakin aka cillo mata Wani Abu da Batasan ko menene ba,daukar ta xataga anshigo cikin dakin anxo gareta Amma saitaga kokarin barin dakin Wanda ya shigo din kawai yake,tai karfin halin cewa da muryarta wacce Bata fita sosai da Dan Allah kaxo ka kwance ni Nanan din inane waya kawo ni nan,cak mutumin ya tsaya Amma Bai juyo ba,ta qara Mai Mai ta masa tambayar ganin baiyi magana ba yasata cewa,Dan Allah kaxo ka kunceni yay Banxa da ita ya kyaleta saima ficewa da yay daga dakin ya rufo kofar ,take ruky ta fashe da Kuka ta tabbata itama kenan sacetan akai kenan, kamar yadda aka sace Khalil, innalillahi wainna ilaihi rajiun kawai take ambata babu Wanda ya fado mata arai Irin mamah da Yan uwanta ko ya zasuji idan suka wayi gari suka nemeta suka rasa oho,take ta qara sautin Kukan ta,tana ambatan sunan Allah,. tana kokarin kwance jikinta Amma saidai ta gagara Hakan,......



Hanan tana xuwa heardquater, direct office din AA Arab ta nufa,bayan ta isa ta nemi ixnin ganin AA Arab babu Wanda ya hanata,tai knocking kofar office din nasa Yana ciki Yana waya ya,Jin ana knicking kofar office din nasa yasa ya bada ixnin Shiga, bayan Hanan shiga ya aje wayar hannunsa ganin Hanan ce,Hanan tai saluting nasa tareda rusinawa ta gaida shi,AA Arab ya ansa mata da kulawa,tace sir wurinka naxo,ya nuna mata wurin xama, bayan ta xauna ta sanar masa Neman ruky da akai aka rasa ajiya bayan ta tashi daga aiki, take tunanin alokacin incidence din ya faru,xataje government house wajenta,AA Arab ya fesar da numfashi yace naji labarin tun jiya Kuma mun tura jami'an tsaro lungu da Sako ashiga patrol,yanxu haka Nima daga binciken inda xamu ganta na dawo kafin na shigo office, Saidai a inda naga motarta tama nayi mamaki,sbd ta wannan hanyar tabi wacce mutane Basu fiya yawaita ba, Kuma anan aka samu nasarar dauketa din,Dan namasa an kawo motar tata nan yanxu haka tana nan headquarter,a bangaren bincike,ya nuna mata handbag din ruky da wayarta Dake kan table din gabansa yace,Basu dauki komai ba tunda komai nata Yana a cikin motarta ita kawai suka dauka, ai Saidama naga motar Tatama sannan na ganeta,.Dan tabbas naga fitarta Nima alokacin da xata fita,yace Abu dayane yake damuna shine bamusan su waye suka dauketa ba tunda har yanxu wata alama wanda zai nuna sheda ko Kuma suspect,idan masu garguwa da mutane ne yaci ace sun kira,to matsalan dai shine har yanxu bamu da guarantee,din ainihin su waye suka dauketa,Hanan ta sauke numfashi hawaye na sauka daga saman fuskar ta tace mungode sir Allah ya Saka da Alkhairi,AA Arab yay qasa da murya yace stop crying Hanan in Sha Allah xa'a sameta ko itace kawar taki.,Hanan tana goge fuskar ta jinjina masa kai AA Arab yace in Sha Allah xa'a ganta, Hanan tai tai murmushi ta danyi tunanin seconni, acikin tunanin ta hango ta mike tai Mai sallama ta nufi kofar fita daga office din jitake kamar ta dawo ta fada masa cewa tana zargin Alhaji sunusi, Amma kawai saita fasa daga nan xuwa gobe idan Ba'a sametaba, xata fada masa kawai ko Allah zaisa adace daga haka taja masa kofar, firgigit ta dawo daga tunanin da take, Jin Yana magana ta xuba masa ido



jiya naga fitarta Kuma awannan lokacin aka sanar min dacewa alokacin abun ya faru ,ki kwantar da hankalinki Hanan in Sha Allah muna Nan muna bincike karki damu, kudai kucigava da addu'a, Hanan tace thank u sir, Allah ya Saka da Alkhairi,kirane ya shigo wayarta ta dubu wayarta ganin daga government house ake kira tace sir bari naje office,AA Arab ya jinjina kai yace ok Allah ya bayyana ta, kudunga kula Hanan tai murmushin karfin hali tace in Sha Allah,kamar ta sanarwa da AA Arab cewa tana zargin Alhaji sunusi,say Kuma tace bari kawai idan Ba'a ji labarin ta daga nan xuwa gobe ba,zata fada masa in yaso sai ayi bincike,. bayan fitar Hanan daga office din AA Arab ya jawo wayar Ruky,Dan ya duba ganin akashe take ba charging yasa ya ajiyeta,ya dauki wayarsa Dake ringing ya kai kunne.,bayan yaji abinda aka fada daga can yace ok , inaso kusa ido sosai akowani angel.nima Ina nan xuwa daga haka ya aje wayar...







07066508376________
'?Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD?mode=ac_t







*____JAMI'AR TSARO ____*



*____THE WOMEN POLICE ____*



*NA*



*____NAJA'ATU UMAR FAROOQ ____*



*____(MRS SARAKIES)____*




*=?1?QUEEN OF WRITERS ASSOCIATION(QOWA) =?1?*




*Bismillahirrahmanirrahim*



_______season one ep 4?? 4??



__________?&


Kafin kice me awunin wannan ranar tuni lvr ya Baxu a gari cewar ansace JAMI'AR TSARO ,ga Kuma Dan jarida dashima ba'a gama alhinin Saba,su anty mufeeda da ya Tahir Suma a TV suka ji, ai kafin kice me hankalinsu ya tashi suka fara buge bugen kira Dan qara tabbatar wa,suka kira mamah awaya saidai Bata samu damar daga Kiran nasu ba sai ya hanaf suka samu tuni ya tabbatar musu da haka ,Dan haka sukace idan sun samu jirgin dazai tashi yau xasu biyo su taho,ya Tahir ne ya samu jirgin da zai tashi karfe 11 na dare daga Lagos xuwa kaduna,....



Anty mufeeda kuwa Bata samu jirgin da xai taso daga Abuja xuwa kaduna aranar ba dole saidai ta bari xuwa Washe gari,alokacin data samu lvrin batan da ruky tai taci kuka harta godewa Allah,Dan abin yaxo mata abaxata,Dan Dakyar ta samu mamah tai picking call dinta Dan ita mamah Batasan abinda xai ta-da musu da hankali kwata kwata,haka sukaci kukunsu suka godewa Allah, daga karshe ma sai mamance ta koma bawa anty mufeeda bakin tai Shiru,aranar kuwa babu kalan binciken da ba'a yiba Amma sama ko qasa annemi Rukayya ko sanin labarin inda take anrasa , tun mamah suna xuba ido hardai suka sare,daga qarshe mamah tace kodai masu garguwa da mutane ne suka dauke Ruky,....



Nan ma suka xuba idan suga sun kirasu suji idan sun kira ko xasu bukaci Wani abun Amma shiru kakeji, bangaren su AA Arab suna iya bakin kokarinsu, Amma babu Wani bayani, tunda Hanan ta fita sai dare ta dawo Dan itama ta shiga cikin ayarin binciken Amma shiru kakeji,haka ta dawo jiki duk amace, ataikaice dai a wannan Rana ma dai Basu rintsaba, har ya Tahir shima Yaxo acikin wannan dare dashi shima aka hadu aka shiga halin alhini, Washe gari da sassafe maman Hanan ta dawo gidan ,maman Shareef ita agidan ta kwana,wajen karfe 7:30am saiga anty mufeeda itama ta sauka agidan, wujiga wujiga da ita cikin tashin hankali , idan ta ya kumbura yay suntum sbd kukun data ci,....



Ga yayanta su biyu mimie da moha, mijinta baya kasar shiyasa Bai biyo suba, Amma ya kira mamah ya tayasu jaje yace Kuma in Sha Allah xai dawo qasar nan Bada dadewa ba, tana xuwa batai wata wataba ta rungume mamah, tareda sakin Wani marayan kuka,itama mamah rungumeta tai xuciyar mamah saita qara karyewa Jin yadda mufeeda take kuka kaman ranta xai fita, yanxu mufeeda ce kadai ta rage mata indai ba'a samu Rukayya ba,maman Hanan ta dinga rarrashinta, ganin taki yin shiru yasa maman Shareef Dan dakawa mufeeda tsawa akan tabar kukan haka ,so take Wani ciwon ya kama mamah itada ya kamata ta dinga rarrashinta,.....



Haka mufeeda ta saki mamah tareda jan gefe ta xauna tana share hawayenta, da tissue,'ya'yanta Suma suka xagayeta suna tayata, ganin haka yasa Hanan tai kiransu , mimie ce taje Amma shi moha ya makale ajikin momynsa, kafin gari ya gama wayewa gidansu su ruky ya cika da Yan jaje kamar Wani biki, wasu na xuwa wasu na fita,aciki kuwa harda shareef shima gava daya acikin tashin hankali yake,da Jin wannan lbr,Yan uwansu both father and mother duka sunxo domin lvr ya riskesu,dayake wasu ba'a nan cikin garin Kaduna suke ba ,tuni ya hanaf ya kai musu babban carpet compound an shimfida musu,ansa tempol wlh duk Wani masoyan bayin Allah nan dole ya tausaya musu idan yaga ahalin da suke ciki,su kansu masu aikin gidan gabadaya kamar Wanda aka musu mutuwa haka sukaji,Dan tabbas ahalin gidan AIG umar MaiTama,mutanan kirkine da baxa su taba manta alkhairinsu garesuva,,itama Kuma Rukayya babu ruwanta Batada Raina mutane, tana Basu girmansu, tunda wannan tarbiyar da mamah ta daura su akai kenan,....


Wajan karfe 11 :00am Hanan ta fito daga dakin Dake qasa ta fito cikin shirin fita aiki,idanta ya kumbura yay suntum sbd kukun data ci,bayan ta shigo tsakiyar falon adai lokacin da Kuma Alhaji sunusi ke shigowa cikin falon shida Jama'arsa,acikinsu kuwa harda babajo Ali,tsantsar Damuwa ce qara afuskar Alhaji sunusi, Daya Ara ya yafa Wanda kina Gani saiki rantse da GSK ne,har a cikin xuciyarsa,haka jama'ar wurin suka ansa masa sallamar da shida mutanan da, tareda Basu wurin xama,suka qarasa shigowa falon adai inda mamah take xaune kan sallaya cikin dogon hijabi da carvi a hannunta, kanta a qasa ta dago jin muryar Alhaji sunusi Yana gaisheta, mamah ta ansa cikin dauriya, Alhaji sunusi cikin damuwa yace wlh hajiya Halima bansani ba,sai daxu da safe nake Jin lvr Ashe abinda ya faru kenan , Allah ubangiji ya bayyana ta, Allah yasa tana Hannun nagari,Nima in Sha Allah xanyi iya bakin kokarina ata bangarena wajen bincike da Gano inda take,....



Mamah dai kawai jinjina masa kai take,yace Kuma an Bada cigiyar ta gidan TV,maman Shareef tace ai tunjiya aka Bada cigiyar ta, Alhaji sunusi Yana jinjina kai yace in Sha Allah xa'a ganta,xanyi iya bakin kokarina Nima ta wajena, Hajiya Halima ki kwantar da hankalinki Dan Allah karki sawa kanki damuwa ya haifar miki da wani ciwo tabbas da xafi bayan da Amma dole sai an hada da hkr,yasa hannu a aljihu ya Ciro kudi Dami guda ya ajiye agaban mamah,yace ga wannan a rage Wani Abun, Allah ubangiji ya bayyana ta , Allah yayi gaggawar tona asirin Wanda sukai wannan aikin kowa ya ansa da Ameen,yace anjima Hajiya SA'A xata xo ita da lateef,daga haka ya mike yay musu sallama sannan suka fita daga falon,....



Itadai mamah tayi mamakin wai yau Alhaji sunusi ne ya Basu kudi, tunda take bayan rasuwar babansu ruky xata iya kirga saunawa Alhaji sunusi ya tava Basu kudi,Hakan data tuno da mijinta yasa ta share hawayen ta,baba hasiya ta kammala break fast ta kawo wa mamah nata maman Shareef ta karba xata Bata dukda Baci takeba har sai sun tilasta mata tukunna aka shiga fito da break fast ana bawa Baki na ciki Dana waje,Hanan kan tunda Alhaji sunusi ya shigo falon data gaidashi taga yadan kafeta da ido,tadan tsorata,Dan saitaga kamar murmushi ma yay mata, tunda ya fara yiwa mamah jaje take hankalce dashi,kwata kwata ta kasa gaskata maganar ta na cewar Alhaji sunusi Yana da sa hannu awajen batan Rukayya, ganin yadda ya nuna damuwa da addu'ar Allah ya tona asirin Wanda sukai wannan aikin yasata kokontar maganar ta,kodai Alhaji sunusi baida hannu akan sace Rukayya da akai, dan gani take inda iyada hannu abatan Rukayya bazaiyi addu'ar Allah yay gaggawar tona asirin Wanda suka dauke taba,....



Ganin yana shirin fita daga falon yasata yin saurin itama ta fita Dan ta tari abin hawa Dan tana San anjima Idan ta tashi daga wajen aiki ta biya heardquater wurin AA Arab taji ya ake ciki, Alhaji sunusi Yana shirin fita daga falon hanaf Yana shigowa shida ya tahir kallan kallo suka tsayayi, har kusan seconds 30,ya Tahir ne ya xungureshi,ganin yaki gaida Uncle sunusi, Alhaji sunusi ya Maida kallansa kan ya Tahir Yana ansa wa Tahir da kulawa, ganun haka yasa hanaf gaidashi ciki ciki, kamar Wanda akayi dole fuskar sa acunkushe ,Alhaji sunusi ya ansa masa da dan murmushi,dayi musu jaje , sannan Alhaji sunusi ya fita daga falon, suma suka shigo Dan wajen mamah sukaxo,......




___________?&


Yau kwana Daya kenan da kawo Rukayya wajen nan, gabadaya baxatace ga Wanda ta Gani ba ido da ido ko taga fuskar Saba sbd kullum arufe take da kyalle,yo ko dakin ma baxata iya kiyasta ya yake ba,bare Kuma wurin da take xaune ,jiyan sai da daddare akaxo aka kwance ta daga daurin da aka mata, dakin har yanxu babu Wani haske, Yadda ta fuskanta kamar kullum dakin ahaka yake cikin duhu,Wani Irin bread kawai ake kawo mata, shine abincinta,sai ruwa pure water guda biyar dashi ta Dan samu ta rama sallolun da Suke kanta, tayi kukun tayi ihun tayi salatun har ta godewa Allah, ganin dai babu Mai xuwa gunta bamu Kuma Mai sauraronta,bare akawo mata dauki yasa ta Maida hankali ga addu'ar da take babu Wanda take tausayi da tunani Irin mamah da Yan uwanta da duk Wanda xai damu da halin da take ciki,sai Khalil da shima Yana ranta, kardai Wanda suka dauke Khalil sune itama suka satota,idan ko hakane Bata rasa dayan biyun kila duk mutum dayane, Kuma Babu Wanda take tunani Irin Alhaji sunusi, Amma xata xubo ido taga waye yasa a kawota nan,koma waye ai xaixo ....



A Yanxu tana wannan tunanin taji motsin Bude kofar dakin ,da akayi tana zaune atakure waje Daya,bayan ya ya shigo as usual fuskarsa arufe take duk duhun dakin taga haka,aje mata bread din hannunsa yay nesa da ita,sai Kuma ya juya ya nufi kofar zai fita Batareda ya mata magana ba,tai karfin halin cewa Dan Allah waya kawo ni nan,cikin rawar murya ,yay Banxa ya kyaleta ta Kara Mai Mai ta masa tambayar, nan ma dai Bai kulataba, harya Bude kofar dakin ya fita ya rufo kofar,haka ta kifa kanta cikin kafun ta ta fara rere kuka,.Mai cin Rai..




?&Abangaren Khalil kuwa tunda aka kawo shi wanna kurkukun wajen Bai farka ba bare yasan halin dayake ciki,Dan wata Irin allura aka masa Mai gusar da hankali harna tsawan kwana biyu, Saiyanxu yake farkawa da kansa Wanda yay Masa masifar nauyi, kokarin tashi xaune yake Amma ya kasa,haka ya dinga kokarin tashi xaune Amma Abu ya gagara,domin gabadaya jikinsa ya mutu,Jin motsin Bude kofar dakin dayake ciki,yasa yadan Bude idansa,kadan aka dalleshi da futula take ya rintse idonsa, sai Kuma aka juya aka fita daga dakin tareda jawo kofar aka rufe, batareda ance masa komai ba.....



Khalil ya qara Bude idansa kadan ganin a inda yake take abinda ya faru dashi ya shiga dawo masa bit by bit,ai tuni ya dafe kansa Jin yadda akai yaxo gunnan,
,da kyar ya tashi ya xauna yana bun jikinsa da kallo , take hawaye ya fara xubo masa,.Jin abinda ya faru dashi, shidai yasan ya baro wajen aiki ya tari napep Wanda xai Kaishi unguwar su,tunda ya hau wannan napep din da wasu mutane biyu ke ciki, kawai yaji Bai yadda da mutanan ba ganin yadda suke kamar Yan maye, Amma ya basar, suna cikin tafiya yaga sun dau wata hanya, zaiyi magana kawai yaga sun jawo shi sun rufe masa Baki sannan suka caka masa Wani karfe a cinyar sa,Wanda yake tunanin allurace,take awajen jikinsa ya saki yaji ya kasa Koda daga Dan yatsansa ne,to daga nan Bai qara sanin inda kansa yake ba sai Yanxu daya farka,take ya rintse idansa ya fara ambatan sunan Allah...




A bangaren AA Arab kuwa,bayan Hanan taxo office dinsa daxu,da yamma,ya tabbatar mata da cewa in Sha Allah,bayan magrib idan ya tashi daga aiki,,kafin ya wuce gida xai xo gidansu Rukayya yay musu jaje,Hanan taji dadi sosai dan babu musu tace Allah ya kawo shi,anan sukai exchanging numbers,sbd ta tura masa address din ya bawa driver sa Kuma idan yaxo gidan ya kirata,haka ko akayi bayan magrib Hanan tana zaune afalo kusa da anty mufeeda,ga mimie akan cinyar ta tana Bata abinci,sanye take da hijab dogo har qasa,Kiran AA Arab na shigowa wayarta ganin shine yasa, tai picking bayan tai sallama ya shaida mata cewa suna kofar gidan tace gatanan xuwa,.....



Bayan Hanan ta sauke wayar ta dubi anty mufeeda ta fadawa anty mufeeda cewar ogansu na gun aiki yaxo xaiyiwa mamah jaje,anty mufeeda tace badawa ta shigo dashi bari ta fadawa mamah,haka Hanan ta sauke mimie dakan cibiyarta , tasaka bowel din abin cin agaban ta,ta mike tai hanyar fita daga falon Dan xuwa ta shigo da AA Arab babu dadewa suka shigo da AA Arab Wanda ke biye da ita abayanta,bayan ya shigo falon kansa akasa,da sallama abakinsa cikin nutsuwa duk mutanan falon suka ansa masa, kowa ya Gane shine ogan su ruky tunda anty


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login